ya kawo ƙarshen wannan duhu, ya ba mu damar haɗuwa da ƙawayenmu cikin salama.
Hawaye sun zuba daga idon kowa, ba wai kawai saboda baƙin ciki ba, har ma saboda ƙarfin soyayya da bege da muka ɗauka a zuciyarmu.
https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
BAYAN WATA
SABON SALO
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️✍️
08101235739
SHARE FISABILLILAHI
MASU TAMBAYA DA WANDA SUKE KARATU KAR KU MANTA CEWA JOHN NA BAMU LABARIN KASHIFA NE
INDA SABON SALO YA SHIGO LABARIN DA CEWA IHSAN DA ADO MA'AURATA NE SUNA BAWA YARAN SU LABARIN BAYAN WATA LITTLE YAZID DA IMAN .
***********************************
PAGE 44
Daga wancan lokac bamu sake jin labarin Maryam da Munir ba rayuwa ta cigaba da gudana amma ba tare da nutsuwa ba cikin zuciyarmu akwai gibi – wani ɓangare da aka yanke mana da kyar mun rasa su cikin harbi, cikin ƙwantenan duhu, kuma har yau, bamu sani ba – shin sun tsira? ko kuwa duniya ta ci nasara a kansu?
Dani da Ihsan muka cigaba da tafiya… muka iso Dubai cikin gajiya da karyewar zuciya ba mu da komai sai juna da ɗan ƙaramin kaya da muka zo da shi amma zuciyarmu ta cika da mafarkin Maryam da Munir – su ne tamkar jinin tafiyarmu, farin cikin tafiyarmu.
Rayuwar Dubai ba ta karɓe mu da fara’a ba, sai dai da ƙalubale amma a kullum kafin mu kwanta sai mu kalli sama, muna addu’a:
“Ya Allah, idan suna raye, ka ba su ƙarfi. Idan sun mutu, ka ba su rahama kuma idan akwai wata hanya, ka haɗa mu da su.”
Watanni suka shige... duniya ta cigaba... muna nan cikin gwagwarmayar rayuwa, amma a cikin kowace rana, muna jiran wata rana da za ta bayyana kamar hasken safe a bayan dare mai duhu...
Rayuwa a Dubai ba ta zo da sauƙi ba, amma da ƙoƙari da juriya, ni da Ihsan muka fara sabawa muka kama sana’o’i a boye, karatun sana’a, aikin gini da gyaran gidaje a hankali, Ihsan ta fara ɗinki, ni kuma na shiga harkar ɗaukar kaya a kasuwar Dragon Mart.
A cikin wannan wahalar… soyayya ta fara hure cikin zukatanmu duk da cewa mun sha alwashin barin zuciya ta huta, amma lokaci ya tabbatar mana: mun zama juna mun fahimci cewa ba wai kawai haɗuwa ce ta bazata ba – alƙawari ne daga Allah.
Mun yi aure cikin tawali’u, ba tare da dangi ba, ba tare da kawaye ba – sai dai zubar hawaye da addu’a wannan aure ne da ya yi asali daga wahala, ya tsiro cikin kuka, ya girma da tausayi, kuma ya zama ginshiki na sabuwar rayuwa.
Ado ya samu wata dama ta musamman wani dattijo dan Najeriya mai suna Alhaji Abdulrahman ya ɗauke shi matsayin ɗa ya yaba masa da gaskiya, rikon amana da tausayi ya koya masa dabarun kasuwanci, har ya saka shi a cikin harkar shagunan kayan masarufi. Ado ya fara haskawa… ya girma a kasuwa, amma zuciyarsa ba ta manta da abokansa ba – musamman Maryam da Munir da Yazid.
Kowanne daga cikinmu yana da rana da dare, amma a zuciyarmu akwai tambaya ɗaya da ke daure tunani:
“Ina Maryam da Munir?”
A yau idan muka zauna, idan muka yi dariya, ko muka ci abinci, sai mu tuna: wasu biyu sun tafi tare da mu daga gida, amma yanzu... har yanzu ba mu san inda suka ƙare ba.
A Dubai muka haife ku.
Sunan ka — Yazid mun sanya shi ne saboda wani aboki na gaske, wanda ya sadaukar da ransa wajen kare rayuwarmu.
'Yar uwarka kuma — sunanta Maryam.
ba domin baƙon suna bane, a'a mun sanya mata sunan ne domin tunawa da Maryam, wacce muka rasa a cikin hanya.
