x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - SHIRYAYYAR ƘADDARA

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 140573 words

Category: Love Stories

Views 442

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
suka nufo court ɗin,ganin irin gudun da suke ne yasa mutane darewa suka basu hanya, tuni security's sun buɗe masu gate suna ƙarasowa ciki suka shige , sai da suka gama dai daita parking tukun suka shiga fitowa kowanen su sanye yake da journalist jacket black color a gaban rigar anyi rubutu da farin paint inda aka rubuta press da mayan haruffa.


ba ɓata lokacin suka shiga fito da kayan aikin su cameras ne yan uban su dan duk yan jaridar dake wurin babu masu nagartatun kayan aiki masu tsada kamar na su.


cikin ƙanƙanin lokaci suka gama dai daita kayan aikin su bayan sun gama daidaitawa ne aka buɗe back seat na motar dake gaban tv broadcasting van car, wata matashiyar budurwa ce tafito sanye take da pant suit white color tayi roling da black ɗin veil,high hills ne a ƙafarta black color,fara ce kyakyawar gaske wurin cameras ɗin ta nufo cikin takun ƙasaita.

Kallo fa ya koma sama gaba ɗaya hankalin mutane ya dawo kan su sai ƙus ƙus ke tashi a wurin.


wannan matashiyar budurwar ce ta fara gabatar da shirin nasu cikin harshen hausa amma saboda zaƙin muryar ta kamar bada hausa take magana ba

“masu kallon mu barkan mu da sake saduwa acikin shirin mu mai farin jini GANI YA KORI JI, a inda muke kawo maku shari'ar hajiya Asma'u wacce ake zargin dasa hannunta a kisan mijinta wato CP ( commissioner of police ) na wannan jaha ,masu kallon mu idan baku manta ba a wancan lokacin koto ta ɗaga sharia'ar zuwa goma ga wanta febrairun shekarar da muke ciki bisa ga wasu dalilai, a yaune adadin kwanakin da koto ta yanke dan zartar da hukunci suka cika , ku biyo mu dan jin yanda shari'ar zata kaya”


tana gama faɗa ma'aikatan suka kashe kemarorin, wani daga cikin ma'aikanta ne yace “good job BALQIS babu wanda zaice ba LAATIFA ba ce” ɗan ya mutse fuska tayi tana faɗin “thanks” tana komawa back seat ɗin motar data fito, jinjina kai kawai yayi,yana sakin murmushi tana shiga cikin motar wayarta dake ringing ta ɗauka picking call ɗin tayi haɗi da kara wayar a kunnenta, muryar mai kiranta ne ya daki dodon kunnan ta

“ hello balƙis ya aikin yake tafiya?”

ya mutse fuska tayi tana faɗin “wallahi bawani abun duk wahala ne, kuma ni banga amfanin bin wannan shari'ar ba”


“haba balqis miye abun wahalar aciki, na kalli live kuma naga kinyi ƙoƙari, ke da yake ba yar jarida bace shiyyasa zaki ce haka”

taɓe baki tayi tana faɗin “ni dai wallahi kin haɗani da Aiki Aunty laatifa”

“kai balƙis miyasa za kice haka bana jin daɗi kina faɗin haka sai naga kamar na takura maki ne ba da son ranki ki kayi ba” jin abun da laatifa tace yasa balqis cewa “ni baki takura man ba, dan nayi niyya ne yasa na zo”

“shikenan sai kin dawo amma dan Allah kar kice ma dady ni na nace kizo please”

“zance mashi ni nayi niyya ba ke ki ka sani ba,amma kin tabbata zaki cika man alƙawari na?”

“nagode ƙanwata sai kin dawo karki damu”

“ok sai na dawo” balƙis ɗin ta faɗa tana rejecting kiran iska ta fesar daga bakinta,wayarta ta shiga shafawa tana kallon wallpaper wayar tana sakin murmushi,sai sakin murmushi take tana aikin shafa wayar, matso da wayar tayi zuwa fuskarta kissing screen ɗin wayar tayi tana faɗin

“am eager to see u my hero,i miss u”

tana cikin wannan shauƙin taji hayaniya tayi yawa ga kuma jiniyar motocin security Army's da yake glass ɗin motar da take ciki na gaba a buɗe yake,tsaki taja tana faɗin

“i hate this sound gaskiya Aunty latifa baki kyauta man ba” ta faɗa tana ɗan jan tsaki, nocking ɗin ƙofar motar taji anyi da sauri ta juya tana kallon mai yin nocking ɗin ranta a haɗe tace “what?”

