da yake a zuciyarsa cikin 30minuts suka shiga cikin Anguwar su Hajiya Nafisat Mommah dinsa, bosso estate Gidan hajia nafisa tasa, direct ya nufa, yana zuwa bakin gate ɗin Gidan, ya Danna horn da gudu gate man yazo ya wangale masu kofar gate ɗin, Gidan, direct motar su ta shige tsakiyar compound d'in Gidan Allah sarki baiwar...Allah..
"Tunda suka shigo cikin Gidan FAREEDAH ta ji gabanta na fad'uwa, lura da yayi da yanayinta hakan yasa cikin tsansar tausaya mata ya zagayo yabude mata marfin motar, sannan ya Kama hannuwanta kafin cikin sanyin murya had'i kwantar mata hankali NABEEL ya bud'e bakinsa. Yace"
Haba FAREEDAH Dan ALLAH
ki kwantar da hankaliki kidai na tsaka damuwa a cikin ranki,kinji ko!...
"Dan razana FAREEDAH tayi kafin cikin tsananin fad'uwar gaba ta buɗe bakinta tace"..
Babu komai kalbinerh kawai dai tsoro nake ji , saboda nasan rabuwa mu tazo, ko?
,, share ta yayi batare da yace da ita komai ba sukanufi hanyar nufi hanyar da zai Sada sa da babban parlourn Gidan.wao part d'in Hajiya Nafisat NAFISAT ,..
A tare suka
shiga cikin Gidan,...
Zaune Mommah take a cikin parlourn tare da Azmerh da NABEELAH yayinda Azmerh take zaune agefen Mommy haka zalika itama NABEELAH sun saka Mommy
a tsakiyar su, ..
Mtswww
Azmerh Tana ganin shigowar su NABEEL da FAREEDAH ta ja masu tsaki
tare da kauda Kai ......
Gaba dayansu su FAREEDAH da NABEEL suka zube bisa Saman lallausar center carpet din Falon suna kwasar gaisuwa ,"cikin kasaita da isa da nuna izza Momman take ansar gaisuwar tasu, kallon FAREEDAH tayi sannan cikin dak'awa FAREEDAH Tsawa Mommy ta bud'e bakinta
tace tace"Ke kuma bakar juya. Babban munafuka diyar bokaye, maza maza ki tashi ki bani waje zan yi magana da ɗana munafuka annamimiya algugunmah
shegiya bakar juya..
"Jiki a sanyaye FAREEDAH ta mik'e ta nufi dakin NABEELAH yayin da ita kuwa Mommy sai da taga shigewar FAREEDAH sannan ta maida kallon izuwa gurin NABEEL cikin tsansar bacin rai had'i da d'aure fuska Mommah ta cigaba ......da cewa, " NABEEL shin a duniyar nan kana da wacce ta fini? "
Shi ko NABEEL da kansa yake aduke cikin ladabi da biyayya
ya bud'e bakinsa yace
" Babu Mommah
"To me yasa ka ke kyamar abunda na kawo maka, bayan kasan cewa shine mafi kusan Chi a gare Ka inji cewar mommy..
Cikin sanyin murya NABEEL yace "
Mommah Bana kin Azmerh amatsayin kanwa amma huja daya ne na baki ,to kiyi hakuri gami da uzuri kasan cewa mu tare da FAREEDAH shin ne burina "
"To shikenan Inji cewar mommy..
Sannan ta buɗe baki cikin tsantsar masifa haɗi da bala'in da suke cinta tana mai cigaba da faɗin"
duk Wanda ka ga ya kona rumbunsa yasan inda toka take tsada ne,...soboda dan ya sayar ,ya samu riba,... to Kai a cikin wannan wane riba kasamu a tsawon wannan lokachin da Kake tare da ita,?"cikin fad'uwar gaba NABEEL yace "
Momma ba zan dai na baki hakuri ba domin babu jayayyah atsakanin ni da ke ,amma Dan Allah kiyi hkr kibar magana Azmerh "
Kallon mamaki Nabeelah yake ma mommy kafin cikin tsananin bacin rai NABEELAH tace "haba momma
Dan Allah ki....