Maryam da zuciyarmu har yanzu tana yi mata addu’a ta kasance mace mai ilimi, mai jajircewa da zuciya mai kyau ga tausayi da ban dariya
amma duk da wannan wadata da kwanciyar hankali...
bamu taɓa mantawa da wahalar rayuwa ba.
wannan shi ne... BAYAN WATA.
Ta ɗaga kai, ta kallesu ta fara: “mun tashi daga gida da buri mun bar ƙasarmu ba domin mun wuce, a’a domin rayuwa ta ƙi barinmu lafiya muka nufi hanyar da ba kowa ke komawa ba hanya mai cike da hazo, da duhu. a wannan hanya muka rasa abokai, muka rasa jini, muka rasa zuciya… sai dai bamu rasa fata ba.”idanunta suka cika da hawaye, amma sai ta murmusa. “mun tafi da Yazid — wanda sunan ka ke ɗauke da shi ya rasa ransa wajen kare mu mun rasa Maryam — wacce sunan 'yar uwarka ke ɗauke da shi — har yanzu bamu san inda take ba, ko ina take ba amma duk da haka, Allah ya azurta mu da wata Maryam — wacce ta koma Iman, mace mai kyau da nagarta da rahama.”
“Kuna rayuwa mai kyau yau.
Kun tashi da lafiyayyen gado, abinci mai ƙamshi a ɗakin da ke da duminsa, makaranta mai tsari, da soyayyar da ba ta da tsoro amma ku sani akwai wani lokaci, lokacin da ruwa ne kawai ke ɗaukar mu.ruwa mai duhu, mai cike da fargaba ko zai zubar da mu,
ko zai ɗauke mu zuwa gaba mun zauna da duhu mun tashi da safiya, da yunwa a ciki,
ƙishi a leɓe, hawaye a ido mun rayu akan shata mun shiga tsakiyar dabbobi don su ɓoye mu kashin awaki a jikin mu , rashin ruwa bala'e ne har fitsaren mu munsha a sanadin rashin ruwa ƙishi ya kusa zama ajalin mu muna tashin hankali tsakanin rana da da zafin sa cikin wannan yanayi muka nemi halal —
halal namu da wuya, ba da wulakanci ba.
Yau da za a zana mana hoton masu tafiya —
ba tare da sun san inda za su sauka ba tabbas zamu dakatar da su, mu ce musu:
‘Ku jira.’
domin azabar da muka sha ta fi wadda harshe zai iya fassara.
Wannan shine… Bayan Wata.”
Cikin rawar murya da dukan zuciya, Ihsan ta kalli ‘ya’yanta, tana faɗa da tausayi:
A wannan lokacin yaran suka rungume su Ihsan da Ado, zuciyoyinsu cike da tausayawa. Daya daga cikin yaran ya ce:
“Daddy … Mommy … zamu rayu da daraja.
zamu tuna da inda muka fito.
zamu zama masu taimako da tausayi. zamu ci gaba da alkhairan da kuka fara.”
Ado ya daga kansa cikin nuna jin daɗi, ya ce:
“ku zama sakonmu ga duniya.”
Suka ɗan rungume juna cikin nutsuwa shiru ya lulluɓe dakin, amma zuciya tana magana. kuma daga wannan rana, sabon babi ya fara.
Wannan shine Bayan Wata –
lokacin da duhu ya janye, rana ta fito.
https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
🎇BAYAN WATA 🎇
( Beyoung the moon ).
SABON SALO
Labari da tsarawa
Narnah ƙanwar soja
( Sayeedan Adda )
*********
HIKIMATA ABIN ALFAHARI NA
Marubuciyya tana da damar halittar mutum ta kashe shi ta raya shi, tunda 'ƙirƙirar labari ne. ta haɗa masoya, ta wargaza soyayya tsakanin masoya.
Itta baiwa daga Allah ce, ubangiji ke bada itta ga wanda ya so duk wanda aka ba wa itta, sai ya sarrafa ta yadda ya ƙi so: wani ta jawo masa arziki, wani kuma ta janyo masa ɗaukaka da masoya masu girma da daraja...
*****""
Sadaukar wa littafin Bayan wata sabon salo Ga Abokina Mallam Najeeb wanan Sabon salo naka ne shi ke ɗauke da martabar sunanka thank you with your support 🙏
Page 45
"Sometimes... agogo baya karya yana nuna wanda kaddara zata haɗa ka da shi."
Yammacin Jumma’a ce mai sanyin iska da launin zinari a sararin samaniya rana na dushewa a hankali, tana barin haskenta cikin launin kwalli mai laushi anan ne, cikin cunkoson jama’a da motsin kasuwanci, wata ƙamshi mai sanyi da tsabta ke tashi daga babbar kofar Sahad Stores Abuja.
