x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - BAYAN WATA

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 71166 words

Category: Love Stories

Views 131

04 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
a gare ni."

Ado ya duba sama, yana murmushi da ƙyamshi, sannan ya ce:
"Idan muka kai Libya lafiya, zan gaya muku sirrin da ya sa na bar gida."

John ya ɗago kansa, ya ce:
"To, mu haɗa zuciyarmu." suka kama tare da muryar da ke daɗi ga kunne, duk da gajiya da yunwa, suka rera:

Bayan wata akwai dare,
Bayan dare akwai haske,
Bayan yunwa akwai cika,
Bayan hawaye akwai dariya.

Idan rana ta ɓuya,
Mun san wata zai leƙo,
Idan hanya ta dushe,
Mun san ƙafafunmu zasu kai.

Bamu daina ba, bamu ja baya ba,
Zamu cigaba har gobe ta zo.
Mu da juna, zuciya ɗaya,
Rana ta fito daga bayan wata"…

Yayinda suka rufe baitin ƙarshe, wutar da John ya kunna ta ƙara walƙiya, kamar yadda wata ke ɗaukaka cikin dare.

Tun daga wannan daren, wannan waƙa ta zama taken tafiyarsu duk sanda sun gaji, ko dare ya musu tsayi, ko cikin su ya fara kuka, sai daya daga cikinsu ya fara:

> “Bayan wata…”
sauran su kuwa sai su ɗaga murya cikin amsa, kamar ruwa da tsuntsu:
“…akwai dare… bayan dare akwai haske…”
suna shiga cikin sabuwar rana da sabuwar fata.


continued..... narnah ƙanwar soja ✍️










https://chat.whatsapp.com/DoFR3n8lLtI1RB5Zd2z2IT



🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
AFTER THE MOON
BY
NARNAH KANWAR SOJA







💫Royal Star Association,💫
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star



Page 3 & 4
28 / 4/ 2025
Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin posting kullum ba ,
mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya
show me some love guy's 🩷



بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وسلم




Wurin da suka iso na kusa da bodar Libya da Niger wata ƙaramar unguwa ce dake shan gajiyar gabar duniya motar da ta biyo hanya daga Agadez zuwa kusa da Libya ta sauke su a unguwar Sakar, inda suka ce daga nan za a wuce da ƙafa har zuwa Sabha a cikin Sahara.

Yayinda dare ke neman yin nisa, suka haɗu da wasu 'yan tsirarun matafiya da suka ce akwai hanya ta gefen jeji wacce ake bi don gudun jami'an tsaro.

John ya ja su a gaba, yana ɗauke da wata ƙaramin ƙaho na ruwa da bag ɗin burodi guda ɗaya kacal. Yazid da Ihsan na bayansa suna rera wasu baitin Bayan Wata da karfin zuciya, yayinda Maryam ke sanye da hijabi mai kauri, tana riƙe da Ado a hannu, suna tafiya a hankali cikin duhun dare.

Amma a kwana na biyar a cikin Sahara, bayan sun wuce wani yashi mai launin toka, a lokacin da rana ke ƙoƙarin ɓullo daga gabas,
Maryam ta hantsila ƙasa da karfi, “Aaaaaaah…!” ta fasa ƙara, jikinta na karkarwa kamar daji na girgiza, gaba ɗaya suka tsaya cak.
Ihsan ta durƙusa da sauri, tana girgiza ta. “Maryam! me ya faru?”

Maryam ta duba ƙafarta—tsohuwar alƙalamin takalmi ya tsinke, kuma dutsen da ta taka ya huda tafin ƙafarta, jini na zuba kamar famfo.

Sai hawaye suka cika idon Ihsan
Ado kuwa ya durƙusa yana duba ciwon da kwarewa kamar ƙwararren likita “Dole ne mu tsaya nan ba za ta iya cigaba da tafiya ba ” ya faɗa don yagaji da dogon tafiyar da babo matsaya,

John ya kalli yamma, inda duhun jeji da yashi ke cike da sauti marar ƙauna. “ba mu da lokaci… idan muka tsaya, mayakan macijin nan zasu iso.”
“mayakan macijin?” Ihsan ta tambaya da fargaba,
“'Yan fashin daji Idan suka same mu, ba abinci ba ruwa ba 'yanci...” ya dakata yana ɗauke numfashi
Yazid ya ɗago kai, idanunsa na cike da yaji ya ce:
“To a ɗauketa ba zamu tafi mu bar Maryam ba !” yana kauda fuska don dai har ga Allah cikin wanan yunwar bashi da kuzarir ɗaukar ta ,sai John ya ce da karfi “Ni zan ɗauketa!”



