Sai murya mai rauni daga cikin ɗaki:
“Kayi tafiyarka Najeeb babu wani abu da ya rage tsakaninmu.”
Shiru sai dai a zuciyar ta, Iman ba ta iya kwantar da ruwan da ke motsa a kirjinta ba. bai ce uffan ba — ya bar kofar a hankali.
Ita kuma ta zauna kusa da gadonta, tana matse tawul ɗin jikinta, tana kallon hular gashinta da ke gefen madubi, tana tunanin yadda zuciya ke da rauni fiye da fata.
Iman ta juya da sauri, tana ƙoƙarin buya, amma ruwan da ke ratsawar jikinta da tawul ɗaya ya hana ta daidaituwa. Sai wani yatsin ƙafarta ya kwace...
Wuffff!
Kafin ta faɗi — hannunsa ya kama ta. Ya tallabe ta da ƙarfi, jikinta ya sauka daidai a ƙirjinsa, inda fuskarsu ta gogar juna.
Shiru...
Numfashinsu na haɗuwa, kamar ana karanta sirrin zuciya a cikin iska mai dumi.
Gashinta mai ɗumi da kamshin sabulu ya rataya a gefen fuskarsa, yana bin ƙamshi kamar furanni masu tsiro bayan ruwan sama.
Idanunta biyu sun lumshe, na shi kuma suna kallonta — a tare da mamaki da al'ajabi.
“Iman…” ya ce da ƙasa-ƙasar murya, kalmomin da suka fita daga cikin zuciyarsa kamar kirari.
“Na…na faɗi,” ta ce a hankali, tana juyar da kanta a hankali cikin kunya.
Ya jinjina kai “Na kamaki ne... ba don na shirya ba, sai don zuciyata ta kasa bari ki faɗi.”
Zuciyarta na dukan wani irin bugun da ya saba da kwanciyar hankali. Ya lumshe ido, ya dan ja numfashi — kamar yana gasa da zuciyarsa ta gaskiya da wuta.
“Ki yarda da ni Iman... Ina sonki ba son da ya zo da ido ba — son da ya fara da tsoro, ya girma da ƙauna, kuma yanzu ya zama imanina.”
Ta ɗago kanta da ɗan sauri, tana kallonsa.
sai ya janye hannunsa cikin nutsuwa da ladabi “Ina jiran lokacin da zaki so na... da zuciyarki. Amma har yanzu — bari na tsaya a gefe.”
Ya juyawa ƙofar baya yana tafiya, amma a karon nan, ita ce ta kalla bayansa.
Kafin ya fice, ta ce cikin siririyar murya:
“ba zan manta wannan rana ba.”
Ya tsaya kadan, ya dan lumshe ido. Sannan ya fice Ƙofa ta rufe, zuciya ta buɗe.
Iman ta zauna a gefen gadonta, tana matse tawul ɗin jikinta, amma ba sanyi take ji ba — zuciyarta ce ke tafasa. A tsakankanin kaifin tunani da sanyin zuciya, kalaman Najeeb suna maimaituwa a kwakwalwarta kamar faifan waka mai raɗaɗi:
"Idan zan bar duniya... zan fi so na bar ta bayan kin ji gaskiyar zuciyata."
Ta runtse ido.
Ta tuna lokacin farko da suka haɗu, lokacin da zuciyarta ta fara dukan wani irin bugun da bata taɓa saninsa ba. Duk da girman laifin da ya taɓa aikatawa a baya, zuciyarta ta ƙi daina tuna shi da haske fiye da duhu.
Sai kawai...
Ƙofar ta bude.
Iman na zaune a bakin gado, lulluɓe da dogon veil mai launin zinariya, amma ba zuciyarta bace da launin farin ciki ta rasa yadda zata warware duniyar da take ciki — soyayya, kunya, da wani abu da ya fi ƙarfi da kalmomi.
