x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - BAYAN WATA

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 71166 words

Category: Love Stories

Views 137

04 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
kullum tana kallo daga gefen ruga tana mafarkin rayuwa mai zurfi, tana ɗora fatarta kan murya da waƙar wani saurayi da ya taɓa tsayawa bakin tabki yana kallo duk da cewa bataye ilimin zamani ba amman tabass tana da ilimin addini da ilimin sanin halayyar ɗan Adam



Kamar yadda kowacce shekara take kasancewa, haka wannan shekara ma ta zo da nata alkawura ,daga nesa, ƙura ta fara tashi. Yara suka fara ƙwala ihu suna fadin:
"ga motar Alhaji! ga motar Alhaji!!"

Motoci biyu Honda guda fari da ɗaya baki suka bayyana cikin natsuwa, suna karasowa cikin ƙauyen Gembo Saƙa-saƙan ƙura ke biye da su, kamar girgijen albarka. dun tsaya kai tsaye a gaban bukkar Moddibbo, wanda shi ne babba kuma mai daraja a wannan yanki wata irin lumana da nutsuwa ke lullube daƙalin gidan nasa, kamar yana jiran zuwan ɗan sarki.

Alhaji Saminu ya fito daga motar fari cikin dogon riga shadda mai launin zinariya, da rawanin da ke sa hasken rana ya bayyana a goshinsa. Murmushin sa na cike da annuri, yana ɗaukar zuciyar kowa da kallo kallonsa kaɗai na saka mutum jin kwanciyar hankali.

Moddibbo kuwa, ya fito da kansa daga cikin ɗakinsa, cikin natsuwa irin ta dattijo mai hangen nesa. Suka runguma kamar ’yan



Moddibbo kuwa, ya fito da kansa daga cikin ɗakinsa, cikin natsuwa irin ta dattijo mai hangen nesa. Suka runguma kamar ’yan uwa da suka jima ba su hadu ba. baiwa da mutunci sun kasance tsakanin su tun shekaru goma da suka wuce — alaƙar da ba kuɗi ko matsayi ba ne ya ɗaure, illa kirki, imani da gaskiya.

“Barka da zuwa, Alhaji,” Moddibbo ya furta cikin murya mai nauyin daraja.
“Lafiya lau, Moddibbo. Allah ya tabbatar da alheri kamar kullum,” Alhaji Saminu ya amsa da ladabi.

Maza da yara sun fara taruwa a kofar gida, ana kallon motoci da murmushi, yayin da matasa ke harhada shannaye daga gindin kuka da ke kusa da gona, domin Alhaji ya saba fita da kansa yana zaɓar dabbobin da zai yanka domin hidimar Sallah ga iyalansa da maƙwabta.


Bayan doguwar gaisuwa ta mutunci da girmamawa tsakanin dattijan biyu, sai ga Halima yarinya mai kyaun da ke bayyana a hankali kamar safiya mai sanyi ta fito da kwanon madara a hannunta, fuskarta daɗaɗɗiya, idonta mai cike da nutsuwa, ta isa gaban baƙi cikin kamewa da girmamawa.

"Assalamu alaikum," ta faɗa da siririyar murya

"Wa alaikumus salam," Alhaji Saminu da Moddibbo suka amsa a tare, suna kallonta.

Alhaji Saminu ya karɓi madarar hannunta, yana dubanta cikin ido da murmushi da ke ɓoye wani sirri mai zurfi. Halima ta sunkuyar da kanta, tana juyawa cikin girmamawa kamar yadda aka koya mata.

Bayan ta shige ciki, Alhaji Saminu ya ɗan juyar da kallonsa zuwa ga abokin zamansa.
"Moddibbo... shekarun Halima sun cika goma sha biyar yanzu, ko ba haka ba?"

Moddibbo ya gyara zamansa, ya ɗan sosa gemunsa yana murmushi mara kyar.

"Eh, haka ne. shekaru goma sha biyar rabon da ka min wannan alkawarin."

Alhaji ya lumshe ido. "Na tuna sosai ka ce Halima zata zamo matata, kuma kai da kanka zaka miƙa min ita ranar da ta kai munzalin aure."

Moddibbo ya ɗan sauke ajiyar zuciya, yana kallon ƙasa.

"Ka sani Alhaji... ban taɓa mantawa da alkawarin nan ba. kuma na tsaya akan shi har yau saboda girmanka da darajarka a idona. Amma fa mutane sun fara tambaya, sun fara zargi... wasu na cewa wai ni na hana Halima aure saboda son zuciya wasu ma na ganin kamar ina fuskantar matsin lamba daga wani ɓangare."

