x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 21 - BAYAN WATA

  • 60001 words
  • 63000 words
  • Out of 71166 words

Category: Love Stories

Views 144

04 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
hijab masu tsada.

Tafiyar za ta kasance kamar mafarki – cikakken tafiya daga Abuja → Madinah → Makka → Jeddah.

***************
Zuwa Ƙasa Mai Tsarki

Washegari da safe, Abuja International Airport ya cika da hayaniya, walwala da motsin tafiya. Iyayen Iman da Yazid – Daddy da Mommy – suna sanye da kaya masu kyau da nutsuwa, fuskokinsu cike da annuri da godiya ga Allah. Tare da su akwai ƴan uwa da abokan arziki da suka yi nasara samun wannan tafiya.

Iman ta fito cikin doguwar abaya blue mai sheƙi da veil white, fuskar ta cike da natsuwa da fara’a. Yazid na gefenta yana rike da small carry-on luggage, yana duba boarding pass ɗin su.

Tayi murmushi cikin zuciya. "Ya Allah, na bar komai a bayana… har da Najee– ehm…" ta taɓe baki tana sauke ajiyar zuciya.
Gaskiya, zuwa ƙasa mai tsarki ba kamar duk tafiya ba ce. Rayuwa da abubuwan duniya na koma baya, ruhu na kama tafarkin Allah.
“Iman! Ga takalman ki sun kusa zamewa…” Mommy ta ce da dariya, tana gyara mata hijab Yazid ya leƙa daga bayan trolley:
“kin fi kowa kyau yau… kamar ba ke ba!”
Iman ta saki dariya tana jefa masa harara.
“bari dai ka gani lokacin da na iso Harami, da ka ga tsoron da zan ji da farin ciki, da wata irin nutsuwa…”

A cikin jirgi, komai cikin lumana da salati ana zaune cikin jerin kujeru business class, inda aka raba kayan karatu, dates da ruwan zamzam. Flight attendant ɗin sun amsa da "Assalamu Alaikum" cikin ladabi, kowa da fuskar tsarki.

Iman ta kalli tagar jirgi, tana ganin kasa na raguwa ƙasa "Wai ni har na bar Abuja kenan? Wannan rayuwar can, rubuce-rubuce, Instagram, kukan zuciya… komai na duniya ya bace a idona yanzu."
ta lumshe ido, hawaye suka sauko cikin farin ciki "Allah! Na barka da komai ka kawo ni gun Ka lafiya, ka karɓi zuciyata kamar yadda take."
Yazid yana gefenta, ya sauke ajiyar zuciya “Na saba da tafiya, amma wannan tafiyar... sai dai in ce haji ce ta ni’ima. Allah yasa mu dawo da rahma da canji.”





Bayan tafiya mai albarka da natsuwa, jirgin ya sauka a King Abdulaziz International Airport – Jeddah. An karɓe su cikin kulawa da jagora na musamman, an ɗauke su cikin mota mai sanyi da tsabta – sun hau hanyar zuwa Makkah Al-Mukarramah, gari mai albarka.

Kamar mafarki ne a zuciyar Iman lokacin da suka fara hango babban Clock Tower da minaret na Masjid Al-Haram suna leƙo daga nesa. Ta sauke hawaye, zuciyarta na bugawa da ƙaunar wurin da Allah Ya ke kira har aka karɓe su.

> “Wannan ba gidan kowa ba ne, ba wurin yawon buɗe ido ba ne – wannan ƙasa ce mai tsarki. Ni dai Iman… na sauka.” ( tare da ƙanwar soja mai ɗauko rahoto daga cikin jakar Iman lolz)


HOTEL: Swissôtel Makkah

An kai su Swissôtel Makkah, ɗaya daga cikin fitattun hotel-hotel guda bakwai da ke cikin ginin Abraj Al Bait Complex – d’aya da Clock Tower. Hotel ɗin yana da fuska kai tsaye zuwa Harami, kuma suna kallon Ka’abah daga manyan windows ɗinsu.

Swissôtel Makkah ya amshi su da kulawa an basu suites masu kyau da tagogi masu kallon Ka’abah kai tsaye. Komai ya cika da tsari da tsabta:
– Gidan wanka mai fumfuna na zamani
– Beddings farare masu ɗumi da tsafta
– Kayan sha da kayan ciye-ciye na musamman
– Wi-Fi da Qur’ani a cikin kowane ɗaki


Iman ta hau gadon ta, ta kalli Ka’abah daga taga “Allahu Akbar wannan wurin ya fi kyau da tsarki fiye da duk inda na je. Nima fa yau na iso ƙofar rahama.”



Ta dafa kirjinta, zuciyarta na bugu da sabuwar soyayya – ba soyayyar duniya ba, sai wacce ke cike da tsoron Allah da shauƙin kusanci da Ubangiji.

Mommy ta shiga ɗakin tana kallon ta.
“Iman, Allah Ya albarkaci zuwan mu wannan tafiya za ta canza mana komai imanin sabon yanayi tamkar ban taɓa zuwa nan ba inajin wani bayyanar abu tamkar Ubangiji ya amshe addu'a na na tsawon shekaru …”
Iman ta kalli mahaifiyarta, ta ce cikin tausasayyen murya:
“Mommy… na yarda yanzu: akwai natsuwa da zaman lafiya a ƙasar da zuciya ke kiran Ubangiji fiye da duniya.”



Cikin natsuwa da tsoron Allah, Iman, Yazid da iyayensu suka shirya cikin kayan Umrah — Iman cikin farar abaya mai ɗaukar ido, da nikabinta da ya leƙa da kyakkyawar nutsuwa. Yazid cikin farin ihram yana waƙar Qur’ani cikin ƙasa da murya. Su Daddy da Mommy kuwa, kowanne ya sha ado da dattijantaka da ladabi na masu tafiya ga Allah.

Gaban ƙofar King Fahd Gate, zuciyar Iman na harbawa kamar ana bubbuga ganga. Sai da ta kama hannun Mommy tana dafe ƙirji.
"Mommy... wannan shine Harami? Shine nan Ka’abah ke ciki?”
Mommy ta dafa kanta, ta ce:
"Eh... nan ne mafita ta duniya. Mafarkin kowane mumin."
Suna taka kafarsu cikin masallacin, sai kwarjininta ya daki su. Fuskokinsu suka kai ƙasa, zuciya ta cika da rawar murya, hawaye na zuba... har suka isa da'irar Ka’abah.
Iman ta tsaya cak tana kallon wannan Ginin Mai Tsarki da aka gina da duwatsu masu ɗauke da tarihih.
“La ilaha illallah…” “Subhanallah…” “Na iso… ya Rabb.”

Suka kama tawaf – juyawa bakwai suna ambato:
“Labbayka Allahumma Labbayk…”
Kowace juya, Iman tana kuka cikin zuciya. Idanunta a rufe, zuciyarta na faɗin:
“Ya Allah, ka tsarkake zuciyata kamar yadda Ka tsarkake wannan Gini.”

Yazid yana gefenta yana karanta Suratul Ikhlas da Suratul Falaq, yana kariya gareta cikin sirri.

Suna kammala tawaf, sai suka nufi Safa da Marwah. Iman tana dafa hannu, tana kallo yadda mutane ke gudu da nutsuwa — tana tuna da labarin Sayyida Hajarah.
“Ina son in zama kamar ita, mai tawakkali dakwazo
Bayan kwana biyu na ibada da natsuwa a Makka, Iman, Yazid, Ihsan, da iyayensu suka kama hanya zuwa Madīnatul Munawwarah — birnin Annabi ﷺ, birnin haske da rahma.

Suka hau jirgin ciki sharaf, kamar aljanna a duniya. Duk sun sa kayan hajjajai masu kyau. Iman cikin doguwar abaya mai launin ruwan zuma, Ihsan cikin sky blue hijab mai laushi da tsafta, Yazid da farin jallabiya da hula, Mommy da Daddy cikin kamun kai da kwalliya irin ta masu biyayya ga Allah.