Bai jira amsa ba, ya ɗauki Maryam sama kamar jaririya, jikinta yana rawa saboda zafi da ciwon da ke yawo cikin jinin jikinta suka cigaba da tafiya , duhu ya koma, rana ta sake bayyana da ƙyalli, amma zuciyarsu na makare da tsoro da azaba.

Lokacin da rana ta ɗora bisa tsakiyar sararin sama, Ado ya sha ruwan ƙarshe da suka rage ya yayyafa kan Maryam.

Yazid kuwa ya saka dariya duk da gajiya yana cewa “Yau rana na cin mutum, amma jiki na cin gado…” sai Ihsan ta hau waka a hankali:
“Bayan wata… akwai dare…”
John ya karɓa cikin murya mai ƙarfi kamar jarumi
“Bayan dare… akwai haske…”



Suka kama waƙar cikin kuka da dariya a lokaci guda waƙar ta zama mafakar zuciya.

Maryam da aka daura a bayan John, tana raɗa wa kanta:
“Zan rayu… saboda ku…”

Washe gari rana na haskakawa cikin yashi kamar zinariya, suka iso wata ƙaramar sansanin ‘yan gudun hijira da ke bakin Libya, wanda wasu likitoci daga ƙungiyoyin jinkai ke taimaka wa nan ne aka kwantar da Maryam cikin wani tantin asibiti na wucin gadi An gyara ciwonta da tsafta, aka bata allurai da ruwa, har ta fara murmushi.

John da Ado suka sauke ajiyar zuciya. Yazid kuwa ya durƙusa ya shafa gashinta yana cewa: a cikin kunnen ta “kin tsira Maryam… ki tabbata za ki rayu har mu ga Dubai!”

Ihsan kuwa, da ta zauna a jikin wata tsohuwar matashiya mai suna Mama Simbi—wacce itama gudun hijira ce daga Ghana ta kalli sauran matafiya da kuma wasu daga cikin mutanen sansani, sai ta ce da natsuwa:

“Kafin rana ta sauka yau… zan ba ku wani labari. Labari ne wanda ban taɓa fitar da shi ba… kuma shine zuciyata ke ɓoyewa tun ina zan bayyana labarin da Narnah ƙanwar soja ke da burrin fitarwa sai dai bata samu dama ba ne Ihsan zanyi amfani da wannan damar.”



Gaba ɗaya suka zauna, wasu suka ɗebo ruwa, wasu kuma suka jera kan buhuna da katifu. cikin nutsuwa da natsuwa, Ihsan ta gyara zama, idonta na kallon nesa kamar tana komawa zamanin da ya wuce.

Sauran matafiya suka runtuma cikin nishadi, wasu suna cewa, “Labarin fa kenan!” wasu na gyara zama kamar za su rubuta da likitochin da tawagar Bayan wata duk suna sauraron ta




(Yanzu fa lokaci yayi na shigowar sabuwar rayuwa cikin Bayan Wata—wannan labarin Ihsan da za ta fara ba su a sansani, zai kasance labari cikin labari, wanda zai haɗa ƙauna, yaƙi, al’amuran fada da sirrin da ta ɓoye har yau. )


PRINCESS RAHILA
EPISODE ONE
2000 Years Back

Sunanta Rahila – kyakykyawa ce tamkar hasken wata, bakar fata mai sheƙi, jikinta dirin coca-cola shape gashinta ya sha bamban da na kowa a masarautar Buga African, kuma idanunta sun yi farin haske har cikin duhu. murmushinta na bayyana haƙora masu tsabta da kyau halittarta ta ban mamaki ce, fiye da na kowace mace a wannan ƙarni.

Rahila ita ce tilon 'yar da King Numan ke da ita bayan shekara da shekaru ba tare da samun ƙarin 'ya'ya ba, sai ya tara soyayya da dukiyarsa gaba ɗaya ya miƙa mata. Baiwar da bai ba kowa ba, ya ba Princess Rahila – wacce ake kira da wannan suna cikin girmamawa.

Masarautar Buga African ta kasu gida biyar:

1. Yankin Burum


2. Yankin Dusrum


3. Yankin Tursum


4. Yankin Kurum


5. Babban yanki – Buga African, karkashin King Numan.



Tunda mahaifiyarta ta rasu tana da shekara biyar, Rahila ta tashi tare da mahaifinta duk wata buƙatarta ana cikawa, kuma soyayya ce ke ratsa tsakaninsu tana da shekaru goma sha biyar amma ta riga ta kware wajen amfani da makamai kamar takobi, kwari da baka, guggar zana da salon yaki – duk sabili da Slave Kodo, babban gwarzon bawa kuma mai ba King Numan kariya.

