gani a kayi tafashe da kuka abun yayi matuƙar ɗaurema brisster kai hajiya Asma'u kuwa jikinta sanyi yayi zuciyarta ta karaya, ta san da wahala ta ƙubuta, Aisha ka ɗaice shedar da take ganin zata iya taimakawa wajen faɗar gaskiya.
wicked side smile brisster hashim ya saki, yana kallon macen dake kusa da shi su ka kashe ma juna ido, da yawan brisster's ɗin dake wurin sun jin daɗin yanda abun ke tafiya ƙalilan ne abun ya taɓa zuciyar su.
sai da ta gama kukan mai isarta tukun Alƙali yace“koto na saurarenki”
“wallahi ni ban san komai ba, hasalima bana garin abun ya far.....”
da sauri brisster zulaihat ta tari numfashin matar tana faɗin
“my lord!, shaidata ta shiga halin ruɗani, tana tsoron magana a gaban court sabo....”
da sauri matar tace “babu ruɗanin da na shiga, kuma ba wai ina jin tsoro ba ne , gaskiya ce nake faɗa, bana nan abun ya faru” matar ta faɗa with full confidence,mamaki kamar ya kashe mom, saboda Aisha tana Abuja komai ya faru amma a gaban koto tace bata nan, brisster hashim har ƙara gyara zama yake abun yana tafiya yanda yake so.
“laifi ne katse shaida yayin bada amsar da Alƙali ya tambaye shi, brisster ki kiye”
“tuba nake” ta faɗa
“ina ki ka je a lokacin da abun ya faru?” Alƙali ya jefa mata tambaya
“naje garin mu domin duba jikin ɗana da ke fama da ciwan daji ( cancer ), kuma hajiya Asma'u da kanta ta bani izinin tafiya ita da mijinta”
“ A ranar yaushe ki kayi tafiyar?”
“na tafi garin mu ranar laraba a washe garin ranar Alhamis nake samun labarin abun da ya faru”
“mi yasa baki dawo ba da ki ka samun labarin abun da ya faru da ubangidan na ki?”
“saboda lalurar ɗana, jikinshi ne yayi tsanani shiyyasa ban samu damar zuwa ba”
ƴan rubuce rubuce Alƙali yayi kafin yace “zaki iya komawa ki zauna, kotu za tayi bincike akan bayanan da ki ka bata, lawyer masu ƙara ko kana da tambayoyin da za kayi ma malam Aisha” miƙewa brisster hashim yayi yana gyara zaman coat ɗin shi, cikin takun ƙasaita ya nufi tsakiyar koton, cikin maganar ƙasaita yake faɗin “my lord, ina so zanyi ma shaida wasu ƴan tambayoyi”
izini Alƙali ya bashi
“godiya nake” ya faɗa yana matsawa in da Aisha take tsaye
“malam Aisha ina so zanyi maki wasu ƴan tambayoyi,ya zamantakewar iyayen gidan naki take, shin kafin mutuwar cp ko a kwai wani saɓani da ya taɓa shiga tsakaninshi da uwar ɗakin ki, ko akwai rashin jituwa tsakaninsu, wasu dai Abubuwa maka mantan haka???”
“babu yallaɓai,a kwai fahimta a tsakaninsu, marigayi yana matuƙar kyautata ma matar shi hatta mu ƴan aiki ya ɗauke mu da matuƙar daraja”
jinjina kai brisster hashim yayi yana faɗin “ita fa uwar ɗakin taki, ya nata halayen su ke, bata da wasu ɗabiu marasa kyau wanda baku jin daɗin su???”
ran brisster zulaihat ne ya fara ɓaci da irin tambayoyin da brisster hashim kema Aisha
“gaskiya babu”
“koda a ɓoye bata da su?” ya sake mata tambayar, miƙewa brisster zulaihat tayi rai a ɓace “objection my lord”
“sustained”Alƙali ya faɗa yana bata izini
“lawyer masu ƙara kamar yana son tursasa witness ɗina akan dole sai ta faɗi abun da bashi ba”
“brisster hashim ka kiyaye” jinjina kai brisster hashim yayi
“malam Aisha a ra'ayin ki ne ki ka tafi gida ko kuwa uwar ɗakin kice ta nuna dacewar tafiyar ki a wannan lokacin?”
