x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - BAYAN WATA

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 71166 words

Category: Love Stories

Views 138

04 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ta faɗi ƙasa ta riƙe ƙafafun Ihsan tana faɗin:
"Allah! Allah ka karɓi ranmu gaba ɗaya! kada ka bar mu muna kallon juna muna mutuwa a hankali!"
wani mugun guguwa ya taso daga gabas, yana kawo yashi mai ƙona ido.
Cikin idonsu, suna gani ne kamar wani haske yana fitowa daga bayan saharar.
amma idon su ya kasa tantance ko agaji ne ko mutuwa ce da ta zo daukarsu.
Sun ji ƙarar mota da sauti irin na mashin — da dukan karfi kamar ana fafatawa da lokaci.
Yazid ya ta da kansa sama yana kiran:
"Munananan!! taimako!!! ku taimaka mana!!! akwai mara lafiya!! ku taimaka mana!!"
Motar ta tsaya da daddare kamar an tsaya tsaye da lokaci.
mutum biyu suka fito cikin rigunan masu agaji, suna tsala gudu zuwa gare su.
dayan ya durƙusa a jikin Ihsan, ya sa hannu yana duba numfashinta sai ya girgiza kai da sauri."Quick! bring the kit! she's in critical condition!!" ya faɗa da sauri da turanci mai nauyi.
John da Ado suka tsuguna suna ta kiran Ihsan da hawaye a idonsu.
Maryam kuwa ta riƙe hannunta tana ta kuka tana faɗin:
"Ihsan... ki dawo... don Allah... kar ki bar mu!"

An jefa su cikin wata ƙaramar mota — da gudu suka nufi wani wuri mai nisa.
Kowanne daga cikinsu na jin zuciyarsa tana faɗuwa kamar ana yanke igiyar rayuwa daga jikinsu yayin da suka shiga mota, Yazid ya riƙe hannun Ihsan yana kuka yana faɗin:
"Ki tsaya mana Ihsan! don Allah ki zauna! Ki zauna har mu kai ki wuri lafiya..."



Amma Ihsan kamar wata ran da ke ƙarewa, kawai ta motsa baki kadan ta furta wani abu maras karfi: "Yazid... ka yafe min... idan na tafi... ku cika burinmu......"



Motar ta yi ta fizgar da gudu, taya tana huda yashi kamar wata gungurawa cikin ruwan teku a cikin motar, Maryam ta kama hannun Ihsan gam kuka kawai take, hawaye yana zuba kamar an ballo buta.

Yazid yana rububin addu'a a zuciyarsa, yana karanta duk addu'o'in da ya iya.
Ado ya sunkuyar da kai yana faman kiran "Ya Allah! Ya Allah!".
John kuwa ya zamanto gum, shi kadai yana rarrafe a bayan motar, idonsa ya zama jajur kamar wanda aka shayar da hawaye.

Bayan tafiyar kusan rabin sa'a cikin saharar mai zabga wuta, suka isa wani sansanin agaji.
wani tsohon sansani ne, wanda ƙungiyoyi masu taimako ke amfani da shi a bakin iyakar sahara da Isra'ila.

Cikin gaggawa aka kwaso Ihsan da gadonta mai ɗaure da hannu, suka nufi ɗakin tiyata.
an duba numfashinta, zuciyarta, suka saka mata ruwan da ake ta tsinkayar numfashi.

Maryam, Yazid, John da Ado an zaunar da su a wani ƙaramin daki mai sanyi, a kan katifu na roba una kallon juna cikin shiru, dukka kowa na jin tamkar rayuwarsa na karyewa.

Kusan awa guda suka zauna cikin wannan matsanancin yanayi na shiru da damuwa — har sai da wani likita mai dogon hanci da farin fata ya fito yana daure da safar hannu, yana share gumin goshinsa.
ya tsaya a gabansu sannan ya dafa kafada Yazid cikin tausayi, ya ce da su da karamin murya:
"She's alive... but very weak very... very weak. She needs prayers and strong heart."
"ta rayu, amma jikinta yana da rauni ƙwarai. Sai da addu'a da ƙarfan zuciya." gaban su ya faɗi gaba ɗaya.
Yazid ya fashe da kuka kamar karamin yaro.
Maryam ta rusuna ta fasa da kuka mai ƙarfi, tana ambaton sunan Ihsan kamar wacce ta rasa komai.
John ya shafa kansa da hannu biyu, yana jin kamar duniya ta tsaya.
Ado kuwa ya dafa bango, yana fitar da iska mai zafi daga zuciyarsa.
bayan wasu awanni, suka sami damar shiga dakin da aka kwantar da Ihsan.
Idonta a lumshe, numfashinta a sannu-sannu kamar kyandir da wuta ke ƙarewa.
Tana sanye da kayan lafiya masu tsafta, an ɗaura mata bandeji a wurin da macijin ya sare ƙafarta.