"Ke NABEELAH Dakata
Mommy ta daka mata tsawa ta hanyar katseta, sannan ta cigaba da cewar "Kuma ki tashi ki bar wajen nan kafin in karkarya maki kasusuwa..
Ay kuwa kafin kace k'obo cikin tsananin jin tsoro kar tasha duka wajen Mommah NABEELAH miƙe tsaye kai tsaye ta nufi bed room d'inta ......Acikin d'akinta ta tadda FAREEDAH tana zauna a saman gadonta ta had'a Kai da gwiwa duk abin duniya ya isheta, kallon tsatsan tausayawa take ma FAREEDAH kafin cikin ranta tace Allah sarki rayuwa, Allah sarki baiwar Allah Allah ya isar maki, Allah ya kareki daga sharrin makiya da masu son ganin bayan aurenki,,,,, Mommy wai wanne irin laifi FAREEDAH ta aikata maki ne wai Kika tsane ta haka!kwata kwata narasa mesu FAREEDAH da NABEEL suka
tsarewaa tsohuwar banzar Nan datake so taga Bayan auren su, tsanar tayi yawa wai wannan wane irin masifa ce haka!,.
Dafa kafadar FAREEDAH NABEELAH tayi yayinda FAREEDAH ta dago Kai a razane!!!
Kallon FAREEDAH NABEELAH tayi Kafin Cikin sanyin murya Nabeelah tace" Dan Allah aunty FAREEDAH
kiyi hakuri da abunda Mommah take yin maki..
"FAREEDAH ta dube ta sannan tace "wallahy Nabeelah ban taba ɗaukar abinda Mommah take yi min amatsayin wani Abu ba saboda aganina ta damu da halin da nake cikine Kuma tamkar uwa nake ɗaukar Mommy agurina saboda Haka kada ki damu ta ƙarasa maganar tana mai sakin murmurshi dole.
"Momma ba uwarki bace suka jiyo murya kamar daga sama Azmerh ce ta cigaba da shigowa dakin sannan ta cigaba da cewar "nace Momma ba uwarki bace domin kuwa inda ace Mommah uwarkice ba zaki mallake mata ɗa ba, Kuma ina son ki saka a cikin ranki cewa ni baby Azmah yaya NABEEL Sai ya aure ni ko yana so ko baya so, kuma ni nan da kike gani na lafiyayyiya ce, ba kamar keba bakar juya "smiling kurum FAREEDAH tayi ba tare da tace da ita komai ba ...
Bangaren su Mommah kuwa cikin daka masa Tsawa mommah tace "ba damuwa zan baka zabi Abu uku ,na daya Ina son Ka rabu da FAREEDAH har Abadah kwata kwata baka ba ita, na biyu Ina son Ka Kara aure, cikin two weeks...cikin daga murya ta cigaba da cewar "......na uku , ko ka bani nono na... da... na baka... kasha ....
A matukar razane NABEEL ya d'ago kansa ya kalli mommy sannan yace "Dan Allah Mommah kiyi hakuri ,ba zan iya rabuwa dake.ba ko dana wuni daya, kina nan aMatsayin uwa agare ni ,but Mommah kiyi hakuri ba zan iya yi ma FAREEDAH kishiya ba,... Cikin tsananin bacin rai Mommy ta d'aga hannunta ba tsaya wata wata ta sauke masa zazzafar mari tare da fad'in " Ni zaka gaya wa zancen banza! To Bari kaji yau nake bukatar answer nan, ba Sai tomorrow ba ,Dan Haka meye zabinka? "Mommah na zabi hakuri agurin ki , ki yi min alfarma kasan cewa zama na da FAREEDAH ..
"Inna lillahy wa Ina ilaiheem rajioun inji cewar Mommy shikenan ta gama mallake min ɗa murmurshi dole tayi kafin cikin tsananin bacin rai ta bud'e bakinta ta cigaba da cewar
"NABEEL tunda nariga na rantse cewa baza ka zauna da wannan matsiyaciyar yarinya nan ba,......to ku je gida duk wani abunda kasan tazo maka dashi Gidanka ,to ta kwashe Shi ta tafi ..in Kuma ba Haka ba duk abinda ya faru da Kai ,hmmm Kai Ka so ,Tana gama maganarta Mik'e, tsaye kai tsaye ta..nufi hanyar upstairs tare da haurawa sama.
NABEEL kallon photo mahaifinsu yayi, Wanda yake manne a jikin
bango parlourn ,..
*Division tuni NABEEL ya shiga *TUNA BAYA*
wani kyakkyawar Alhaji me matukar kama da NABEEL sak👌🏻 ne na hango,suna tsaye da Shi da hajiya nafisat a cikin tsakiyar parlour su,kallon Hajiya Nafisat Alhaji yayi sannan tsansar farinciki Alhaji yace "hajiya ni zan wuce gurin aiki" cikin sanyin murya Mommah tace "Alhaji maganar da mukayi jiya da kai Kuma fa, bamu k'arasaba kace min Sai yau .Kuma yau gashi zaka fita ,kar... Cikin daka masa Tsawa ya katseta! ta hanyar fad'in "..
Hajiya Nafisat muyi magana dake jiya,jiya maganar da muka yi dake biyu zuwa uku, cikin daka mata tsawa haɗi tsananin bacin rai ya cigaba da cewar "wace magana A ciki kike nufi?..
"To Ina da maganar ne da wuce magana NABEEL da Azmah Inji cewar Mom.
"Hajiya ke ma wani lokaci. fa kin fiye rigima, wannan Abu ai ba namu bane ,tunda yarinya Tana so, Shima ai NABEEL ɗin Sai atambaye Shi in yana so ,meye na wani wahala a ciki.
Kai tsaye ya nufi inda suke tsaye cikin sauri ya ƙaraso gurin su a inda suke tsaye yana mai dubansu cikin tsansar kulawa ya buɗe bakinsa yace "..
Ina kwana Abba? Good morning Mom?
"Lafiya my dear son
Inji cewar Abba yana mai kallon ɗan nasa sannan ya cigaba da cewar "Kai ya maganan yarinya nan Azmerh yar Gidan Hadiza??.
"Abba ni ai ba magana kowa atare da ni ,.
Inji cewar NABEEL sannan ya cigaba da cewar "Abba jiya ba mu gama magana dakai ba. a Hanyar mu ta dawowa daga office ba Jiya ba!..
"OK natuna Inji cewar Abba
Sannan ya cigaba da cewar "
FAREEDAH NABEEL ɗin ka ko?,yar Gidan Malam SANI ko,?
"Eh Abba Inji cewar NABEEL yana mai washe baƙi sannan cikin fara'a ya cigaba da cewar " ita fa, Abba ita nike son ita nake matuƙar kauna..
"kai Masha Allah,yana mai washe baki shima inji cewar Abba tare da kallon mommy sannan ya cigaba da cewar
"To ke kin ji...
"Agaskiya bazai yiwu ba,
Inji cewar Mom tana mai kallon su kafin cikin masifa da bala'i ta cigaba cewar "haka kawai aje aɗauko na waje abar na gida! Wallahy Allah bazai yiwu ba,kuma wannan yarinya ai tayi gadon tsiya ƴar matsiyata ne kuma ba ahalinmu bace..Wallah bazata sabuba...
"OK Inji cewar Abba sannan ya cigaba da cewar "kina da wani tsari naki kenan Wanda kike so ki nuna mana, to Bari in gaya maki, ni har abunda yaro yake so ayi .shine zanyi anan ba naki tsarin ba ...
"Abba! NABEEL yakira sunar mahaifin nasa cikin fara'a.
