x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - BAYAN WATA

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 71166 words

Category: Love Stories

Views 143

04 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
tarihi—don shiryawa ko rushewa."

Aljanin ya saki wata doguwar ajiyar zuciya, sannan ya dago idanunsa masu launin toka yana kallon Kashifa.

"Yar uwata... ita ce ta fara kuka."
muryarsa ta yi rauni, kamar yana tuna da wani lokaci mai cike da azaba.

"Kukan tausayi gare k kukan nadamar abin da iyayen mu suka aikata. Ihu ta saki – ihu na hakikanin takaici da juyayi. Ihu mai karfi da ya girgiza sama da kasa, ya barin kauyen nan da bak’in duhu."

"Tun daga wannan rana... ƙauyen nan bai sake fitar da amfanin gona ba ƙasa ta bushe. Itatuwa sun karye ruwan rijiyar ya koma ja kamar jini." ya sauke kansa ƙasa, yana cigaba:

"mun bar ƙauyen mun nufi birni a can muka sami labarin addinin Musulunci muka karɓa da zuciya daya muka tsarkake zuciyarmu da imani."

"Amma duk da hakan... ba mu taɓa daina kallon ki daga nesa ba mun kasance muna lura da ke, Kashifa."
ya dan yi shiru, sannan ya karashe da murya mai zurfi:

"Saboda ke... ke ce muka yarda kin fi kowa cancanta. Cancanta ta ɗaukar fansar da ke cikin jin daɗin yafiya. Fansar da ke a cikin ƙaunar da ke shirin dusashe tarihi."



Aljanin ya ɗago ido ya zuba su cikin na Kashifa wutar hasken da ya haskaka dajin ta dan ja baya, kamar tana sauraron shiru. Sai kawai muryarsa ta sake rawa, da ɗan kuka a ciki:

"Rashin tsoro ki shi ne ya jawo zuwanki nan. kuma saboda hakan, mun fahimci cewa lallai mun kai ga karshen fansa."

Ya durƙusa kamar yana neman afuwa daga wata sarki, ya ce:

"Mun tuba, Kashifa muna neman gafara ba mu sake jin daɗin kisa ba mun fahimta, mun gane... mummunar azabar da iyayenki suka sha ba ta da laifi sai rashin fahimta tsakaninmu."

"Yanzu muna tambayar ki da zuciyarmu gaba ɗaya... ya kalli ƙasa, sannan ya ɗaga idanu da hawaye:

"Zaki ɗauki fansa a kanmu kamar yadda iyayen mu suka ɗauka akan ku? ko kuwa... zaki yafe mana, ki tsarkake wannan ƙauyen da zukatanmu daga laifin da ya gabata?"

Shiru ya mamaye wurin. Iska ta daina motsawa dajin ya mutu duhu ya tsaya cak, yana jiran amsarta.



Zuciyar Kashifa ta fara narkewa kamar ƙanƙara cikin rana hawaye suka gangaro a idonta — ba don rauni ba, sai don tarihi. Ta kalla su aljanun biyu da ido mai daci da tausayi.
"An muku rauni tabbas kisa kisa ne wannan zalunci ne amma ku kuma… kun ɗauki fansa akan bayin Allah waɗanda ba su san komai ba. Laifin wasu baya shafan kowa!”



Ta runtse ido, ta dafe kirjinta da hannunta mara takalma, jin radadin da ya wuce rai. “Na ji, kuma har yanzu nake jin radadin mutuwar iyayena... amma hakan ba zai sa ni ci gaba da jini ba fansar da ba ta hana jini zuba ba, ba fansa bace... zalunci ne da aka ɗinke da sabon zalunci.”

sai ta miƙe a hankali, kamar wata sarauniya da hawaye suka tsarkake zuciyarta.
“zan yafe zan tsarkake zuciyata — ba don cewa ban damu ba, amma don in fara sabon fata. Amma ku kuma...” ta nuna su da hannu:

“Ku zama haske a cikin wannan duhun. Rijiyar da aka haifar da kukan jininku, ku mayar da ita rijiyar salama. Ku kare rayuka, ku wanke wannan wuri da alfarma.”

Duhu ya fara raguwa... wani walƙiya ya bayyana a sama... kamar rahama ce ta sauka daga sama.




Kashifa ta ɗaga kai, tana mai tausasa murya.
“Yanzu kuma… ku bi bayana ku tafi da ni ku koya addinin musulunci wannan hasken da kuka gani yana tasowa daga zuciya ce mai neman gaskiya tsawon lokaci ina ganin wannan mafarki, a kullum ina ganin ku, amma rawar da kaina ke yi ba ya bari in gane da gaske menene.” ta juyo da ƙarfi, idonta cike da ƙarfi da ƙasaita.
“Yau na gane, kuma zan ɗauke ku a matsayin ’yan’uwa mu tafi ilimi zamu nema, haske zamu bi. Allah yana karɓar tuba.”