Kallon da ya biyo bayanta a jiya har yanzu yana ratsawa a kwakwalwarta. Murmushinsa, shigarsa, murya mai natsuwa... da hannunsa da ya riƙe ta a lokacin da zata faɗi.
Tunani ke nan har sai ga ƙaran takun sa na shigowa falo.
Najeeb.
Ya shigo cikin shigar jallabiya ta larabawa, farin karfi, gwanin burgewa, da hula mai ƙyalli a kansa. Fuskarsa ta shafa attar mai ƙamshi, gashinsa yana kwance a gefe, idanunsa kuwa su ne suka dawo da ita daga cikin tunani kamar an buɗe kofar sirri a zuciyarta.
Ta ɗan girgiza kai, tana maida hankali.
Ya ce da murya mai nutsuwa:
“Iman, lokaci ya yi muna shirye tafiya.”
Ta ɗan gyaɗa kai, tana ƙoƙarin ƙyale kallonsa, amma bai yiwu ba kallon da yake mata yanzu… shi ya fi duk wanda ya mata a baya girma da nauyi.
Ta miƙe tana kallon ƙasa, zuciyarta na rawa kamar rigar ruwa.
Suka kama hanya zuwa filin jirgi a cikin mota ana dariya da raha. Ihsan da Maryam a gaba, Ado da Munir a wata motar, sai su Najeeb da Yazid a motar su.
Iman na zaune kusa da Najeeb, amma sai da nisa — kamar tana jin ana karanta sirrinta.
A cikin jirgi, komai ya lafa. An zauna cikin nutsuwa. Ana cikin iska mai sanyi, ana kallon ƙasa daga sama.
Ta juya ta leƙa Najeeb da sauri, sai suka haɗa ido.
Bai ɗauke nashi ba.
Ita kam sai ta kauda nata, amma zuciyarta na ambato: “Wannan kallon, me yake nufi? Me yasa yaki sauka?”
Ta daure zuciyarta, ta kifa kai, amma numfashin zuciyarta na tafasa kamar ba jirgi suke ciki ba — kamar zuciya ce a gaban gobara.
An sauka.
Sun sauka lafiya a Dubai.
Wata babbar motar kirar Rolls-Royce Phantom ce ta karɓo su daga filin jirgi — sai wata bus mai zaman kansa don ɗaukar kayayyaki da sauran su.
Iman ta kalli birnin daga cikin gilashin motar. Hasken fitilu yana walƙiya kamar taurari sun gangaro duniya. Dukkan alamun birni mai wayewa da yalwar arziki ne — amma zuciyarta… zuciyarta ba fitilu take gani ba, kallon Najeeb ne kawai ke mata haske da duhu a lokaci guda.
Bayan mintuna talatin, suka isa.
Gidan ya tashi har sama:
Ginin bene ne na falon hawa biyu, fentin launin shunayya da zinariya, tare da fitilun chandelier masu launin blue crystal daga Austria. Kofar gidan ba ƙaramar ƙofa bace —
ta sarauta ce! A saman kofar, an sassaka sunan:
"Bayt Al-Hikmah — The House of Wisdom & Grace."
Falon shiga kuwa… babu inda za ka kalla ba tare da ka tsaya ba. Kushin Turkish, gilashi na Paris, shinfidar Morocco, bust of love carved in white marble — komai na nuna cewa Ado da Ihsan sun mallaki duniya da duniyar zuciya.
Wata sabuwar mace ta karɓi Iman, ta ce:
“Welcome, beautiful lady. Your room is this way…”
An kai Iman wani ɗaki da ya dace da sarauniyar larabawa. Gado mai launin milk gold, labule mai sheƙi, da jakuzi a wani sashe mai moonlight tiles. Ta tsaya tana kallon kanta a madubi, sai kuma taga Najeeb a baya.
“Iman,” ya ce da wata murya mai sanyi, “zaki iya hutawa yanzu. Amma bana tunanin zan iya hutawa idan har...”