Batare da Abba ya amsa ba ya dube ɗan nasa "yayinda shi kuwa NABEEL cikin tsansar farinciki ya cigaba da cewar "yaushe zamuje muga iyayen nata ?"ai NABEEL ko yau Kake so,zan tura baban ka alhaji Rabi'u, jeka na sallameka," ihu mom ta kurma kafin cikin ihu mommy NABEEL tace" ni Gaskiya wannan abun bazai taba yiwuwaba ! haka kurum aje auro mana diyar mayu., shi yasa tun tana ƴar karamar ta nayi masifar tsanarta , haƙa kurum yarinya tun tana yar kankanuwarta ta makalewa ɗana, harda Wani canzawa sunarta suna wai FAREEDAH TA NABEEL shi yasa Ni wallahi tun tana ƴar karamar ta natsane ta nace na tsane ta natsane ta, FAREEDAH aduk inda kike Allah ya tsine maki ALBARKA
ƙarasa maganar ta cikin ihu.
"Mtsswww
tsaki Abba ya ja mata
Tare da furta "mahaukaciyar mata,
shashsha kawai sannna suka nufi hanyar fita daga parlourn suka bar ta tsaye sai famar surfa masifa take ita dai
*WANENE NABEEL!*
Sunar mahaifinsu Alhaji Suleiman Sai mahaifiyar su Hajiya NAFISAT , su FULANI ne daga yola, Balaguru Sukai daga garin su ,suka sauka a Minna,damar can suna da yan'uwa a cikin jahar minna mahaifinsu harkar kasuwanchi yake, Kuma Allah yasa masa albarka, Dan har kasa waje yana zuwa, Alhaji Suleiman yana da ƴaƴa biyu, babban sunar sa NABEEL sannan Sai da Hajiya Nafisat tayi shakara biyar sannan ta haifi kanin sa wato Ahmed , Ahmed yaro ne kyakkyawah,..
Zaman lafiya suke ba Mai jin kansu ,bayan wasu shekaru, watarana mahaifinsu yayi tafiya ,ya tafi, metting a Abuja, akan hanyarsa ta dawowa Allah ya aiko masa da hatsarin inda anan take Allah ya amsa abunsa, Sai dai muce may your soul rest in perfect peace Alhaji ,..
Tunda Abban su ya rasu NABEEL shi yake kula da kaninsa Ahmed, domin kuwa yanzu Haka Ahmed ya tafi karatunsa a can kasan waje, AHMED kuwa yana can yana Ta karatunsa,...
Cikin kwanciyar hankali..
Su NABEEL yara ne kyakkyawai kana ganin su kasan sunsha nono Fulani, yanzu Haka NABEEL Shi yake kula da. company. mahaifinsu
SULEIMAN SALIHU COMPANY NIGERIA LIMITED sunar *company*,, . ****
Ya fad'i hakan acikin zuciyarshi yana mai sake jin tsananin shaukin son mahaifin nashi na ratsa zuciyarsa
cikin zubar da hawayen yace ".Abba!!!Innalillahi wa inna ilaihirraju'un yau nasan da ace kana raye hakan bazata faruwa ba Nabeel ya faɗi cikin shesh shekar kuka sannan ya cigaba da cewa "Allah yaji kan ka da rahama Abba Allah yasa can tafi maka nan,,,,,,,
*_ALLAH YA GAFARTA MANA KURA KURAN MU YAKUMA SA MUCIKA DA KYAU DA IMANI_*
#COMMENT'S DOMIN ALLAH !
#SHARE FISABILLAH!!
#THANKS FAN'S !!!
*Ni dai TAKU HAR KULLUM B'INGEL FULBE INA MATUƘAR ALFAHARI da ku MASOYANA ALLAH YA BAR KAUNA*
*AISHA FULANI GAL CE*
[7/4, 4:42 PM] Fulani Gal✍🏻: 💖💖💖💖💖💖💖💖
💗💗💗💗
💖💖
🌹
*FAREEDAH NABEEL*
🌹
💖💖💖💖💖💖💖💖
💗💗💗💗
💖💖
🌹
By
*A'ISHA FULANI GAL*
*🌺 CHAPTER 7-8🌺*
*DEDICATED TO :-MY LOVELY FRIEND XAYYNEB💤💤💤(XEXEN FASAHA*
__________Bayan sati biyu
kyakkyawan matashin ne na hango, janye yake da trolley ɗin sa, ya shigo cikin tsakiyar compound ɗin Gidan hajia nafisat , AHMED Kyakkyawa ne haɗe da iya shiga ya tsaru iya tsaruwa .sumar kansa ya wanda ya tarashi luf dashi baki ga tsantsi da laushi ,ita ka dai ma abun kallo ce. da burgewa. ɗan gemu nan tare da ɗan saje Kaɗan Sai sheki suke yi suna walwali, fatarsa kadai ita ma abun burgewa ce Sai ka rantse yanzu aka fito dashi daga cikin engine, farine irin tas ɗin nan, sannan Kuma yana da wani irin kyau da Karin kwarjini,Ba Sai na faɗa ma ba kasan naira da Hutu tare da jindadi, sun ratsa shi ,sanye yake cikin kananan kaya white and blue color kamshin daddadar turaren jikinsa gaba daya ya mamaye compound d'in Gidan, shi dogo ne amma ba zankaleleba de-de ne ,Shi, ba ramanme ba Kuma shi ba me kiba ba atsakiya yake kirjinsa me Ɗan faɗi normal, eye's d'insa Dara Dara suna lumshewa, face d'insa Tana da Dan tsayi Kuma Tana da Dan fadi normal face, hancinsa dogo Dan chib baiyi tsini da yawa ba, bakinsa Dan karami pink lips dashi, yana shinning, fatarsa Fara ce tamkar bature Haka ma sumar kansa take unique ce kamar ruwa two Haka yake, tafiyar sa kamar ta basarake ta maza masu ji da kansu, AHMED ba zai haurawa 25years ba, domikuwa yana ji da kuruciyar a lokacin sa.
Cikin wani irin taku dake nuna zallah kwarjininsa ya nufi hanyar da zai Sada sa da babban parlour Gidan. part d'in Hajiya Nafisat ..
De-de lokacin NABEELAH ta fito daga cikin bed room d'inta,A hankali ya murda handle d'in kofar parlour , da sallama ɗauke abakinsa,ya shigo ,shigowarsa cikin parlourn yayi de-de da fitowan NABEELAH daga cikin bed room d'inta, haka zalika yayi de-de da Kai dubanta zuwa ga kofar shigowa parlour, a daidai lokacin ne kuma narkakkun idanuwansa suka sauka a kanta..Tana sanye da 'kananun kaya wanda suka matse ta riga da wando tight! hattar da shatin nipples ɗinta sai da suka fito, wandon ya manne a jikinta ya fito da sharp din jikinta ,tsayawa Ahmed yayi yana kallon ta daga sama har ƙasa,Sakamakon yanayin kayan dake sanye a jikinta kananu ne masu matukar fitar da sura.shigarta tafi da imaninsa ,kai daga shi har ita tsayawa sukayi suna kallon junarsu, yayinda ko wanne su yake kallon Ɗan uwan nasa daga kasa har sama ,sukai Kusan minti ashirin haƙa zuwa can
Sai naji NABEELAH ta buɗe bakinta Cikin zazzakar Muryar mai matuƙar daɗin sauraro tace ...
"Sannu da zuwa "cikin ranta take cewa da gani wannan kyakkyawan matashin yaron nasan shine Autah Mommah da take yawan bani labarinsa , ashe wannan masifafiyar matar ta iya haifuwan kyawawan yarah ,domikuwa shakka ba nayi wannan matashin saurayin yafi yaya NABEEL had'uwa Nisa ba kusa ba, wow he's so cute so sweet so Handsome ,duk
wannan magana a
Cikin ranta take yi shi ..
Hajiya Nafisat ce ta fito. daga cikin kitchen,cikin