Fadar King Numan cike take da dukiyar duniya da bayi duk da cewa bai ƙara aure ba bayan rasuwar matar sa, yana amfani da wannan damar wajen tilasta wa matan bayi duk matar bawa da ta rasa mijinta, ko baiwar da take kyakkyawa, za ta faɗa hannun sa.

Rahila ta kai shekaru ashirin kyaunta ta kai kololuwa duk sarakuna da attajirai sun so mallake ta amma ta ƙi. a cewarta, ba za ta bar fadar mahaifinta ba kuma ba za ta zauna ƙarƙashin kowane namiji ba. Wannan ra’ayi nata yasa wasu sarakuna suka rasa idanuwansu saboda kallonta da soyayya.

Ta yi imani cewa mahaifinta zai rayu har abada ta ɗauka rayuwarta zata kasance cikakkiya har abada a haka ne ta fara koyon mugunta, ta nuna ƙarfin hali da alfahari. Ta san ta fi kowa kyau da ƙarfi. Ta ƙi yarda wani namiji ya kwanta da ita.

Tana ganin ƙarfinta da na mahaifinta da na mayaƙa – musamman Slave Kodo – zai iya kareta har abada amma sai wani abin mamaki ya faru…

Lokacin da ta dawo daga kogin da ta saba wanka, tana kwance a gadonta, bayi biyu na tausa ƙafarta, wasu na shiryata, sai wani bawa ya shigo cikin gaggawa tayi mamakin ganin shi ya shigo ɗakin ta ba tare da izini ba. Cikin fushi ta watsa masa mari har sai da ya firgita.

Yana kokarin cewa “The king sees…” amma ta katse shi da bacin rai, “So what? He's my father, I can go to him anytime I want!”

Da ƙyar ya fice, amma cikin mintuna sai ga King Numan da kansa ya shigo ɗakin wani abu ya dame shi, hakan yasa Rahila ta shiga fargaba – abu da ba ta taɓa ji ba. Bai taɓa shigowa ɗakin ta ba da kansa.

"My baby, we must leave Buga African immediately!" ya faɗa cikin damuwa.

"What? Leave our kingdom? What is happening?” Rahila ta tambaya, cikin tsoro da rashin yarda.

"Zuma people (Dursum) have invaded our palace! We've been betrayed. Even our soldiers have been sold out!" in ji King Numan.

"NO, Father!" ta ce cikin jin kai. “nu shugabanni ne! Dole mu yaƙi mu mallaki su mu mayar da su bayi!”

Ta ɗauko takobinta mai haske, wanda ta keɓe, tana shirin yaƙi. Amma fa, yaƙin da ya zo ba kamar sauran bane.

Cikin hanzari, Slave Kodo ya shigo. “Your majesty! Prince Tarhim na Dursum ya shiga tsakiyar fadar da mayaƙansa!”

King Numan ya kama hannun Princess Rahila. "My jewel, please, follow Kodo. He will take you to safety."

“No! I won’t run like a coward!” Ta ce cikin kuka da bacin rai.

Amma King Numan yasan lokaci ya kure kuma burinsa shine ya ceci tilon 'yarsa
King Numan ya dube ta da ido mai cike da ƙauna da alhini. Hannunsa yana rawa yana riƙe hannun 'yarsa Rahila, kamar yana ƙoƙarin ƙara ji da ƙarfi a jikinsa da ya fara rauni.

"My jewel... I know my time has come," ya furta cikin rauni. "But I will not let them take you. You must live, even if I die."
Princess Rahila ta dafa ƙirjinsa da duka hannayenta biyu, idonta na cike da hawaye masu ƙyalli, tana girgiza kai. "No Baba, don’t say that! You will live! we will fight together!"
Amma Sarki Numan ya girgiza kansa cikin sanyi."I’ve seen this in my dream... Kodo knows what to do. He’s been waiting for this day."


Yayi kallon ƙarshe ga Slave Kodo, wanda yanzu ya yi shiri da kayan yaƙi, gashi yana kama da jarumin da ba a taɓa ganin irinsa ba.
"Kodo," in ji Sarki Numan cikin murya mai ƙarfi, "take her... and make sure she survives. That’s an order."
Kodo ya durƙusa, ya ce da kwarjini:By the gods of Buga Afirican, I will protect her with my life."
Princess Rahila ta sake fashewa da kuka. Tana janye hannunta daga na mahaifinta tana cewa:"Baba... don’t let them take our land..."
Sarki Numan ya matsa kusa da ita, ya sa hannu a bayanta ya rungume ta na ƙarshe. Ya furta a kunne ta da ƙasa sosai:
"You are the land now. You are Buga Afirican. Go... before it’s too late."
Sai ga wata ƙara ta fashe daga wajen fadar. Wuta ta fara tashi daga ɓangarorin fada, ƙamshin hayaki da jini na ratsa iska. Wakilan Zuma da Prince Tarhim sun karya ƙofa, sun shigo da mayaƙa cikin izza da azama.
Slave Kodo ya ɗauki Rahila kamar jaririya, ya fice ta wata ɓoyayyar ƙofa dake bayan gadonta—ƙofar da aka gina shekaru dari da suka gabata domin irin wannan lokaci.
Sarki Numan ya tsaya da kafarsa, ya zare takobinsa mai daraja, wanda aka gada tun zamanin kakanninsa Ya fuskanci mayaƙan Zuma da ƙarfi, yana ba da na ƙarshe na jinin sarauta domin kare masarautarsa.

An bar fadar cikin hayaki. An bar sarki cikin yaƙi. an fita da Rahila cikin duhu.

Wannan rana ce ta zame wa Buga Afirican tarihi Ranar da wata sarauniya mai ƙarfi ta rasa gida, ta rasa uba, amma ta samu sabuwar rayuwa—rayuwar da zata yi nasara ko ta mutu tana ƙoƙari......




Continued by narnah ƙanwar soja ✍️









https://chat.whatsapp.com/DoFR3n8lLtI1RB5Zd2z2IT




🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
AFTER THE MOON

BY
NARNAH KANWAR SOJA
( Sayeddan Addah )






💫Royal Star Association,💫
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star



Page 5 & 6

Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin posting kullum ba ,
mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya
show me some love guy's 🩷

بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وسلم


Haka abin ya faru da Sarki Numan haba ɗaya mutanensa sun gaji da mulkinsa, wasu daga cikin mayaƙansa sun juya masa baya, suka sayar da kansu ga mutanen Dursum, wanda suka sayi rabin mayaƙan domin samun nasara a kansa.

"Kado, ka kula da ‘yata. Ita kaɗai ce abin da na mallaka," inji Sarki Numan, ya faɗa wannan karo fiye da goma.

"Eh, mai martaba, zan kareta da raina," Kado ya sake amsawa cikin nutsuwa.

" Baba ka bar ni na tafi tare da kai!" Princess Rahila ta faɗa cikin kuka, tana faɗawa jikin mahaifinta.

Ba ta son wani abu ya same shi ita fa ba komai ba ce idan ba tare da mahaifinta ba.

“Je Kaɗo , tafi yanzu da ‘yar gadona. Ka kiyaye ta kamar zinariya.” Sarki Numan ya faɗa da murya mai ƙarfi, irin ta jarumai, sannan ya juyawa wajen baya yana barin gurin.

Princess Rahila ta sake gudowa ta rungume mahaifinta daga baya da jin ɗumin hawayenta a bayansa, zuciyarsa ta raunana sai dai ya ƙi juyawa saboda kar ta hango hawaye a idanunsa — alamar rauni ga jarumi kamar shi.

Duk da haka, yana son Rahila ta ci gaba da tunawa da shi a matsayin jarumin sarki, gwarzon da yaƙi bai faye shi ba, ba mai zubar da hawaye saboda galaba ba.

Bayan wani lokaci, Rahila ta saki mahaifinta, sannan ya tafi ba tare da ya waiwayo ba.
Baba Baba Ka kalleni ko sau ɗaya,” Rahila ta faɗa tana fāɗowa kan gwiwowinta, amma Sarki Numan bai waiwaya ba yana ƙoƙarin ɓoye hawayensa.“My princess, dole mu tafi yanzu,” Kado ya faɗa yana ƙoƙarin tashi da ita, amma ta ture shi.“Kar ka kuskura ka saka kazamin yatsunka a kaina!” ta faɗa cikin ƙiyayya.
(Duk da girman haɗari, girman kai na sarauta ya mamaye ta.)
Kado bai ce uffan ba. ya saba da halayenta, tun da shi ya horar da ita duk da haka, shi kansa bai tsira ba suka fice ta wata sirriyar hanya da ba kowa ke san da ita ba, sai dai shi da Sarki Numan.
Yayinda Sarki Numan ya dawo fadar sa, sai ya tarar da rabin masarautar an lalata ta. Mayaƙan Dursum sun riga sun mamaye wajen.
Sarki Numan ya shiga ɗakin sirrin da ke ajiyar makamai, ya sa tufafin yaƙi, ya ɗauki manyan takubba guda biyu zuciyarsa cike da fushin jarumi, ya kuduri niyyar mutuwa a matsayin gwarzon sarki maimakon guduwa kamar gwanin fargaba.

A lokacin yaƙi...

Yaƙin ya riga ya barke, sara suka hannu da ƙafa. Sarki Numan ya fafata kamar zaki, yana yanke mayaƙa tamkar bishiyoyi lokacin da ya hango Prince Dursum, tun da farko ya ɗauka Prince Tarhim ne, sai dai da ya kalli fuskar, ya gane cewa uban ne — Sarki Mujus. Da haka ya soki kansa ƙasa, alamar ƙarshen nasarar da yaƙin zai iya kawo masa.

Sarki Numan ya ci gaba da gwabzawa har sai da zuciyarsa ta fara kasa dukan da kyau. Bugun zuciya ya rikice, zuciyarsa ta mutu da ganin 'yarsa cikin halin ƙaskanci ya sulale ya fāɗi ƙasa, ya zubar da makamai, hawaye na zuba daga idanunsa.

“Ba zai yiwu ba! wannan ba gaskiya ba ce!” ya ƙwala ihu cikin azaba.

“… ku bar ta ku kyaleta, ku bar ta haka kawai,” Sarki Numan ya roƙa yayin da aka jawo Princess Rahila cikin sarka, tana kuka.

Jikinsa ya kasa tsayawa, ya durƙusa, yana kallon Prince Tarhim yana ja da sarkar Rahila, har ta durƙusa ƙasa yana kai ta gaban mahaifinta, yayin da wasu zaratan mayaƙa suka kewaye su yanda yake ganin ‘yarsa tamkar bayi, ya girgiza zuciyarsa sosai.

Princess Rahila ba komai ce a wannan lokaci ba face bawa, jikinta da datti da ƙura, gashinta ya bazu.

“Ga ‘yarka, Sarki Numan babu sauran princess, yanzu bayi ce a ƙarƙashin masarautar Zuma,” inji Prince Tarhim, ɗan Sarki Mujus — jarumin da ya kashe dabbobi da suka kai hari garinsu, Zuma shekaru 27 ya fafata yaƙe-yaƙe masu yawa.

Dogo ne, baƙi fari, da kyakkyawar fuska. Fuskarsa da sunansa suna tayar da hankali, musamman ga mata.“Wannan ba zai faru ba!” Sarki Numan ya ƙara faɗa.

“, ku bar mahaifina shi ne Sarki na Buga Afirka,” Rahila ta faɗa cikin kuka.
Sarki Mujus ya fusata, ya jawo gashin kanta. Rahila ta yi ihu cikin ciwo da azaba.
“Great king kike kira? kin san abin da mahaifinki ya aikata wa mutanen masarautata?” inji Mujus.
Sarki Numan ya ce, “Kaɗo ne ya yi alkawarin kare ki.”
“Baba Kaɗo ne ya ci amanar mu,” Rahila ta faɗa cikin murya mai cike da raɗaɗi. Mahaifinta ya firgita.

“Kado? Amintaccena?”
“Eh, Baba ya ƙaddamar da komai.”
Kado ya bayyana yana faɗi, “Na tuna kuka na iyayena da ‘yar’uwata lokacin da suka mutu a hannunka. kayi musu hukunci da wuta saboda haraji na jure, na koya darasin rayuwa har na zama bawan da kake amincewa da shi amma yau sai na ɗauki fansa ta, in ga yadda ‘yarka ke zama bayi, kamar yadda ka mayar da ‘yan’uwanmu bayi.”Sarki Numan ya ƙara fashewa da kuka, “Kado, me nayi maka har ka yi haka?”
“Zan bar ka da rai, Sarki Numan amma zan tabbatar ka gani da idonka lokacin da ‘yarka ta fuskanci cin mutunci kamar yadda wasu suka fuskanta.”
“Don Ubangiji… a kyale ta ku daina wannan,” Sarki Numan ya ce yana ihu, yana ƙoƙarin miƙewa a lokacin ya sharɓi wuka daga hannun wani mayaƙi.
...ya sharɓi wuka daga hannun wani mayaƙi, ya sharɓa a cikinsa da ƙarfi, jini ya fara malala daga
End Ads