kowa yana ganin yana murna amma shi da zuciyarsa sun san gaskiya , ya san Halima ba ta kai matsayin aure ba tukuna ta girma da sauri, amma zuciyarta har yanzu karama ce, tamkar macen da bata fara sanin al'amuran soyayya ba.
Sai dai kuma, Moddibbo mutum ne mai daraja da mutunci ya rike amanar Alhaji Saminu fiye da yadda wasu ke rike 'ya'yansu. Yana fatan Alhaji Saminu zai kare martaba da tsaron Halima kamar yadda ya rike alkawari na shekaru goma sha biyar.
Wani iska ya buso daga arewa, ya kada ganyen kuka da ke bakin ruga Halima ta lumshe ido, tana jin iskar kamar wata alama ce daga sama ko soyayya zata zo daga baya? ko kuwa hakan nan ne rayuwa ta rubuce mata?
Bayan sati biyu da cikar alkawari, ƙauyen Gembò ya sake fuskantar wata rana da ba za a taɓa mantawa da ita ba rana ce da komai ya sauya—rana da tarihi ya ƙara rubutun zinariya cikin ƙwarya mai ƙyalli.
A safiyar ranar asabar, tun ƙarfe tara da mintuna goma, sai ga jere-jeren motoci guda shida masu sheƙi da ƙyalli irin wanda bai saba zuwa ƙauyen ba, motoci ne kirar Lexus LX 570 guda biyu, guda bakar fata, guda kuma fari ɗan haske mai cike da adon zinariya. Sauran kuwa motoci ne kirar Hilux da Toyota Highlander, dukkansu cike da kaya, kujerun zamani, manyan jakunkuna da akwatuna masu lulluɓe da furen ado da yajin rawaya.
A wata ƙaramar Prado, wanda aka ɗora babban laifan jajjayen furanni da tutar Kaunar aure, Alhaji Saminu ne ya fito sanye da babban ɗan-baban Shadda mai launin zinariya da ruwan hoda , babbar hula ce ta fulani bisa kansa, mai ɗinki na musamman da adon sarka fitarsa daga mota ta sa yara suka yi tsalle, mata suka fara cewa:
“Ga angonmu ya iso! Allah ya sa a dace!”
Shi kuwa, yana da murmushin da ba'a san a zuciya akwai tsoro da jin nauyin amanar da ya ɗauka ba bayansa, abokansa biyu da shaidu—Alhaji Babangida da Alhaji Laushi—duk sun fito cikin kayan zamani ƙauyen ya sha ado kamar an shirya masa sallah gari ya ɗau shela da kade-kade na kalangu da waka:
“Alhaji Saminu yazo!
angon Halima yazo!”
Tun daga makon da ya wuce, iyayen Halima sun ɗora shagalin al'ada, mata na unguwa sun taru kullum ana sallake, ana gasa binkami, koskoso, da kilishi. Halima tana zaune cikin ɗakin mahaifiyarta marigayiya, cikin duhun tunani da zumudin rayuwar da ba ta san me take cike da ita ba ,aka yi mata lalle, aka sa mata ƙwarya ta ruwan turaren wuta a gefenta, aka shafa mata manshanu a fata, aka ɗinke mata zani da riga mai alamar Fulani na gargajiya—jar zani mai adon ratsi da santali na tsaf.
An saka ta cikin wani ɗaki mai ƙyalli da kilishi, ana yayyafa mata ƙamshi da bakhour, ana duba fatarta da gashinta, yarinyar ce kyakkyawa da kyau na halitta, ba ado ke ƙawata ta ba—rashin yawan maganganu da nutsuwar ta ce abin kallo.
A gaban limamin ƙauye da shaidu, aka daura auren Halima da Alhaji Saminu da sadaki naira dubu ɗari biyar, da sarkar zinari da kayan gida., adaidai lokacin da aka furta "na ɗaura", Halima ta fashe da kuka mai ƙarfi. Sai dai ba kuka na soyayya ko jin daɗin aure ba ne—kuka ne na rabuwa da matar mahaifinta, wacce ta raineta tun rasuwar mahaifiyarta, wani kuzarin tunani ya cika ta, kamar tana jin kamar yanzu rayuwarta ta sauya daga yarinya zuwa amarya, daga ƙauye zuwa birni.
