sha'awar kasancewa tare da ita a dau dai wannan lokacin yana fisgarsa tamkar walkiya:
Wani numfashi mai nauyi ya saki — yana jin tamkar zuciyarsa zata fashe da nauyin soyayya da radadin rashin tabbas.
idanunsa suka kai ga fuskarta.
Daidai lokacin da yake shirin sauke wata ƙaramar ajiyar zuciya, sai suka ji motsi da sautin takalmi mai nauyi,
Alhaji Saminu ne ya shiga jikin sa akwai alamar gajiya da fushi, yana janye zuciyarsa da sauri daga tunanin da take shirin narke shi.
Alhaji Saminu ya tsaya cak, yana kallon yadda Halima ke manne da wani saurayi, shi kuma saurayin kamar an soka masa gashin zuma a ƙirji fuskarsa ya cika da shakku da mamaki.
Yayi wani takun ɗan girma da iko, ya nufo su.
Abdullahi ya gano hakan cikin kwana na biyu na idon sa ,ya ja hannun Halima da sauri, cikin ladabi da nutsuwa, suka tafi daga wurin.
Halima kuwa, tana kallon Abdullahi tana kuka mai sanyi, hawaye na bin fuskarta tamkar silin ƙwai da ya fashe a hankali.
bata so a raba su bata so a bar wannan ɗan lokaci ya wuce ba.
Har lokacin da suka rabu, Halima na ta juyawa tana kallonsa cikin raɗaɗin zuciya — kamar tana jin cewa ba za su ƙara saduwa ba, tana maimaita sunan sa a zuciyar ta da jaddada cewa tabbas shine a mafarkin ta ,
shi kuma Abdullahi, da yatsun sa guda huɗu ya shafi labbansa a hankali yana jin ɗumin halittarta har yanzu a jikin sa, yana binta da kallo tamkar yana so ya hango sirrin da bai bayyana ba.
Duniya ta yi wa zuciyoyinsu nauyi
wani sanyi da rashin lafiya na musamman ya mamaye Abdullahi, zuciyarsa na fuskantar wani sabon yanayi da bai saba da shi ba.
Halima ta kasa daure hawaye tana cikin ɗa
Abdullahi ya tsaya cak yana kallonta, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, amma ya tilasta kansa ya sake ta ta tafi da Alhaji Saminu.
aguje zuciya, yana ji tamkar an sare wani ɓangare na ruhinsa.
yana kallon bayanta har ta ɓace a cikin motar , ya runtse idanu cike da damuwa, numfashi mai nauyi ya suɓuce daga bakinsa.
Da zarar Alhaji Saminu ya dawo, ya zube a babban kujerar falo yana huci.
wani irin kishi ne da fushi ya turnuƙa masa zuciya har yana jin idanuwan sa na sauya launi Hajiya Nafisa da sauran matansa suka taru suna kallon sa cikin mamaki da tausayi, amma basu isa su tambaye shi komai ba.
Ya ɗauki kofin shayi dake gabansa, ya buga da ƙarfi a ƙasa, kofin ya tarwatse.
yara suka firfito daga ɗakunan su suna kallon sa cikin tsoro
Halima kuwa, tana zaune a bayan kofa , tana kokarin hana hawaye kwarara daga idanuwan ta tana jin tamkar wata sabuwar ƙaddara ce ke shirin saukar mata.
a wannan daren, gidan ya cika da nauyin shiru da hayaniyar zuciyoyi shiru mai ɗauke da kishi, da ƙyalle-ƙyallen wani mugun fushi da za a sake fallasa a kan Halima…
https://chat.whatsapp.com/BsQ0CkOCA83FgwnQ177z9y
🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
AFTER THE MOON🌕
BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA
💫ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION 💫
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star
Page 21 / 22
Bayan Shekaru Biyu
Tunda ranar da suka rabu a babban ɗakin taron hotel ɗin Abuja, Halima da Abdullahi basu ƙara ganin juna ba. kamar dai wata fata da iska ta ɗauka ta ɓoye a doron ƙasa, haka soyayyar da suka ambato da shiru a idanuwansu ta ɓuya cikin zuciyarsu duk da lokaci ya shude, rana ta fito ta fadi sau dubbai, a zuciyarsu har yanzu tamkar jiya aka faru.