Aljanin ya zube ƙasa kamar dutse da aka karya daga tsauni ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro. “Subhanallah... Subhanallah! Yabo ya tabbata ga Allah, Mahaliccin Aljannu da Mutane!”



Ya fashe da kuka, yana sunkuyar da kai ƙasa, yana faɗin:

“mun ga haske… mun ji gaskiya. An tsarkake zuciyarmu da kalmominki. Allahu Akbar! Allahu Akbar!”
haske mai launin zinariya ya rufe gun. Daidai lokacin rana ta fito, kamar ana bude sabon shafi.
BAYAN SHEKARA ƊAYA



A lokacin da jama’a suke kallon wannan mamaki, sai ga Kashifa ta bayyana cikin kwanciyar hankali, murmushi a fuskarta, tare da bayanan ilimin Musulunci da ta kawo wa ƙauyen Tsuntsuwa bayan hannunta na dama da hagu, aljanu biyu ne tsaye suna kallon kowa cikin shiru, kamar masu tsaron ta a gefensu kuma, babo mai sanyi da kallon firgita, wanda ke sa kowa jin tsoro, ya tsaya.

Kashifa ta ɗaga murya cikin nutsuwa, tana bayyana cewa yanzu lokaci ne na warkarwa da fahimta, ba na tashin hankali ba ta yi kira ga al’ummar ƙauyen su rabu da tsohuwar al’adun fansa, su rungumi zaman lafiya da ilimin addini jama’ar ƙauyen na saurareta da cikakken hankali, duk da har yanzu akwai wasu da ke rikicewa a zuciyarsu.

Kashifa ta yi nuni da cewa wannan hasken da aka gani da ruwan sama mai rahama alamar albarka ce daga Allah, kuma daga yanzu za a fara sabon zamani a ƙauyen Tsuntsuwa.



Daga nesa, sai ga Kaka Mairo ta bayyana cikin hanzari, idanuwanta cike da hawaye, tana rungumar Kashifa da ƙarfi sosai kowa a wurin ya tsaya cak, yana kallon wannan lamari da mamaki, suna tambayar juna cikin shiru, “Me ya faru? Kashifa bata mutu ba? Me yasa wannan haske ya bayyana?”

Kashifa, cikin tausayi da ƙarfi, ta amsa da muryar da ta ɗan yi rauni:
“Ban mutu ba… wannan haske da kuka gani, alamar ne ta albarka da rahama daga Allah. Wannan rana ce ta sabon farawa, babu ƙarfi a cikin fansa ko azaba, yanzu lokaci ne na zaman lafiya da gafara.”
Fatu kuwa, tana tsaye kusa da su, fuska cike da farin ciki da kwanciyar hankali, amma bata yi magana ba ta duba kowa da ido mai cike da amincewa da fata, tana jin cewa wannan shi ne ƙarshen duhu da suka rayu a ƙauyen Tsuntsuwa.



Sarki Idris ya ɗaga hannu a hankali, ya yi shiru na ɗan lokaci yana kallon Kashifa cikin nitsuwa. Sai ya ce da murya mai laushi da hikima:

“Yarinyata, mun san cewa ba sauƙi ne ke gare ki ba. amma mun zo nan domin mu saurari labarinki, duk abin da kike da shi a zuciyarki. Kada ki ji tsoro, wannan ƙauye gaba ɗaya na tare da ke, kuma muna son mu fahimci komai daga bakin ki.”

Kashifa ta ɗan yi shiru, ta duba kowa da kowa a idon su kafin ta fara bada labarinta cikin nutsuwa da ƙarfi. Kowa ya yi shiru, suna sauraron kowace kalma da take faɗa, suna jin cewa a ƙarshe an kawo ƙarshen wannan tsananin duhu.



Kashifa ta fara bayar da labarin cikin hikima da natsuwa, tana bayani dalla-dalla yadda ta tsira daga duhun ƙauyen, yadda ta gano addinin Musulunci, da kuma yadda wannan ilimi ya kawo mata kwanciyar hankali da canjin rayuwa.

Yayin da take magana, idanuwan mutanen ƙauyen sun yi ƙara haske, wasu na damuwa, wasu kuma suna jin wani sabon fata na farawa a zukatansu. Maganganunta sun shafi zukatan su, suna jin gaskiya da nufin zaman lafiya.

