x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 16 - BAYAN WATA

  • 45001 words
  • 48000 words
  • Out of 71166 words

Category: Love Stories

Views 142

04 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
mafarkin gida; ta na lumshe idanu kamar mai adana sirrin zuciya; Ado kuwa sai kallon sararin sama yake yi kamar yana neman amsa daga sama.Sai John ya kalli kowa, yana murmushi da ƙaramin dariya mai sa nutsuwa.

"Ku saurara," ya ce, yana zura ido ga kowannensu, "zan baku labarin nishadi – na gaskiya domin mu ɓata lokaci mu manta da ƙuncin hanya."
kowa ya juyo gare shi. Ihsan ta ɗago kanta tana fadin, "Toh John, bari mu ji. Amma kar ya kasance na ban tsoro fa."
John ya dariya. "Wallahi ba tsoro ba ne, sai dariya, amma ku zauna lafiya ku saurara."
sai ya fara da murya mai ɗauke da salon barkwanci:




...................................

https://chat.whatsapp.com/Bd1Zu1cwIO81A7rrATd4Cu


💫⭐BAYAN WATA 💫⭐
sabon salo
By
Narnah Kanwar soja
08101235739






PAGE 37




Kauyen Tsuntsuwa ƙauye ne da ke labe a cikin zurfin wani kwari, inda duwatsu suka zagaye shi kamar gadin sirrin duniya. Rana tana faɗuwa kamar kullum, amma a Tsuntsuwa, faɗuwar rana na nufin ƙarewar alfarma domin daga nan ƙauyen yana komawa hannun duhu da shiru.

Babu lantarki, babu hanya mai kyau, babu makaranta sai ƙarar kwanoni da gudun yara, sai shawagi da kururuwar matan da ke wanke wanke a bakin rafi , idan ka taka ƙasa a Tsuntsuwa, zaka ji ƙurar da take ɗauke da tarihin shekaru ana cewa kauyen yana da shekaru fiye da ɗari uku, kuma babu wani mai rikodin tarihi da ya rubuta komai a kansa.

Gidajen mudu ne, daga laka da kwalli, sai rufin buhu da zogale gidan mai unguwa shine mafi girma, amma da ka shiga zaka san sarki da talaka daidai suke mutane suna rayuwa cikin sauƙi da daraja, amma jahilci ya shafe zukatan su har ya zama girma.

A tsakiyar kauyen akwai tsohuwar bishiyar tsafe-tsafe, wacce kowa ke shakkarta ana cewa an binne aljanun da suka kafa Tsuntsuwa a karkashin ta a kusa da bishiyar kuma akwai rijiya mai zurfi da aka hana yara kusantar ta ance rigima a ciki ke jawo mutuwa wasu kuma na cewa “duk mutumin da zai yi hankali a Tsuntsuwa, sai ya manta da hankali nasa.”



A cikin wannan ƙauye ne aka haifi Kashifa wata kyakkyawar halitta mai kimanin shekaru goma sha ukku fari a launi, doguwa a halitta, mai idanu dara-dara kamar dare ba kowacce yarinya bace ba; facce ce ta ƙauyen. Ita ta tashi cikin cikin duhun jahilci da namun daji, amma zuciyarta cike take da haske da tambaya.

Kashifa yarinya ce mai kwaikwayo, mai yawan tambaya, mai son saka ido cikin komai ta fi ƙarfin 'yan mata, ta fi kuzari da saurayi. Idan Kashifa ta ce zata shiga rafi, kowa zai hau tsaye; idan ta ce zata hau itace, to ka yi shirin cin kwallon kunya.



Tsakar rana rana na dumama tamkar ana soyayya da rana kai tsaye. Kashifa da ƙawarta Fatu suna zaune a ƙarƙashin bishiyar ɗan kanzon su na gunduma idon su biyu sai kalle-kalle suke yi, suna nazarin hanyar da zata fi sauƙi su kutsa gonar Mangoron Malam Dandago.