Alhaji Saminu ya ɗan sunkuyar da kai, muryarsa na nuna laushi da tausayawa.

"Moddibbo... ka sani Halima tana da muhimmanci a gareni fiye da yadda za a iya fassarawa da baki amma idan hakan zai cutar da mutuncinka ko na yarinyar... sai mu sake duba hanyar da za a bi cikin adalci da amana."

Moddibbo ya ɗan kalli tsohon abokinsa, yana girgiza kai da murmushi mai ɗan nauyi.

"Alhaji, ni dai ba zan karya alkawari ba kuma Halima ma ta san da cewa tana da wani babban makoma da muke jiran lokaci ina so a kyautata komai cikin tsari da girmamawa... da zarar ka ce lokaci yayi—ni a shirye nake."

Alhaji Saminu ya ɗaga kai, idonsa na ɗauke da abu fiye da kalmomi.
"To lokaci yayi, Moddibbo kuma Halima zata dawo gareni—amma ba kawai a matsayin amarya ba, a matsayin amanar da zan ci gaba da kulawa da ita kamar zinariya mai tsarki."





Get ready fans ga Halima ga Alhaji Saminu menene abinda wannan gajeren labarin Maryam ya ƙunsa , let's go..........










https://chat.whatsapp.com/BsQ0CkOCA83FgwnQ177z9y



🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
AFTER THE MOON🌕

BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA


SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star


15 / 16
08 / 5/ 2025


Kamar yadda aka saba duk shekara, Alhaji Saminu bai taɓa yin ƙasa a guiwa ba wajen nuna ɗimbin darajarsa a idon mutanen ƙauyen Gembò amma wannan karon daban ne. wannan karon ba kawai don shanaye ya zo ba ya zo ɗaukar amana.



A gaban Moddibbo da wasu dattawan gari guda biyu, Alhaji Saminu ya fito da sadakin Halima. kudi ne masu yawan da fulani ba su fiye gani ba a lokaci guda baya ga hakan, ya kawo 'yan dabbobi da kayan gyaran amarya, tare da alkawarin dawowa bayan Sallah da sati biyu—kai tsaye daga birnin Tarayya Abuja inda matarsa ke zaune.

Moddibbo ya karɓi sadakin cikin nutsuwa da girma ya san me hakan ke nufi: yanzu Halima zata koma karkashin Alhaji Saminu amma ko da yake zuciyarsa na cike da nauyin amana, bai nuna ba, saboda a rayuwa irin tasu, alƙawari tamkar doka ne da ba za a karya ba.

Halima kuwa... ta zauna a gefen mahaifinta da cike da kunya, fuska a kasa kamar yadda aka koya mata, duk da cewa an ba ta labarin cewa rayuwar birni ce zata zame mata gaba, kuma Alhaji Saminu mutum ne mai arziki da daraja—amma a zuciyarta babu motsin soyayya ko ɗokin aure.

Zuciyarta tamkar fili ne, babu shuka, babu furanni kawai akwai wata siririyar lafazi da take maimaitawa a ranta:

"Na yarda da mahaifina na amince da kaddara. kuma zan bi Alhaji Saminu, ko da zuciyata ba ta motsa ba."

Irin wannan biyayya ce da ta sa ta karɓi sadakin da lafazi guda biyu:
“Na yarda.”

Moddibbo kuwa kamar kowa yana ganin yana murna amma shi da zuciyarsa sun san gaskiya , ya san Halima ba ta kai matsayin aure ba tukuna ta girma da sauri, amma zuciyarta har yanzu karama ce, tamkar macen da bata fara sanin al'amuran soyayya ba.

Sai dai kuma, Moddibbo mutum ne mai daraja da mutunci ya rike amanar Alhaji Saminu fiye da yadda wasu ke rike 'ya'yansu. Yana fatan Alhaji Saminu zai kare martaba da tsaron Halima kamar yadda ya rike alkawari na shekaru goma sha biyar.

Wani iska ya buso daga arewa, ya kada ganyen kuka da ke bakin ruga Halima ta lumshe ido, tana jin iskar kamar wata alama ce daga sama ko soyayya zata zo daga baya? ko kuwa hakan nan ne rayuwa ta rubuce mata?


Bayan sati biyu da cikar alkawari, ƙauyen Gembò ya sake fuskantar wata rana da ba za a taɓa mantawa da ita ba rana ce da komai ya sauya—rana da tarihi ya ƙara rubutun zinariya cikin ƙwarya mai ƙyalli.