Maryam ta durƙusa kusa da ita tana kuka.
Yazid ya riko hannunta yana kuka a bayyane.

Ado da John suna gefen gadon, suna addu'a cikin harshen su.

Lokacin nan, Yazid ya matso kusa da kunnenta yana faɗin da kukan zuciya:
"Ihsan... kin ce burinki mu tsaya tare... kin ce mu cika mafarkinmu... wallahi bazan bari ki mutu ba! wallahi sai mun kai ki Dubai... sai kin huta... sai kin cika burinki...!"

Sai hawaye suka kwace daga idon Ihsan, duk da baccin da take yi — karamar murya kawai ta fito daga bakinta:
"Yazid... Allah ya saka... da alkairi..."
Sai ta sake lumshe idonta da ƙarfi.
Jikinta yayi sanyi, har suka dinga firgita ko numfashinta ya tsaya



Bayan kwana biyu da ciwo ihsan ta fara samun lafiya sosai domin kumburin ƙafarta yayi sauki hankalin ta ya fara dawowa jikin ta da taimakon ƴan uwan ta musamman Yazid wanda duk cikin su ya fisu tausayi da ban dariya shi kuwa nasani duk lokacin da aka samu matsala tabbas yana taimakawa da barkwanci sa kamar dai koyaushe Ihsan na zaune sun zagaye ta nan suka fahimci wanan filin ba gun tsaro bane domin anan tafka wasu ayyukan sirri ne tsakanin border Jordan da Ethiopia ana tafka ɓarna a kowane lokaci sojojin na iya kawo musu hari a hankali Ado yace " kafin ke ƙara samun lafiya kwana biyu zamu bar gun nan ana safaffarar kwayoyi ko matafiya ne a kowane time bamu da tsaro ammann ku kwantar da hankali ko bare na baku labarin wani masarautar mayaƙa ta zakkar da...".

Bai gama magana ba Yazid ya matso " ahh haba ne fa nagama shirri zan baku labarin AlJANNIN SAJIDA idan nagama wani lokacin sai ka bayar da naka mu saurarra "
cikin hasala suka fara chachakar kansu akan wazai fara bada labarin Ihsan da tai shiru tana kallon su cikin sha'awa da burgewa nan ta ɗaura da cewa " Ado tunda kaine babba kawai ka haƙura ka barshi next time sai ka bamu " Maryam ta amsa da cewa " kasan Yazid da rigima tsiyar" duk dariya sukaye nan John yace " Yazid filli domin ka ina matukar son labarun aljannu Amman ka tabbatar ba zasu zo mana a Bachi ba duk suka nitsu cikin kulawa da juna da samun nitsuwa Yazid ya ɗaura da cewa
" Kar kuyi mamaki wanan Labarin nawa zan gayyamu ku tamkar labarin nawa ne ma'ana zanyi amfani da salo akaina kuma ina tabbatar muku bashi da tsawo domin dai bai kai sauran labarai da ya gabata ba '".




Lokaci yayi da Yazid zai bamu labarin AlJANNIN SAJIDA labari ne cikin labari ina fatan zamu chigaba da tafiya cikin kulawar ku

let's go
Narnah ƙanwar soja ✍️









🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
Book two

BY

NARNAH KANWAR SOJA

💫ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION 💫



SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star




Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin posting kullum ba ,
mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya
show me some love guy's 🩷

بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وسلم


26 / 27

Rayuwa tana da ɗanɗano kala-kala wani lokacin kana cikin dariya amma zuciyar ka na kuka, wani lokaci kuma kana cikin shiru ne, amma ranka yana tafasa da ruɗani.