"Kashifa wallahi yau zan ci sabuwar mangoro!" cewar Fatu tana ɗaura zaninta kamar jaruma a film.
"Fatu ki rage murya mana! ki manta da yadda ya kama Mu’azu ya sa shi tonon kasa da cokali har sai yazo har ƙasa!" Kashifa ta faɗa tana dariya.

"Eh mana, amma Mu’azu gajere ne, mu fa muna da gudu!" da sallama suka zura kai cikin gonar, suka fara zabga wa mangoro mari. Mangoro na faɗowa kamar ana jefar da azurfa daga sama. Fatu ta zuba cikin buhun riga, Kashifa kuma tana tsince mai laushi.

Cikin kwana da wani, muryar Malam Dandago ta daki kunnensu kamar karar kararrawa "A’a yau na kama ku! wai ni da gonata ba komai ba ce?!"
Kashifa ta zura mangoron hannu cikin hijabi, Fatu kuma ta jefar da nata tana fadin:
"Gudu Kashifa gudu! Dandago ya fito da sanda!" gudu suka rika yi kamar an sako su daga rijiyar sha'ani. Fatu ta ruga ta faɗi ta tashi, Kashifa tana cewa:
"Idan ya kama mu wallahi sai ya sa mu shan ruwan tafki da cokali!"
Dandago ya biyo su amma sai ya tsaya yana huci da tsaki:
"sai dai in kama ku da duban hankali... amma wallahi sai na ce da iyayenku!"

Suna isa bayan gida, suka shaƙa juna da dariya suka faɗa a kasa suna juyi Fatu ta ce:
"wallahi wannan shine mafi zafi da daɗin mangoro da na taɓa ci!"
Yayin da gudu ke neman sufi sauri da iska, Kashifa ta ruga da kafa irin ta gudun “Marathon”, bata ko kallon gaba tsautsayi

“Yiiiiiiii!” wata kara ta tashi! Gani aka yi wani tsoho ya yage ya zube a ƙasa, wata leda mai fassarar “Egg carrier from heaven” ta baje, ƙwai ya watsar tamkar an watsa jinin rake!
“na shiga ukku na lallace !” Kashifa ta tsaya cak tana fadin:

"Wayyo na shiga uku! Wallahi ban ganka ba Malam!"

Tsohon ya tashi da cikar ƙwazo da huci yana nunata da yatsa:
"Ni Malam Sambo ne! Na shekara biyu ina kiwon kaza don in samu na kasuwa, ke kuma cikin 'yan saniyar ware kike zo ki lalatamin arziki da gudu!"
Fatee ta taho tana dariya tana rik'e ciki tana faɗin:
"Kai Kashifa! kin lalata kwai! Wallahi ke ce makashiyar kwai kaza' yanzu!" Kashifa tana tafa hannaye tace:
"Wai Malam don Allah ya rage fushi! Wallahi gudun Malam Dandago muke, shi kuma sai na makale a jikinka."
Malam Sambo ya dumfari Kashifa yana faɗin:

"To wallahi sai kin biyan kudin kwan nan! ko kuma ki zo ki kwana da kaji na in zaki gane yanda ake kiwon su!" Fatu ta daka tsalle tana faɗin:
"Ai wallahi Kashifa sai kin yi 'nagudar kaji! kin lalata arzikin mutumin kirki!"

Kowa da kallo a kauyen, yara sun zo suna tsugunne suna tattara 'yan kwan da suka rage da rai. wata kaka tace:
"sai addu'a ya shirya 'yan mata yanzu, gudu kawai ba kallon gaba!"






Ya zata kaya tsakanin Malam Sambo da Kashifa?...
https://chat.whatsapp.com/Bd1Zu1cwIO81A7rrATd4Cu

BAYAN WATA
SABON SALO
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️✍️
08101235739
SHARE FISABILLILAHI







MASU TAMBAYA DA WANDA SUKE KARATU KAR KU MANTA CEWA JOHN NA BAMU LABARIN KASHIFA NE
INDA SABON SALO YA SHIGO LABARIN DA CEWA IHSAN DA ADO MA'AURATA NE SUNA BAWA YARAN SU LABARIN BAYAN WATA LITTLE YAZID DA IMAN .

***********************************

PAGE 38




Wani ƙwarya-ƙwarya rikici a tsakiyar ƙauyen tsuntsuwa Kashifa na tsaye a gaban Malam Sambo, jikin sa duk ya baɓɓare da kwai, fuska ta kumbura da fushi kamar zai lashe duniya. Fatu dai tun can tuni ta juya gefe kamar mara lafiya da gudu.

"Wallahi Kashifa, yau zaki gane cewa ni ba ɗan wofi bane! wannan kwai zan siyar ne a kasuwa gobe!" ya daka murya da karfi
Kashifa ta runtse ido, ta ce da wata muryar tausayi, "to Malam ai ba da gangan bane... Ka sani dai ni yarinyar da bata da laifi ce..."
"Karya! Karya nake ji! Idan kin dafa ni da gangan ko a'a, sai na ɗau fansa!"

Kashifa na kallon shi da alamar rauni da kuka, ta sunkuya kamar mai neman gafara mutane sun tsaya gefe suna jiran yadda rikicin zai kare.

Amma kafin ya ƙara magana, Kashifa ta zaro ƙasa daga gefen hanya – daidai wani dattin laka da ruwan kwai a ciki – ta fizga hannu kamar zata mika masa hakuri… sai kawai ta watsa masa duka a fuska!

"Kai! Idona! Idona Kashifa!" Malam Sambo ya kama ihu yana taka rawa, hannunsa na gogewa cikin ido da kwai da laka.

Mutane suka saki dariya.

"To wallahi malam, daga yau ka sani, ba a hura mini ido da kwai kuma a bani cin mutunci ni ce Kashifa ƴar Kulu, ba’a tsorata ni da kwai ba!"

Sai wata mata ta fasa dariya tana cewa:
"Allah ya isa! Wannan dottijo yaci karo da Kashifa ƴar magajin dare! ai sai dai ya wanke ido da ruwan daddawa!"
Kashifa ta fizgi ƙafafunta da karfi, ta fasa gudu tana cewa "In ka gama kuka malam ka bar hanyar mangwaronmu!"

Yara suka biyo ta da dariya da ihu, wasu suna taɓa Malam Sambo da:
"Malam, munce kar ka yi wa Kashifa magana, ai kace kai dodo ne!"
suna shigowa gida kamar gwaggwabar iska — Mangoro a hannu, dariya a baki, turɓaya a ƙafafu.

Kakarsu, Inna Mairo , na zaune bisa tabarma tana tsuma kayan ƙauye: kifi mai ƙamshi, dambu da kwai da aka bar a kasa saboda tashi tana sanye da mayafi mai datti wanda ba’a iya banbance launi ba — kamar tsohuwar barkono da gishiri sun yi aure.

"Kashifa! Fatu ! ku daga ina haka da wannan yunƙuri kamar an aiko ku daga Sahabbai?"
Kashifa ta ajiye mangoron ta kamar zakaran da ya lashe dambun masara.

"Inna, ba laifi bane idan yaro ya ci abinci daga gonar da Allah ya halitta! ai ba mu sace ba, mu dai ɗiba muka yi!" Fatu ta karɓa da cewa:
"Inna kuma Malam Sambo ya ce zai ga mana kashi saboda an buge shi da kwai! Wallahi da yaga halin Kashifa, ya gane ba buɗa-baki ba ce."

Inna ta girgiza kai tana dariya:
"Kashifa, ke ba mace bace ke muguwar tsuntsuwa ce da aka haifa da kafa biyu da laɓɓe guda biyu! wata rana zaki tada ƙauyen nan gaba ɗaya!"
Fatu na gefe tana jujjuya mangoro tana cewa:
"To inna tunda muna da wannan ɗakin garwaya na kaɗan da ke da firam mai rami, sai mu zauna mu huta mu ci mangoro."

Kashifa ta haye tabarma suka zube a cikin ɗakin ƙanana: gadon kara biyu, tulu mara aiki, da bokiti mai fashe a gefe.
Sun jera mangoron a cikin kaskon tuwo, sai su ce:"Wannan shi ne gatan mu a yau jikan mangoro da dare cikin dakin tsohuwa!"

Kaka ta ajiye gishirin da take tumshewa, ta ce:
"Sai ku san da safe zaku tashi da gudawa — in Malam Sambo ya shigo da sanda ku san ba satar mangoro ake yi ba."

Kashifa ta ɗan buɗe kofa tana kallon waje, sai ta ce "Inna idan ya zo, mu turo kwai da dambu sai ya koma da burin shi." wani irin ihu da hayaniya ya tashi a waje kamar ana kwasar mutane zuwa Llahira.

Kashifa da Fatu suna tsakiyar ci mangoro, sun kasa ci sun kasa hadiyewa kamar tsuntsaye da suka hango baƙin gizo.

Kaka Inna Mairo ta ja zani ta fito, tana zare idanu da sandarta a hannu.
"Wa ke ihu a kofar tsohuwa haka?! Ko dai gobarar rijiya ce?!" sai kawai ta hango Malam Sambo, mai mangoro da wasu maza biyar, kowanne da sanda ko kasko a hannu, wasu suna da kwai a riga sun kwara musu. Idanunka su sha.

Malam Sambo na ihu yana cewa:
"Ina Kashifa! wacce ta buge ni da kwai ta kuma kwace mangoro kamar Allah ya sauke su a saman gonar mutane?!"
Mai mangoro ya ce:
"Wallahi in ban ga ta ba yau, sai dai an zo da karar kwashe gawa a kwashe ni da zuciya!"

Kaka ta dafa bango tana shan numfashi kamar mai zazzaɓi.
"Wayyo ni Mairo wannan Kashifa zata bani tabo a ƙarshe ashe mangoro da kwai suka jawo min rundunar maza a kofar gida?"

Kashifa ta leƙo daga ƙofar ɗaki, tana tafe da ɗan kwano cike da goro da mangoro da dan buhuna a wuya, ta ce:
"Malam Sambo... wallahi bugeka da kwai ba da gangan na yi ba amma ka duba lafiya da shan kwai da magani , ai komai da lada."

Malam Sambo ya ja numfashi ya daka tsalle,
"Wato kin taya ni ci gaba da hauka? Ku fito! Ku fito ku fuskanci ƙaddara!"
Fatu ta ce:
"To malam mu fito, amma kayi hakuri fa ai mangoron naka ya janyo rikici fiye da gwangwani!"

Kaka Mairo ta tsaya tsakanin su da runduna kamar tsohuwar gwarzon soja.
"Ku yi hakuri, ku gafarce su gaba dai za mu rama na rantse da sandar nan ba zasu ƙara ba."Malam Sambo ya ce:
"Ai sai sun gyara gonata kuma sai sun bani kwai hamsin na fansa! kuma...!"

Kashifa ta yatsine baki ta ce "to me kuma? sai a ce mu biya da yawu kenan?"
"wallahi malam..." ta ce tana sunkuyar da kai, "...ina so na ce maka..." kawai ta ɗibo ƙasa a hannu — CHUWA! — ta watsa masa.

"Ahhhhh! ido na! wayyo mangoro na!" Malam Sambo na birgima yana rike ido Kashifa da Fatu suka yi sukuwa kamar an aiko su daga sama.


Fan's ya wannan page nin
ina fatan labarin Kashifa na kayatar da zuciyar ku mujeee zuwa muga karshe labarin Kashifa..

Narnah ƙanwar soja ✍️✍️



https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC


BAYAN WATA
SABON SALO
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️✍️
08101235739
SHARE FISABILLILAHI







MASU TAMBAYA DA WANDA SUKE KARATU KAR KU MANTA CEWA JOHN NA BAMU LABARIN KASHIFA NE
INDA SABON SALO YA SHIGO LABARIN DA CEWA IHSAN DA ADO MA'AURATA NE SUNA BAWA YARAN SU LABARIN BAYAN WATA LITTLE YAZID DA IMAN .

***********************************
1 / 6 / 2025
PAGE 39





Yayin da rundunar maza ke zazzaga ihu da gudu Kashifa da Fatu suka nausa wajen rijiya, rigima na biye da su kamar gobara a daji wani daga cikin mazajen ya hango inda suka nufa ya yi kara: "kai! kada ku shiga hanyar rijiya mai hatsari! ai an hana kowa wucewa can tun shekaru masu yawa!"
Sai dai Kashifa da gudunta na agwagwa a iska, ba ta ji komai ba Fatu na kiranta tana haki: "Kashifa! Kashifa! daga nan ba wucewa! Sarkinmu ya ce ya hana zaki mutu ne!"
Kashifa na cigaba da tsalle kamar ƙaramar damisa sai gashi ba zato, ta shige har tsakiyar hanyar rijiyar.
Fatu ta tsaya cak!
tana haki, tana duban baya da gaba, tana jin saukar ƙafafun mazan da suka tsaya su kansu suna fargaba.
mun shiga ukku !” wani daga ciki ya furta.
“Yarinya ta shige hanyar da sarki ya ce shaidanu ke rayuwa a can.”
Malam Sambo ya ja baya da sassarfa:
“Ni dai na riga na ce mu dawo ido ɗaya ya isheni…”
Fatu ta fashe da kuka:
“Kashifa! ki fito wallahi ba wanda zai kamamu. ki fito kafin wani abu ya same ki!”
sai dai an wayi gari — Kashifa ta ɓace cikin hayakin rijiya.
Wata ƙasa ce mai fashewa da iska irin ta tsufa, ana jin ƙarar iska tana kiran sunanta kamar an saka mata sunan a cikin guguwa:

“Kaaaashiiifaaa… Kaashiiifaaa…”

Fatu ta tsugunna, tana kuka kamar karamar yarinya "wayyo Allah, don mangoro ne da kwai Kashifa ta shiga wuta ta mutu ta bi iska "

Malam Sambo ya ja sanda ya ce:
"Wallahi wannan yarinya ta kai mu ga hauka. ba zan sake binta ba."

Kaka Mairo da ta iso da gudu ta tarar da Fatu a kasa, sai ta ɗauke ta da duka sanda, tana cewa:
“Ke , kin kai diyata ga rijiya mai tsafi? wallahi zan buga ki har mangoron ya fito da kansa!”




Washe gari... rana bai ko fara hango ƙasa ba, sai ga garin ya cika da hayaniya.
A kofar hanyar rijiyar nan mai hatsari, mutane sun taru kamar ana raba sadaka: dattijai, matasa, yara da kowa na firgice, wasu na hawaye.
Sarki Idris da rawanin sa mai fadi, ya iso cikin takun mulki.
gaban sa akwai fadawan sa, kuma Malam Sambo yana bin bayansu da sanda a hannu, yana yatsina fuska kamar wanda ba ya jin daɗin shiru.
Wani dattijo ya yi magana cikin murya mai ƙarfi:
“Shekaru 300 da kafuwar kauyen nan kuma kowa yasan hatsarin daki tattare da hanyar nan kenan da aka hana wuce wannan hanya. duk wanda ya shiga bai fito ba ashe yau yarinya ‘yar gidan Mairo ta shiga!”

Sarki ya kalli hanya da idon tsoro da mamaki:
“Wannan ba wasa ba ne akwai abin da ke faruwa a nan cikin.”
Kaka Mairon tana kuka tana tsugunne:
“Sarki ka ceci jikan ta… Kashifa bata da hankali, wallahi kawai satar mangoro ce ta jawo mata shiga banza.”

Fadawa na kalla juna suna girgiza kai.
wani ya ce “Wallahi ko kuwa jinnai na nan me ya sa ba wanda ke rayuwa idan ya shiga?”

Sai ga Fatu da kai a ƙasa, tana tsugunne tana hawaye kamar ruwan sama:
"Ni ce na jawo ta nice nace mu je ai da ban ce mu ɗebo mangoro ba..."
Sarki ya ce:
“Shiru! A turo malam bori a san menene ke faruwa ta mutu ko zata ko akwai rayuwa kuma a ajiye alƙalami da lauje a rubuta wannan rana, domin tarihin gari ba zai manta da ita ba.”

Takalmin Kashifa aka tsinta a bakin hanya da jinin yatsar ƙafa a gefe.Wani tsoho ya furta da harshen kauye:
“Idan Kashifa ta fito da rai, to akwai sirri. kuma akwai wuta a cikin ruwa.”

Washe gari...
Garuruwa uku sun haɗu a kofar hanyar rijiyar da aka daina bi tun zamanin Sarki Gidado.

Mutanen kauye da Sarki Idris, dattawa da malaman tsafi sun taru kowa da dariya mai ƙarewa da damuwa mara iyaka.
Kaka Mairo na kuka da kururuwa, tana ta kiran sunan Kashifa da murya mai firgita Fatu ta durƙusa gaban Sarki, hawaye na gangarowa daga idonta:




Sarki Idris ya juya ya kalli masu bori
“shin me yasa babu wanda ya taɓa shiga ya dawo? me ke ciki? mun san aljani ne ko tsafi?”
Shehu ya girgiza kai cikin tsananin fargaba:
“ bayan shekaru 300, ma’anar wannan hanya ta ɓace a cikin tarihinmu. Littafin duhu ne ya ɗauke ta amma duk wanda ya shige ta ko mutum ne ko dabba ba a taɓa ganin sa ba ko jin sa.”

Jama'a suka hau ihu “Kashifa! Kashifa! A
Sarki Idris yace cikin kururuwa “ba wanda zai kusanci wannan hanya! a kafa doka — a fitar da sanarwa! wanda ya sake yunƙurin shige hanyar nan zai fuskanci hukuncin kauye. amma yanzu...a kewaye hanyar nan da shaida ko bayan mutuwar ta sarki magana kiyaye zaiga alamar bazai iya ƙetarewa baa

maso bori suka zauna cikin shiru, kowa ya durƙusa, zuciya cike da ɓacin rai da tsoro.
a can cikin daji... shiru ne tsit.
kamar ba a taɓa rayuwa ba a duniya....



Narnah ƙanwar soja ✍️✍️


https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC


BAYAN WATA
SABON SALO
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️✍️
08101235739
SHARE FISABILLILAHI







MASU TAMBAYA DA WANDA SUKE KARATU KAR KU MANTA CEWA JOHN NA BAMU LABARIN KASHIFA NE
INDA SABON SALO YA SHIGO LABARIN DA CEWA IHSAN DA ADO MA'AURATA NE SUNA BAWA YARAN SU LABARIN BAYAN WATA LITTLE YAZID DA IMAN .

***********************************
03 / 6 / 2025
PAGE 40



Bayan kwana bakwai da ɓacewar Kashifa…
ƙauyen tsuntsuwa tabbataccen duhu ya koma kamar baya da haske ba a jin dariya a ƙofar rafi, ba a ƙara ganin yara suna wasa da kekuna a kasan itacen tsamiya kowanne gida ya ɗauki
End Ads