Sai ya tsaya. Ita ma bata ce komai ba.
Zuciyarta sai harbawa take kamar ana bugunta da rawani.
Ya ɗan matso kusa “Na san akwai abinda ke yawo a zuciyarki, Iman. Amma ki sani — tun farko ba zato ba tsammani na faɗa tarkon da ba zan so kubuta ba...”
Ta juya a hankali, idanunta sun cika da soyayya da tsoro.
Ya matso. Kamar ba kowa a duniya sai su biyu.
Sai yayi murmushi yana faɗin:
“Jiya... lokacin da na tare ki daga faɗuwa, na fāɗa — a zuciyarki. Kuma har yanzu ban samu hanyar fita ba.”
Iman ta kauda kai, amma fuskarta na fashe da laushi da launin fatan so. Kafin ya ce wani abu, sai wata yarinyar gida ta shigo da ruwa mai sanyi da kunu, tace:
“Ma’am, dinner is ready. Everyone is at the table.”
Najeeb ya janye a hankali, yana kallonta har ya fita. Ita kuwa ta zube a jikin madubi, zuciyarta na bugun kalmarsa. “Na faɗa… kuma ban fita ba.”
Dinning Hall — Cikin Dare, Cikin Rabo
Wurin cin abinci kuwa wani sashe ne daban. Babban teburin marble mai siffar daraja, fitilu a sama kamar taurarin Burj Khalifa, abinci kuwa larabci da na Nigeria sun gauraya — hummus, lamb mandi, dankali spicy, tuwon shinkafa da miya.
Maryam da Munir, Ado da Ihsan, su Yazid da Najeeb da Iman — sun zauna cikin farin ciki da raha.
Amma idanun Iman da Najeeb… su kadai suka fi magana a ɗakin. Kallon da bai da kalma, murya da bai da lafazi.
Sai zuciya da zuciya ke karɓar saƙo.
Washegari da safe.
An shirya. An sa kaya masu kama da casual official. Iman na cikin wando mai siririyar fata da riga mai launin cream, gashinta a daure cikin salo na 'Elegant Bun', Najeeb kuma cikin farin shirt da bakar wando, sai turaren sa mai sanyi da gwaninta ya gama janye hankalinta.
Sun fito tare da Maryam, Munir, Ihsan da Ado. Motoci biyu suka nufi katafaren “Al-Manāra Travel Support Holdings”, wato Company ɗin da ke taimaka wa matafiya da kuma masu neman mafita daga wahalhalu irin su hijira, asara, da barazana.
AL-MANĀRA HOLDINGS — CIGABA DA JINƘAI
Ginin yana tsakiyar Dubai, kusa da Business Bay. An yi masa gini mai siffar fatauci da aiki — amma cikin aminci da kamala. Ko da suka sauka, wasu ma’aikata suka fito da gaisuwa da fara’a.
“Marhaban! Mr. Ado, Mrs. Ihsan! Welcome home!”
An yi musu jagora zuwa babban hall — inda hotunan matafiya biyar (Maryam, Munir, Ihsan, Ado da Yazid) suke rataye cikin manyan frame, suna wakiltar labarin gaske da azanci.
Najeeb da Iman na tafiya gefe guda.
A lokacin da ake gaisawa da shugabannin ma’aikata, Iman da Najeeb suka ɗan ja gefe suka tsaya a wani corridor wanda aka kawata da window masu kallon Emirates Tower.
Kamar daga sama aka saukar da nutsuwa — babu hayaniya, babu kururuwar birni. Sai numfashin juna kawai.
Najeeb ya ce da ita a hankali:
"Iman, na fahimci duniya ba ta da wani armashi idan babu wanda kake so a cikinta."
Ta kalle shi kamar tana ƙoƙarin musun kanta.
“Ka tabbata kuwa?” ta ce, idonta a rufe, muryarta na raɗa.