Najeeb ya iso cikin shiga mai kyau, ya zubo white senator ɗin da aka yanke bisa tsari, an danna masa ɗinki na zamani da ɗan kyan embroidery a wuyansa hularsa ta jitu da safa, sai takalmansa masu walƙiya da suka haura baƙi suka karawa tafiyarsa annuri wuyansa na sanye da agogon zinariya, wayarsa a hannu, yana latsawa kamar mai karanta wasu bayanai masu muhimmanci.
Idanunsa suna haske kamar waɗanda ke ganin gaba da nesa, sai miskin kyalli na confidence da ke daddare a fuskarsa. Jama’a na kallonsa – wasu suna fadin:
"Waye wannan kamar Balarabe ?"
"Ba shakka ɗan manya ne ko diplomat!"
Wani kidan qasida ne na Maher Zain yana tashi daga cikin motar da ya fito daga ciki, yana ɗaukar zuciyar wanda ke kusa duk cikin Sahad, babu wanda bai lura da zuwansa ba – kamar yana ɗauke da wani ɓoyayyen saƙo daga wata rayuwa da suka taɓa mantawa da ita.
fitillu suna sheƙi kamar taurari da suka sauko don bautar masu siyayya kowa na gab da kammala siyarsa, amma a ɗaya gefen katafaren building ɗin nan, lefṭar ya buɗe cikin kakkarfar murya da "tingg...".
Najeeb, cikin kamala da nutsuwa, ya taka ya shiga hannunsa rike da katanin electronics, wayarsa a hannu ɗaya, yana kallon notification na "New shipment received - Check email."
Kanshi ɗauke da ƙamshi mai sanyi, daga nesa zaka ce kamar an fitar da shi daga cikin kwali.
A ɗaya ɓangaren store ɗin kuwa, Iman na fitowa daga sashen home décor, Iman ta shigo cikin rigar Valentino purple da gyale mai launin zinariya, doguwar gashi na gyararre da leɓanta masu sheƙi. Hannunta na ɗauke da small purse daga Louis Vuitton kayan da take duba amma sai ga shi yana ɗaukar hankalinta...
"Shine? ko dai yana kama?"
Najeeb na tsaye da natsuwa irin ta wanda ya saba da rayuwar manyan kasuwanci. Hannunsa ya na sauƙa kan agogon hannu — Rolex Sky-Dweller, silver da blue — yana duban lokaci ba tare da ya kalli Iman kai tsaye ba.
🌀 Tana ƙarasowa leftar, sai ido ya sauka kai tsaye kan fuskar Najeeb. Shi kuwa ya danna maballin close, ƙofar na fara rufewa — amma da gaggawa ya fasa, yana nazari kan kyakkyawar mace da ta tsaya a gabansa.
"After you," ya ce, da muryarsa mai laushi wacce ta daɗe da jin turanci da harshen duniya.
Iman kuwa ta shigo cikin lefter kamar sarauniyar wadda duniya ke bi da hange. Idonta a na'urar maballin, amma kunnenta na sauraron numfashinsa ta juyar da kai, ta ce da murya mai kaifi:
"Ba lallai ka tsaya ka rufa min ƙofa ba. I've seen better manners elsewhere."
Iman ta lumshe ido, ta ce da siririyar murya:
"Thanks sorry, I was distracted."
Kofar ta rufe iska mai sanyi ta buga jikin leftar. Shiru ne ya mamaye tsakanin su wanibl ƙamshin turaren su na ratsa zukatansu, amma zuciya biyu na bugawa da sauri wata rana, wata hanya, amma kamar an jima ana jiran wannan haɗuwar.
seconds biyu suka zama kamar mintuna. Najeeb ya kalli bayan Iman, ya ce:
"You remind me of someone I once lost… deeply."
Iman ta juyo da mamaki. "really? that’s strange… you look like someone from a story I wrote and forgot."
Nan ne suka kalli juna – kamar dare da rana da suka hadu a fata tashin hankali, juyin zuciya, da alamomin cewa:
"wannan ba haɗuwa bace – wani ɓangare ne na KADDARA."
Najeeb ya ɗago kai a hankali, sai kallon ɗaya kawai ya yi mata — wanda ya cika da izza da confidence — sannan ya ce da siririyar dariya mai nauyi:
"You’re welcome... but next time, try leading instead of assuming you own the place."