“Itace tace ya kamata na tafi na duba jikin shi , da tace man haka sai nace mata zan shirya ranar juma'a ko asabar naje amma sai tace na shirya gobe na tafi da farko naƙi amincewa da tafiyar a washe garin nace kawai zan tura masu kuɗin su fara amfani dashi kafin zuwa ranar juma'ar na tafi, amma sai ta zaunar dani ta nuna man dacewar na tafi a goben shine na amince”
“da tace ki tafi a lokacin ba kiyi wani tunani ba ko akwai dalilin da yasa tace kije?”
komawa tayi ta zauna tana cizon yatsa na rashin bata dama da Alƙali yayi, side smile brisster hashim ya saki
amsar tambayar da brisster hashim yayi mata ta bashi
“banyi tunanin komai ba, saboda idan ahalina suna cikin matsala ta kan fini shiga damuwa akan halin da nake ciki,shiyyasa banyi zargin komai ba”
jinjina kai brisster yayi “mudi mai gadi ya sanar da koto cewa akwai wani matashin saurayi dake yawan zuwa wurin uwar ɗakin na ki, baki taɓa tunanin mike kawoshi wajenta ba , ko miye alaƙarta da shi ???"
“sunan sa Abid, ɗan ƙanwarta ne dake zaune a ƙasar waje, yana yawan zuwa wurinta duk lokacin da yazo suna samu saɓani da marigayi saboda kwata kwata jinin marigayi bai haɗu dana Abid ba, saboda Abid yaro ne mara tarbiya baya girmama na gaba da shi , gashi duk lokacin da yazo sai ya takura ma yarinyar su , hakan yasa marigayi baya son yana zuwa gidan, ita hajiya sai ta nuna ba taji daɗi ba kan nuna kyara da tsangwama da yake akan yaron, a ranar da mu kayi magana kan tafiyata ya zo gidan har saɓani ya shiga tsakanin shi da marigayi ya dake shi, abun yayi matuƙar ɓata ran hajiya har su ka samu saɓani da marigayi, bayan mungama magana da ita naje ɗakina na wanke kayan da zan tafi da su na zagaya baya zanyi shanya na hangesu ita da Abid suna tattauna wasu maganganu wanda ban san mi su ke tattaunawa ba, nayi ƙoƙarin naji abun da su ke faɗa amma abun ya gagara saboda tazara dake tsakanin mu,bayan na koma ɗakina cikin dare naji Abid ɗin yana waya a bayan ɗakina kamar yana faɗama wanda suke waya saɓanin da su ka samu da marigayi bana jin mi na ciki wayar ke faɗa masa na dai ji yana faɗin a cikin satinnan ya kamata suyi aiki a kanshi ko zai daina mashi shiga hanci da ƙudindine, na tsorata da jin abun daya faɗa har na kasa bacci , washe gari tunda safe na samu hajiya da maganar amma sai ta nuna kar na damu da abokan kasuwancin shi yake waya”
tunda Aisha ta fara jera wannan jawabin gaban hajiya Asma'u ke faɗuwa bata taɓa sanin komai dake faruwa a gidan Aisha na sane ba sai yanzu.
“abokan ka suwanci, ko kin san wane irin ka suwanci yake?, sannan wane saɓani ya shiga tsakanin shi da marigayi?”
“gaskiya ban san kasuwanci da yake ba, amma na taɓa jin labari a wurin mai gadi cewa yaron yana harkar kayan maye , kuma dukiyar da yake juyawa ta hajiya Asma'un ce ”
jinjina kai brisster yayi
“wane saɓani ne ya shiga tsakanin shi da marigayi?” ya sake maimaita mata tambayar
“gaskiya ban sani ba”
juyawa brisster hashim yayi ya kalli Alƙali “my lord , tun ranar da mai gadin gidan ya ba police duk wasu bayanai akan yaro suka tsaurara bincike sai dai kash bayan kwana biyu da fara binciken na su aka samu gawar shi yaron a cikin gidan shi anyi mashi kisa makamancin na marigayi,hakan na nufin hajiya Asma'u ta tura Aisha gida ne dan ta samu damar aiwatar da shirinta ba tare da wani ya ganota ba,sannan ta sallami ma'aikatan gidan dan kar su ga abunda zai faru,Abid ya ƙi bata haɗin kai ne shiyyasa ta tura makasan da su ka kashe cp su ka kashe shi dan kar ya zame mata matsala”
“Objection my lord”
jinjina mata kai Alƙali yayi alamar amincewa
“my lord lawyer masu ƙara na son tabbatar da laifi akan wacce nake karewa ba tare da ƙwararan hujjoji ba”
“brisster hashim ka kiyaye”
“tuba nake”
jinjina kai Alƙali yayi kafin ya ɗauki pen ɗin shi yayi ƴan rubuce rubuce
“lawyer masu ƙara ko kana da sauran wasu tambayoyi da za kayi ma malam Aisha”
“su kenan tambayoyin da nake son yi mata” brisster hashim ya faɗa, tsaki brisster taja a zuciyarta tana faɗin
“ko ina amfanin wannan tambayoyin”
“lauyan wanda ake ƙara ko kina da wasu tambayoyi da za kiyi ma malam Aisha?”