Cikin jirgi, Iman ta kalli Ihsan tana murmushi:
"Kin san me? Ni a Madinah zan sake jin numfashina."
Ihsan ta share hawayenta, ta ce "Shekaru ashirin da biyar kenan... kullum addu’a nake Allah ya bayyana 'yan uwana. Kwanan nan ina jin zuciyata na karɓar amsa.
Suna sauka, gabar Masallacin Annabi ﷺ tana lumshe ido kamar tana karɓar bakinta. Sai suka sauka a Dar Al Taqwa Hotel – hotel mai kallon harabar masallaci.
Tana fitowa daga mota, kallon minaret na masallacin ya sauya dukkan jikinta. Ta zube ƙasa tana kuka. “Ya Rasulallah ﷺ... ga bawa mai laifi, amma mai ƙauna… na zo!” Iman da Mommy suka dafa ta, suma hawayensu na gangarowa.

Suna shigowa, zuciyoyi suka narke. Hasken fentin masallaci, kafet ɗin kore mai santsi, da ƙamshin miski sun rufe kowacce damuwa.
Suka nufi Raudah, wurin da ake ce wa Aljanna ce a duniya — daga mimbarin Annabi ﷺ zuwa gidansa.

🌿 Addu’ar Iman…

Iman ta durƙusa tana faɗin:

> “Ya Allah, ina gaban ƙabarin Annabinka ﷺ. Ka tsarkake rayuwata, ka bani zaman lafiya da wadata cikin halal. Ka rufe tarihin na baya ga bamu zaman lafiya a kasar mu na Nigeria ka sauwaƙa mana fittintunin zamani .”

Yazid na gefenta, yana fadin “Ya Rabbi, ka haɗa zuciyoyin mu cikin ƙauna sabodaKa. Ka bamu aure mai albarka da zuriyya masu tsoronKa.”


A gefenta kuma, Ihsan ta zuba ido cikin girgiza kai, tana tuna lokacin da suka sha wahala, baƙin ciki, yunwa da ƙorafi. Sai ta kalli Iman tana fadin:
“Allah ya rubuta farinciki a ƙaddara ta. Idan wannan ce hanya ta, to na yarda Ya Rabb.”


Bayan sallar Isha'i, suka koma hotel. Gaba da gaba da masallaci, dakin su na kallon Rawdah, Iman ta tashi da Azkar. Daga window tana kallon al'umma masu shiga masallaci da daren dare.


( 🕊️ Wanda ya bar komai saboda Allah, Allah zai bashi komai fiye da tsammani. ).


Bayan kwana biyu da isowarsu Madinah, watan Ramadhan ya kama. Gabar masallacin Annabi ﷺ sai armashi da ƙamshin shaƙaƙƙen ruhin tsarki da tausasawa. Duk inda ka kalle, sai ka ga darajar wannan wuri da wannan lokaci.


🕋 Iman, Ihsan, da Yazid sun tashi da azumi…

Cikin dakin hotel, saƙon megaphone daga Masallaci ya shiga:

"Ya ayyuhan-nas… qad jaa’akum Ramadhan… shahrur-rahmah, wash-shahrul-maghfirah!"



Duk suka bude idanu, zuciyarsu cike da natsuwa. Iman ta kalli agogo — ƙarfe 4:30am, lokacin sahur. Sai ta tashi a hankali, ta nufi kitchen na suite ɗin su. Ihsan na biye da ita, Yazid yana tafe da 'yar murmushi.
Sahur a cikin zaman lafiya… Sun shirya abinci:

Khobz (bread na Larabawa),

foul (wake mai miya da man zaitun),

qahwa (coffee na Arab),

dates masu ɗanɗano,

da lemon tea mai zafi Iman ta kalli Yazid “Wallahi natsuwa irin ta Madinah daban ce. Kamar zuciyata na sabuwa.”
Yazid ya murmusa:
“Sabuwar zuciya, sabuwar fata… da sabuwar soyayya.”



Bayan azahar, suka je ziyara:

Uhud — inda Annabi ﷺ ya yi yaƙi.

Gidan Sayyidah Fatimah – sun tsaya suka yi addu’a.

Masjid Quba – wanda Annabi ﷺ ya ce:

“Duk wanda ya yi alwala a gida, ya je ya yi sallah a Quba, yana da lada kamar Umrah.”
Ihsan ta kalli Iman “Zuciyata na ta kuka, amma cikin farin ciki. Na ji kamar ina ganin su Sayyada Khadija da Fatimah.”

Lokacin iftar, duk suka fito suka samu taburma a harabar masallaci. Gaba da su, wani dattijo daga Pakistan ya jero: ruwan sanyi dabino ruwan yogurt da gurasa mai zaƙi.
Sun bude baki cikin tsarki da albarka. Bayan sallah, sai Yazid ya kalli Iman ya ce:

“Wallahi duk duniya babu inda na fi jin cewa Allah yana kusa da ni irin Madinah.”
Iman ta ce cikin sanyi:
“Ina fatan daga nan Allah ya cigaba da rufe mana tarihin baya da bude sabuwar dama.”




A daren Tarawih, duka suka tsaya kamar an dasa su. Hawaye na gangarowa, zuciya na mika, da harshen su yana faɗin:
“Rabbighfir li, wali-walidayya, warhamhum kama rabbayani saghira.”


BAYAN AZUMI
Iman da Yazid suna tsaye a bakin window na dakin su da ke Fairmont Makkah Clock Royal Tower Hotel, kallon masallaci suke cikin nutsuwa da shauƙin kwana guda kafin Laylatul Qadr. Bayan sallar Asr, Yazid ya juyo ya ce:

"Yanzu kam lokaci yayi… mu shirya mu je siyayyar sallah. Mun gama azumi "



Iman ta murmusa, tana gyara gashin ta cikin veil mai launin zinariya da fure-fure. Kwalliyar ta da ta kwanta cikin fararen kaya masu sulbi, sai ka ce sarauniyar Larabawa.



Sun hau lif din hotel din su suka sauka kai tsaye zuwa ƙasa, inda yake haɗe da Abraj Al Bait Mall — shahararren wuri mai ɗauke da shaguna na duniya irin su: Harrod Cartier
Gucci Zara Arabian Oud

da kuma shagunan kayan Musulunci irin su Al-Haramain da Ajmal Perfumes.
Yazid ya siya: Agogo Rolex, White Thobe mai ɗinkin saudi style, da turaren Oud Muattaq.


Iman kuwa ta shiga:

Boutique na Abaya, ta zaɓi riga black silk abaya da aka yi da zinariya,

Turare mai suna Shaghaf Oud Aswad,

Da kuma takalmi mai launin lu'u-lu'u daga D&G.


> "Yazid, wannan turaren kamar zuciyata ya shige," tace tana lumshe ido. "Ke ce ke cikinsa," Yazid ya amsa da murmushin kaunar ƙanwar sa
Bayan siyayya, sun zauna a wani café da ke saman bene — Al Makan Café, inda aka musu:

Vanilla Qahwa

Ajwa smoothie

Date tartlets


Suna zaune suna kallon masallaci, sai Iman ta ce:
"Na ji kamar ba zan koma duniya ba. Wannan Makka sai ta tsarkake ni gaba ɗaya."
Yazid ya ce:
"Ni ma dai kamar zuciyata ta sake. Kuma nasan wannan siyayyar, ba sallar ce kawai muke shiryawa ba… sai mun yi siyayyar sabuwar rayuwa."


✨ Kafin su koma hotel...

Suka wuce gold jewelry store — Yazid ya siya mata ɗan ƙaramin sarka mai sunan "IMAN" da lu'u-lu'u. "Za ki riƙe wannan kamar yadda na ke riƙe ki cikin raina."
Iman ta ɗaga kai, hawaye ya kawo ƙyalli a idonta, tace:

"Ka cancanci fiye da zuciya, My brother Yazid."
Haurawa upstairs sukaye inda zata raka sa ya zaɓi kayan tsaraba ga abokan sa little Yazid dake ta faman gwada wani jalabiyya a madubi ya hango Iman ta tsaya chakk ko ƙofta ido bata iyawa jinin hukunta ya tsaya chakk duk ruhinta ya tafe akan ................



To be continued by narnah Khadijah 🥰🥰🎊

Happy weekend





https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC




🎇BAYAN WATA 🎇
( Beyoung the moon ).
SABON SALO

Labari da tsarawa
Narnah ƙanwar soja
( Sayeedan Adda )



*********
HIKIMATA ABIN ALFAHARI NA
Marubuciyya tana da damar halittar mutum ta kashe shi ta raya shi, tunda 'ƙirƙirar labari ne. ta haɗa masoya, ta wargaza soyayya tsakanin masoya.

Itta baiwa daga Allah ce, ubangiji ke bada itta ga wanda ya so duk wanda aka ba wa itta, sai ya sarrafa ta yadda ya ƙi so: wani ta jawo masa arziki, wani kuma ta janyo masa ɗaukaka da masoya masu girma da daraja...

*****""

Sadaukar wa littafin Bayan wata sabon salo Ga Abokina Mallam Najeeb wanan Sabon salo naka ne shi ke ɗauke da martabar sunanka thank you with your support 🙏




ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION 💫



Page 50 / 51




HAPPINESS IN BAYAN WATA 🎇



Ana cikin haka…





Yazid na daga gefen madubi yana gwada jalabiyya, yana ɗan murɗa hannun rigar, idanunsa suka kai ga fuskar kanwarsa Iman.

Sai ya hangi canjawa a fuskarta:
zuciyarta ba kamar da ba.
fuskarta ta dau wani launin zafi da ɗan firgici.
kamar wacce ta ga abin da ya tayar mata da ƙwaƙwalwa.
“La haula wala quwwata illa billah…” ya furta a ransa cikin mamaki.



Ya riga ya san halin kanwarsa ba shirme take ba amma yau, kallon da take yi wa wancan saurayin mai gilashi ya girgiza shi.

Ya maida kallonsa gare shi. Sai ya ce a ransa:
“Innalillahi… wannan ba ƙaramar halitta ba ce. Ga kwarjini, ga nutsuwa, ga kyau irin na mutanen da aka fi ƙima. Idan ba ɗan wani sarki ba ne — to sai dai ya fito daga gidan gwamnati kai tsaye.”



Yazid ya ɗan ƙanƙame jikin sa cikin riga, yana fitar da numfashi a hankali.
Sai ya ƙara cewa a zuciyarsa:

> “Kanwata Iman ta kusa rikicewa saboda kallo ɗaya. Wannan saurayin akwai shi da wani sirrin shanye zuciya. To amma ni da nake nan da ita shekaru, ban taɓa ganin tana rawar jiki haka ba...”



Ya kalli Iman, ta kasa tsayawa wuri guda. Hannunta na ɗan karkarwa. Idonta yana ƙoƙarin komawa gefen saurayin, amma sai ta murɗe fuskarta kamar wacce ta ci karo da tunanin da bata shirya ba.

Sai Yazid ya ɗan sosa gemunsa yana dariya a zuciya:
“Watakila yaron Sarkin Makka ne ai ga yadda ya ɗaura alkyabba kamar wani amintaccen ɗan gidan girmamawa ga arziki, ga girmamawa a fuskarsa ga nutsuwa da kwarjini… Allah ya kyauta.”
ya matso kusa da ita, yana faɗin da dariya:
“Iman… me kika hango ne haka? ko aljani ne a madubi?”
Iman ta yi ƙoƙarin dariya, amma muryarta ta sare, tana jan numfashi tana juyar da kai:
“Kamar wani ne na sani kawai… babu komai.”



Yazid ya yi shiru, amma zuciyarsa ta fara leƙen bayan madubi.
Waye wannan saurayin?

Iman ta danna rigarta, ta matso da hijabinta sosai kamar tana buya da hijabin tace da murya mai rauni amma cike da ɗoki:
"Yazid… mu bar shagon nan… yanzu-nan…"



Yazid ya kalleta da mamaki.
Amma ya lura da yadda idanunta ke yawo kamar masu neman mafaka ba ta iya tsayawa wuri ɗaya.

Yayin da suke ficewa daga cikin babban shagon tsarabar dake cikin katafaren "Abraj Al-Bait Mall", suka kusan kai ƙofa kenan…

Sai suka ji muryar namiji mai sanyi da natsuwa, amma tana da sauti da zai tsaya maka a ƙwaƙwalwa "Iman?"

Tayi turus kamar ba ita ba, taji jikin ta yayi sanyi har ƙafafunta suka kasa ɗaukar nauyinta.

Yazid ya tsaya cak.
Cikin faɗuwar gaba, ya juyo ya kalli inda muryar ta fito.

Wannan ba kowa ba — sai NAJEEB!

Sai lokaci ya tsaya kamar an yi shiru a duniya.
yana tsaye a gefen wata madubaiyar bulo, jalabiyyarsa ta milk white tana shan hasken fitila, gashinsa yana murɗewa a gefen hancinsa, fuskar sa tana cike da halin jarumta da kwarjini.

Iman ta kasa furta komai.
Kallon ta a kansa, numfashinta na wani irin sauka da hawa.
Zuciyarta ta ce "toh ashe ba mafarki bane? Ashe shi din ne — da gaske NAJEEB ya bayyana?"



Yana kallonta da kyau, cikin nutsuwa, ya ƙara matsowa, muryarsa cike da ladabi "kin yi shiru Iman… baki gane ni bane?"



Iman ta kura masa ido, sai ta daga hannu kamar wacce zata ce "kai ne?", amma sai ta kasa sai ta juyo gefe tana ƙoƙarin ɓoye hawaye da suka fara cika mata ido.

Yazid ya tsaya yana kallon ikon Allah.
“Da gaske wannan ne Najeeb? Ashe shine wanda ya yaye hankalin ‘yar uwata cikin mintuna kaɗan…”



Iman ta lula…
A zuciyarta, komai ya ƙage wani sanyi ya mamaye zuciyarta, amma kuma wani irin ɗaci ya shige mata makogwaro sai yanzu ta kara tabbatar:"Na rasa… kuma na samu. Amma a wane hali?"


A lokacin da kalmar "Iman?" ta fita daga bakin Najeeb — ba Yazid kaɗai ne cikin mamaki da razana ba...

.


Daddy Ado da Mommy Ihsan suka shigo shagon, suna tafe da sauri kamar masu bin kira daga zuciya.
Mommy Ihsan har da ƙarin ledoji a hannu, Daddy Ado kuma na saka agogon sa, tamkar wanda yake fuskantar abu mai nauyi da yake so ya tabbata.

Da suka shiga — sai suka tsaya cak.

Hankalinsu ya kwanta kan fuskar saurayin da ya kira "Iman" da muryar da ke jirkita jin zuciya.

Kallon su ya canza... daga mamaki zuwa shakku, daga shakku zuwa amincewa da abu mai nauyi da suka daɗe suna jinkirta yarda da shi.

Mommy Ihsan ta lumshe ido. Ta buɗe.
Ta tsinci kanta cikin tunani mai nauyi. Sai ta faɗa da ƙasa-ƙasa, kamar magana da kanta:
"Wannan shi neNajeeb."

Iman kuwa...
Ta riƙe hannun rigarta da ƙarfi, zuciyarta na bugawa kamar ana busa gangar yaki a cikinta.
Sai ta juyo a hankali…
Ta haɗa ido da Najeeb kamar kiran zuciyarta ta ce:
"me kake nema yanzu? wane abu kake so ka kawowa rayuwata a cikin wannan tsarkin da na samu?"



Najeeb ya matso ƙasa fuskar sa cike da ɗoki amma yana ƙoƙarin zama mai nutsuwa.

Mommy Ihsan ta share hawayen da ba ta sani ba ya gangaro mata.
Alhaji Ado ya matso gaba yana ƙare wa Najeeb kallo "kana da tambaya a cikinmu yaron nan…"


Daddy Ado ya matso daga bayanta. Sai da ya taka sau biyu kamar mai kallon tsohon hoto da aka ba shi mamaki.

Ya tsaya ya lumshe ido.
sai kuma ya furta da murya mai taushi amma mai nauyi:"In dai wannan ne… to fa gaskiyar duniya tana da salo."

Suna kallon sa kamar ƙauyawa da suka fara ganin silima — ko kamar iyaye da suka ga abin da ‘ya’yansu suka ɓoye tun shekarun baya.


Yazid ya kalli Mommy
End Ads