A safiyar ranar asabar, tun ƙarfe tara da mintuna goma, sai ga jere-jeren motoci guda shida masu sheƙi da ƙyalli irin wanda bai saba zuwa ƙauyen ba, motoci ne kirar Lexus LX 570 guda biyu, guda bakar fata, guda kuma fari ɗan haske mai cike da adon zinariya. Sauran kuwa motoci ne kirar Hilux da Toyota Highlander, dukkansu cike da kaya, kujerun zamani, manyan jakunkuna da akwatuna masu lulluɓe da furen ado da yajin rawaya.

A wata ƙaramar Prado, wanda aka ɗora babban laifan jajjayen furanni da tutar Kaunar aure, Alhaji Saminu ne ya fito sanye da babban ɗan-baban Shadda mai launin zinariya da ruwan hoda , babbar hula ce ta fulani bisa kansa, mai ɗinki na musamman da adon sarka fitarsa daga mota ta sa yara suka yi tsalle, mata suka fara cewa:

“Ga angonmu ya iso! Allah ya sa a dace!”



Shi kuwa, yana da murmushin da ba'a san a zuciya akwai tsoro da jin nauyin amanar da ya ɗauka ba bayansa, abokansa biyu da shaidu—Alhaji Babangida da Alhaji Laushi—duk sun fito cikin kayan zamani ƙauyen ya sha ado kamar an shirya masa sallah gari ya ɗau shela da kade-kade na kalangu da waka:

“Alhaji Saminu yazo!
angon Halima yazo!”


Tun daga makon da ya wuce, iyayen Halima sun ɗora shagalin al'ada, mata na unguwa sun taru kullum ana sallake, ana gasa binkami, koskoso, da kilishi. Halima tana zaune cikin ɗakin mahaifiyarta marigayiya, cikin duhun tunani da zumudin rayuwar da ba ta san me take cike da ita ba ,aka yi mata lalle, aka sa mata ƙwarya ta ruwan turaren wuta a gefenta, aka shafa mata manshanu a fata, aka ɗinke mata zani da riga mai alamar Fulani na gargajiya—jar zani mai adon ratsi da santali na tsaf.

An saka ta cikin wani ɗaki mai ƙyalli da kilishi, ana yayyafa mata ƙamshi da bakhour, ana duba fatarta da gashinta, yarinyar ce kyakkyawa da kyau na halitta, ba ado ke ƙawata ta ba—rashin yawan maganganu da nutsuwar ta ce abin kallo.

A gaban limamin ƙauye da shaidu, aka daura auren Halima da Alhaji Saminu da sadaki naira dubu ɗari biyar, da sarkar zinari da kayan gida., adaidai lokacin da aka furta "na ɗaura", Halima ta fashe da kuka mai ƙarfi. Sai dai ba kuka na soyayya ko jin daɗin aure ba ne—kuka ne na rabuwa da matar mahaifinta, wacce ta raineta tun rasuwar mahaifiyarta, wani kuzarin tunani ya cika ta, kamar tana jin kamar yanzu rayuwarta ta sauya daga yarinya zuwa amarya, daga ƙauye zuwa birni.

Moddibbo ya share hawayen sa da alwala, yana murmushi mai cike da damuwa, yana fatan Halima zata dace da sabon rayuwar da zata tafi ciki, a zuciyarsa yana fatan Alhaji Saminu zai rike ta fiye da yadda aka rike ’yar sarki.



Alhaji Saminu ya bar ƙauyen ba da hannu ba. Ya bar da ɗimbin kyaututtuka: kudi ga matan unguwa, jakunkunan shinkafa, kayan abinci, sabbin riguna da ɗinkin zamani ga matasa, har da jakunkuna ga yara da aka ce "na makaranta".

Wajen fitarsu, aka shigo da sabuwar amarya cikin sabuwar rigar aso-ebi da kwalliyar santali, aka ɗaura mata gyale mai nauyin zinariya, aka raka ta da kalangu da wake-wake, aka saka ta cikin motar farin Lexus, sai ga kafila ta nufi birnin Abuja.

Amarya ta fito daga ƙauye—amma fuskarta na cike da tambayoyi. Shin me birnin ke ɓoye mata? Me Alhaji Saminu zai kasance gareta? shin wannan aure zai fassara soyayya ne, ko wata kyauta ta biyayya ce da ba zata taɓa jin daɗin ta ba?