Ya matso kadan, ya kama hannunta cikin nata:
“A cikin wahala na rayuwa, Allah ya ajiye min ke a matsayin rahama kuma soyayyarki… tafi Dubai da duk daular duniya daraja a zuciyata.”
Ta fashe da murmushi, sai hawaye suka gangaro kadan.
“Na so ka tun farkon haduwarmu, Najeeb. Amma tsoro ne ya hanani furtawa.”
Sai suka rungume juna a hankali — hug mai cike da soyayyar gaskiya ba wani lallata ba.
Kamar komai ya tsaya sai su biyu.
Sai shiru sai bugun zuciya.
A wannan lokacin ne Ado ya leƙo daga gefe, sai ya kalli Maryam yana faɗin:
“Na ga hasken soyayya. Yau kam, mun cika alkawari — daga wahala zuwa farin ciki.”
An yi hoto tare a gaban ginin, tare da ɗaukar documentary short daga Iman, domin jaridar da take aiki da ita a Najeriya. Ta bayyana cewa yanzu Al-Manāra Holdings za ta buɗe reshe a Abuja domin taimakawa matafiya marasa galihu.
Iman ta juya ta ce:
“A duk inda mutum yake a duniya, akwai fata. Amma idan aka ba mutum ƙauna da dama — sai ya zama tauraro da kansa.”
Najeeb ya ce “Iman… ke tauraruwa ce da ba zata taɓa dushewa ba.”
DUBAI TO ABUJA
Bayan dawowa daga Dubai, su Najeeb da Iman da sauran iyalai sun huta a wani katafaren gida a Asokoro, Abuja — gidan Ihsan da Ado suka mallaka tun kafin tafiyarsu. Lokacin da aka shakata, sai suka shirya tafiya Kano domin cika wata alkawari da suka ɗauka tun lokacin da suka sha wahala.
Yazid ya mutu a hanya — mutuwar da ke ɗaya daga cikin manyan tabo da suka ɓata zuciyar su. Amma yanzu lokaci ne na fansa, na lada da alheri.
KANO – GIDAN YAZID FOUNDATION
Sun iso cikin manyan motocin girmamawa. Wani sabon katafaren gini da ke gabar kwanar Hadejia Road, an ɗora Foundation ɗin da sunan:
Yazid Foundation — Gida na Ƙauna da Taimako.
Cikin gidan marayu da dakunan kwana da nishaɗi.
Makarantar addini da boko mai girma da aka rubuta a saman kofar sa:
"Wannan gida ne na kyautatawa domin ladar rayuwar Yarima Yazid — wanda bai rayu ba amma ya bar daraja."
Maryam ta tsaya a bakin kofar masallacin da hawaye suka cika idonta. Munir ya riketa a hankali. Ihsan da Ado na tsaye gefensu, suna fuskantar sabuwar hanyar alheri.
A CIKIN MASALLACI
An gudanar da walimar saukar Alkur’ani daga yara marayu guda goma sha biyu da suka rigaya suka haddace., domin girmama sunan marigayin.
Najeeb da Iman sun zauna gefe a gaban masallaci. Lokacin addu’ar kabari, Iman ta saka ƙwalla cikin zuciya ta ce:
"Ya Allah, ka bawa Yarima Yazid mafaka mai albarka. Ka sanya wannan gida hujja mai haske gare shi."
Najeeb ya kama hannunta a hankali, ya ce:
"Yazid ba ya nan da jiki, amma ran mu cike yake da shi. Kuma wannan gida, wannan aiki, ya fi duk daular duniya."
a nan aka roƙi addu'a, aka karanta suratul Mulk, sannan aka watse da nutsuwa da tausayi.
Gida ya cika da yara marayu. Najeeb da Iman sun kafa wani shiri mai suna "Matafiya Cikin Ƙauna" wanda ke ba da tallafi da damar rayuwa ga marasa galihu da ‘yan gudun h
da ‘yan gudun hijira.