Tsiwa ta hadu da izza. Iman ta kura masa ido tana jin kamar ya karya mata ginin girman kanta na yar masu kuɗi amma ba zata baje ba ta gyara tsayuwa, ta ce:
"Hmm. I guess 'big boys' now come with too much attitude and too little courtesy."
Najeeb ya matse dariyarsa ya zare wayarsa daga aljihu, yana dannawa kamar ba a gabansa ba, sannan ya ce da sauƙin murya:
"Exactly that’s why some of us don’t wait for likes to feel important you just know who you are."
Kafin Iman ta bata rai sosai, lefṭar ya tsaya.
sai kowannensu ya fice a gefe daban — kamar ba su yi magana ba, amma zuciyarsu na kwaɗayi, tamkar sautin tambaya:
"Waye wannan?"
"A ina na san shi?"amma rana ce da za ta bar sanyi. Ranar da kaddara ta ɗan jefa ƙuri'a — kuma ta gyara tsari a cikin zukata biyu da ba su san sirrin juna ba tukuna...
"Sometimes... agogo baya karya. Yana nuna wanda kaddara zata haɗa ka da shi."
Sahad Store upstairs yau kamar wani mini Dubai yake kayan alatu, turaruka, agogo, jakan fata, da kayan designers sun sha kwalliya a racks kamar su na jira mutum guda — Iman.
Turarukan “Maison Francis Kurkdjian” — wanda ba kowa ke iya kamshin su ba.
Ya kalli kayan, sannan idonsa ya sauka a kan turaren da Iman ke dubawa Sai ya ce da murya mai sanyi:
"You won’t find your scent in shelves… such a presence deserves exclusivity."
Iman ta ɗaga kai a hankali, kamar ba ta sa ran magana ba, amma murmushinta ya ɗan bayyana ta ce:
"Really? and what exactly does exclusivity smell like?"wata rana, wata rana kuma yau ce. Idonsu ya haɗu, zuciyarsu ta ɗan bugawa.
Najeeb ya ɗauko wani turare daga glass case, ya ce:
"Try this. It's called ‘Oud Satin Mood’ — classic, deep, unforgettable… kinda like the person I'm seeing right now."
Kamshin turare ya buɗe musu ƙofar zumunci, kalmomi sun fara fita a sanyi, ƙila a rikice, amma zuciya na ɗaukar ajiya. Kusan suyi magana sai wani staff ya ce:
"Sannu ku duka... turaren nan da agogon nan suna cikin exclusive couple’s gift package."
kallon da suka yi juna sai suka saki dariya...
A hankali zuciyarsu na furta kalmar da ba su ce da baki ba:
“Shin kece?”
“Ko kai ne?
Iman ta ce da tsawa mai kwalliya:
"I don't need a timekeeper. I make my own timing." Najeeb ya ce, yana dariya:
"That’s exactly what I thought the first time I saw you I guess timing agrees with us again."
Sai kallon idanu ya jima, har sai jikin turare ya faɗi daga hannunta ya zaro hannu ya tare kafin ya faɗi ƙasa.
Ta kwace masa da ƙarfi kamar zata zuba masa a fuska.
Fuska a haɗe ta juyo a zafafe da nufin bangaje shi, cikin rashin sa'a santsin plat shoe na ƙafarta ya haɗu da na tiles ya zamar da ita suuu!!.
Zazzaro ido suka yi daga uta har shi, cikin zafin nama ya finciko hannunta ta faɗo kan ƙirjinsa. Dim!!, dim!! didim!!! dim!!! Zuciyoyinsu ke bugawa a tare cikin wani mugun gudu, gabaki ɗaya sun manta inda kansu yake sun ƙure juna da kallo ido cikin ido yayin da kowa ke karanta wani babban lamari a tare da ɗan uwansa.
Da sauri Iman ta ɗan gyara numfashi tana ƙoƙarin zamewa.
"Lokaci yana faɗin abu daban da zuciya, ko?" Najeeb ya faɗa cikin muryar raɗa.
Ta kalle shi tana turo baki gaba, kafin ta ce
"Ka cire hannunka ko sai na saki kukan da zai tarwatsa wannan shagon."
Ya janye jikinsa cikin hanzari yana sakin wani yalwataccen murmushi gami da sauke nannauyar ajiyar zuciya
“Sai dai kukan zuciyar ki, shi ba zan iya tsayar da shi ba.”
Iman ta ji kamar zuciyarta ta faɗi — ba saboda soyayya ba, a'a saboda kunya da ƙiyayya da shagwaba da suka haɗu waje guda.