Abdullahi, da zarar ya koma gida, ya shiga tashin hankali mai tsanani mafarkin Halima, kallo daya da ya yi mata, da sautin murya da numfashinta, suka mamaye dukkan tunaninsa duk da irin dattijon haiba da ƙwazo da yake da shi, ya zama tamkar yaro a duniyar soyayya. ya yi iya ƙoƙarinsa ya guje mata, ya ɓoye a cikin aikin sa da tafiyar kasuwanci, amma zuciyarsa ta ƙi amincewa da sabuwar rayuwa har dai iyayensa suka matsa, suka zaɓa masa matar aure daga cikin manyan iyalan su, suka lallaɓa zuciyarsa da hujjar cewa "ba a dukan soyayya ake rayuwa ba."
Da damuwa da karyewar zuciya, Abdullahi ya karɓi zabin iyayensa amma a zuciyarsa ya san: soyayya ta gaskiya daya tal ce kuma Halima ce yayi aure a matsayin ɗan biyayya, ba a matsayin ɗan farin ciki , bayan ya tabbatar da cewa Halima mata ce a gidan Alhaji Saminu.
A bangaren Halima kuwa, rayuwarta da Alhaji Saminu ta fara dusashewa da kwanciyar aure. Alhaji Saminu bai sake kallonta da idon da ya saba da shi ba tun ranar da ya ga yadda ta rungume wani saurayi a hotel kullum yana ganin tamkar ta kai girma da zata saki jiki da wani ko da kuwa ba laifinta bane, ko da kuwa ransa ya tabbatar cewa tsoro da ruɗani ne suka jefa ta.
Auren Halima ya koma tamkar ɗakin sarauta mai cike da shiru da fargaba matansa na farko na ci gaba da wulakanta ta, musamman Hajiya Mariya, wacce kullum take ƙoƙarin ganin ta gaza Halima kuwa, tana rayuwa ne tsakanin kuka da shiru, tsakanin mafarkin soyayya da gaskiyar rayuwa kullum cikin tunanin cewa ƙaddara ce ta raba ta da masoyinta, kuma soyayyar da take jin daɗinta tun ƙarama ba zata cika ba har abada.
"Idan soyayya kaddara ce, to ni na riga na mallake ta, ko da da hawaye zan sha..." Halima na faɗa cikin zuciyarta a duk dare, yayin da take kwana tana duban sararin sama daga taga mai ɗimbin ƙawatawa, amma mara 'yanci.
Rayuwa ta ci gaba da tafiya...
sai dai zuciyoyin masoya biyu suna ci gaba da harbar juna da addu'a cikin nisa, cikin rashin sani ko Allah zai kawo wata rana su haɗu ko kuwa soyayyar su zata kasance soyayyar da bata da makoma?
duk da wulakanci da mugun hali da Halima ke fuskanta a gidan Alhaji Saminu, zuciyarta ta ki rabuwa da sunan Abdullahi.
Abdullahi — wanda tun ranar da suka haɗu a hotel din, zuciyarta ta tabbatar da cewa shine mafitar rayuwarta.
duk daren da ta kwanta cikin kuka da zubar da hawaye, da ƙaunar da take shirin fashe mata ƙirji, sai ta runtse ido tana kiran sunansa da shiru.
"Abdullahi... kai ne mafita ta... amma ka riga ka zama mafarki..."
ko da cikin jikinta yana girma, bata daina jin ƙaunar Abdullahi ba. Sai ma ƙara shigewa da ƙara jin saukin duk wani raɗaɗi idan ta ambaci sunansa a ranta.
Amma fa duniya bata tsaya jira ba,rayuwa ta cigaba da danne ta a karkashin ƙafa, har ta kai ga lokacin haihuwa ya kure.
ranakun karshe da suka rage mata a duniya, wahala ta fi karfin bakinta cikin da ta ɗauka cikin ciwo da azaba ya girma har ta cika da tsoro da fargaba ba wanda ke kula da ita
ba wanda ke tambayarta lafiya ko da take ciwo dare da rana, sai Alhaji Saminu ya ce da ita "ke kanki kika ja wa kanki, na gaji da wannan kuka da ciwo ."
ba komai ya jawo hakan ba sai sanin cewa tsantsan soyayyar da takewa wani alhali tana da nata auren
A karshe, ranar da komai ya ƙare
ranar da zatai haihuwa Halima ta shiga wani ciwo da ba a iya kwatantawa, Alhaji na chan hotel yana meeting bai ma san cewa Qatar haihuwar ta ya kama ba.
A kwance a ɗakin da aka ajiye ta cikin wulakanci, ba likita, ba uwargida, ba taimako sai kuka da ciwon da ke yawo daga ƙasan jikinta zuwa ƙirjinta yana neman karya ta.