*********************************


Juyawa tayi da ƙarfi kamar wadda aka hangi zuciyarta ta nitse cikin ruwan kogin ɓacin rai. tana mai huci da numfashi mai nauyi, ta faɗa jikin Moddibbo kamar jaririya, ta rungume shi da ƙarfi, tana kuka mai girgiza zuciya dukkan gangar jikinta na rawar jiki, murya na rawa kamar ana buɗe gidan hawaye a zuciya.

Moddibbo ya kama kanta yana bubbuga bayanta da hannunsa mai sanyi da tausayawa.
"Allah ya sa ki dace Halimatu," ya faɗa da wani murya da yafi shiru nauyi. "ki rike mutunci, ki tsaya da imani kiye koyar da mahaifiyar ke a fagen haƙuri zaki ci ribar zaman duniya ... rayuwa ce bata da tabbas."



Shi kansa idonsa cike da ruwa, kodayake zuciyarsa ta taɓu sosai—ya jima yana kallon Halima tamkar zinariyar sa wanda yanzu ya mika hannunsa ya mika ta ga duniya. ya mika al’amuranta ga wani mutum da ya fi shi daraja da kima, amma ba shi da tabbacin soyayya.

Bayan kuka da ban kwana mai cin rai, sai Halima ta shige cikin motar Alhaji Saminu da zuciyar da ba a iya fassara. Alhaji yana ƙoƙarin rarrashi da annuri, yana ƙyalƙyala dariya mai taushi yana faɗin:

"Amaryata kada ki damu, Abuja ba abin tsoro ba ne ke zauna lafiya, za ki ga alheri."
Halima bata ce komai ba ta fuskanci gilashin motar tana kallon ƙauyen su da ke raguwa a bayanta kamar mafarkin da ya ɓace. hannunta na cikin haɗaɗɗiyar rigarta, amma zuciyarta na cikin tsohon zanin ƙauyenta.



Motoci suka fice daga Gembò, suka fasa hanyoyi masu kura, suka dosa garin Yola inda jirgi zai tashi zuwa Abuja. Halima na zaune cikin mota, amma kamar a mafarki ta kasa kallon sabbin gine-gine da suka wuce su, kamar ba su da ma'ana gareta.

A lokacin da suka isa filin jirgi, an ce mata "Halimatu! Ki sauka ",ta sauka cikin rigima, tana kallon ƙasa kamar tana tsoron ƙasa ce zata buɗe ta haɗiye ta ba ta san me ake nufi da “ticket” ba ba ta san yadda ake biya ba yanzu ne Halima ke fara jin bambancin rayuwa, ta kasa cire takalmanta a wajen sakan na’ura, sai da ma'aikaciyar ta fara dariya ta ce:
“Yarinya! ba salla za ki ba wannan tsafta ne da dokar jirgi.”
taji kunyarta sosai Idonta ya cika da ƙyama da tozarta a zuciyarta:
“kai! ashe akwai duniya kamar haka?”



Bayan an kaita cikin jirgin, aka ɗaure mata seat belt, ta riƙe kujerar kamar wacce ke cikin ruwa mai zurfi. Da jirgi ya tashi, ta saki ƙara mai firgitarwa:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Wayyo Moddibbo…! na mutu!”
Alhaji Saminu ya rike hannunta da dariya “babu komai Halimatu, jirgi ne ke tashi kawai.”



Kamar sabuwar tsuntsuwa aka ɗauke daga ciyawa, aka ajiye cikin gini mai fanfo. As zuciyarta, birni kamar wata. Amma tambaya ɗaya ke ci mata rai: Shin wannan sabon garin da take ciki zai taimake ta ta samu sabuwar rayuwa, ko zai ɓata mata tunanin da take tsaye da shi tun ƙuruciya?


Tunda suka hau cikin jirgin sama, Halima ta kasa zaman lafiya idanunta na zagaye cikin hadadden komai wanda ba ta taɓa mafarkin wanzuwarsa ba , tana kallon tagar gefe, tana ganin sararin samaniya da ƙasa na raguwa kamar yadda aka rage wa tunaninta hankali. amma wani abu ya sake ɗaukar mata hankali...

A kujerar bayan nata, wani saurayi ne zaune, ya murtuƙe fuska, idonsa kamar na damisa mai zurfin tunani , fuskar sa doguwa ce, fara tas kamar bulo, ƙuncinsa yana da ɗan launin ja, bakinsa siriri ne amma mai ɗan ƙasaita gashin kansa an rage shi tsaf yana sheƙi, sai karan agogon zinare a hannunsa na hagu ya ƙara ɗaukar hankali.

Shima yana kallon Halima, ba da sha’awa ba, amma da mamaki da tausayi kadan kamar yana cewa da kansa, “Ina aka samo irin wannan ‘yar ƙauye mai tarin kamala?”
suna cikin tashi ne Halima ta saki ihun da ya gigita kowa
“Wayyo Allah naaa! waye ya ce jirgi zai ɗaga?! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”



Mutane sun juya suna kallonta, mata suka dinga dariya a nutse, wasu kuma suka tausaya amma shi saurayin da ke baya—ya kalli fuskarta da jajayen idanu, yana juyar da kansa a hankali cikin murmushin gefen baki, kamar wanda ya saba da irin haka a rayuwar zuciyarsa , sun sauka a filin jirgin Abuja, wanda ya bude musu sabon shafi a rayuwa.



Alhaji Saminu ya nufi Maitama da su, inda katafaren gidansa ke cike da girma da kima. gidan na da kofa babba mai lanƙwasa kamar ƙofar masallaci a Makka. farfajiya ce a waje, da lambu mai yalwa, sai tsuntsaye ke ta raira waka kamar sun san sabon baƙuwa ta iso.



Yayin da Halima ta kalli ƙofar katafaren gidan, zuciyarta na wani irin doki da tsoro da fargaba, wani sashe na ruhinta na faɗin "kin fito daga ƙauye, amma an jefa ki cikin birnin masu hannu da shuni..." da zuciya ɗaya ta shiga, sanye da kayan aure na gargajiya: mayafin fulawa, zobba a yatsu, da dankwali mai yatsin zinariya.

A cikin gida, motoci sun sha jerin gado, masu gadin gidan biyu a ƙofar shigowa suna miƙa gaisuwa da ban girma. Gidan kuwa – katafaren alfarma ne wanda ba a taɓa mafarkin Halima zata taka kafarta ciki ba. Babban falon yana da manyan tagogi masu labulen fata na turkiyya, cike da fitilu na chandelier masu hasken zinariya, cikin falon ne Hajiyah Nafisa ta karɓe ta da murya mai cike da mamaki:

Matar Alhaji Saminu, Hajiyah Nafisa, ta fito sanye da kayan alfarma gashinta a jikin mayafi yana sheƙi kamar rigar sarauta ta kalli Halima da murmushi na ɗan lokacin, amma idanunta na cike da alamun tambaya:
“Itace wannan yarinyar?”
Halima ta kasa magana ganin palon gida kadai ya isheta tiles ne na zinariya da hoda mai sheƙi, fanfo a bango da tebur na gilashi. tana takawa kamar ana binsa da ƙasa. Zuciyarta na cewa:
“To wallahi... haka birni yake ko dai na mutu ne an kawo ne gidan aljanna ?” kwalliyar da aka yi mata da kayan Fulani na auren ƙauye—maye da zobe da mayafi na fulawa—ya sa ta ƙara haske , amma a fuska akwai shakku, akwai salo na “ba sani ba sabo.” sai dai akwai mutunci a tafiyarta, wanda ba’a koya shi a birni.
“Nafisa itta ce amaryata na biya sadakinta tun can ƙauye kamar yadda na gaya miki. Allah yasa alkhairi.”
Hajiyah Nafisa ta tabe baki cikin murmushi mai nauyin fahimta daga kallon ta ɗaya ka gane ko da tana ƙoƙarin karɓarta, zuciyarta ba ta cikin hakan gaba ɗaya.


Sai da aka kai ta ɗakinta da aka tanadar mata cikin gida ɗaki mai faɗi sosai, bangon sa mai launin cream da zinariya an shimfiɗa masa carpet mai laushi, akwai gado babba da labule mai juyawa kamar na sarauta taga biyu na dakin suna kallon lambun cikin gida, inda tsuntsaye ke ta shawagi, cike da kyan gani. dakin na da fanka da AC, amma Halima bata san amfani da komai ba. Sai kallon su take kamar kayan sihiri.

Ta zauna a gefen gado daidai lokacin wata mai aiki – Hasiya – ta shigo da murmushi a fuskarta. Hasiya daga Sokoto ce, mai ƙanƙantar jiki da zubin kawaici atake suka fara haɗuwa Hasiya ta ce da ita:
“Wallahi Aunty Halima kin yi kyau, da gaske ne ke daga ƙauye?”
“Eh... daga Gembo,” ta ce da dariya mai daɗin ji. “kin taɓa jin sunan kauyen?”
“A'a, amma yanzu na ji ki. sai
End Ads