“Wuce ni! Ina ruwanka da ni!”
ya ɗan matsa gefe yana faɗin
“Toh, Allah ya bada haƙuri tunda nayi abun a yaba ya zama laifi, ban shirya ganin wannan kyakkyawar halittar a ƙasa bane shi yasa na tare!”
Wufff!
Ta yi yunƙurin tafiya da sauri, tana kaɗe gyalenta, ya tashi kamar banner, amma ƙafarta ta sarke da gefen rug.
rimm!!
Ta faɗi a ƙasa.
Kayan leda na “Lancome” da “Versace perfume” suka zube… shagon yaja ido.
Masoya biyu sun zo ta hanyar agogo suna rike hannu — sai suka tsaya suna kallon ta.
Ɗaya daga cikinsu ya furta da mamaki:
"Wallahi kamar scene ne daga 'Karma in High Heels'." wata budurwa na gefe ta ɗan lumshe ido ta ce:
“OMG! Ta faɗi a gaban that fine guy! 😩😭”
Najeeb dai…
Ya tsaya hannayensa zube a aljihunsa, yana ƙoƙarin hana dariyarsa fitowa.
A hankali ya taka kusa da ita ya ɗan durƙusa saitin fuskarta kafin ya ce
“Next time ki karɓi turaren ki zauna lafiya zaki fi dacewa da Rolex fiye da ƙasa.”
Iman ta haɗiye numfashi ta kalle shi — kallo na kunya da zafi, kallo mai cike da tambaya:
“Waye kai?”
Sai kawai ya janye Versace turaren daga ƙasa, ya miƙa mata:
“Wanda zai saka ki manta da faɗuwar yau... ko ki tuna da ita har abada.”
Iman ta miƙe daga ƙasa da sigar ɗan rawar jiki, sai ta gyara mayafinta kamar wacce za ta ɗauki fansa a gasar duniya.
Ta matso kusa da Najeeb, idonta cike da ƙyashi da borin kunya da girman kai irin na 'yan manyan gida.
“Daga faɗuwa har zaka bi ni? Me nake da kai?”
Sai ya yi murmushin da ke iya janyo fans a TikTok:
“Kinyi kyau da fushi, amma fushi ba zai iya janyo min gaba da ke ba...”
Ta ɗan buɗe baki da mamaki, sai ta haɗe rai ta ce:
“Kai ne kawai kake ganin haka ka daina min ruwan yawu da magana kamar ‘classic line’.”
Sai ta juyo da sauri — gyalen ta na tashi kamar tsintsiyar shara tana tafiya da ƙyau, duk da cewa zuciyarta na bugawa saboda faɗuwar da ta sha.
Ta harare wasu budurwai da suka ƙyalƙyale da dariya, sai suka kama baki da “OMG! 😭 She’s fierce!”
Najeeb kuwa...?
Yayi ƙasa da ƙafa yaje payment section da style irin na manyan masu kudi, yana kadawa da card ɗin sa na black platinum.
“Dukkan kayan da waccan budurwar ta saya – hada da turaren Versace da agogo – ka haɗa su cikin bill ɗina.”
Ma’aikaciyar store ɗin ta buɗe baki:
“Toh ranka ya daɗe.”
Ya ɗan murmusa, ya juya kamar wanda ya gama mission, sannan ya wuce ba tare da waiwayar baya ba.
Iman ta iso wajen cashier, tana ta hararan duniya, zuciyarta cike da faɗuwar lamarin da ta sha.
Sai tace da ƙarfi:
“Ina bill na please?zan biya.”cashier ɗin ta ce da fara’a:
“Already paid, .adam gentleman din da kika faɗi a gabansa ya biya komai.”
“Whaaat?!”
ta buɗe ido, ta ɗauke numfashi. Sai kawai ta lumshe ido tana fadin:
“Wayyo Allah, faɗi guda na mayar da shi ‘Prince Charming’?”
Wani murya daga nesa ta ce: “kuma kin ce masa ya daina bibiyarki...” ta juya da sauri. Najeeb ya ɓace.
Iman ta lumshe ido, zuciyarta na bugawa tamkar kararrawar wuta kawai ta ce da cashier din:
“Yayi hakan da gangan wallahi wannan raini ne!”
Cashier ɗin ta ɗan matsa gaba da voice of gossip:
“To Madam, ai duk abinda ke faruwa muna ganin sa a camera hakan ma ya faru a gabanmu sai fa nace ke kika faɗi, ya kamaki kamar Cinderella, agogo ya zube...”