Ihsan da Daddy Ado — yana kallon yadda suke kallon Najeeb da irin wannan shakkar da ake gani a fuskar wanda ya gane abu amma har yanzu bai yarda ba.
"Me yasa suke kallon sa kamar haka?"
ya tambayi kansa, zuciyarsa na bugawa da tambayoyi.
Har yanzu bai iya haɗa hoton da ke yawo a kafar sada zumunta da wannan mutum mai tsayin daka, sanye da farar jallabiya, wanda yanzu ya tsaya gaban su da tawali’u da kwanciyar hankali.
Iman kuwa...
Tana jin nauyin duniya a ƙirjinta.
Tana jin zuciyarta na bugawa da sauri kamar ana busa gangar yaki a cikinta.
Sai ta juya...
Ta haɗa ido da Najeeb.
Idanu hudu.
Kamar hoton da aka ɗauka shekaru baya yana dawowa cikin rayuwa.
Kamar lokaci yana neman dawo da duk abinda ta ɓoye tun cikin duhu na zuciyarta.
"Me kake nema yanzu?"
"Wane abu kake so ka kawowa rayuwata a cikin wannan tsarkin da na samu?"
Zuciyarta ce ke tambaya amma bakinta shiru.
Najeeb ya matso ƙasa Fuskar sa cike da ƙaunar da take ƙoƙarin fitowa daga cikin damuwa da nadama.
Ya tsaya. Ya kalle ta.
Ya furta cikin muryar da bata canza ba — murya mai sanyi, mai ɗauke da raɗaɗin wanda ya farka daga mafarkin baƙin ciki:
Mommy Ihsan ta share hawayen da bata sani ba ya gangaro mata.
Daddy Ado ya lumshe ido, sannan ya ce da murya mai ƙarfi amma mai natsuwa:
"Kana da tambaya a cikinmu, yaron nan..."
"Kana da tarihin da bai ƙare ba."
Sai Iman ta numfasa...
Ta kalli Mommy Ihsan ta kalli Daddy Ado ta kalli Yazid wanda ke tsaye cikin rudani.
Sai ta ce
Kafin Iman ta iya motsawa daga inda take tsaye… Wata Balarabiya ta shigo cikin shagon.
mace ce sanye da abaya mai kyalli kamar an dinka ta da zinariya, haɗe da mayafin da ya lullube kanta daidai da al’adun gida, amma kuma jikinta yana bayyanar da ɗaukaka, kima da zallar kuɗi.
Fuskarta cike da annuri, sheƙi na lafiya da kwanciyar hankali yana bayyana a kowanne motsinta.
Takalminta sun shige ƙasa suna yin ɗan ƙara mai laushi kamar ana bi da murmushi a kasa.
Tana tare da wani babban mutum – mai shekaru kamar tsakanin hamsin sanye da shadda mai tsada, fuska mai cike da kwarjini da nutsuwa irin ta manyan masu mulki ko ‘yan kasuwa. Ana ganin kamala da daraja a ko’ina a jikinsa.
Sun tsaya cak.
Dukansu suna kallon Najeeb da murmushi mai ɗauke da gamsuwa da alama kamar sun same shi cikin abin da suka daɗe suna jira.
Sai babban mutumin ya furta da murya mai ƙarfin kwarjini da taushin tausayi:
da harshen larabci"Najeeb, yaro na… haka ka zo? ba ka fa sanar da mu ba."
Balarabiyar ta matso ta riƙe hannunsa da dariya "Anta! Ma sha Allah… da gaske kana nan mun gaji da jiranka!"
Mommy Ihsan ta kalli Daddy Ado da sauri.
Yazid ya waigo da sauri ya kalli su.
Iman kuwa… gaba ɗaya jinin jikinta kamar ya tsaya. Hannunta ya soma rawar da ba za ta iya hana ba.
“Yaro na…”
“Mun gaji da jiranka…” Waɗanda suke ne? su waye a rayuwar Najeeb?
shin shin zai yiwu yana da wata rayuwa da babu wanda ya sani? kuma me wannan ke nufi gare ni?
Zuciyarta na faɗaɗa da tambayoyi. Duk da haka, sai idonta ya sake sauka kan fuskar Najeeb — wanda ke kallonta da tausayi da damuwa, kamar yana fargabar lamarin zai ɓace masa kafin ya bayyana komai.
"Maryam…?"
Daddy Ado ma a tare da ita kamar an saka su cikin script ɗin ɗaya ya furta:
"John…?"
Maryam da John, waɗanda suka waigo a lokaci guda kamar jikin su ya gane da kiran.
Iman ta juya a hankali tana kallon su.
Yazid ya ɗaga gira yana so ya tabbatar da abinda ya gani.
A cikin shiru mai nauyi, an ji Maryam cikin wata kakkausar murya, kamar wadda aka kama da laifi "Ihsan? Ado??"
John ( Munir ) kuwa kamar zai ja baya yana kallo da tausayi da ruɗani. Bai san ko ya matso ko ya tsaya ba.
Kowa ya zuba ido.
Wani shiru… kamar na wuta kafin ta kama.
sai Mommy Ihsan da Daddy Ado a lokaci guda kamar an saka su a fim ɗin dariya su ce da murya ɗaya "ke da kai? kuna tare?! "
Sannan suka juya su kallon juna su sake faɗin:
"Ihsan?"
"Ado?"
Hankali ya tashi!
Yazid ya fashe da dariya yana kama ciki.
Najeeb ya kalli Maryam da John da mamaki yana cewa "Kuna nan ma?"
Iman kuwa tana kallon kowa tana jin kamar ta faɗi a ƙasa — amma sai ta kama baki tana dariya ƙasa-ƙasa.
Duniya ta rikice a cikin babban mall na Makka.
:
Maryam Al-Fulan – Fitacciyar ‘yar kasuwa a gabas ta tsakiya.
Munir John Al-Mujtaba – Masanin tattalin arziki da haɗin gwiwar kamfanonin duniya.
Suna kallon Najeeb da murmushi mai cike da ƙauna, wanda shi kuma yake kallon su da ɗan ɗoki da kunya. Fuskar Najeeb na nuna cewa wannan al'amari mai nauyi ne — ya san lokacin bayyanar gaskiya ya zo.
Maryam ta ƙaraso da sanyi da kwanciyar hankali. Ta ce cikin muryar da Iman ta sani daga nesa
Mommy Ihsan ta zaro ido tana kallon Maryam sosai.
Daddy Ado kuwa ya furta da karfi:
"Maryam! Munir!!"
Iman ta kalli su, sai kuma ta kalli Najeeb — tana kallon zuciyarta na fasa kamar ƙaho.
Sai Mommy Ihsan ta furta, cikin mamaki da dariya, tana kallon Ado:
"Ka ce min wannan shi ne Najeeb ɗin da Iman ke kuka dashi shekaru biyu da suka wuce!"
Ado ya ce "Ke kika ce a rufe! amma yanzu… shi kenan wannan ai Allah ya riga ya rubuta!"
Yazid ya zura hannu a aljihu yana kallon shirin silima live!
Ihsan ta saki ledar tsaraba daga hannunta kamar wacce ta manta da komai a duniya, ta yi tsalle ta rungume Maryam da hawaye mai zafi amma na farin ciki.
"Maryam! ashe kuna raye?! ashe baku mutu ba?! ash ashe duk wannan rayuwa sai yau zan sake jin wannan ƙamshi?!"
Maryam ta rungumeta da ƙarfi, cikin tausayi da murmushi mai taɓa zuciya.
"Ihsan... muna tare da ku ne duk wannan lokacin. Sai dai zaman lokaci ya hana bayyana."
Daddy Ado kuwa ya isa gaban Munir, suka kalli juna na tsawon lokaci. Daga nan ya buɗe hannuwansa ya rungume shi kamar babban ɗan’uwa da suka dade ba su haɗu ba.
"Munir! Ashe kai ne?! ashe kai ne?! Wannan ba mafarki bane?"
Munir ya ce cikin natsuwa:
"Rayuwa ce Ado, sai da ta ɗauki ruwa, sai yanzu ta dawo da iska mai sanyi."
Little Yazid kuwa ya kwaso gudu ya faɗa jikin Munir suka rungume juna sosai.
Najeeb ya dafa kan sa yana murmushi:
"Kai Yazid! Ashe yanzu kai ne ƙaramim Yazid namu da na rasa shekaru da dama?"
Iman kuwa... ta tsaya daga nesa, tana kallonsu kamar wanda ke kallon fim.
Ta ɗauki wayarta, ta fara ɗaukar hoto da hawaye a idanuwanta — hawaye masu daɗin gaske.
tana ɗaukar hoton komai da komai — kama daga Ihsan da Maryam, zuwa Ado da Munir, har zuwa Yazid da Najeeb.
Sai ta ce da zuciyarta:
"Wannan hoton, ba kawai na dauka bane. Na ɗauki tarihi ne... labari ne da zan tuna har ƙarshen rayuwata."
AFTER SOME HOUR'S
Motoci uku ne suka ratsa cikin wani sanannen layi na 'Yan larabawa a Makka. Layin da kowanne gida ke da masallaci a ciki, kuma gidaje masu ƙamshi da tsari na Musulunci da larabci irin na asali.
A cikin mota ta farko akwai:
Maryam, tana riƙe da hannun Ihsan, sai Iman dake gefe tana kallon titin da shakku da tsoro da farin ciki ke rikicewa a fuskarta.
Mota ta biyu:
Najeeb a kujerar direba, sai little Yazid
Motar ƙarshe:
Ado da Munir suna hira da dariya irin wacce ba su yi tsawon shekaru goma ba.
A karshe suka tsaya a gaban wani katafaren gida mai babbar ƙofa da alamomin larabawa a jiki — filastik na zinariya da yashi.
Kofar gidan har da gardin larabawa biyu masu rawani da alamomin tsaro. Gidan yana da babbar alamar "Bayt Al-Rahma" — Gidan Rahama.
Sun shigo babban parlour mai faɗi kamar fili — fentin fari, ja da zinariya, fitilun chandelier guda biyu sun rataye daga saman rufin da ke da ado na gold calligraphy (zane na kalmomin larabci).
Cikin gidan akwai:
Sofa masu launin beige da ruwan zinariya.
Big-screen plasma TV a bango, yana nuna hoton Ka’aba kai tsaye daga Masjid al-Haram.
A tsakiyar bango babban Frame da aka rubuta “After the Moon – Bayan Wata”, tare da hoto na matafiya biyar a cikin sahara – Ihsan, Maryam, Munir, Yazid Ado.
Haddimai larabawa biyu suka karɓi jakunkunansu, suka miƙa musu ruwa da gahwa a gilashin zinariya.
Sautin oud (wakar larabawa) mai sanyi na fita a hankali daga bangon waje.
Maryam ta kama hannun Ihsan suka zauna akan kujera, Iman ta zuba ido tana kallon bangon da hoton su.
"Wallahi... wannan gida ne na gaskiya," Ihsan ta faɗa cikin sauke numfashi.
Najeeb ya kalli frame ɗin hoton da ke bango ya ce "Wannan shine burin Mahaifiyata – a taƙaice rayuwar ta na baya ya dawo a zahiri cikin hoton da zai zauna har abada."
Munir ya dafa kafadar Ado ya ce "Ado, yanzu gaskiya ta bayyana. Rayuwa ta gyaru mun dawo gida."
Yazid kuwa yana zagaye da dariya, yana shan juice, yana cewa:
"Daddy Najeeb, ni yanzu na zama ɗan gida biyu fa!"