Kuka take kamar zata fashe.
Tana kiran Baffa, tana kiran Abdullahi, tana neman taimako amma shiru!
Abdullahi a lokacin yana cikin wani babban business meeting, yana fuskantar matsin rayuwa sakamakon tarin matsaloli da ya dinga samu tun da ya yarda da zaɓin da iyayensa suka masa.
soyayya da Halima ta fara girma masa a zuciyarsa ba ta gushe ba, kullum yana mafarkin fuskar ta, murmushinta, da halayenta.
amma bai san halin da take ciki ba.
bai san tana shirin barin duniya ba.
A cikin tsananin raɗaɗin haihuwa, Halima ta ƙara ruɗewa, ta kurma ihu, ta kifa kanta a shimfiɗa tana ihu kamar rai na fita:
"Ya Allah... Abdullahi... Abdullahi... na yarda da ƙaddara..."inda yayi dai dai da shigowar Alhaji sakamakon korar Hajiya nafisa sai dai, kafin a kawo taimako, kafin a kawo likita halin ya lalace ,numfashinta ya fara yanke-yanke.
zuciyarta ta yi shiru.
Idonta ya tsaya a sama yana kallon wani abu da kowa baya gani, ahankali Halima ta kwantar da kanta gefe, ta saki numfashinta na ƙarshe da kalmar:
shahada , ta mutu.
ta mutu cikin radadin soyayya.
ta mutu cikin ciwon zubar da hawaye.
ta mutu ba tare da samun saukin zuciya ba.
Bayan rasuwar Halima...
Tunda aka sallaci Halima tare da jaririnta da bai samu damar saukar numfashi ba, gidan Alhaji Saminu ya sauya tamkar makoki.
duk wata annashuwa da alfahari da yake alfahari da ita a da, ta shige masa ta barshi da nadama da dimuwa.
Alhaji Saminu ya dinga zubar da hawaye cikin sirri — hawaye na butulci da rashin amana da ya yi wa baffa Moddibbo, wanda ya amince da shi ya ba shi Halima cikin kwanciyar hankali.
yanzu kuma ya gane: ya ci amanar sa... kuma duniya ta rama masa cikin kunya da asara!
zuciyarsa ta kasa kwanciya.
Ko motsin iska da aka yi cikin gida sai ya tuno Halima ,ya zauna ya shafa kansa yana cewa:
"Ni Saminu... ni na kashe Halima da hannu na. ni na lalata amana!"
A ɓangaren Abdullahi kuwa, yana zaune cikin ofishinsa ne duka business da meetings ɗin sa suna tafiya, amma zuciyarsa ta gaza samun natsuwa tun ranar da suka rabu a hotel.
Ana cikin haka sai ya ga sakon gaggawa daga Alhaji Saminu:
"Ina mai baka hakuri, Halima ta tafe gidan gaskiya yanzu ta tafi ta tafe da kuka rashin ka tabbas soyayyar da take ma gaskiya ne ... ta mutu kuma ban cancanci gafararta ba."
Zuciyarsa ta buga!
Idanunsa suka cika da kwalla.
ya dinga kallon sakon kamar zai kira Halima ta amsa masa amma ya sani, babu mai amsawa.
"kin mutu Halima?..." Ya fadi da baki a raunane, numfashinsa yana fita da ƙyar.
sai wayar ta faɗi daga hannunsa.
Gaban mutane sai ya durƙusa.
kamar an fasa masa zuciya, dukkan jikinsa ya rikice, gaba ɗaya duniya ta tsaya masa cikakkar shiru.
"Halima...
Halima...
na bar ki cikin wahala, na kashe ki da rashin ƙarfin zuciya ta..."
Cikin kukan da bai taɓa fuskanta ba a rayuwarsa, Abdullahi ya fito daga taron ya fice kamar mahaukaci, yana rike kirjin sa da hannuwa biyu, yana kuka tamkar jariri, yana ambaton sunanta.
Duniya ta kare masa a wannan rana.
ya rasa komai.
ya rasa zuciyarsa.
ya rasa Halimarsa
sai tunanin mafarkinsu na yara ya fara dawo masa.
yanda take dariya, yanda take tsoron iska mai kaɗawa...
yanda suka tsaya suna kallon juna a hotel ba tare da sun fahimci komai ba — har abada.
Abdullahi ya narke kamar karamin yaro yana kuka ,ya rasa inda zai kai zuciyarsa.