Suna na Ishaq ne matashi ne mai matsakaici tsayi da kyau nagarta baƙar fata gari ne A ranar Lahadin nan ne wata ƙawarmu a makaranta, Sajida budurwa ce mai jini a jika a ƙalla tana da shekaru goma sha takwas fara ce fatt kyakkyawar yarinya kowa ya santa da suna baby Sajida ta gayyace mu zuwa bikin zagayowar ranar haihuwar ta ban yi wata-wata ba, na shirya cikin shigar ƙananan kaya wanda suka ƙara min kyau da nagarta ina cikin farin ciki da zuwan wanan ranar domin zamu haɗu da abokan makarantar mu na ɗauki mota na fara ɗauko abokaina guda biyu: Ameer da Abdul




“Lafiya lau,” na faɗi a zuciyata lokacin da muka ƙaraso bakin gidan Sajida mun zo da ɗan jinkiri, domin wani abu ya ɗan tsaida mu a hanya amma da alama ba mu makara da yawa ba, domin kowa yana nan, kuma taron yana da ɗimauta.

tsoffin fuska da sabbi, 'yan makaranta da 'yan unguwa, iyaye da ɗangi komai yana nan kamar ɗaurin aure idanun mutane sun zuba inda za a yanka cake, amma ban gane me ake jira ba har sai da Sajida ta nufe mu da gudu.

“Lalle da babban baƙo!” ta faɗi hakan tana saki murmushi murmushin da na ji tamkar wata ƙaƙƙarfar ƙugiya ce ta ja zuciyata na tsaya cak ina kallonta, sai kuma na ji kaina na mayar da mata daidai murmushin da bata taɓa gani daga gareni ba.


Sajida kyakkyawar yarinya ce don kowa ƙon wanda ya rasa Allah ya zuba mata hasken idano tamkar farin wata tsayawar fari ga cikakken tsarin halittar jiki tabbas idan tayi murmushi ko maƙiyanta sai ya tsaya kallon halittar fuskanta

“Ina son mu yanka tare cake, kai ne babban baƙo kuma aboki na na musamman ,” ta faɗi hakan a cikin kasalalliyar murya da bata da karyatawa na waiwaya, idona ya haɗa daAbban ta wanda ya girgiza kai alamar amincewa haka nan Umma ta murmushi kawai take yi Abdul da Ameer kuwa sai dariya suke min.

Ban san ya akayi ba, sai dai na tsinci kaina da hannu ɗaya na rike wuƙa, ɗaya kuma hannunta muna tare yankan cake shewar jama’a ta kaure, liƙi ya fara kwaranya kamar ruwan sama.
Wani abu ya faɗa zuciyata: dhin wani abu ke faruwa a zahiri ne, ko kuwa mafarki ne kawai nake? domin a lokacin, hankali na ya riga ya fita daga jikina.

**

Bayan an ci an sha, lokacin da dare ya fara ruruwa ne na ce wa Sajida muna shirin tafiya. amma ita kuma tace, “A'a, sai munje gida ku huta.” na ce: “gidanmu zamu huta mana.” Sai Abdul yayi dariya yace: “kai Bilal, idan kaga gida irin nasu, baza ka ce a tafiya ba.”
Gidan ya fito kamar aljanna haske ke fita daga ko ina, kwalliyar da ba a saba gani ba. muka shiga muka zama kamar 'yan ƙauye, duk inda ido ya sauka sai jin kaɗa da ban mamaki. aka kawo mana abinci irin na manya, drinks iri-iri — wato lallai ba wargi ba ne wannan gidan.

Bayan mun sha mun koshi, na faɗa wa Sajida cewa muna son tafiya. Tace “to,” sannan ta kira Abbanta domin mu yi sallama. Abban Sajida ya ce, “dama ina son muyi magana da kai, amma yanzu dare yayi. sai ka zo wata rana.”
Yace: “kin basu kyautar da nace?” tace: “Na saka mai gadi ya saka musu a boot.” muka ce “nagode” muka fito.

Muna fita, Sajida ta rako mu har mota, tace: “Kyautar na ciki, kowa ɗaya.” muna tafiya sai Abdul yace: “Wallahi dole a duba kyautar nan.”

Ya buɗe boot — muka ga jaka cike da gwalagwalai da kuɗi dollars ne da wasu kuɗaɗe da ban taɓa gani ba.