“sorry dama cewa zanyi ki fito ga BARRISTER ZULAIHAT nan ta ƙaraso” ya mutsa fuska tayi tana faɗin ok

fitowa tayi daga motar sai wani sa hannu take tana kare fuskanta saboda zafin rana.

wasu jibga jibgan motacin sojoji ne ke shigowa cikin court ɗin gaba ɗaya sun cika court ɗin da ƙarar jiniyar su yayin da tsakiyar su wasu expensive bullet proof latest car ne masu nufashi guda biyu fara da baƙa.

Anan compound ɗin court ɗin su kayi parking,security Army's ne suka fara fitowa daga cikin motacin su hannuwan su riƙe da manyan bindigu ga wasu soke a ƙugun su.


farar motar su ka nufa, wani jibgegen security guard ne ya buɗe back seat ɗin motar.


wata kyakyawar baturiyar mata ce ta fito daga back seat ɗin a ƙalla zata kai kimanin shekara 50 a duniya, kyakyawa ce ajin farko ƴar gayu kai tsaye idan ka kalleta ba zaka ce tayi waɗannan shekarun ba a duniya,sanye take da fararen flat pant suit a jikinta ta yafa farin mayafi a kanta,tana da dara daran idanu farare wanda cikin su ya kasacen Ash ne a manne su ke da farin medical glasse,fuskarta ɗauke take da ni'imceccen murmushi.




𝑏𝑎𝑟𝑟𝑖𝑠𝑡𝑒𝑟 𝑧𝑢𝑙𝑎𝑖ℎ𝑎𝑡 𝑘𝑒𝑛𝑎𝑛 𝑓𝑖𝑟𝑠𝑡 𝑤𝑖𝑓𝑒 𝑜𝑓 𝑡ℎ𝑒 𝑓𝑜𝑟𝑚𝑒𝑟 𝑝𝑟𝑒𝑠𝑖𝑑𝑒𝑛𝑡 𝑜𝑓 𝑛𝑖𝑔𝑒𝑟𝑖𝑎,𝑤𝑎𝑐𝑐𝑒 𝑚𝑢𝑡𝑎𝑛𝑒 𝑘𝑒𝑚𝑎 𝑙𝑎𝑘𝑎𝑏𝑖 𝑑𝑎 𝑙𝑎𝑢𝑦𝑎𝑟 𝑎𝑙'𝑢𝑚𝑚𝑎ℎ.



daga front seat na motar security guard ce ta fito hannunta riƙe da black coat da white hand bag sai briefcase rataye a ƙafaɗar ta wanda nake kyautata zaton na barrister ne.

wani daga cikin security guard ɗin ne ya buɗe back seat ɗin baƙar motar dake bayan wacce barrister zulaihat ta fito,ƴan mata ne guda biyu su ka fito, dukan su baƙar abayace a jikinsu anyi mata aiki da golding stones sai sheƙi da ɗaukar ido su ke, sunyi roling da glenta,fuskar ɗaya sanye take da niƙab,ɗayar kuwa sunglasses ne manne a fuskarta dake ɗauke da fara'a,hannunta riƙe da ƴar madaidaiciyar bag ta company Gucci golding color,tana matuƙar kama da barrister zulaihat kamar an tsaga kara.



cikin tafiyar ƙasaita balqis ta ƙaraso wurin su tana sakin murmushi,tana isowa hugging ɗin barrister tayi tana faɗin “good morning mom” raba jikin su barrister tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace
“morning balqis, yau kece da kanki?” murmushi balqis tayi tana faɗin “ayyuka ne su ka yima Aunty laatifa yawa shine tace nazo nayi attending wannan shari'ar dan bata so tayi missing”

“good,laatifa ba dai aiki ba” barrister ta faɗa,ƴan matan nan ne suka ƙaraso wurin su, mai niƙab ɗin ce ta gaishe da balqis yi tayi kamar bata san da ita take ba,saima kyauda kai da tayi tana kallon gefe, yamutse fuska mai kama da barrister tayi tana faɗin “Abun ma yar haka ce ko Aunty balqis” murmushi balqis tayi kamar ba ita ba tana faɗin
“miye kuma yumnah shagwaɓa” bubbuga ƙafa wacce aka kira da yumnah ta shiga yi tana turo baki da faɗin
“mom kina jin Aunty balqis ko, ba zata daina ce man haka ba”
“bana cike da wannan shiritar taki yumnah,balqis nayi ciki”

barrister ta faɗa tana yin gaba, bin bayanta yumnah da wannan budurwar dake sanye da niƙab su kayi yummah na cigaba da shagwaɓarta security guard ɗin na biye da su.

murmushi kawai balqis tayi tana komawa wurin aikinta.


Yan jarida na ta so suyi magana da barrister amma security guard ɗin ta sun ƙi ba su dama,amma saboda ƙwaƙwa irinta ƴan jarida ana ture su amma suna jefoma barrister tambayoyi.



A bakin ƙofar office ɗinta security
su ka tsaya macen dake ɗuke da jakarta da rigarta ce ka ɗai ta shiga ciki sauran securitys ɗin kuma su ka zagaye office ɗin yanda ko ƙuda bai isa ya gitta ba tare da sun ƙwamushe shi ba.


Wani irin haɗaɗen office ne naji da faɗa, yasha expensive desk da leather chair's masu shegen kyau ,barrister zulaihat kujerarta ta nufa ta zauna,akan desk ɗinta securityn ta ajiye mata hand bag ɗinta sannan ta rataya mata coat ɗinta jikin office suit hanger,wasu files ta ciro daga cikin briefcase ɗinta ta shiga dubasu tana ƙarasa haɗa hujjojine kafin lokacin shiga court ɗin yayi.


saman sofa dake cikin office ɗin yumnah su ka nufa su ka zauna sai a lokacin ne ɗayar ta yaye niƙab ɗin dake fuskar ta, masha Allah na furta da ganin kyakyawar fuskar matashiyar budurwar wacce a shekaru bazata wuce sha tara ko ashirin ba kusan sa'anni ne da yumnah.

damuwace ƙarara akan fuskarta, murmushi yumnah tayi tana faɗin
“yanzu dan Allah da ki ka cire wannan abun ba kiji daɗi ba?” kallon yumnah kawai matashiyar tayi ba tare da tace komai ba
“zaki fara wannan shirun naki ko, mom kiyi mata magana mana ta saki jiki da ni ko dan taga na damu da ita” yumnah ta faɗa tana wani ɓata fuska, girgiza kai kawai barrister tayi tana cigaba da aikin dake gabanta ba tare da tace ma yumnah komai ba.



“mom kema shirun zaki man?” ta faɗa tana turo baki kamar zata fashe da kuka

“yumnah wai miyasa ke baki san lokacin da mutum ke son magana da lokacin da bai so ba, baki san halin da take ciki bane zaki dameta?”

a hankali ta kama kunnenta tana faɗin “sorry mom, zama da damuwa bashi ke maganin matsala ba, that's why nake son ta ɗan saki jikinta” kallon matashiyar tayi tace

“sorry NAINARH idan na takura maki, inaso ki saki jiki ne kawai”

murmushi wacce aka kira da nainarh ta saki
“karki damu baki takura man ba, nagode da kulawar ki a gare ni”

martanin murmushi yumnah ta mayar mata tana buɗe hand bag ɗin data shigo da ita, ciro wayarta ƙirar iPhone 14 pro max tayi dialing wata number,waya ta shiga yi cike da shagwaɓa.



miƙewa barrister tayi da sauri security ta matso tana harharɗa files ɗin dake kan desk ɗin tana maidawa cikin briefcase, ganin haka ne yasa su yumnah miƙewa da sauri nainarh na maida niƙab ɗinta tana ɗaurawa, kallon su barrister tayi tace “ina zaku?” yumnah tace “mom ba time yayi ba”
“eh, ku zauna anan duk yanda shari'ar tayi za kuji” duƙar da kai nainarh tayi alamar ba haka taso ba


matsowa barrister tayi ta dafa kafaɗar “sorry nainarh ba dan wani abu yasa nace ku zauna nan ba sai dan tsoron abun da zai biyo baya acikin court, nan sai kin fi samun tsaro”

“shikenan mom,amma ba za'a neme ni ba?” nainarh ta faɗa
“babu mai neman ki, idan yiwuwar hakan ma ta taso za'a zo a tafi dake ne, fatana dai ki kwantar da hankalin ki” gyaɗa mata kai kawai tayi.


Komawa su kayi su ka zauna barrister kuma su ka fice,security tunda su ka ji alamun buɗe ƙofar office ɗin su ka gyara tsayuwar su tana fitowa su ka nufi cikin court ɗin har lokacin yan jarida basu daina binta da jefo mata tambayoyi.





ciki su ka ƙarasa security guard biyu ne suka shiga cikin court room haɗi da macen sauran su ka tsaya a waje, lokacin da su ka shiga court room ɗin a cike take,duk wani mai ruwa tsaki ya hallara suna zaune a mazaunin su yan jarida sun saita kamarorin su jiran a fara kawai su ke, balqis na daga zaune saman chair daga can baya,Attorney tables da aka tanada domin su ta nufa zama tayi security na ajiye mata briefcase ɗinta daga gefenta su ka tsaya,gaishe da ita attorneys ɗin su ka shigayi tana amsa masu cikin kulawa , mutum biyu ne a cikin su ko kallon in da take ba suyi ba,wata macece da wani namiji,fuskar ko wanen su a haɗe take kamar an aiko masu da saƙon mutuwa, namijin ya jingina da head board ɗin chair ɗin da yake zaune hannunshi riƙe da ƙwallon wasan chess yana wasa da ita saman desk,murmushi saki tana faɗin “good morning BARRISTER HASHIM” sai a time ɗin ya juyo masha Allah na faɗa kyakyawa ne na gaske fatar jikinshi chocolate color ce, kallonta yayi da wasu lumsassun idanuwanshi, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai yana faɗin “morning” kamar irin anyi mashi dolen nan,girgiza kai kawai tayi tana buɗe briefcase ɗinta ta fito da files da laptop ɗinta dake ciki......
_*Episode 3_4*_



*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘


_________________________



Prison officers ne su ka shigo su biyu sai mata guda biyu ma'aikatan prison sun sako wata mata a tsakiyar su yayinda police maza gudu biyar ke a bayan su kowanen su riƙe yake da bindigar sa,uniform ɗin prison ne a jikin matar inda a gaban rigarta aka rubuta number 106 da farin fenti’ black ɗin hulace a kanta,hannunta a sanye yake da handcuff, kanta a duƙe yake har su ka ƙarasa cikin court ɗin, kusa da brisster zulaihat matar ta zauna yayin da police ɗin su ka tsaya a bayan su.

ƙus ƙus ne ya fara tashi a cikin court room ɗin wasu na tausaya ma matar yayin da wasu ke kiranta da munafuka in sha Allah asirinta sai ya tonu.

shiru su kayi sun kafe juna da ido kowa na so yayi ma ɗan uwansa magana amma ya kasa daga brisster har mata,ƙwalla ne ya taru idon matar da sauri brisster ta miƙa mata handkerchief tana faɗin “karki kiyi kuka, in sha Allah yau gaskiya za tayi halinta” jinjina mata kai matar tayi tana goge hawayen dake zuba a idonta, brisster ma dauriya kawai take amma itama kukan take son yi kawai ta daure ne dan karta ƙara karyama matar zuciya.

A hankali matar tace “ina nainarh?”
“suna office ɗina ita da yumnah, na hanata shigowa nan ne dan ban san wani abu ya faru da ita” jinjina kai kawai matar tayi da ka ganta ka san tana cikin matsananciyar damuwa.

ɗaya daga cikin prison offices ɗin ne yace “hajiya za mu iya tafiya?” miƙewa matar tayi su ka nufi in da aka tanada domin zaman su,zama tayi matan su ka sata a tsakiya.

miƙewa su kayi gaba ɗayan su saboda shigowar alƙali,saida alƙali ya zauna tukun suma suka zauna,bayan koto tayi tsit, miƙewa judicial Assister yayi ya gabatar da ƙara bayan ya kammala ne alƙali ya buƙaci da lawyer masu ƙara ya fito.

Cikin ƙwarewar aiki clerk yake typing duk wani abu da ake furtawa a cikin court kama daga sunaye mutane har zuwa yanda shari'ar ke tafiya ga DAR (digital Audio recording ) box a gefenshi tana ɗaukar komai.

miƙewa tsaye brisster hashim yayi wasu files dake gabanshi ya ɗauka yana ajiye chess ball ɗin dake hannunshi, fitowa yayi daga inda yake zaune yana wani gyara zaman coat ɗin dake jikinshi,papers ɗin dake hannunshi ya miƙama judicial Assister, juyawa yayi ya miƙama alƙali.

“my lord wannan rahoton gawar marigayi ne wanda ƙwararon likitoci su ka gudanar tare da horoton cctv camera dake gidan shi, sai bincike da ƴan sanda su ka gudanar akan shatin hannun hajiya Asma'u da aka samu a jikin bindigar da aka kashe marigayi da duk wasu wayoyi daya amsa kafin faruwar abun,sai sunayen witness”

yana gama faɗa ya koma mazauninshi ya zauna yana ɗaukar ball ɗin shi ya cigaba da juyata saman table.

miƙewa mom tayi cikin taƙon kamala ta fito tsakiyar court,ɗan rissinar da kai tayi tana kallon alƙali alamar girmamawa, jinjina mata kai alƙalin yayi,takardar dake hannunta ta miƙama judicial Assister tana faɗin
"my lord wannan sune jadawalin shedo da nayi ma court alƙawarin kawowa"

tashi judicial Assister ɗin yayi ya miƙama alƙali takardar, amsa alƙalin yayi yana ɗaukar glass ɗin shi ya manna a ido, ya ɗan ɗauki tsawan lokaci yana duba duka takardun harda wanda brisster hashim ya bada kafin yace“zaki iya tafiya” godiya tayi mashi tana komawa ta zauna.

“idan malam Aisha tana kusa ta matso gaban koto” Alƙali ya faɗa, a hankali matar ta miƙe daga cikin mutanen dake zaune saman chair, jikinta sai rawa yake daga ganin yana yinta bata cikin natsuwarta,ƙarasowa tayi ta tsaya a cikin witness stand, tashi mom tayi ta nufi in da matar ta tsaya.

ƴan jarida nan su ka fara ɗaukar komai, tasowa balqis tayi ta dawo inda mutane su ke hannunta riƙe da abun magana,juyawa tayi saitin da attorney su ke karab idanunta su ka haɗu da na brisster hashim wani ɗan iskan kallo ya watsa mata wanda yasa ƴan hanjin cikinta kaɗawa ita kaɗai ta san ma'anar wannan kallon daya watsa mata , da sauri ta duƙar da kai tana juyawa ta bar wurin da sauri, gyaɗa kai yayi yana maida hankalinshi ga Alƙali.


Rantsuwa Alƙali ya fara sa Aisha tayi akan zata faɗin gaskiya, kafin ya ɗaura da cewa “court na san sanin cikaken tarihin ki?”
kasa magana tayi saboda wani irin rawa da jikinta yake har sai da Alƙali ya sake magana “kina ɓata ma koto lokaci" da ido mom tayi mata alama data kwantar da hankalin ta, magana ta fara cikin rawa rawar murya dake nuna rashin natsuwarta

“suna na Aisha Usman shekaruna 42 ni ƴar asalin garin faskari ce dake jahara katsina,nazo Abuja ne ta dalilin wata ƙanwar mahaifiyata itace sanadiyyar fara aikina a gidan marigayi”


“malama Aisha tsawan wane lokaci ki ka san marigayi da matar shi hajiya Asma'u?”

“tsawan shekara goma sha biyar”
“ko zaki iya faɗa ma court yanda zamantakewar gidan take tsakaninki da masu gidan?”

“mutanene masu karamci da san al'ummah ko da kuwa ya kasance na ƙasa da su ne, duk tsawan shekarun dana ɗauka tare da su basu taɓa nuna man cewa wai ni ƙasa nake da su ba, hajiya Asma'u ta ɗauke ni tamkar ƙawarta kuma ƴar uwarta,haka marigayi tamkar ƴar uwarshi ta jini haka ya ɗauke ni”

ƴan rubuce rubuce Alƙali yayi kafin ya ɗago yana faɗin “ko zaki iya bama court labarin yanda kisan marigayi ya....” tun kafin Alƙali ya ƙarasa magana tayi saurin ƙatse shi jikinta na rawa tace “wallahi ni ban san komai a game da kisan marigayi....”

desk Alƙali ya buga yana faɗin “nan court ce, ki san yanda zaki riƙa magana, laifi ne Alƙali na magana ka tari numfashin shi, ki kiyaye”

“tuba nake” ta faɗa

tunda Alƙali ya fara magana gaban matar nan ke faɗuwa, tama kasa ɗagowa ta kalli Alƙalin ko mutanen dake cikin court ɗin,brisster hashim kuwa da wannan matar tunda Alƙali ya fara gabatar da ƙara ya mida hankalin shi kan Alƙali ko motsin kirki ba yayi ƙwallon chess ɗin dake hannunshi ma ajiyeta yayi.

tambayar Alƙali ya sake jefa mata, kawai sai
End Ads