ALƘALAMIN NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️✍️
https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
🎇BAYAN WATA 🎇
( Beyouda ‘yan gudun hijira.
ALƘALAMIN NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️✍️ng the moon ).
SABON SALO
Labari da tsarawa
Narnah ƙanwar soja
( Sayeedan Adda )
*********
HIKIMATA ABIN ALFAHARI NA
Marubuciyya tana da damar halittar mutum ta kashe shi ta raya shi, tunda 'ƙirƙirar labari ne. ta haɗa masoya, ta wargaza soyayya tsakanin masoya.
*****""
Sadaukar wa littafin Bayan wata sabon salo Ga Abokina Mallam Najeeb wanan Sabon salo naka ne shi ke ɗauke da martabar sunanka thank you with your support 🙏
ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION 💫
Page 54 / 55
SECOND TO THE LAST PAGE
BARKA DA JUMA'ATU BABBAN RANA
Washegari bayan dawowa daga ziyarar kabari da buɗe gida, Maryam ta buƙaci su tafi wani wuri — wani wuri mai nauyi a zuciyarta, inda duk wasu damuwa da jin ƙasa suka fara a rayuwarta.
Su Munir da Iman da Najeeb da sauran ‘yan gida suka rakata cikin nutsuwa. Motoci suka nufi tsohuwar unguwar su Maryam, anguwa da yanzu lokaci ya sha kanta amma ƙuruciyar rayuwa ta Maryam ta tsaya a cikinta har yanzu.
Gidan da suka tsaya ba babba ba ne. Gida ne da duwatsu da tubali suka hau a kai, buhun shara ya makale a jikin bango, ruwan famfo na zubowa a gefe. Wani ƙaramin bishiya ya toshe rabin kofar gidan. Amma duk da haka, akwai ɗan ginin tarihi da ke bayyana cewa:
"Wannan gida na Maryam ce — iyayenta suka gina shi da hannu, da jinƙai da addu’a."
Maryam ta tsaya gaban ƙofar gida, tana kallon fatar bango da ke fallarwa kamar yana faɗin:
"Kin dawo, ‘yar gida. Mun kiraki shekaru talatin da suka wuce."
An shiga ciki. Duk da cewa gidan yana buƙatar gyara, amma yana cike da numfashin ƙuruciya
bango da aka daɗe ba a shafa ba, ɗakin da ta taɓa kwana a ciki tana kuka da yunwa, da kwandon da mahaifiyarta ke ajiyewa shinkafa. Maryam ta tsuguna a ɗaya daga cikin dakuna tana shafa ƙasa.
Munir ya tsaya yana kallonta. Iman ta kama hannunta tana kuka.
Maryam ta ce a hankali:
"Wannan ƙasa ce ta rayuwata. Duk duniya na zagaya, amma ina da iyaye da suka fara gina mini mafarki a nan — duk da ba su da komai sai kauna."
Motar Maryam ta tsaya a ƙofar tsohon gidan mahaifinta. Wata ƙaramar kofa ce amma har yanzu tana da ƙwanƙwasa da ke sa mutum ya dakata kafin shiga. Duk gidan yana da warin tarihi, ko ƙamshin ƙasa mai ɗumi da fatar mutane masu tawali’u.
Tana fita daga mota, sai zuciyarta ta ɗauki wani irin nauyi mai nauyi da sauƙi a lokaci guda.
“Baba…”
Kafin ta kai kofa, wani dattijo ya fito daga tsakar gida. Fatar jikinsa mai tsufa, kayan jikinsa daɗɗaɗɗu amma tsaftattu. Idanunsa suka sauka a kanta cikin mamaki da ƙanƙan da kai.
“Maryam?” ya furta da wata murya mai karkarwa, kamar wanda ya kira mafarki ya amsa masa.