Moddibbo ya share hawayen sa da alwala, yana murmushi mai cike da damuwa, yana fatan Halima zata dace da sabon rayuwar da zata tafi ciki, a zuciyarsa yana fatan Alhaji Saminu zai rike ta fiye da yadda aka rike ’yar sarki.
Alhaji Saminu ya bar ƙauyen ba da hannu ba. Ya bar da ɗimbin kyaututtuka: kudi ga matan unguwa, jakunkunan shinkafa, kayan abinci, sabbin riguna da ɗinkin zamani ga matasa, har da jakunkuna ga yara da aka ce "na makaranta".
Wajen fitarsu, aka shigo da sabuwar amarya cikin sabuwar rigar aso-ebi da kwalliyar santali, aka ɗaura mata gyale mai nauyin zinariya, aka raka ta da kalangu da wake-wake, aka saka ta cikin motar farin Lexus, sai ga kafila ta nufi birnin Abuja.
Amarya ta fito daga ƙauye—amma fuskarta na cike da tambayoyi. Shin me birnin ke ɓoye mata? Me Alhaji Saminu zai kasance gareta? shin wannan aure zai fassara soyayya ne, ko wata kyauta ta biyayya ce da ba zata taɓa jin daɗin ta ba?
*********************************
Juyawa tayi da ƙarfi kamar wadda aka hangi zuciyarta ta nitse cikin ruwan kogin ɓacin rai. tana mai huci da numfashi mai nauyi, ta faɗa jikin Moddibbo kamar jaririya, ta rungume shi da ƙarfi, tana kuka mai girgiza zuciya dukkan gangar jikinta na rawar jiki, murya na rawa kamar ana buɗe gidan hawaye a zuciya.
Moddibbo ya kama kanta yana bubbuga bayanta da hannunsa mai sanyi da tausayawa.
"Allah ya sa ki dace Halimatu," ya faɗa da wani murya da yafi shiru nauyi. "ki rike mutunci, ki tsaya da imani kiye koyar da mahaifiyar ke a fagen haƙuri zaki ci ribar zaman duniya ... rayuwa ce bata da tabbas."
Shi kansa idonsa cike da ruwa, kodayake zuciyarsa ta taɓu sosai—ya jima yana kallon Halima tamkar zinariyar sa wanda yanzu ya mika hannunsa ya mika ta ga duniya. ya mika al’amuranta ga wani mutum da ya fi shi daraja da kima, amma ba shi da tabbacin soyayya.
Bayan kuka da ban kwana mai cin rai, sai Halima ta shige cikin motar Alhaji Saminu da zuciyar da ba a iya fassara. Alhaji yana ƙoƙarin rarrashi da annuri, yana ƙyalƙyala dariya mai taushi yana faɗin:
"Amaryata kada ki damu, Abuja ba abin tsoro ba ne ke zauna lafiya, za ki ga alheri."
Halima bata ce komai ba ta fuskanci gilashin motar tana kallon ƙauyen su da ke raguwa a bayanta kamar mafarkin da ya ɓace. hannunta na cikin haɗaɗɗiyar rigarta, amma zuciyarta na cikin tsohon zanin ƙauyenta.
Motoci suka fice daga Gembò, suka fasa hanyoyi masu kura, suka dosa garin Yola inda jirgi zai tashi zuwa Abuja. Halima na zaune cikin mota, amma kamar a mafarki ta kasa kallon sabbin gine-gine da suka wuce su, kamar ba su da ma'ana gareta.
A lokacin da suka isa filin jirgi, an ce mata "Halimatu! Ki sauka ",ta sauka cikin rigima, tana kallon ƙasa kamar tana tsoron ƙasa ce zata buɗe ta haɗiye ta ba ta san me ake nufi da “ticket” ba ba ta san yadda ake biya ba yanzu ne Halima ke fara jin bambancin rayuwa, ta kasa cire takalmanta a wajen sakan na’ura, sai da ma'aikaciyar ta fara dariya ta ce:
“Yarinya! ba salla za ki ba wannan tsafta ne da dokar jirgi.”
taji kunyarta sosai Idonta ya cika da ƙyama da tozarta a zuciyarta:
“kai! ashe akwai duniya kamar haka?”
Bayan an kaita cikin jirgin, aka ɗaure mata seat belt, ta riƙe kujerar kamar wacce ke cikin ruwa mai zurfi. Da jirgi ya tashi, ta saki ƙara mai firgitarwa:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Wayyo Moddibbo…! na mutu!”
Alhaji Saminu ya rike hannunta da dariya “babu komai Halimatu, jirgi ne ke tashi kawai.”
Kamar sabuwar tsuntsuwa aka ɗauke daga ciyawa, aka ajiye cikin gini mai fanfo. As zuciyarta, birni kamar wata. Amma tambaya ɗaya ke ci mata rai: Shin wannan sabon garin da take ciki zai taimake ta ta samu sabuwar rayuwa, ko zai ɓata mata tunanin da take tsaye da shi tun ƙuruciya?
Tunda suka hau cikin jirgin sama, Halima ta kasa zaman lafiya idanunta na zagaye cikin hadadden komai wanda ba ta taɓa mafarkin wanzuwarsa ba , tana kallon tagar gefe, tana ganin sararin samaniya da ƙasa na raguwa kamar yadda aka rage wa tunaninta hankali. amma wani abu ya sake ɗaukar mata hankali...
A kujerar bayan nata, wani saurayi ne zaune, ya murtuƙe fuska, idonsa kamar na damisa mai zurfin tunani , fuskar sa doguwa ce, fara tas kamar bulo, ƙuncinsa yana da ɗan launin ja, bakinsa siriri ne amma mai ɗan ƙasaita gashin kansa an rage shi tsaf yana sheƙi, sai karan agogon zinare a hannunsa na hagu ya ƙara ɗaukar hankali.
Shima yana kallon Halima, ba da sha’awa ba, amma da mamaki da tausayi kadan kamar yana cewa da kansa, “Ina aka samo irin wannan ‘yar ƙauye mai tarin kamala?”
suna cikin tashi ne Halima ta saki ihun da ya gigita kowa
“Wayyo Allah naaa! waye ya ce jirgi zai ɗaga?! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”
Mutane sun juya suna kallonta, mata suka dinga dariya a nutse, wasu kuma suka tausaya amma shi saurayin da ke baya—ya kalli fuskarta da jajayen idanu, yana juyar da kansa a hankali cikin murmushin gefen baki, kamar wanda ya saba da irin haka a rayuwar zuciyarsa , sun sauka a filin jirgin Abuja, wanda ya bude musu sabon shafi a rayuwa.
Alhaji Saminu ya nufi Maitama da su, inda katafaren gidansa ke cike da girma da kima. gidan na da kofa babba mai lanƙwasa kamar ƙofar masallaci a Makka. farfajiya ce a waje, da lambu mai yalwa, sai tsuntsaye ke ta raira waka kamar sun san sabon baƙuwa ta iso.
Yayin da Halima ta kalli ƙofar katafaren gidan, zuciyarta na wani irin doki da tsoro da fargaba, wani sashe na ruhinta na faɗin "kin fito daga ƙauye, amma an jefa ki cikin birnin masu hannu da shuni..." da zuciya ɗaya ta shiga, sanye da kayan aure na gargajiya: mayafin fulawa, zobba a yatsu, da dankwali mai yatsin zinariya.
A cikin gida, motoci sun sha jerin gado, masu gadin gidan biyu a ƙofar shigowa suna miƙa gaisuwa da ban girma. Gidan kuwa – katafaren alfarma ne wanda ba a taɓa mafarkin Halima zata taka kafarta ciki ba. Babban falon yana da manyan tagogi masu labulen fata na turkiyya, cike da fitilu na chandelier masu hasken zinariya, cikin falon ne Hajiyah Nafisa ta karɓe ta da murya mai cike da mamaki:
Matar Alhaji Saminu, Hajiyah Nafisa, ta fito sanye da kayan alfarma gashinta a jikin mayafi yana sheƙi kamar rigar sarauta ta kalli Halima da murmushi na ɗan lokacin, amma idanunta na cike da alamun tambaya:
“Itace wannan yarinyar?”
Halima ta kasa magana ganin palon gida kadai ya isheta tiles ne na zinariya da hoda mai sheƙi, fanfo a bango da tebur na gilashi. tana takawa kamar ana binsa da ƙasa. Zuciyarta na cewa:
“To wallahi... haka birni yake ko dai na mutu ne an kawo ne gidan aljanna ?” kwalliyar da aka yi mata da kayan Fulani na auren ƙauye—maye da zobe da mayafi na fulawa—ya sa ta ƙara haske , amma a fuska akwai shakku, akwai salo na “ba sani ba sabo.” sai dai akwai mutunci a tafiyarta, wanda ba’a koya shi a birni.