Bayan ta gama, Sarki Idris ya mike tsaye, ya yi addu’a tare da roƙon Allah ya sa wannan sabon haske ya tabbata a cikin ƙauyen ya yi kira ga kowa da kowa da ya rungumi addinin Musulunci cikin kwanciyar hankali, fahimta, da yarda, domin kawo ƙarshen dukkan ƙiyayya da tashin hankali da suka yi ta addabi ƙauyen.

Mutanen ƙauyen suka amsa da farin ciki da karɓar wannan sabon tafarki, suna yi wa Kashifa godiya da fatan alheri. An fara gudanar da ibada, koyar da al’adar Musulunci, kuma ƙauyen tsuntsuwa ya fara sauyawa zuwa wuri mai albarka da zaman lafiya.


Nan suka kutsa cikin hanyar, ga rijiyar da bishiya, inda Kashifa ta kafa ƙaramin makarantar karatu don manya da yara.

A cikin wannan makaranta, mutane na koyon karatun Al-Qur’ani, ilimin addini, da sauran darussa masu amfani da za su taimaka wajen bunkasa rayuwarsu. Kashifa na koyar da su da zuciya ɗaya, tana ƙarfafa su da nuna musu muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai.

A hankali, ƙauyen tsuntsuwa ya fara haskakawa da farin ciki, yara suna dariya, manya suna tattaunawa cikin kwanciyar hankali, kuma kowa na jin cewa wannan sabon rayuwa ce mai albarka.






https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC


BAYAN WATA
SABON SALO
BY
NARNAH KANWAR SOJA ✍️✍️
08101235739
SHARE FISABILLILAHI







MASU TAMBAYA DA WANDA SUKE KARATU KAR KU MANTA CEWA JOHN NA BAMU LABARIN KASHIFA NE
INDA SABON SALO YA SHIGO LABARIN DA CEWA IHSAN DA ADO MA'AURATA NE SUNA BAWA YARAN SU LABARIN BAYAN WATA LITTLE YAZID DA IMAN .

***********************************


PAGE 42 / 43
.
Kashifa ta dube Malam Sambo da mai gonar Mangoro da dariya mai sanyi, tana cewa,
“Don Allah, kar ku bini da sanda, ku bar ni a hankali. Wannan haske da kuka gani ba nawa bane kawai, na mu ne duka — na wannan ƙauyen tsuntsuwa, na zukatanmu, na zaman lafiya da muka fara ginawa.”

Ta yi murmushi sannan ta ci gaba da cewa,
“Ku sani, wannan sabon shafi ne, ba zamu bari tsohuwar duhu ta dawo ba.”

Malam Sambo da mai gonar Mangoro suka kalle ta da mamaki, suka fahimci cewa yanzu lokaci ne na hadin kai da yafe wa juna.

Daga nan suna zaune a cikin gida, sai ga Kashifa ta shigo gun Fatu da magana a kunnenta, tana cike da kwadayin Mangoro. Ta ce,

"Fatu kin san dai gonar Mangoro na da mahimmanci a gare mu tunda halittar Allah ne, ba sata ba ce, kuma ba za mu bari a ci gaba da barna ba mu tafi gonar Mangoro mu gyara ta, mu kula da ita yadda ya kamata."

Fatu ta kalle ta da murmushi, ta amsa da cewa, “Lallai, kin fadi gaskiya zamu tafi tare mu tabbatar da cewa gonar ba ta sake zama wurin rigima ba.”

Suka shirya suka fita tare zuwa gonar Mangoro, cike da burin kawo zaman lafiya da gyara al’amura.

John ya kalli Ihsan da Maryam da murmushi mai ɗauke da natsuwa, sai ya ce:




“To, mun dawo cikin kabarin bayan wata… yanzu zan baku labarin Kashifa sosai, domin na bayyana muku wani sirri da na ɓoye daga ƙasar Makka.”

Ihsan ta yi ihu a hankali, idanuwanta sun kumbura da hawaye, ta ce:
“Ka sani, kafin ka fara, kai ka ga ido na ya kumbura da kuka labarin Kashifa ya taɓa zuciyata sosai.”

Maryam ta matsa kusa da su, ta ƙara cewa:
“Irin wannan labarin yana da matuƙar amfani, musamman ga waɗanda ke neman ilimi da fahimtar gaskiya.”

Sai John ya ɗauki numfashi, ya fara bada labarin cikin nutsuwa, duk suna sauraro cikin shauƙi da tsananin sha’awa.

A lokacin da muka isa Makka, na karɓi addinin Musulunci yanzu kuma, ba a kira ni da suna John ba, sai Muhammad Munir sabon suna na cikin wannan sabon rayuwa da na fara.






DARASIN LABARIN KASHIFA


Labarin Kashifa ya kasance ɗaya daga cikin labarai masu ƙarfi da suka taɓa zuciya, inda ya nuna mana muhimmancin yafiya, canji, da imani a rayuwa Acikin wannan labari, mun ga yadda kisan kai, rikici, da aljanu suka addabi wani ƙauye har tsawon shekaru, amma kuma yadda zuciyar ɗan adam zata iya canzawa idan aka yi amfani da ilimi da addini.

1. Yafiya: Hanya Mafi Karfi
Ko da yake ƙauyen Tsuntsuwa ya sha wahala da azabar rashin adalci da kisan kai, Kashifa ta nuna mana cewa mafita ba ta cikin ɗaukar fansa ba, sai dai ta hanyar yafiya. Wannan yafiya ta kasance ba ta manta da abin da ya faru ba, amma ta zama hanya ce ta tsira da zaman lafiya Yafiya tana kawo sauƙi ga zuciya, tana kawar da girman kai da ƙiyayya, tana kuma bada damar sake gina rayuwa cikin nutsuwa da jituwa.

2. Canji Mai Dorewa Ta Hanyar Imani
Bayan tsawon shekaru na rikici da firgici, mutanen ƙauyen sun yanke shawarar karɓar addinin Musulunci, wanda ya kawo musu sabuwar hanya ta rayuwa da fahimtar juna. wannan canji ya nuna mana cewa babu abin da ba zai yiwu ba idan mutum ya bude zuciyarsa don karɓar sabon ilimi da kyawawan dabi’u. Imani ya zama tushen da ya mayar da ƙauyen tsuntsuwa wuri mai haske da walwala.

3. Ilimi A Matsayin Makami
Kashifa ta kafa makaranta a ƙauyen domin koyar da yara da manya ilimi na addini da na duniya, domin tabbatar da cigaban ƙauyen. wannan yana nuna cewa ilimi ba wai kawai karatun littattafai bane, har ma da koyar da tausayi, hakuri, da fahimtar juna, wanda yake da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaba a kowanne wuri.

4. Hankali Da Hikima Wajen Yanke Shawara
A lokacin rikici, mafi yawancin mutane sukan dauki matakai cikin fushin zuciya da fargaba. Amma labarin Kashifa ya nuna mana cewa a kowanne yanayi, yin amfani da hankali da hikima wajen yanke shawara shi ne babban makami na warware matsaloli. Shawarar da aka dauka ta dogara ne akan ilimi, yarda da addini, da kuma fahimtar gaskiya, ba bisa son zuciya ko ƙiyayya ba.

5. Haske A Cikin Duhu
Labarin Kashifa yana koyar da mu cewa duk da yanayi na duhu da wahala, haske zai bayyana idan an dage da hakuri da yawaita addu'a da imani. Tsuntsuwar da aka rufe da duhu ta rikici ta koma wuri mai albarka da zaman lafiya bayan zuwan Kashifa da koyarwar musulunci. Wannan yana nuna mana cewa ba wai duhu ne zai dade ba, sai dai haske ne zai wuce.


Kammalawa

Labarin Kashifa ba kawai labari bane na ƙauye da aljanu ko rikici, amma babban darasi ne ga rayuwarmu ta yau da kullum yafiya, ilimi, da imani suna da muhimmanci wajen kawo zaman lafiya a zukatanmu da kuma al'ummarmu baki ɗaya wannan labari ya karfafa gwiwa cewa kowane mutum yana da damar canzawa, kuma akwai haske a kowane duhu idan muka rungumi gaskiya da alheri.



John ya dawo Muhammad Munir daga yanzu sunan matafiya biyar
IHSAN wacce ta bamu labarin ( PRINCESS RAHILAT)

MARYAM wacce ta bamu labarin ( HALIMATU SADIYA )

YAZID wanda ya bamu labarin ( ALJANIN SAJIDA)

ADO wanda ya bamu labarin ( MASARAUTAR ZAKAR )

JOHN WATO MUNIR ya bamu labarin ( KASHIFAH ).

A yanzu mun gama dukkan labarai nasu zamu afka cikin Bayan wata sabon salo

Duk suna cikin farin ciki marar misaltuwa, kowa na murnar dawowar John, wanda yanzu ya koma Munir, cikin addinin Musulunci. fuskar Maryam cike take da annashuwa, tana ta mikewa da saukowa, tana godiya ga Allah da ya bude masa idon zuciya.

"Sannu Munir, mun yi matukar farin ciki da ka samu wannan haske," ta furta da murya mai taushi cike da jin dadi.