Maryam ba ta iya jurewa ba. Ta yo guje kamar ƴar shekara goma, ta faɗa jikinsa tana fadin:
“Na dawo Baba… Na dawo daga duniyar da ta raba ni da ku.”
ya rungume ta, yana hawaye kamar karamin yaro.
“Ashe ke kike nan? Ashe haka kika wahala? Ashe auren tsoho ya mayar da ke arziki da sayar da raina? Maryam… na rasa ke tsawon shekaru talatin. Kamar yau aka yanke ni daga zuciya ke gafarta min tursasawa da na miji a baya .”
Daga cikin gida, sai ga wasu matasa guda uku sun fito da mace guda. Maza ukun ƙanninta ne — yara da suka tashi ba tare da cikakkiyar uwa da ta ci zarafinsu da azaba. Duk sun girma, amma zuciyarsu har yanzu da raunin rashin Maryam.
Maryam ta zuba musu ido. Ta fahimce su — kamar yadda take fahimtar wuta idan ta ga hayaki. Ta rungume su ɗaya bayan ɗaya tana kuka, tana cewa:
“Ku gafarceni. Na yi tafiya da ba zan iya bayani ba amma daga yau, zan zame muku uwa da ‘yar’uwa.”
Matar kuwa, ‘yar kishiyar da ta wahala da Maryam, ta tsaya gefe tana kallon su. Maryam ta matso kusa, ta kama hannunta da ƙyautatawa tana fadin:
“Kin sha wahala a nan, ba laifinki ba ne. Amma yanzu ba za mu sake rayuwa da ƙiyayya ba wannan gida zai koma gida na kowa da kowa.”
Maryam ta ce da mahaifinta:“Baba, daga yau wannan gida zai zama Cibiyar Azanci da Kyautata Rayuwa. Za mu gina masa dakin koyon sana’a, dakin karatu, Kuma za mu sanya sunan ka a ƙofar gidan."
Mahaifinta ya fashe da kuka yana fadin:
“Maryam, ke ce ƙarshen mafarki. Wannan mutunci ya fi na duniya.”
Munir da Iman da Najeeb da su Ado da Ihsan suna kallon abin cikin jin daɗi da girman zuciya. Duk suka yarda cewa gidan da aka barwa Maryam da hawaye, yanzu ta dawo da shi da alfahari.
Dukkan maƙwabtan tsohon unguwar Maryam sun fito don maraba da ita. Kamar ba ita ba ce da aka manta shekaru talatin da suka wuce. Da wuya a tantance tsakanin hawaye da murmushi a fuskar mutane, domin dawowar Maryam tamkar dawowar haske ce bayan duhun shekaru.
“Maryam, wannan gida har yanzu gida ne. Kuma yanzu mu ne za mu taimaka miki, ba ke kadai ba,” in ji wata tsohuwa da ke tsaye da kwanon tuwo a hannunta.
Wani dattijo ya kawo jakar shinkafa. Wata mace ta kawo masara. Sauran suka kawo barguna, kwanuka, da kayayyakin amfani. Wasu kuma suka bada ginin da za a dawo da su ciki su huta kafin tafiya.
“Wannan gari ba zai sake barinki ki fita da hawaye ba, Maryam,” cewar wani saurayi da ya taba kasancewa ɗan ƙaramin yaro lokacin Maryam tana da shekaru goma.
Maryam ta juyar da idonta zuwa danginta:
“zamu kwashe ku gabaɗaya zuwa Abuja. komai ya canza wannan gidan zai zauna a matsayin alamar juriya, amma zamu tafi domin a ji daɗi da walwala.”
Bayan makonni biyu a Abuja, inda suka samu nutsuwa da kwanciyar hankali, sai abubuwa suka ɗauki sabon salo. Iman, ƴar jarida ce mai kwazo wadda ta tattara tarihin tafiyar su biyar cikin littafi a kafar BBC Hausa, an shirya ƙaddamar da litattafin mai suna: