x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - BAYAN WATA

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 71166 words

Category: Love Stories

Views 140

04 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
naka" ? na amsa da " jiki kam yayi kyau tunda yanzu gashi har na fita kasuwa.

" Alhamdullah tunda yanzu kaga ka sami lafiya yau idan ka tashi daga kasuwar sai kazo gida mu tattauna maganar mu, ji nayi gabana ya faɗi zuciyata ta buga da ƙarfi kaina yamin nauyi domin naji ya ambaci zuwa gidansa, nayi shiru daga chan sai nace to Abba in sha Allah zan zo, amma yanzu da safe yakamata na zo saboda bana son yamma yamin ballantana kuma dare.

Ya amsa da shikenan sai ka zo, nikuwa haka na juya motana na nufin gidan su sajida jim kadan na isa, ina shiga na tarar an hadamin abinci iri-iri tamkar za'a tarbi wani babban basarake ko shugaban ƙasa.

Abba yamin izini da na zauna sannan yamin nuni da na fara cin abinci tukunna sai muyi magana, nayi breakfast kafin na fito na faɗawa "Abba ni yanzu a koshe nake, "haka dai Abba ya matsamin dole naci kadan daga cikin abincin.

Bayan na kammala sannan Abba ya tara iyallan yayi gyaran murya " nasan bakasan dalilin da yasanya nake nemanka ba"? , nace eh Abba gaskiya bansani ba sannan kuma zuciyata cike take da son jin abinda zaka fada."

" Ishaq na zauna nayi nazari gami da tunani ganin irin shakuwa da Aminanan taka da tausayin juna da yake tsakanin ka da Sajida. wanda yanzu har kun zama tamkar yaya da kanwa, to ne da Umma SAJIDA mun yanke wani hukunci.

Wanda zan fadamaka a yanzu amma kamin alkawarin cewa zaka kar6i abinda muka zo muku da shi domin kasan bazan cutar da ku ba".

Maganganun Abba sun sakani cikin rudani gami da wani dogon tunanin daban, shin maye Abba ya yanke a kanmu? Yanzu idan namar alkawari kuma ya faɗi abinda bazan iya cikawa ba fa.

Haka na faɗawa Abba cewa nayimaka alkawari domin bazan iya musu da maganarka ba 'Abba" domin kana bani kulawa tamkar uba agareni duk abinda uba zayyiwa Ɗansa kanamin bazan iya butulci agareka ba."





Abba yayi murmushi sannan yace Allah yamaka albarka, dama ba wani abu bane face ina son ka auri Sajida mikewa nayi zunbur tamkar wanda aka sanyawa shocking da lantarki muka hada ido da SAJIDA ta sakarmin wani tattausan murmushi sannan ta sunkui da kanta .

Abba yayi murmushi " zauna mana ai dama nasan dole zakaji mamaki gami da farin ciki marar musaltuwa amma kuma ba abin mamaki bane, duba da duk abinda sajida take so to muma muna son shi.

Yanzu ina son ka turo iyayenka domin muyi magana gemu da gemu bana son auren ya wuce 2 weeks," nikam tuni na fada cikin dogon tunani gami da damuwa wacce ta gagara 6oyuwa a fuskata.

Ganin damuwar da take kan fuskata 'Abba" yacemin kar ka damu domin duk dawainiyar auren ni zan dauka bana son ka kashe ko naira ɗaya, Allah sarki shi a tunaninsa wannan ne damuwa ta.

Nikam tunanin maganar aljanun nan ce ta faɗo a zuciyata da tunanin abinda zai faru da ni muddin akayi wannan auren, ni babban abinda yafi dawuna shin maye tsakanin "SAJIDA" da sarkin aljanu shin, aljanna ce ko bil'adama?




Tabbas kyawun ta ya kai yaja hankalin duk wani ɗa namiji sannan kwalliya tsafta gami da iya ado, ni kaina ina jin kaunarta a cikin zuciyata amma tsoron abinda zaije ya dowo shine a cikin raina.

" Ni zan wuce domin ina son na tafi kasuwa kar na makara " na faɗa masu mukayi sallama sannan na fito abin mamaki wannan karon batamin rakiya ba bayan na fito na wuce kasuwa.

Ban iya aikata komai ba a kasuwar sai tunanin na saka wancan na warware wancan hakadai har lokacin tashi yayi sannan na rufe shago na wuce gida.

Ina shiga gida Umma na tarar a falo tana karatu nikam sai na zauna na jirata har ta kammala sannan na faɗamata cewa ina son muyi magana, wacce magana ce wannan ɗana Umma tace ai da ka bari idan ka watsa ruwa sannan ka ci abinci ka huta sai muyi maganar.

" Aa idan da hali muyi maganar yanzu to shikenan ina saurarenka."

Na kwashe duk yadda mukayi da iyayen Sajida na faɗamata ALHAMDULILLAH "ummm" tace abinda na dade ina mafarki abinda na dade ina jira abinda na dade ina yiwa tanadi yau kam gashi Allah ya kawomu.

'Umma" tace yakai ɗana guda ɗaya tilo kasani cewa na Dade ina jiran wannan naga kayi aure domin ka zama cikakken mutum sannan naga jikana, lallai kam yau ranar farin ciki ce a garemu dan haka gobe tun safe zan tafi gidan kawunka Alh 'labaran"suje a tsayar da magana.

Nikam yaƙe ne yake bayyana a fuskana domin bana son Umma ta fahimci akwai wani wanda yake damuna, yanzu ka shiga ciki ka watsa ruwa sannan kazo mu ci abinci.

Bayan mun ci abinci mun kammala sannan mukayi fira da ita sosai tace " kasan fa ranar bikin nan naka duk da tsufana dole nayi rawa na chashe"

Duk da ina cikin damuwa bansan lokacin da dariya ta kamani ba gami da jin kunya, nace ummana gaskiya ina alfahari da ke kuma lallai ko bayan nayi aure bazan iya barinka ba dole gida ɗaya zamu zauna. "




Nan dai mukayi fira sosai har dare yayi sannan 'umma" ta wuce ɗakinta ta barni a falour nikam sai na dauka wayana ina buɗe data sakon sajida ne ya shigo wayana Kamar haka: Angaishi da autan samarin duniya ina fatan ka isa gida lafiya? gaskiya nayi sa'ar kasancewata zan zama mata a gareka burin da yadade a cikin zuciyata yau gashi Allah zai cikamin shi.

Duk da baka ta6a furtamin kalmar so ba amma sai dai naga hakan a cikin idanuwanka sannan naji hakan a cikin bugawar zuciyarka, Kamar yadda nima na gagara fadar hakan a gareka yau kam zan fada.

Ni 'sajida" Ina son ka ina kaunarka sonka ya riga yayi nisa a cikin zuciyata ta yadda bazan iya rageshi ba ballantana har na iya cireshi, dan Allah ina son ka zama garkuwa a gareni kazama uban 'ya'yana ka kasance tare da dani a kowanne irin yanayi, da wannan nake maka sallama masoyina bissalam ka kulamin da kanka.

Babu zato ba tsammani kwatsam sai naga wani sako ya shigo wayana Kamar haka: yakai bil'adama shin ashe bakaji jankunnan mu a gareka ba ashe taurin kai ne da kai.

Tabbas Auren SAJIDA a gareka tamkar tamkar ka sayi tikitin yin bankwana da farin ciki zaka kulla alaƙa da bala'i da masifu a rayuwarka, domin kuwa tun daga ranar da aka haifi Sajida" ta zama mata a gareni kuma nayi alkawarin babu wani bil'adama komai hatsabibanci shi da ya isa ya aureta take wayar tawa ta fara ci da wuta a tsorace nayi wurgi da ita ta window ɗin da yake a falon.

Lekawa nayi window ɗin ina hangen wayar a haka har ta ƙone kurmus sannan naga wannan tokar ta tana rikidawa ta zama wata siririya tamkar igiya sannan tana mikewa a hankali take naga ta zama wani siririn aljani mai siffar ban tsoro.

