kallon Zaabith dady yayi
“zaabith ka kuwa haɗu da Muhsin??”
“A'a dady,ya dai kirani jiya yace yau su ke sa ran isowar su Mubarak”
“kai yaushe za ka tafi can kenan?”
“ƙarfe ɗaya su ke sa ran isowa,sai na tafi after Isha” wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar kainart jin yau zai koma
“good” kawai dadyn yace ba tare da ya sake cewa komai ba,kallon Zaabith momy tayi
“yau zaka koma ne?”
“A'a,sai next week” ya bata amsa, kainart ba hakan ta so ba ta so ace tafiya zaiyi ko ta samu ta huta da uƙubar shi.
Dady da Zaabith ɗin su ka fara tashi sai Irfan da Waseef,tashi kainart tayi itama ta fice aka bar momy da su Ammar.
*Big Daddy's house*
wajen awa biyu su ka ɓata wurin gyaran part ɗin, gyara su kayi mashi na musamman ko ina ka shiga sai tashin ƙamshi yake haɗe da sanyin AC.
“sannunku da ƙoƙari Ishrat,wannan idan dady ya gani dole ya baku tukwici” murmushi kawai Ishrat ɗin ta saki
“ai ina jin ku saki curtains ɗin kawai a kashe bulbs,tunda an kammal”
da to su ka amsa mata suna nufar bedrooms da falukan dan ciki umarninta,duk wani kayan wuta da su ka san sun kunna sai da su ka kashe shi hatta AC ba su bari a kunne ba,kayan da su kayi amfani da su suka kwashe,ficewa su kayi daga part ɗin bayan sun kammala.
ƙofofin bedrooms ɗin Yumnah ta rufe tukun suma su ka fice, direct part ɗin dady ta nufa Nainarh kuma ta nufi bedroom ɗin su,bata samu dady a part ɗin ba har ya fice,key's ɗin kawai ta ajiye ta fice.
A zaune ta samu Nainarh bakin bed,da kallon mamaki ta bita
“yanzu Nainarh maimakon ki shiga kiyi wanka sai ki zauna,ni ban san mi yasa ki ke haka ba komai sai nace kiyi sai kace wata ƙaramar yarinya?”
“ba haka bane,naga ke sauri ki ke saboda fitar da za kuyi ,shine na bari idan kin fito sai na shiga”
wani ɗan iskan kallo Yumnah ta watsa mata “mi ki ke nufi da fitar da za muyi,kina nufin ban da ke??”
“haɗuwa fa za kuyi da family ku ni miye nawa na zuwa”
“gaskiya Nainarh bana jin daɗin irin wanann abun,ni kawai ki tashi ki shiga wanka karma su mom su shirya su fara jiran mu”
“yumnah gaskiya ni bazan je ba,taro ne na familyn ku, taya za ayi naje”
“wallahi sai kin shirya mun tafi kin ma ji na rantse,kullum naita fama dake kamar wata yarinyar goye” Yumnah ta faɗa tana nufar dressing room ɗin ta.
tashi Nainarh tayi ta shiga wanka ta so Yumnah ta ƙyaleta dan bata san wane irin kallo family ɗin su za suyi mata ba ganin ta shigo cikin su,ba lallai suyi maraba da ita ba.
bata jima da shiga wanka ba Yumnah ta dawo bedroom ɗin jikinta ɗaure da towel,zama tayi gefen bed ɗin, Nainarh na fitowa ta tashi ta nufi toilet ɗin har ta kai bakin ƙofa ta tsaya “kayan da zamu sa na nan na fito mana da su”
gyaɗa mata kai Nainarh tayi
ƙofar bedroom ɗin ta buɗe ta shiga, dressing room Nainarh ta nufa, dressing mirror ta nufa,zama tayi saman stool, expensive body lotion ɗin dake jere saman dressing mirror ta ɗauka,shafama jikinta ta shiga yi, simple make up tayima fuskarta Masha Allah tayi kyau abunta.
tashi tayi ta nufi kayan da Yumnah ta ɗauko masu, expensive egyptian abayas ne Black color anyi masu ado da royal blue ɗin yadi a hannun,sunji adon stones a jikin su sai sheƙi suke.
ɗaya daga cikin rigunan ta ɗauka ta zura a jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba kamar wata balarabiya,kallon kanta tayi a gaban mirror ita kanta ta yaba da kyawun rigar a jikinta,baby ribbon ta ɗauka ta ɗaure gashin kanta,mayafin rigar ta ɗauka tayi rolling, masha Allah kawai zamu ce Nainarh Allah yayi mata wani irin sanyi kyau,ba ƙaramin haska farar fatar ta rigar tayi ba,shagala tayi da kallon kanta a mirror.