Zuciyata tayi wani irin nishi, wata damuwa ta fara girgiza ruhina meyasa yasa irin wannan kyauta? me nake nufi a gare su?
a haka muka bar maganar a tsakanin mu da alkawarin gobe zamu kuma gidan su Sajida mu mayar musu da dukiyar su nan na ajiye Ameer da Abdul a gidan su .
**

Ina kan hanyata gida lokacin da motata ta tsaya chak wurin duhu ne, babu kowa na fito na duba fetur akwai nayi ƙoƙarin tada motar taki tashi kamar wasa.
Ina cikin ƙoƙari na kira wani daga abokaina kawai na juya, na hango Sajida a cikin mota. tana min murmushi , da sauri na rintsa ido na domin wanan gizo gizo da take min ya fita a kan ido na , sai dai ganin abun nakiye da gaske itace
na rufe mota da sauri na fita zan gudu — na juyo, na same ta a gabana tana nan, murmushi kawai takeyi. wani murmushi ne mai saka zuciya rawa...

Ina juya motar, kawai na ganta a mirror tana tsaye a bayan mota sai na ji numfashina ya tsaya... duhu ya mamaye komai.

Umma na tana gefena, Ameer da Abdul suna nan zuciya ta kamar an watsa mata ruwan sanyi.
“me ya faru dani?” na tambaya da rauni.

Abdul yace: “hatsari kayi. wasu suka kira mu a daren jiya amma fa, abin mamaki — kai kaɗai muka tarar a wurin...”
Umma na tace: “Sajida ta kira tace a maka ya jiki...”

*to, me Sajida ke nufi? Wacece ita a zahiri? kuma me wannan kyauta ke nufi?


" Bamuga mutanan da suka kira wayar ba sannan kuma number ɗin da aka kirani da ita private number ce ballantana mu kira muyi musu godiya, umm kuma Sajida tace ayi maka jiki kafin su zo ita da iyayenta ,wallahi , yarinyar hankalinta ya tashi jin halin da kake ciki, sai kuka take yi."

Fadar sunan Sajida da Ameer yayi ya sanya na tuna da abin da ya faru da ni a wannan dare. Na faɗawa Ameer dan Allah ya kira Sajida ya faɗamata cewa na sami sauki, kar ta zo.

Cikin rashin fahimta, Ameer, Umma sukace, "Haba Bilal, meyasa zakace haka, bayan kuma kana kwance a asibiti? Aikam yakamata tazo domin kasani cewa hankalinta bazai ta6a kwanciya ba muddun batasan halin da kake ciki ba." Nace, "Umma, nifa wallahi, indai sai Sajida tazo asibitin nan ne to a kira likita ya sallameni, gara nayi jinyata a gida." Umma tace, "to, wai maye matsalar ne?" nace, "Babu komai."

Nan Ameer ya kira number Sajida, amma abin mamaki, wayanta a kashe, wanda tunda nake da ita ban ta6a ganin wayarta babu chaji ba. maye mai zaisa wayanta a kashe? a zuciyata nace, "Lallai akwai abinda yake shirin faruwa."

Na juya na kwanta, ina tunanin shin yanzu idan Sajida tazo nan da wanne irin siffa zatazo kuma da wanne kudiri zatazo?

Drip ɗin da aka sanyamin ya ƙare, hakan ya sanya Ameer ya kira doctor domin ya sakamin wani , likita tana shigowa tayi sallama, muryan Sajida naji hakan ya sanya na juyo da sauri kawai nayi arba da Sajida cikin kayan likitoci.

Idanuwana suka zaro, zuciyata ta buga da ƙarfi duk da ciwon da yake jikina, na zabura na nufi kofa a guje. Ameer da Umma suka kamoni suna lafiya!!! lafiya!!! lafiya!!! nikam inata buɗe baki amma nakasa magana inata nuna Sajida da hannu. Umma tace, "Likita ce fah, nikam Sajida kawai nake gani."

Tanata matsowa kusa da ni, hakan ya sanya na suma. Abinda ya tayarwa Umma hankali matuka, ta fashe da kuka tana cewa, "Ɗana Sameer , Allah baka lafiya, Allah yasa ba ta6in hankali ka samu ba."

Bayan na suma ne sannan Sajida da iyayenta suka zo asibitin sun gaisa da Umma, sannan ta faɗamusu cewa anyimin alluran barci ne saboda na sami hutu sai zuwa dare zan farka.