Soyayyar Halima ta zama masa mafita da karfi.
yanzu kuwa... an binne mafarkin sa da soyayyarsa a ƙasa.
ƘARSHEN LABARIN HALIMA
Bayan rasuwar Halima, kwana biyu kacal sai Abdullahi ya tashi daga gida ya nufi inda aka binne ta , zuciyarsa cike da nauyi kamar dutse mai nauyi, idonsa kuwa har ya kumbura da kuka da rashin bacci.
Lokacin da ya isa makabarta, an waye gari — iska tana kadawa, rana na nufar faduwa.
kabarin Halima yana can gefe, kamar ba halitta ce ciki ba wsai iska da tsuntsaye.
Abdullahi ya tsaya daga nesa yana kallon kabarin — jikinsa ya mutu, zuciyarsa tana sukar numfashi kamar zai yanke, ya karaso a hankali, kafafunsa kamar an daure su
ya durƙusa a gaban kabarin, ya dafa ƙasa da hannayensa biyu cikin rawar murya ya fara addu'a:
"Ya Allah, ka gafarta wa Halima... Ka sanyata cikin Aljannah tayi ƙoƙari ta zauna da kowa da mutunci ta sha wahala ta mutu cikin rashin adalci. Allah ka mayar mata da jin daɗin da duniya ta hana ta."
"Allah ka haɗa zuciyata da ita a lahira idan babu haduwa a duniya."
Yana cikin addu'a sai hawayensa suka fara gangarowa ba tare da ya lura ba.
Kamar yaro ƙarami ya fashe da kuka mai sauti, yana jijjiga kansa da kafadunsa.
mai karatu da kansa sai ya ji zuciyarsa na karyewa — hawaye na sauka daga idonsa.
Domin kuka ne na gaskiya, na azaba da soyayya da ba ta sami cikar burinta ba.
Abdullahi ya zauna a ƙasa har rana ta fara faduwa.
Iska mai kaɗawa tana motsa ganyen kabari.
Daga nan sai ya ɗaga kansa sama, yana kallon sararin samaniya da idon da ya riga ya ƙumbura, yana faɗin cikin muryar da ta rame:
"Halima... zaki kasance a zuciyata har abada."
"kaddarata ta jefa ni nesa da ke, amma soyayyarki za ta kasance kamar numfashina."
"Allah ya haɗa mu a wuri mafi alheri."
Daga nan ya tashi da ƙyar, yana tafiya daga kabarin da matakin zuciya mai nauyi — ya bar soyayya a ƙasa, ya ɗauki kewa a zuciya.
Maryam ta yi shiru na ɗan lokaci, idanuwanta na cike da hawaye waɗanda suka zuba akai-akai. Ihsan ta dafa kafadarta cikin tausayawa—tun daga farkon labarin Halima ta kasa dafa kuka. John, da alama ba zai iya zamewa ba, ya gyada kai da ƙiyayya:
“Maryam, me irin labari ne wannan? mai tsuma zuciya, mai ban tausayi… me yasa ta mutu? me yasa ba su haɗu ba daga kallo na biyu suka rabu?”
Yazid kuma, wanda zuciyarsa ta yi sanyi ganin halin da ƴan masarautarsu suka tsinci kansu, sai ya sauke ajiyar zuciya, ya ce:
“Na yi tunanin zaki ba mu labarin da zai ƙarfafa mana zuciya amma sai gashi kin ba mu labarin da ya tabbatar mana: ba kowane buri ne a duniya zai taɓa cika yadda muke so ba.”
"Ƴan uwa na matafiya "suka kalle juna Gaskiya ce: a duniyar marubuta da ’yan wasan kwaikwayo, za a samo labarin da ya haɗa auren jarumai har su cika buri amma a zahiri akwai ƙaddara a soyayya—ba duk buri ne ke cika ba. anan sai Maryam ta miƙa ɗan gajeren labari na gaba, na Ummi:
“Ummi maƙobchiyar mu, tun tana yarinya take soyayya da ɗan uwanta. , sun yi rayuwar ƙauna mai ƙarfi ƙaddara bai amince ta aure saba nan ta aure wani daban amma mijinta ya sake ta, ya ci gaba da rayuwarsa ta chigaba da jimammen zawarci duk da haka, soyayyarsu ta ƙarfafa su na shekaru , suka sake ƙulla amana da alkawarin aure …
Amman kash ƙaddara bata amince ba Allah bai yardar musu ba nan aka haramta mata auren sa yanzu ta kuma yin wani aure sun zaɓi ɗaya a zuciyarsu, sun ƙebewa junansu ƙauna ta musamman wannan labarin na gaske ne—ba don jin daɗi ba, amma domin mu gane: soyayya na da ƙaddara, kuma ba koyaushe ake samun ƙarshe mai daɗi ba.”