“wayyo Allah na sister Nainarh ke ce haka?,kai masha Allah kinga yanda rigar nan tayi maki kyau kuwa?, wallahi kamar mutum ya saceki ya gudu,karfa ki rikita mana samarin family a kasa gane kan su”
dariya Nainarh ta fashe da ita jin irin sambatun da Yumnah ke mata,sosai Yumnah ta shiga zuzuta kyan da Nainarh tayi,ita kuwa ban da dariya babu abun da take.
“bari nayi sauri na shirya ko na samu nayi maki pics kar wannan wankan ya tafi haka nan” ta faɗa tana nufar dressing mirror.
shaf shaf tashiga shiryawa,itama simple makeup tayima fuskarta,rigarta ta ɗauka ta zura Nainarh na daga tsaye sai Binta da ido take harta kammala shiryawa,itama ba ƙaramin kyau tayi ba abunka ga farar fata sai rigar ta sake fito da haskenta.
jinjina kai Nainarh tayi tana faɗin
“masha Allah kema ba ƙaramin kyau ki ka yi ba”
“ban kai ki ba” Yumnah ta faɗa tana ɗaukar wayarta, hand bag ta ɗauko masu mai shegen kyau tare da sunglasses mai ɗaukar ido.
bedroom su ka nufa Nainarh ta ɗauki wayarta dake saman nightstand ajiye,ficewa su kayi daga ɗakin zuwa parlor,anan su ka ɓaje kolin ɗaukar photo, photo Yumnah ta shiga ɗaukar Nainarh ba ƙaƙƙautawa,bayan nan ta kira Ishrat tayi masu a tare.
A tare su ka shigo parlorn,a bakin ƙofar su kaci burki cikin shigar shadda gezna fara ƙal sai ɗaukar ido take,kan su a sanye yake da hula, kwantacciyar sumar kan su sai sheƙi take.
fuskar shi a tsuke take kamar ko da yaushe saɓanin ta ɗan uwan shi dake ɗauke da murmushi yana kallon Nainarh da Yumnah da su ka juya ma ƙofa baya, kallo ɗaya yayi masu ya ɗauke kai yana kai dubanshi ga Ishrat dake ɗaukar su photo,wani ɗan iskan kallo ya watsa mata wanda yayi sanadiyar hautsinawar ƴan hanjin cikinta.
saurin sauke wayar tayi ƙasa har tana sake ɗaukar su wani pic ɗin ba tare da saninta ba,da mamaki Yumnah ke kallonta “Ishrat wai lafiya ki ka tsaya sauri muke,ƙara mana ɗaya kafin mom ta fito” Yumnah ta faɗa tana kallonta
cikin rawar murya Ishrat ta furta
“barkan ku da zuwa ,ina wuni” ta furta
da sauri Yumnah takai dubanta ga...
_*Ep 19_20*_
*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘
______________________________
da sauri Yumnah takai dubanta ga Irfan da Waseef dake tsaye a bayan su, murmushi ta saki
“laa ya Irfan ya waseef ku ne?” yumnah ta faɗa cikin nuna jin daɗin ganin su, wani irin faɗuwa gaban nainarh yayi jin sunan da yumnah ta ambata, idan bata manta ba shine mutumin daya shigo ɗakin su ya sameta daga ita sai towel.
wani irin takaici da kunya ne su ke rufeta ji tayi ina ma ƙasa zata tsage ta shiga,ko ƙwaƙwaran motsi kasawa tayi.
da sauri yumnah ta nufe su
“kun zo a dai dai, Ishrat yi mana photo” nainarh ta faɗa tana shiga tsakiyar su, saurin kallon Irfan da yayi kicin kicin da fuska Ishrat tayi,kasa ɗaukar photon tayi saboda hararar daya watsa mata, ƙofar parlorn mom ya nufa ba tare da ya tsaya photon ba, da kallo kawai yumnah da Waseef su ka bishi, Nainarh kuwa tsananta faɗuwa gabanta yayi lokacin da taga giftawarshi ta idonta.
taɓe baki yumnah tayi tana kallon Waseef “ya Waseef wai mike damun ya Irfan ne?”
“ban sani ba yumnah, kin san halinshi sometimes ba iya mashi ake ba”
“Allah ya kyauta,Ishrat yi mana kinji” yumnah ta faɗa, saurin dakatar da Ishrat ɗin waseef yayi yana nuna Nainarh data juya masu baya.