Wannan aljani yana da munin siffa kwarai da gaske idanuwansa jajaye ne tamkar garwashin wuta sanan ya wangame bakinsa yamin wata mahaukaciyar dariya yana dariya bakin nasa yana kara girma, sannan ya tsuke bakinsa ya murtuke fuska idan kaga fuskarsa saboda tsabar muni sai zuciyar mutum ta tashi har yayi amai sannan ya nunani da hannunsa wanda yake da wasu yatsu zaro zaro wanda duk iyakar kallon kurillar mutum bai isa ya irga adadin yawan yatsun wannan aljani ba.

Kunbunansa kuwa suna da tsayi sannan ga tsini tamkar karamar takobi, sannan wannan aljani ya gyara tsayuwa ya rike kugu yana kallona, nikam addu'a kawai kawai nakeyi a cikin zuciyata wani lokacin ma bansan maye nake karantawa ba saboda tasanin tsoro abinda yabani mamaki shine yin arba da wannan aljani amma zuciyata ta dake har haka.

Kwatsam sai gani nayi wannan aljani yayi wata girgiza sannan naga yanata chanja halitta daga Ƙarshe sai naga yazama guguwa wannan guguwa tayi sama tun ina kallonta har ta 6ace 6at jim kadan sai ganin nayi wayata ta faɗo a dai-dai wurin da wannan aljani ya tsaya, na kalli wayar nan sosai naga tabbas wayata tace wacce ta kama da wuta kuma abin mamaki babu abinda yasami wayar, tsoro ya hanani fita ballantana na iya daukar wayar.



STORY
BY
Iliyasu Falalu Lawal


WRITTEN
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA











https://chat.whatsapp.com/Bd1Zu1cwIO81A7rrATd4Cu




🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
Book two

BY

NARNAH KANWAR SOJA

💫ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION 💫



SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star


Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin posting kullum ba ,
mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya
show me some love guy's 🩷




بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وسلم


Page 28 / 29
18**5**2025





" Yakai masoyina abun alfahari na kuma uban 'ya'yana lallai yanzu haka ina cikin fargaba da tashin hankali wanda bazan iya musaltawa ba domin kuwa a yanzu haka nayi wani mummunan mafarki wanda hankalina ya tashi matuka duk da nasan cewa mafarki ba gaskiya bane amma hankalina ya gagara kwanciya zuciyata ta kasa samun sukuni dai-dai da second ɗaya.

Wannan dalilin ne yasa na kiraka a cikin wannan daren namaka kira babu adadi amma bakayi picking call nawa ba Hakan ne ya saka zuciyata ta sake karaya matuka bacci ya kaurace a idaniyata hankali ya gushe daga kwakwalwata nayi kokarin bare zuwa safiya ya gaggara
Dan Allah idan kaga wannan sakon nawa kamin reply domin tabbatar da lafiyarka, kasani cewa bazan iya barci ba idanuwana zasu kasance suna kan screen wayana har sai naga sakonka."




Babban abinda yabani mamaki dukkan abinda ya faru tsakanina da wannan aljani shine ta fadamin cewa tagani a mafarkinta sannan ta faɗamin cewa lallai idan bataga kirana ba ko sakona to gari yana wayewa zatazo har gidan mu da safe.




WASHEGARI
Ina gama karanta sakon kenan Horn ɗin mota naji a bakim gate a zuciyata nake fada kar dai yarinyar nan da gaske zuwa tayi. Lallai kam nasan ƙaramin abu ne a wurinta haka na fita nazo ina buɗe gate ba kowa na gani ba sai "sajida" tana ganina tayi wani lallusan murmushi nikam na mayar mata da yaƙe domin ni yanzu tsoronta nakeji matuka haka na buɗe gate sannan ta shigo ta gyara parking.

Na kai hannu zan buɗe mata marfin mota amma sai tace haba ba girmanka bane ai nice zanyi hakan a gareka, nace haba kekuwa ina girma ga mijin hajiya mijin gimbiya ai idan ina tare da ke to bana da wani girma face girmanki. Dan haka idan munyi aure ni zan zama driver a gareki, kukun ki, ɗan aiken ki, a taƙaice dai ni zan zama hadiminki.

Tayi murmushi tace kaikam kace zolaya ba kowa a gidan ne Sajida" ta fada naga kai ɗaya nagani kuma naji babu wani motsi a gidan eh nace domin "umma" ta fita kuma dama kin san mu biyu ne a gidan.

" Alhamdullah" Sajida ta fada yanzu sai mu shiga ciki muyi magana domin magana tana bukatan jin haka yasa zuciyata ta buga da ƙarfi idanuwana suka zaro naji tamkar andauki guduma an bugamin a kirjina, domin gani nake tamkar idan dai har muka shiga gidan nan da Sajida to lallai komai zai iya faruwa da ni.

Murya na tana rawa nace haba kekuwa kinga cikin gidan babu kowa bai kamata ace mu shiga mu kebe daga ni sai ke kinga mu ba mata da miji ba kuma Annabi {SAW} yace matukar mace da namiji zasu kebe ba muharraman juna to lallai shaidan zai kasan ce na ukun su kuma kinga mutane da zargi bana son wasu kananan maganun su dinga yawo a kanmu.

'Sajida" tayi murmushi sannan tamin wani irin kallo cikin alamun mamaki tace ashe baka yarda da tarbiyyar da iyayen mu suka bayar a kanmu ba ashe kana tunanin zamu iya cin amanar junan mu? cikin sanyin murya nace haba sajida ba haka nake nufi sam kafin nagama rufe tayi charaf tace to indai hakane mu shiga ciki muyi magana.

Tana gama fadan hakan ta kunna kai ta nufi cikin gidan tana murmushi ko waiwaye batayi, nikam cikin Alamun sanyin jiki da fargaba nabita a baya.





"Sajida" tana shiga ta nemi wuri ta zauna sannan nima na shigo nace to bari na kawomiki kayan breakfast tukunna, tace a'a nayi breakfast a gida tukunna na fito nace duk da haka to bari na ɗan kawomiki ko ruwa ne kinsan bakonka Annabinka "Sajida" tace au ashe kallon baƙuwa kakemin?

Nayi murmushi sannan na wanyance nace ba haka nake nufi haba ai ni da ke mun zama abu ɗaya kawai dai naga kin sha tafiya ne shiyasaka kuma ma kinga idan baki ci komai ba ai ba zanji daɗi ace kinzo har gidan mu baki ci komai baki sha komai ba. "Sajida" tace ni yanzu ba wannan ne damuwana ba nazo domin duban lafiyarka domin jiya nayi wani mummunan mafarki a kanka wai ma tukunna ina kasaka wayanka?.

Tun a lokacin da na farka daga wannan mummunan mafarki ban sake runtsawa ba hankalina bai kwanta har sai yanzu da nake tare da kai shin baka kirana ba da kuma saqonnina "sajida" tace.

Nikam sai na wayance na faɗamata cewa lallai banga sakonta ba kuma banga kiranta da yake jiya nasha aiki a kasuwa na dawo gida da gajiya barci ne mai nauyi ya saceni yanzu haka kinga wayan can a chaji bari na dauka na duba sakon naki, a'a barshi kawai ba bukata" ta fada ka zauna kawai sai na fadamaka abinda yafaru da kai a cikin mafarkin ko nace ya faru da mu.

Sajida ta kwashe dukkan abinda ya faru tsakanina da wannan aljani ta faɗamin tabbas babu abinda ya rage wanda yafaru tsakanin da wannan aljani wanda sajida bata fada ba, nayi mamaki matuka sannan tace shin da gaske a daren jiya hakan ya faru agareka kokuwa dai kawai mafarki ne take tambayana.

Naja dogon numfashi sannan na kalli fuskanta naga lallai tana cikin damuwa kuma idan na faɗamata cewa wannan mafarkin gaskiya ne zata shiga tashin hankali yarinya ce wacce bata son damuwa ko tashin hankali kokadan kawai sai na wayance nayi murmushi nace haba Kekuwa masoyiyata tabbas wannan mafarkin naki ba gaskiya bane ai babu wata halitta da ta isa ta rabani da ke walau ko dabba ke har aljan fadan hakan ke da wuya naji wani abu tamkar guduma ya daki kirjina faɗowa nayi daga kan kujerar da nake nayi taga-taga Sajida ta tallabeni tana fadin lafiya maye ya sameka?