Abokai suka taru, suna rungumar Munir, wasu na hawaye suna zuba saboda wannan canjin da ya yi na rayuwa. Ado ya ce cikin murna, "Labarin Kashifa ya koya mana darasi mai mahimmanci, yafiya da fahimtar juna su ne mabuɗin zaman lafiya."

Sai aka ji wani daga cikin su na cewa, "Munir, yanzu kana da sabuwar rayuwa, za mu tsaya tare da kai a kowanne lokaci."

A cikin wannan yanayi na farin ciki da godiya, an shirya daukar su a cikin trailer zuwa wani sabon wuri — wurin da za su fara sabon babi na rayuwarsu, da cikakken sabo da tsarkin zuciya.

Maryam da Munir, suna zaune tare a cikin trailer, suna kallon juna da murmushi, suna jin dadin wannan sabon farawa da Allah Ya basu.


-

Bayan mintuna arba’in da tirelar ta fara tafiya, sai muka ji ana harbi da farko mun ɗauka ƴan sanda ne ko jami’an bincike amma harbin ya wuce ƙima. Tirelar ta tsaya cak wani daga cikin masu raka mu daga baya ya ce da karfi, "ƴan bindiga ne! masu garkuwa da mutane!"

Cikin kwantenan, su Maryam da John sun fara kuka a shiru. Ihsan ta kulle baki da hannunta, tana juyi kamar mai jiri. Fuskar ta cike da damuwa da tsoro.

“Wannan ba aikin gwamnati bane,” Ado ya ci gaba da bayani, “waɗanda suka tare tirelar ƙungiyar masu safarar mutane ce, waɗanda ke sayar da ƴan gudun hijira kamar kaya. Suka ce daga cikinmu za su ɗauki guda biyu su kai Oman don su saida sauran idan har suna da kuɗi ko an biyansu, za su tsallake.”

Duk mun tsaya a cikin rashin tabbaci da firgici. Sai ga Maryam da John cikin kuka, suna rabuwa da sauran ƙawayensu da ƙanƙancewar zuciya. Wasu daga cikinmu suna ta addu'a cikin zuciya, suna roƙon Allah ya cetar da su.

Maryam ta rungumi Isham da ƙarfi, hawaye na zuba daga idon ta. "Munir, za mu tsira, za mu haɗu da iyayenmu, mu rayu cikin salama," ta furta da ƙarfi da ƙoƙarin kwantar da hankali.

Munir kuwa, duk da tsoron da ke ransa, ya murmusa ƙanƙanta. "Insha Allah, Maryam, ba za su raba mu ba. Zan kiyaye ki har abada."

Sai dai kuma, dukkanmu mun san cewa wannan rana za ta kasance jarabawa mai girma ga zuciyarmu da ƙarfinsu.




Ihsan da Ado suna kiransu da ƙarfi, suna ta kiran sunayensu cikin damuwa da kuka. Amma a cikin ƙwantenan, Maryam da John sun riga sun tsaya, sun rufe idonsu da hannu suna ihu, kamar mutane biyu da zuciyarsu ke ƙaryewa a hankali.

Sai aka fisge su daga ƙungiyar, aka ɗaga su cikin ƙarfin hali, ba tare da wata tausayawa ba. "Ku bar su, babu wanda zai ceci su," wani daga masu garkuwa da mutane ya ce da tsanani.

Maryam ta yi ƙoƙarin riƙe John, amma an raba su kamar yara masu laifi. "Munir! Munir! Kada ka bar ni! Kada ka bar ni!" ta yi ihu har cikin ƙwairo, ƙarfin zuciyarta ya fara raguwa kamar ruwa mai zuba daga tafki.

John kuwa, ya rike hannun Maryam ƙoƙarin nuna ƙarfin hali, amma hawaye sun fara kwarara daga idonsa, ya yi ƙoƙarin cewa, "Maryam, za mu tsira, kada ki yi kuka…" Amma sautin muryarsa ya tsaya, ya zama kamar ƙamshin iska mai saurin shuɗewa.

Mun tsaya a wajen hanya, cikin azaba da baƙin ciki, muna ganin yadda suka tafi daga garemu, amma zuciyarmu na karyewa. Wani lokaci zuciyar mutum ta fi jikin sa nauyi, mu kuwa mun ji kamar an fasa zuciyarmu da ƙarfin zafi.

Mun tsallake checkpoint ɗin cikin wahala da tsoro, numfashin mu na matsewa, zuciyoyin mu na cike da fargaba da rashin tabbas. Amma cikin duk wannan bakin ciki, sai muka haɗa ƙarfi da addu’a, muna roƙon Allah
End Ads