“Nafisa itta ce amaryata na biya sadakinta tun can ƙauye kamar yadda na gaya miki. Allah yasa alkhairi.”
Hajiyah Nafisa ta tabe baki cikin murmushi mai nauyin fahimta daga kallon ta ɗaya ka gane ko da tana ƙoƙarin karɓarta, zuciyarta ba ta cikin hakan gaba ɗaya.
Sai da aka kai ta ɗakinta da aka tanadar mata cikin gida ɗaki mai faɗi sosai, bangon sa mai launin cream da zinariya an shimfiɗa masa carpet mai laushi, akwai gado babba da labule mai juyawa kamar na sarauta taga biyu na dakin suna kallon lambun cikin gida, inda tsuntsaye ke ta shawagi, cike da kyan gani. dakin na da fanka da AC, amma Halima bata san amfani da komai ba. Sai kallon su take kamar kayan sihiri.
Ta zauna a gefen gado daidai lokacin wata mai aiki – Hasiya – ta shigo da murmushi a fuskarta. Hasiya daga Sokoto ce, mai ƙanƙantar jiki da zubin kawaici atake suka fara haɗuwa Hasiya ta ce da ita:
“Wallahi Aunty Halima kin yi kyau, da gaske ne ke daga ƙauye?”
“Eh... daga Gembo,” ta ce da dariya mai daɗin ji. “kin taɓa jin sunan kauyen?”
“A'a, amma yanzu na ji ki. sai dai ki gyara nan Abuja fa ne Idan baki yi wayo ba, sai a cuce ki.”
Nan suka fara zama ƙawayen gaske. Halima ta fara ɗan sabawa cikin gidan, musamman da yaran Alhaji Saminu goma da ke gidan. akwai Muneerah da Ruqayyah – ‘yan mata manya masu haɗe da kwalliya da rashin kunya, masu jin turanci da yi wa Halima kallon kamar uwar kauye suna kiran ta “that girl from bush” a bayan ta.
Sannan akwai Aminu Junior da Zaid, samari matasa da suka fi ɗaukar lokaci a wajen gidan basu damu da sabuwar mace, sun fi shagaltuwa da motocinsu da rayuwar club da Instagram.
Yara uku ƙanana—Sulaiman, Abbas, da Fadilasun fi sabawa da Halima suna zuwa ɗakinta suna wasa da ita ta dinga yi musu wasan shanu da dabbobi da kida da rawa irin na ƙauye, suna dariya kamar an saka musu annashuwa a zuciya tana ɓoye wannan zumunci da su domin kada uwayensu su ji.
Matar biyu kuwa, Hajiyah Mariyah da Hajiyah Sabeerah, su ne abokan huldar Nafisa amma Hajiyah Mariyah ce shaidaniya, mai haƙurin fitina da halin mugunta tana kallon Halima da kyankyami, tana cewa:
“Wato wannan ƙaramar ‘yar Fulani ce ta zo mana da daddare? Allah ya sa ba za ta ja mana Alhaji ba.”
Tun daga rana ta fara tsara yadda zata nunawa Halima cewa gidan ba da sauki ba ne. tana tura mata ayyuka kamar ba matar aure ba: “ki share wancan, ki gyara kicin, ki tafi can ki goge banɗaki.”
Halima kuwa, da jin kunyar Fulani da biyayya, sai ta dinga yi tana mika hannu da zuciya, ba tare da kuka ko korafi ba inda Hasiya ta fi shiga tsakiya, tana mata nasiha da rarrashi:
“Ki yi haƙuri Halima, nan ne birni idan kika nuna rashin juriya, sai su hana ki kwanciyar hankali amma Allah yana tare da mai gaskiya.”
A haka Hajiyah Nafisa ta dinga kallon yadda Halima ke yi wa yara wasa, tana girki da kyau, tana wanke-wanke da murmushi da farko tana kyamar ta, amma wata rana ta shigo dakin Halima sai ta ganta tana dinki wa Fadila riga da hannu wani abu ya motsa a zuciyarta. Ta ce da kanta:
“Wannan yarinyar... ba ta da mugunta kuma girmanta yana shigowa hankali.”
Halima kuwa har yanzu bata san haka ba. zuciyarta na yawo ne da tambayoyi: “shin wannan rayuwar ita ce rabona? ina mahaifina da mahaifiyata? W
wannan Alhaji Saminu fa, me yasa yake sona?
wani dalili ne yasa ya kawo ne gidan sa ya ajiye tsawon lokaci bai dawo garine ba?