Idan har kunjee daɗin page nin naga alert a opay na 🤣🤣🤣🤣
Narnah ƙanwar soja ✍️✍️
https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
🎇BAYAN WATA 🎇
( Beyoung the moon ).
SABON SALO
Labari da tsarawa
Narnah ƙanwar soja
( Sayeedan Adda )
*********
HIKIMATA ABIN ALFAHARI NA
Marubuciyya tana da damar halittar mutum ta kashe shi ta raya shi, tunda 'ƙirƙirar labari ne. ta haɗa masoya, ta wargaza soyayya tsakanin masoya.
*****""
Sadaukar wa littafin Bayan wata sabon salo Ga Abokina Mallam Najeeb wanan Sabon salo naka ne shi ke ɗauke da martabar sunanka thank you with your support 🙏
ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION 💫
Page 52 / 53
Yau da rana bayan sun sauke kaya, sun yi wanka sun ɗan huta, gidan ya dauki shiru mai daɗi irin wanda yake zuwa ne kawai bayan gajiya da soyayya, a ɗayan zauren falon, little Yazid da Najeeb suna zaune akan ɗaya daga cikin ƙananan kujeru kusa da window mai labulen zare.
Yazid: “kamar ka taɓa zama dan sanda fa, yadda kake tafiya da tsari.”
Najeeb (yana dariya): “kai kuma kamar ka taɓa zama dan leƙen asiri – sai ka ce kana da sirrin duniya.”
Suna nan suna dariya, kamar yara biyu da Allah ya haɗa saboda zuciyarsu ta dace – duk da cewar yau ne haɗuwarsu ta farko.
IHSAN & MARYAM
A ɗaki mai launin sanyi da kyawawan labule masu zinariya da shukoki na artificial, Ihsan da Maryam suna zaune akan gado suna shan gahwa da busassun ƙwai da miya.
Ihsan (ta kama hannun Maryam): “Maryam... ashe rayuwa zata dawo da mu haka?”
Maryam: “Ni ma ban taɓa tsammanin ba. Amma in Allah yana rubuta abu – zai faru ko ina, ko ta yaya.”
Suka yi shiru na lokaci, suna kallon juna da hawaye masu ɗauke da dariya a cikin idonsu.
A wani ɗaki na yara da aka kawata da ‘yan teddy bear da ƙamshi na vanilla, Iman ta zauna tare da wata yarinya mai shekaru 12 mai farin fata da dogon gashi.
Yarinyar: “Sunana Layan Momi Maryam ce ta ce ki zauna da ni har sai kin huta sosai.”
Iman (ta rike hannunta): “Na gode Layan. Kin daɗe a nan gidan?”
Layan (ta murmusa): “Tun ina shekara shida. Gidanmu ne yanzu.”
Suka zauna suna hira, har Layan ta kawo mata hijabi mai launin ruwa da hoda. Iman ta sanya shi a kai, suka kallon juna cikin madubi suka ce a tare “Beautiful!”
DA DARE DINING ROOM
Ana kwana biyu da isowarsu, da dare suka haɗu a babban daining table mai zagaye. Fitilun zinariya suna kan low dimming, kamar cikin film Abincin da ke jikin table:
Kabsa mai daddawa da nuts
Maraq da lamb
Hummus, tabouleh, da fatayer
Kunun zaƙi da dates
Laban (madarar larabawa mai sanyi)
Maryam ta zauna gefen Ihsan, Najeeb kusa da Yazid, Munir da Ado a gefen hagu. Iman da Layan suna gefe suna dariya a hankali kamar ‘yan mata masu sabuwar ƙawance.
Ado: “To yau mun huta gobe mu fita ziyara!”
Ihsan (ta ɗaga glass ɗinta): “Ga rayuwar da muka dade muna mafarki da ita.”
Suka ɗaga hannu suna yi wa Allah godiya. Duniya ta dawo da murmushi bayan Wata ya ɓullo.
Suna zaune a falon da yake kallon ka’aba daga tagar gilashi mai shara-shara kowa na sanye cikin kayan sanyi masu kyau, dakin na ƙamshi da turaren Oud da jasmine.
Dining table na jiya an gyara shi yanzu zuwa karamin round-table mai coffee da snacks. Iman ta ɗauko karamar wayarta ta ajiye a gefenta.
Ta gyara zama, ta gyara murya, ta ɗan tabe hancinta da style irin na ‘yan jarida Iman (ta kalli Munir):
“Daddy Munir, kafin mu fita ziyara — ni dama akwai tambaya mai nauyi a zuciyata tun jiya.
*Yaya kuka tsira daga ‘trailer’? Bayan aka kwashe ku — me ya faru da ku da Aunty Maryam?
Bayan wata… yaya ‘bayan watan’ naku ya kasance?”
Ɗakin yayi shiru. Kamar ana sauraron azan daga sama Munir ya kalli Maryam, ta gyada kai da idon da ke cike da kewa.
Ya lumshe ido sai ya fara da muryar tausayi wanda zuciyarsa ke da ƙarfi, amma yana ɗauke da raunukan tunani:
“Bayan mun rasa motar nan… bayan an kwashe mu daga trailer ɗin nan da ba zan taɓa mantawa da wari da zufan cikinta ba — sai muka tashi ne a wani sansani a chan gabashin Makka, inda aka ware mu daga juna.
Ban san inda Maryam take ba ban san ko tana raye ba kuma lokaci bai tsaya mana ba — sai ya cigaba da juyawa.”
Ya cigaba da cewa:
“Wata mata Balarabiya ce — ba ta da haihuwa, ta karɓe ni a matsayin ɗanta a lokacin da nake a asibitin da suka ajiye mu bayan mugun ciwon da na sha.
A can na girma... amma zuciyata kullum na mafarkin wani abu daban. Na san ban da cikakkiyar dangantaka da kowa a can — amma rayuwa ta tilasta in gamsu.”
Maryam ta ɗora:
“Ni kuma na samu wani bawan Allah da ya kai ni hospital a Isra'ila. Daga baya ya shirya min takardun tafiya Makka inda na zauna a gidan wata tsohuwa har muka sake haduwa da Munir inda yake aiki a ɓoye kamar ne wasa da gaske muka bayyana wa junnan mu sha'awar aure bayan wani lokaci kadan na samu cikin NAJEEB kuɗi ya fara budewa mukaye biza har muka samu Manyan manyan dama na samun kuɗi Muka koma Saudi da aka ba shi aiki.”
Duk suka juya suna kallonta. Maryam ta kama hannun Munir.
Maryam (cikin shashsheƙar murya):
“Mun shafe shekaru muna addu’a mu sake haɗuwa. Sai Dubai — sannan Makkah — yanzu Allah ya cika mana.”
Iman tana ta rubutu da ido da zuciya.
NAJEEB kuwa — sai kallon Iman yake yi. Yadda take saurare da nutsuwa, yadda kukan ta ke boyewa cikin dan murmushi — ya tabbatar da wani abu:
Soyayyarta na fizgar zuciyarsa fiye da duk wata sanarwa da ya taɓa karantawa.
Sai yace a cikin zuciyarsa “Bari na bayyana komai… amma a lokacin da zai dace — tunda yanzu na san ina da muhimmiyar mace a gabana.”
Ado ya gyaɗa kai. Yazid ya shaƙe gaban Najeeb yana kallon sa kamar jarumi a cikin fim.
Layan da Iman suka kama juna da ido suka ɗan yi dariya.
Falon ya cika da nutsuwa — kamar an yanke ruwan rahama aka zuba.
Wannan lokacin — ba wai shiru suka yi ba — sai hawaye da murmushi. Bayan jawabin Munir da Maryam, sai kowa yayi shiru yana ƙoƙarin lissafa irin wahalar da suka sha kafin su haɗu.
Nan fa Ihsan da Ado suka ɗago kai.
Ihsan (ta dafe kirjinta):
“Wannan labarin sai dai a jikin zuciya — wallahi rayuwa ta juyi ne da kaddara. Amma yanzu, tunda Allah ya haɗa mu, zamu ci gaba da zama tamkar iyali.”
Ado ya ɗan share kwalla, sannan ya kalli su Maryam da Munir yana murmushi.
Ado:
“Mun shirya gayyatar ku zuwa gida da gobe — domin yanzu muna da kamfani mai suna “TALLAFI MATAFIYA” a Najeriya mun kirkire shi domin taimaka wa matasa da suka shiga wahalar neman visa ko tafiya ba bisa ka’ida ba. Mun riga mun buɗe rassan Lagos, Abuja da Kaduna.”
Maryam da Munir suna kallon juna, sai suka murmusa. Maryam ta kama hannun Iman tana kallonta da dariya.
Maryam:
“Ke dai ƴar jarida ce, amma sai kin ji namu ma. Komai da muke da shi yanzu yana nan a Makkah — ba Dubai ba.
Mun mallaki gida, kamfani mai suna Zauren Tafiya, inda muke bayar da training ga matafiya kafin hajji da umrah da kuma ‘yan kasuwa.
A nan Makkah muke — gida ne nan, kasuwanci na nan.”
Ihsan ta lumshe ido tana dariya, tana kallon Ado Ihsan:
“Toh mu fa arzikinmu na Dubai ne — nan da har sai an kira mu a Tashar Arabiya suna ce mana “Ƴan Kasuwar Duniya”.” suka yi dariya gaba ɗaya.
“Bari in faɗi gaskiya nan da nan: kun zama labari, darasi, da abin alfahari a rayuwata. Na gane cewa arziki ba Dubai ba, ko gida mai hawa goma ba — arziki shine lokacin da Allah ya yarda ka tsira kuma ya haɗa ka da mutanen da ka rasa.”
Sai Iman ta ce da murmushi tana kunna recorder Iman:
An gama ziyarar Ka’aba da sallar harami, sun gama siyayya — kaya na larabawa, turaruka, agogo, ababen tunawa. Fuskokin su cike da annuri da kwanciyar hankali.
Motoci sun shiryu a gaban katafaren gidan da suka sauka. Ƴan haddimai na jera akwatuna cikin natsuwa. Ihsan da Maryam na cikin motar gaba suna sanye da kayan hula da tabarau masu kyau. Iman da yarinyar gida na gefe suna dariya. Najeeb da Yazid suna musayar waya kamar tsofaffin abokai. Ado da Munir suna kallon komai da jin daɗin cikar buri.
Yazid (yana kwala kira):
“Dubai... we are coming!”
Iman ta fito daga wanka cikin hanzari, ruwan zafi na ci gaba da fita da ƙamshi a dakin. Guntun tawul ɗin da ta ɗaura a jikinta ya janyo hankalin numfashinta da gaggawa. Gashinta ya barbaje bisa kafadunta, yana ɗiga ruwan sabulu mai ƙamshi kamar 'attar Halabi'.
Tana juyawa zata ɗauki doguwar rigarta kenan —
Sai taji an bubbuga ƙofar sau biyu, da ƙarfi, kamar ana neman rai.
Ta tsaya cak Gabanta ya fadi.
“Iman…” murya ce daga waje — muryar da take gudu tun jiya. Najeeb.
Yadda muryar tasa ta fito, a matakin da ke tsakanin tausayi da ƙauna, sai zuciyar Iman ta shiga wani sabon yanayi. Ba ta buɗe ba, sai dai ta jingina da bango, zuciyarta na bugawa.
“Ba wai zan tilasta ki ba, amma… Iman, ki saurare ni. Idan ma zan bar duniya ne da kaina, zan fi so na bar ta bayan kin ji gaskiyar zuciyata.”