sn kasance cikin shiru da tunani, kowa na jin wannan sabuwar hanyar rayuwa—ta ƙauna da raɗaɗi
BACK TO STORY
zamu chigaba da labarin matafiya guda biyar Maryam ta bamu labarin HALIMATU SADIYA gaskiya ne kaina wannan page ya sani hawaye tabbass soyayya gaskiya ne kuma ba kowane soyayyar bace cikakkiyar.
Ihsan ta bamu labarin Princeces Rahilat
zamu chigaba da tafiya daga Egypt har Dubai ko da ƙafa ne fans ku shirya wannan shine karshen Bayan wata book one
sai mun haɗu a kashi na biyu
********
Alhamdullah
Narnah ƙanwar soja ✍️
https://chat.whatsapp.com/FGzLF7OIMEv3GH7wxkyp0p
🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
Book two
BY
NARNAH KANWAR SOJA
💫ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION 💫
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star
Page 25 / 26
Ganin abun da ya ƙifta kamar aljani ba ƙaramin razanu yayi ba nan suka tsorata da chanza hanya gudun faruwar wata matsalar
suna ci gaba da ja da ƙyar cikin wutar sahara, ƙafafunsu sun kumbura, leɓunsu sun bushe sun fashe saboda ƙishirwa.
Ihsan na karkarwa a hannunsu kamar ganyen da iska ke bubbugawa.
Yazid ya ɗora kanta a kafadarsa, hawaye suna gangarowa daga idonsa, yana faɗin:
" ke ƙara juriya, Ihsan... ki tsaya mana Ihsan... muna nan kusa don Allah kar ki rufe idonki..."
Amma Ihsan ba ta iya magana sai faman lumshe ido take yi, kamar wacce rai ke shirin ficewa daga jikinta.
fuskarta ta juya launin toka, ga zufa mai sanyi na keto mata.
Maryam da John sun tsaya daga baya suna kallo, jikinsu yana tsuma da tsoro
Maryam ta rushe da kuka tana roƙon Allah:
"Ya Allah! Kada ka ɗauke ta! ka taimake mu! Ya Allah... mun yi kuskure amma muna neman rahamarka!"
suna haka ne sai can sun hangi wani ƙaramar motar sahara mai tsawo a nesa kamar mafarki Yazid da karfi ya ɗaga Ihsan a bayansa yana gudu da ita duk da raɗaɗin ƙafarsa. Ado da John suka bi da gudu suna kiran taimako.
Amma duk inda suka nufo su ne kaɗai a cikin dutsen yashi, babu wanda ke jin ihunsu.
motar ta tsaya nesa, tamkar ta hango su... ta kuma juya ta tafi sukayi tsaye a gun, suka faɗi saman yashi kamar duniya ta tsaya.
wani irin ciwon zuciya ne ya cika su.
Ihsan ta lumshe idonta gaba ɗaya tana fidda wani irin sassanyar numfashi kamar wanda ke bankwana da duniya.
Ado ya girgiza ta yana kuka "Ihsan! Don Allah ki bude idonki! Ki dubemu! bamu isa ki mutu a hannunmu ba!" John ya dafa kafaɗarsa yana girgiza kansa cikin kuka "bari ta huta... ta gaji sosai..."
Maryam ta rushe da kuka ta faɗa ƙasa tana faɗin:
"mun rasa ta! mun rasa Ihsan!! Allah ua karɓi ranmu cikin imani !!"
Zuciyar Yazid ta cika da ƙunci yayi azamar daga hannunsa sama, yana roƙon Allah cikin karfi a lokacin ne kuma daga nesa suka hangi wani ƙaramar kungiyar masu agaji masu mashin — suna zuwa da sauri kamar iska!
Shin za su iso kafin Ihsan ta mutu?
ku kuwa sun makara har abada?
✨ BAYAN WATA ✨
Girgizar yashi na sahara tana ci gaba da rufe su kamar ana binne su da ruwan yashi.
rana ta narka musu wuta kamar ana soyasu a cikin kwanon girki.
Ihsan ta zama kaman wacce ta rasa rai gaba ɗaya hannunta ya sakko daga kafaɗar Yazid, ta rame, tamkar reshen bishiya da iska ta kifar.