Ohhhhhhhh ga Halima ga Abuja
a sannu a hankali zamu shiga labarin Halima
continued ƙanwar soja in Sha Allah
✍️
🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
AFTER THE MOON🌕
BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star
15 / 16
07/ 5/ 2025
Iskar hamada ta na kada yashi cikin karfi, tana fasa fuskokin su da ƙaƙƙarfar zafi gaban su babu komai sai fure-furen duhu da tsayayyun ciyayi waɗanda rana ta ƙone su har sun bushe. kusan ko motsi ba ya sake yi sai idan iskar ta kaɗa su kamar wasu fatalwun da ke kaɗa hannunsu don ƙiran mutuwa.
Jiki duk jini, ruwan jiki ya bushe. Fuskarsa ta kumbura, leɓɓansa sun fashe saboda ƙishi da rana dukansu suna daure cikin zafi da juna, Yazid ya ɗaga kai da wahala, yana wani tunani kamar wani ɗan ruhi mai kaifin fahimta, ya fara rerawa da wata murya mai kauri wadda ke ɗauke da ƙyamar wahala:
"Bayan wata...
bayan wata akwai haske
Bayan dare akwai rana
a duhun daji babu alheri,
a zuciya babu tsira..."
Waƙar ta ja kunnensu gaba ɗaya. Ihsan ta ɗan kai hannu ta shafi kafadarsa, Maryam ta rungume ƙirjinta, tana kokarin hana kuka.
"ku shirya..." Maryam tace a hankali, murya kamar tana fitowa daga wani daki mai ƙyama. "Zan baku labarin soyayya "
suka gyara zama, sun sha wahala, " amma labari na da ƙarfi fiye da na ihsan domin wanan labarin soyayya da butulci cin amana da nishadi yana da matukar muhimmanci a yanayin da muka tsinci kanmu "
Maryam ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, tana kallon abubuwan da suka gabata a cikin zuciyarta a yau, ta yanke shawarar cewa lokaci ya yi da za ta bayar da labarin soyayya. Labari wanda ba kawai soyayya ba ne, har ma yana da cike da butulci, tausayi da ƙalubale, wannan labarin yana da ban sha'awa, cike da nishadi, kuma yana dauke da darussa masu nauyi ga wanda zai saurara “amma soyayya ba ta tsaya a nan ba,” Maryam ta ce, tana dariya. “duk da haka, akwai abubuwan nishadi, da tausayi.
( Lokaci yayi da zamu shiga labari cikin labari Maryam zata bamu labari a cikin tafiyar su na Bayan wata a inda aka mafarauta suka kama su ,suna tafiya dasu cikin wahala da zafin rana da yunwa )..
RUGAR FULANI
Rugar tana cikin zurfin dajin Arewa maso gabas, cike da ciyayi kore-kore da ke motsawa cikin sanyi na safe gidajen su cike da tsari na gargajiya, daga bukkoki masu rufi da itatuwa da kwari na fulawoyi masu ƙanshi. a gefe akwai madugu mai fitowa daga tsauni, yana gangarowa zuwa tabkin da shanun su ke zuwa kowane safe a cikin rugan ana jin karajin shanu, da waƙar kiwo da yara ke rerawa, kowane gida na da kangon dabbobi, da inda matan gida ke nono da jujjuya fura.
Sunanta Halima, kyakkyawa ce tamkar wata a tsakiyar dare idanunta farare ne masu zurfi, suna ɗaukar hankali da kyalli mai launin kwayar gwal fuskarta farin fata ce kamar nonon shanu, tana da dogon hanci da siraran leɓɓa gashinta baƙi ne da sheƙi, an nade shi cikin ɗamara ta Fulani mai launin ja da zinariya tana sanye da zanne mai ɗinki na gargajiya, da ƙyarar kunne na azurfa, da zobba masu sarkar ƙaho tana da shekaru goma sha biyar, amma hankalinta da nutsuwarta sun fi na shekaru.
Halima tana da ƙwarewa wajen kiwon shanu, ta san kowanne suna, kuma tana iya busa algaita da wake-waken daji da suka gada. Tana da natsuwa da ladabi, amma cikin zuciyarta akwai mafarkin soyayya da birni, duk da tana jin kunyar faɗa ,a