miƙewa brisster tayi “eh my lord” dama Alƙali ya bata, fitowa tayi brisster hashim kuma ya koma mazauninshi.
“malam Aisha a bayanan da hajiya Asma'u ta bada da kuma binciken da muka gudanar ya tabbatar mana da cewa kina a gidan a ranar da abun ya faru , hasalima kece ki ka fara sanar da su zuwa mugayen mutanen da su ka shigo gidan”
“wallahi brisster bana garin ita da kanta tace naje, munyi maganar da ita yau washe gari tunda safe na tafi”
murmushi gefen fuska brisster ta saki tana faɗin “ƴan uwan naki su su ka bada shedar cewa a ranar ba kije garin naku ba sai a washe garin ranar da abun ya faru”
shiru Aisha tayi ba tare da tace komai ba
“malama Aisha ke koto ke saurare?”
“ranar na tafi sai dai ban samu isa garin ba sai cikin dare,hakan yasa basu san da zuwa na ba sai washe gari”jinjina kai brisster tayi tana juyawa ta kalli Alƙali
“my lord malama Aisha ta sanar da koto cewa bata nan abun ya faru, a binciken dana gudanar ya tabbatar man da tana a cikin komai ya faru”
“binciken koto zai tabbatar da hakan, kina da sauran wasu tambayoyi da za kiyi mata”
“babu sauran wasu tambayoyi da zanyi mata”
“malam Aisha zaki iya komawa mazauninki kafin binciken koto ya kammala”
“godiya nake” ta faɗa tana ɗan rissinar da kai,barin witness stand ɗin tayi ta koma mazauninta ba tare da ta bari sun haɗa ido da brisster ba ko hajiya Asma'u.
brisster wurin zamanta ta koma itama,haka shari'ar ta cigaba da tafiya duk wasu jadawalin sunayen witness ( sheda) sai da Alƙali ya kira su gaban koto yana masu tambayoyi bayan ya kammala masu ya ba brisster's dama suma suyi masu nasu tambayoyi, ko wane sheda da kalar amsar da yake ba dawa a kan kisan marigayi CP,hajiya Asma'u tun tana sa ran kuɓuta har ta sadaƙata tasan bazata taɓa kuɓuta ba daga yanayin amsoshin da shedun ke ba court,brisster ma gwiwowinta sun sage bata taɓa shari'a irin wannan ba tana shari'a akan kisa amma kuma bata taɓa rashin nasara ba amma wannan shari'ar na neman tafi ƙarfinta , shedun da take taƙama dasu gaba ɗaya sun juya mata baya,duk wanda aka kira a cikin su abu ɗaya su ke faɗi hajiya Asma'u ta kashe mijinta kuma suna bada ƙwararan hujjoji wanda dole koto ta yarda .
brisster hashim kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha yasan zaiyi wuya yau bai yi nasara akan brisster zulaihat ba abun da ya daɗe yana jira kenan tsawan shekaru.