A tsorace nace babu komai da ƙyar na koma na zauna kan kujera ina numfashi sama-sama a wannan lokacin jinake tamkar zuciyata zata fito daga kirjina tsabar zafin wannan duka da kuma fargaba da razana wanda suka addabi zuciyata, hakanan nake ƙarfin hali saboda ina tare da ita bana son ta fahimci halin da nake ciki sannan na fadamata cewa yakamata ta tafi gida tunda ta tabbatar ina lafiya kuma mafarki ne ba gaskiya ba sannan nima ina son zan fita kasuwa babu wata kasuwa da zanje kawai dai na kosa ta tafi saboda wallahi a wannan lokacin tsorace nake gani nake tamkar kasancewa da ita zai iya zama barazana ga rayuwata da kuma lafiyata.





"Sajida" tace bana son rabuwa da kai ko na second ɗaya amma yazama dole babu komai idan da rai da rabo ai saura kiris ka zama nawa mallakina, ni yanzu zan wuce idan na isa gida zan kiraka. Mukayi sallama da "sajida" ta wuce.




Na dauka wayana na kira Abdul lallai yazo gida akwai matsala ina cikin damuwa da tashin hankali, ganinan zuwa "Abdul" ya fada da Ƙyar na tashi na shiga ɗakina sannan na kwanta ina numfashi sama-sama ina jiran zuwan Abin mamaki sai barci ya saceni. Kiran sunana naji anayi tamkar daga sama buɗe idona ke da naga abinda yabani mamaki kuma ya tayarmin da hankali matuka Abdul nagani a tsaye fuskarsa cike da mamaki da takaici yana tambayana " shin maye ya kawo Sajida ɗakin ka? ".





Ina dubawa naga lallai"Sajida" ce a gefena tana barci abinta fuskarta cikin da annushuwa nayi zumbur na mike na sauka daga gadon ina goge idanuwana a tunanina mafarki nake sannan na fahimci cewa lallai ba mafarki bane gaskiya ne.

Zuciyata ta cika da sake-sake da tambayoyi wanda bana da amsar su sannan da tunanin tayaya zan fahimtar da Abdul abinda yake tunani ba haka yake ba, ina cikin wannan tunanin ne ta farka cewa take " haba masoyi gaskiya ya munajin daɗin mu zaka tashi ka barni kakuwa san yadda naji daɗinka gaskiya kaidin na mussamman ne ashe haka kake da kwarewa gaskiya idan mukayi aure zanji daɗi sosai, a tsorace na kalli cikin idanuwanta naga tamkar wacce ta sha cocaine hakan yasanya na tabbatar da cewa lallai ba "Sajida" sannan ta dago kanta ta kalli Abdul au Abdul ne mara da babban baƙo "sajida" shikam tsaki yayi sannan ya juya cikin fushi ya fita yana fadin lallai Ishaq kabani mamaki wallahi ban ta6a tsammanin haka daga gareka ba Ashe kai fasiki ne mazinaci wallahi yau da ace wani ne ya fadamin cewa ka aikata hakan wallahi sai inda ƙarfina ya ƙare domin na yarda da kai fiye da yadda na yarda da kaina. Amma abin takaici da idona naga wannan mummunan alaƙar kuma abin takaici da yarinyar da zaka aura wacce iyayenta suka yarda da kai kaji kunya Ishaq dan haka daga yau babu ni babu kai kaga tafita.










Ya juya yafita daga falon nikam inata binsa ina "Abdul Abdul" dan Allah ka tsaya ka saurareni ko juyowa bayyi ba nabishi har gate kawai ya tarbi abin hawa ya tafi idanuwansa cike da ƙwalla, ya tafi ya barni cikin dimuwa tashin hankali da rashin sanin abinda yakamata nayi.

Na duka tsakar gida inata kuka gami da tunanin abinda yakamata nayi, ina cikin wannan halin ne dariya naji mai kama da sauka aradu a tsorace na dago fuskata ba kowa nagani ba sai "sajida" itace take mummunan dariya mai cike da sanya fargaba da tashin hankali sannan tayi wata girgiza take naga ta zama wannan aljanin da yazomin a daren jiya.

Ya fara da cewa " yakai bil'adama mai taurin kai da
End Ads