“wacece wannan ita bazata zo muyi photon ba”
“laa sister Nainarh zo muyi photo tare da ya Waseef” yumnah ta faɗa tana nufar Nainarh ta kamo hannunta zuwa in da Waseef ɗin yake tsaye.
“sannu pretty, muyi photo ko?” Waseef ya faɗa yana sakar mata murmushi, murmushi itama ta sakar mashi tana gaishe da shi, cikin kulawa ya amsa mata, tsakiyar su ya shiga, photon Ishrat ta shiga ɗaukar su a nan Fa'iza ta same su itama ta ɗau wankan Abaya simple makeup ne a fuskarta ba ƙaramin kyau tayi ba.
shiga itama tayi a kayi photon da ita,photona sosai su ka ɗauka Waseef sai da yasa Yumnah tayi masu su biyu shida Nainarh,Fa'iza ma sai da a kayi mata da Nainarh, sai da su kayi mai isar su tukun su ka bari a nan parlor su ka zauna suna kallon photunan.
mom ce ta fito Irfan na biye da ita, ta ɗau wankan Arabiyan Embellished open Abaya launin Royal blue tayi rolling da Veil ,babu makeup a fuskarta amma ba ƙaramin kyau tayi ba, cikin parlorn ta ƙaraso Irfan na riƙe da hand bag ɗinta.
“mom kinyi kyau sosai, dan Allah muyi photo dake kema” yumnah ta faɗa tana nufo mom ɗin
“lokaci ya ƙure Yumnah,na san mu kaɗai ne bamu je ba, ki bari sai wani lokaci” ɓata fuska yumnah tayi ba haka ta so ba.
ficewa su kayi daga parlorn gaba ɗayan su Ishrat na masu a dawo lafiya, parking space su ka nufa, motar Irfan mom da Waseef suka shiga yayin da Yumnah da Nainarh su ka shiga motar Fa'iza,key su kayi ma motocin su ka fice daga gidan zuwa gidan Abbah dake cikin Estate ɗin.
Tafiya su ka yi mai ɗan nisa kafin su ka iso gidan Abbah, katafaren luxury Villa ne na gani na faɗa,yaji kayan alatu kamar baza'a mutu ba,a katafaren parking space ɗin gidan su kayi parking Wanda yake cike da expensive rides masu matuƙar kyau.
fitowa su ka shiga yi ɗaya bayan ɗaya,a tare su ka nufi entrance ɗin shiga gidan mom da su Irfan na gaba yayin da Yumnah da su Nainarh ke bayan su, yanzu ma hand bag ɗin mom ce a hannun Irfan, bakin su ɗauke da sallama suka shiga katafaren parlorn gidan wanda aka ƙawatashi da manya manyan sofas masu matuƙar kyau da tsada.
matasan ƴan mata ne zaune saman sofa kowacen su ta ɗauka wanda Egyptian Abaya ɗaya tayi rolling da veil ɗin yayinda ɗaya kanta yake a buɗe,zallar gashin kanta ne kawai, gaba ɗaya wayoyinsu ne a hannunsu sun tasa gaba sai aikin latsawa su ke.
Kairiyyah da Noor kenan, Kairiyyah ta kasance ɗiya ga Aunty Adama Noor kuma ɗaya ce ga Uncle mutallaf.
sake ƙwaɗa sallama Yumnah tayi yayin da Irfan da Waseef su ka nufi glass elevator dake cikin parlorn.
saurin ɗago kai su kayi,riƙe ƙugu Yumnah tayi tana jijjiga jiki haɗi da kauda kai gefe,da sauri ƴan matan su ka nufo mom.
hugging ɗin ta su kayi cikin girmamawa wacce tayi rolling veil ta gaishe da mom, da fara'a mom ta amsa mata.
“lafiya lau Kairiyyah,ya school?”
“lafiya lau Alhmdllh mom”mom ta faɗa
“momy ina wuni” ɗayar ta gaishe da mom ɗin
“lafiya lau Alhmdllh,Noor zuwan yaushe?”
“jiya cikin dare mu ka zo”
“masha Allah harda dadyn ku kuka zo ne?”
Eh taba mom ɗin amsa, elevator mom ta nufa tana faɗin “bari na shiga wajen Abbah” da to su amsa mata, hugging ɗin Fa'iza su kayi cikin kulawa su ka gaishe da ita,kishi duk yabi ya cika Yumnah ganin sun ƙi kulata,kama hannun Nainarh tayi.
“mu tafi kinji sister”
da sauri Noor tabi bayan su, hugging ɗin Yumnah tayi ta baya “haba sister ba dai fushi ki ka yi damu ba?” fisgewa Yumnah tayi
“ni ki ƙyale ni”
“bazan ƙyale ki ba,sai kinyi haƙuri” murmushi Fa'iza tayi tana nufar su ita da Kairiyyah, Nainarh bin su kawai take da ido.
“sister sannu” Kairiyya ta faɗa tana kallon Nainarh, murmushi Nainarh ta sakar mata tana amsa mata sannu da tayi mata.
lallashin Yumnah Noor ta shiga yi da ƙyar su ka samu ta saki fuska,part ɗin Abbah su ka nufa gaba ɗayan su.
*MOM*💫
a second floor elevator ta sauketa, corridor da zai sadata da part ɗin Abbah ta nufa,tunda ta tunkaro ƙofar shiga part ɗin take jin muryoyin su suna fira cikin nishaɗin, a bakin ƙofar shiga ta tsaya,a hankali ta tura ƙofar ta shiga.
Masha Allah katafaren parlorn ne da yaji kayan more rayuwa, manya manyan sofas ne set uku masu matuƙar kyau da tsada ga taushi kamar audiga,haɗaɗiyar rug carpet ce shinfiɗe a ƙasa, kyakkyawan Dattijo ne mai cikar kamala cikin shigar farar Alkyabba a kishingiɗe saman rug carpet yayi matashi da tumtum yayin da ƴaƴan shi ke kewaye dashi sun saka shi tsakkiya,fira suke cike da nishaɗin.
su goma ne ƴaƴan Abbah dady shine babba daga shi sai uncle Ahmad daga su sai uncle Mustafa da uncle Ubaid daga su sai uncle mutallaf daga shi ne sai barrister Hashim da Aunty mariya daga su sai Aunty Safeenah da uncle Khamis daga su sai Aunty Adama ita ce Autar Abbah.
gaba ɗayan su ne a parlorn uncle Khamis ne kawai babu shima baya ƙasar ne tsawan shekara 19 kenan rabon shi da ƙasar,shi ka ɗai ne a cikin su baya da Aure.
Dady na daga hannun daman shi yayin da dady Ahmad ( mr president ) ke kusa da shi sai
Uncle Mustafa, Uncle ubaid da uncle Hashim, ɓangaren hagu kuma Aunty mariya,Aunty safeenah da Aunty Adama ne sai uncle mutallaf dake tsakiyar su,Irfan da Waseef na daga saitin kan Abbah zaune,gaba ɗaya hankali su na kan Abbah dake basu labarin yarintar su dady cike da nishaɗi.
sallamar mom ce ta katse masu firar da suke,gaba ɗayan su suka kai duban su gareta, murmushi ne ya bayyana akan fuskar Abbah da alama yaji daɗin zuwanta,kaf cikin surikan sa babu wacce yafi so sama da mom,tamkar ɗiya haka ya ɗauketa,idan ka cire barrister Hashim da Aunty Safeenah babu wanda baiyi farin ciki da zuwanta ba,da sauri Aunty Adama ta tashi fuskatar ɗauke da murmushi ta nufo mom.
hugging ɗin juna su kayi hakan ba ƙaramin ɓata ran Aunty Safeenah yayi ba,kauda kai tayi gefe tana jan tsaki, cike da kewar juna suka gaishe da juna,cikin parlorn su ka ƙarasa,wurin Abbah mom ta nufa fuskarta ɗauke da murmushi.
zama tayi kusa dashi “in wuni Abbah,mun sameku lafiya?”
“lafiya lau Alhmdllh,ya gidan ya kuma aiki”
“lafiya lau” Masha Allah Abbah ya furta,duban ta ta kai ga dady Ahmad cike da girmamawa ta gaishe da shi,cikin kulawa ya amsa mata yana tambayar Yumnah.
ɗaya bayan ɗayan tabisu tana gaishe da su,cike da kulawa su ke amasa mata in ka cire barrister da Aunty Safeenah da su kayi kamar ba su san da su take ba,hakan kwata kwata bai dameta ba dan idan da sabo ta saba da halin su,dady baiji daɗin hakan ba ya rasa miye matsalar ƴan uwanshi da matar shi.
“Ashe abun da ya faru da Asma'u kenan?, ubangiji Allah yayi mata mafita,Allah ya kuɓutar da ita,su kuma wanda su ka da baibaye ta da sharrin Allah yayi gaggawar tona masu Asiri” Abbah ya faɗa
da Ameen ya Allah Abbah su ka amsa banda uncle Hashim da yayi tsit kamar baya parlorn
“Allah ya kuɓutar da ita ya kyauta gaba” a cewar uncle Ahmad da Ameen su ka amsa suma,ɗaya bayan ɗaya su ka shiga yi mata jaje in ka cire Aunty Safeenah data miƙe ta nufi ƙofar fita, barrister Hashim kuwa lumshe idonshi yayi kamar mai bacci .
“saffenah!!” Abbah ya kira sunanta,dakatawa tayi da tafiya ta juyo tana fuskantar shi
“ina zaki kowa na nan?”
“zan shiga wajen mama ne,naga an gama firar zumunci tunda har bare sun fara zuwa shiy...”
bata ƙarasa ba sakamakon tsawar da dady ya daka mata
“Abbahn ki ke faɗama haka?,maza ki dawo ki zauna kafin ranki ya ɓaci” murmushi kawai mom tayi bata so dady yasa baki ba.
rai a ɓace ta nufi wajen zamanta zata zauna
“jeki kawai” Abban ya faɗa,babu ko kunya ta juya ta fice,kauda kai kawai dady yayi da alama baiji daɗi ba,kallonshi Abbah yayi yana sakin murmushi haɗi da girgiza kai.
A bakin ƙofa Aunty Safeenah taci karo da su Yumnah, fuskar su ɗauke da murmushi su ka gaishe ta,ta amsa ma kowa amma banda Yumnah da Nainarh da tabi da wani irin kallo mai wuyar fassarawa.
hankali Nainarh ba ƙaramin tashi yayi ba da irin kallon da Aunty Safeenah tayi mata,duk sai taji wani iri dama ba tayi niyyar zuwa ba Yumnah ta jawota tasan dama ba dole bane dangin Yumnah su sota ba.
ganin yanayin data shiga ne yasa Fa'iza kamo hannunta cikin nata,da murmushi akan fuskarta tace “muje ko”
tura ƙofar parlorn tayi su ka shiga bakin su ɗauke da sallama,gaba ɗaya parlorn su ka kai duban su gare su.
Amsa masu sallamar su kayi in ka cire uncle mutallaf daya kafe Nainarh da ido ko ƙyaftawa baya yi uncle Ahmad ma kallon sani yake mata,har suka ƙaraso cikin parlorn uncle mutallaf bai janye idanunshi daga kanta ba har sai da Abbah yayi mashi gyaran murya tukun yayi sauri kauda idoshi daga kanta ya kalli Abban,hararar wasa Abbah ya watsa mashi.
saurin duƙar da kai yayi duk sai yaji kunyar kamashin da Abbah yayi yana kallonta yasan Abbah zaiyi tunanin wani abu shi kuwa har ga Allah kama tayi mashi da wacce ya sani.
zama su kayi kan rug carpet ɗin cikin kulawa su ka gaishe da su suna amsa masu,nuna Nainarh Abbah yayi da hannu
“in ku ka samu wannan mai kama da mariyata?” gaba ɗayan su suka kai duban su ga Nainarh sai da Abbah ya faɗa su kaga kamaninta da Aunty mariya in ka cire mom da dady dan su sunfi ganin kamaninta da Carol ƙanwar mom,sai yanzu uncle mutallaf ya fahimci da wacce take mashi kama.
kallo ɗaya Irfan da barrister suka yi mata suka kauda kai
“ƴan mata yaya sunan ki?” Aunty mariya ta faɗa tana kallon Nainarh
“NAINARH” ta bata amsa,jinjina kai Aunty mariya tayi “masha Allah, Nainarh suna mai daɗi” Aunty mariya ta faɗa, murmushi Nainarh ta saki a hankali ta furta “nagode”
juyawa Aunty mariya tayi ta kalli mom,fahimtar abunda Aunty mariya ke nufi ne yasa mom faɗin “ɗiyar Asma'u ce”
“Allah sarki” Abbah ya faɗa cike da jin tausayin Nainarh,babu wanda baiji tausayinta ba jin itace ɗiyar Hajiya Asma'u, barrister Hashim kuwa ko a jikinshi.
“sannu kinji Nainarh Allah ya kuɓutar da mahaifiyar ki” a cewar Abbah ,gaba ɗaya parlorn su ka amsa da “Ameen ya Allah” fira suka shiga yi cikin kwanciyar hankali.
Noor tunda su ka shigo Irfan ke Binta da wani irin narkaken kallo,itama tunda ta zauna hankalin ta na kanshi,wasu alamomi yake mata da ido wanda daga ita sai shi su ka san ma'anar su,sosai su ka shagala da kallon juna