Magana Alƙali ya fara, tsit kotun tayi kowa na sauraron hukuncin da court zata yanke “binciken kotu ya tabbar da malam Aisha bata nan a ranar ashirin da ɗaya ga watan biyar”
Ajiyar zuciya Aisha ta sauke tana dafe saitin zuciyarta, brisster wani mugun faɗuwa gabanta yayi hajiya Asma'u kuwa tuni hawaye sun taru a cikin idanunta
“bayan kammala haɗa duk wasu hujjoji da binciken koto dana likitocin dake kula da gawar marigayi CP ya tabbatar da hajiya Asma'u itce ta kashe CP” tunda Alƙali ya fara magana brisster hashim ke sakin murmushi, brisster zulaihat kuwa banda faɗuwa babu abun da gabanta ke yi.
“kotu ta yanke ma hajiya Asma'u hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da biyan tara ta naira milayan hamsin”
Wani irin murmushin farin ciki barisster Hashim ya saki yana kallon ƴan uwan shi wanda hukuncin yayi masu dai dai,a ɗayan ɓangaren kuwa barisster Zulaihart wani irin tashin hankali mara misaltuwa ta tsinci kanta, da dama mutanen dake Court ɗin abun yayi masu daɗi yayin da wasu ke tausaya ma Hajiya Asma'un.
ana cikin jimamin hukuncin da court ɗin ta yanke sai ga saƙo daga fadar shugaban ƙasa na nemama Hajiya Asma'u sassaucin kotu daga rataya zuwa ɗaurin rai da rai tare da biyan tara ta nera miliyan ɗari saɓanin hamshin.
Ran barisster hashim idan yayi dubu ya ɓaci ba haka yaso ba yaso hukuncin kisa aka yanke mata ta hanyar rataya bai so ɗaurin rai da rai ba amma idan ya tuna ba wai zata fito bane sai hankalishi ya kwanta, mom ta ɗan ji sassauci da ba kisa bane ɗaurin rai da rai ne sai dai idan ta tuna halin da hajiya Asma'u da nainarh za su shiga hankalinta na tashi.
wasu daga cikin mutane kwata kwata ba su so haka ba gani suke kamar wata maƙarƙashiya ce ake ƙullawa.
Miƙewa Alƙali yayi gaba ɗaya su ka miƙe,ƙofar office ɗin shi ya nufa kamar jira a ke Alƙali ya fita koto ta ɗauki haya niya kowa da abunda ke fitowa daga bakin shi,can compound ɗin curt ɗin kamar zai fashe saboda haya niyar mutane, mom tunda Alƙali ya fita ta kifa kanta saman desk ko motsin kirki ta kasa yi,matsowa wannan security guard ɗin tayi tana bata haƙuri, miƙewa brisster hashim yayi yana wani gyara zaman rigar shi fuskarshi ɗauke da murmushin mugunta, ɗaya bayan ɗaya mutane su ka fara fita daga cikin kotun suna tofa albarkacin su.
hanyar fita prison officers suka nufa da hajiya Asma'u, da ƙyar take taka ƙafafuwanta suna zuwa tsakiyar court ɗin ta yanke jiki ta faɗi a sume, salati mutanen da su ka rage a ciki su ka rabka da sauri mom ta miƙe kusan a tare su ka isa inda hajiya Asma'u ke yashe a ƙasa ita da wasu mata guda biyu, amma kafin su ƙaraso ma'aikatan gidan yarin sunyi mata rumfa mom ka ɗai su ka bari ta ƙarasa in da take, jijjigata ta shiga yi tana kiran sunanta amma ko gezau ba tayi ba, ɗaya daga cikin prison officers ne ya miƙoma mom ruwa,a hannu ta zuba ruwan ta shafa mata a fuska, tayi hakan kusan sau ba adadi amma bata farfaɗo ba mom bata san lokacin da ta fashe da wani matsanancin kuka ba,doctors ɗin gidan yari ɗaya daga cikin jami'an gidan yarin ya kira, ba'ayi five minutes ba sai gasu sun ƙaraso, nurses huɗu mata ne su ka kamata su ka ɗaura saman stretcher,ficewa su kayi da ita daga cikin court ɗin bayan su mom tabi tana goge hawayen dake zarya saman kumatunta, a hanzarce security guard ɗinta tabi bayan ta har zuwa in da su kayi parking Ambulance,ganin fitowar mom ne yasa sauran security guard ɗin nufota da sauri saboda mutane da ƴan jarida da suka fara jefa mata tambayoyi harda na hauka, wasu ma a fakaice magana su ke gaya mata,buɗe Ambulance ɗin ɗaya daga cikin officers ɗin yayi ciki su ka saka hajiya Asma'u,maganganu mutane ke jifa ma mom,tana jinsu amma tayi kamar bata jin mi suke cewa tana nan tsaye har sai da taga ficewar Ambulance ɗin daga cikin court ɗin tukun ta juya da nufin ta koma office ɗinta, juwar da za tayi taga brisster hashim tsaye ya harɗe hannuwa saman chest ɗin shi, wani ɗan iskan murmushi ya sakar mata yana tunkaro in da take tsaye, bashi hanya security guard ɗinta su kayi da alama dai shima ba ƙaramin mutum bane.
zuba mashi ido tayi har ya ƙaraso inda take, murmushi ya saki cikin wata irin murya kalar ta ƴan duniya yace
“ya dai lawyer Al'ummah?, yau ina goyan bayan Al'ummar taki yake?”
ɗauke kai mom tayi wani ƙululun baƙin ciki na tokare mata maƙoshi, dariya brisster hashim ya saki
“see u next time” ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya, barin wurin mom tayi securitys ɗinta su ka bi bayanta, da kallo brisster hashim ya bita har ta ƙarasa inda su kayi parking motocin su,duk Abun da ke faruwa balqis na tsaye tana kallo,hawaye ne su ka taru a idonta ta rasa dalili rashin jituwar brisster hashim da mom, juyawa tayi ta nufi motocinsu ta shiga barin court ɗin su kayi baki ɗaya.
wannan lawyer ce ta nufo brisster hashim dake tsaye
“brisster na lura so ka ke baƙin ciki ya kashe brisster zulaihat a yau ” ta faɗa tana sakin murmushi, martanin murmushi ya sakar mata yana
faɗin “yanzu ta fara gani in dai ni ne”
“Allah ya shirya ka, gaskiya baka kyautawa matar yayan ka ce fa”
“na tsaneta bana son ganinta” ya faɗa yana barin wajen, bin bayan shi lawyer tayi.
waya brisster ta ɗauka tayi dialing number yumnah bugu ɗaya tayi picking “ku fito ina parking space ku same ni” tana gama faɗa tayi rejecting ba tare da ta tsaya jin mi yumnah za tace.
miƙewa yumnah tayi tana kallon nainarh data zuba uban tagumi, girgiza kai tayi tana nufar ta, dafa kafaɗar tayi firgigit nainarh tayi ta miƙe a tsorace har sai da gaban yumnah ya faɗin
“yumnah an gama shari'ar ne?” nainarh tajefa mata tambaya
“ban sani ba, amma dai mom tace mu sameta waje ban sani ba ko an gam....” tun kafin ta ƙarasa nainarh ta nufi hanyar fita da sauri, bin bayanta yumnah tayi.
tana fitowa ƴan jarida su ka yo mata caaa, sai jefa mata tambayoyi su ke marasa kan gado, ruɗewa tayi ta rasa in da zata dosa hawaye har sun fara zuba daga idanuwanta,ganin halin da take ciki ne yasa securitys ɗin nufarta, zagayeta su kayi suna tutture ƴan jaridar, in da mom ke tsaye tana jiran su suka nufa,maganganun mutane ne su ka fara ɗaukar hankalinta da irin kallon da suke binta da shi
“itace ɗiyarta ko kunya ba tajiba ta kashe ma yarinya ubanta saboda neman duniya kawai”
“ai hukuncin da kotu ta yanke mata bashi ya kamata da ita ba hukuncin kisa ne dai dai da ita”
“saboda brisster zulaihat yasa ba'a yanke mata hukuncin kisa ba, kasan suke da ƙasar sai yanda su kayi da talaka” maganganun dake fitowa daga bakin mutane kenan, tunda ta fara sauraronsu gabanta ke faɗuwa.
bayan su yumnah ta biyo sai turo baki take kamar zata fashe da kuka,da sauri nainarh ta nufi mom hawaye na fita daga idanunta “mom ina ummah?” shine tambayar data jefa ma brisster, juyawa mom tayi ta shige motar ta ba tare da tace mata komai ba, motar da ke bayan wacce brisster ta shiga security guard ɗin ya buɗe ma nainarh da nufin ta shiga, a masifance ta maida marfin ƙofar ta rufe tana juyawa zata nufi cikin court ɗin, da sauri