Sajida ta bukaci cewa ita iyayenta subarta a asibitin har sai na farko taga halin da nake ciki, sannan zata tafi idan ta kama ko kwana zatayi ban farko daga dogon sumar da nayi ba sai 12:45 am. Ai kam ina farkawa, nayi tozali da fuskan Sajida, tanata kallona, fuskarta cike da hawa.

Inayin arba da ita na ƙwalla wani ihu mai razanarwa, hakan ya sanya Umma ta farka a tsorace, itama kanta Sajidar tayi zunbur kamar zata ruga. Umma tace, "meya sameka?"

Abin mamaki a wannan karon bakina ya buɗe, ina iyayin magana amma sai nayiwa Umma karyar cewa, "Mafarki nayi, wasu mutane suna bina zasu kasheni." Umma tace, "ai mafarki ba gaskiya bane, yanzu kayi addu'a ka koma ka kwanta."

Washegari, Sajida taje gida ta kawomana breakfast mai rai da lafiya, mukaci nikam, itace ma take bani a baki. Haka ta dinga dawainiya da ni har kwana 12 tukunna aka sallame ni, muka koma gida.

A daren ranar da muka koma gida misalin 1:00 am, hadari ya taso sosai, anata walkiya da tsawa mai ƙarfin gaske. kawai sai aka ɗauke NEPA, sai naji kofar ɗakina tana buɗewa tamkar wani ne zai shigo cikin ɗakin. a tsorace nace, "waye? shiru shiru?"




Na laluba wayana domin haskawa, nagani ina ɗauko wayar na kunna fitila, sai naga Sajida a gefen gado kusa da ni. 6angaren hagu na juya 6angaren dama, nasake ganinta, na ƙwalla uban ihu, nayi tsalle na sauka daga gadon, na nufu kofar ɗakin da nufin na fita na ruga wurin Umma.

Kofar ɗakin ta kulle, sai ji nayi wata murya tare da amsa kuwwa, tana cewa, "haba masoyi, ni kake gudu, nice fah, Sajida, Sajida, Sajida."

Kawai naga ta zama kusan kashi goma ko ina a bangon ɗakin, itace wata tana kiran sunana, wata tana kiran nice Sajida, wata kuma tana cewa, "Ka rabi da Sajida domin kuwa matar sarkin mu ce, hhhh hhhh hhhh." Jinayi kaina yana juyawa, naga ƙofa ta buɗe, a guje na nufin kofar da nufin nabar ɗakin, kawai sai naga wata mace da fararen kaya, babu kai a jikinta kuma ita bata sama bata ƙasa take na faɗi ƙasa a sume.







Iskan da ke kadawa ne gami da sanyi suka sanya na farka daga sumar da nayi a hankali na buɗe idanuwana domin zuciyata cike take da fargabar zan sake ganin wannan hallita.

Abin mamaki a wannan karon banga komai ba, da ƙyar na samu na mike a hakanma ina dafa bango domin a wannan lokacin jikina babu ƙarfi haka na koma cikin ɗakina na fasa zuwa ɗakin Umma na domin bana son hankalinta ya tashi idan tasan halin da nake ciki.

na dauki wayana ina duba time sai naga ashe har 2:00, nayi addu'a na tofa ko ina sannan na kwanta zuciyata cike fargaba.

Bansan lokacin da barci ya sace niba, jinayi ana tashina Ishaq ka tashi kayi sallah yau kam wanne irin barci ne kakeyi haka? a hankali na buɗe idanuwa na "Umma" nagani tace yau kam wanne irin barci kakeyi har rana ya fito bakayi sallar asubahi ba.

"Umma" idan kayi sallar sai ka fito ga breakfast na haɗamaka" , ta juya ta fita haka na tashi nayi sallah sannan nayi brush sannan na fito mukayi breakfast sannan nayi mata sallama na wuce kasuwa.

Bayan na shiga mota na fara tafiya jinayi wayana tana ringing, ina dubawa kiran SAJIDA nagani take jikina ya fara karkarwa tamkar wanda ya fito cikin ruwan kankara, wuri na samu nayi packing sannan na fara tunanin shin na daga wayar ko a'a.

Haka dai nayi ta maza zuciyata tana dukan uku-uku na daga wayar, muryar mahaifin sajida naji yacemin" yaya jikin
End Ads