x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - LINZAMI DA WUTA free pages

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 43517 words

Category: Tale Stories

Views 224

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ga wasu Nan a warwatse...

Yana fito daga dakin jikin shi a sanyaye don ya San Nimra ta fice daga gidan ya San tana wurin mummy taje ta Kai karar shi kamar yadda ta Saba...


Ya koma dakin shi yayi wanka yayi Shirin wucewa asibiti ko gidan mummyn ba zaije ba don Kar ma su Bata mishi lokaci


Ya fito inda yaga Babu motar Nimra Alamar da mota ta tafi. Ya fice daga gidan Yana Jin wani Abu Marar Dadi Amma ya maze. Duk da ba wata soyayya sukayi da Nimra ba Amma mu amalar aure ta saka mishi son ta duk da Bata yiwa son ban Ruwan da zaiyi yabanyar da zai Bata sanssanyar inuwar da zata Mora ba Amma duk da Haka Yana Jin kamar Bai yiww Nimra adalci ba.


Haka ya Isa asibiti ya fara aiki duk da Babu ko Ruwan bunu a cikin sa . Ya wuni cikin Aiki kaca kaca har zuwa karfe biyu na Rana. Gaban shi ya Sara da ya tuna da yanzu zaije gidan mummy wacce ya tabbatar da Nimra ta Kai Mata rahoton Al Amarin da ya faru tana can tana jiran zuwan shi ta wanke shi da tijara Mai daraja ta farko...


Ya hada kayan sa ya wuce Yana Jin cikin shi Yana Kiran ciroma wato yunwa

Ya iso gidan mummy din inda yayi Karo da Hakim Zaune Yana cin abinci ya Zauna suna cin abincin a tare yayi n da Anam Yake ta wara idon ganin Nimra Amma ko kyallin ta Bai hango ba

Suna ta fira tsakanin Anam da Hakim yayin da mummy Nina ta fito da shirin ficewa unguwa wacce kullum ce tamkar ibada.
Sanye take da shiga irin ta Mai wadata kallo Daya zakayi Mata ka tabbatar da matar manya ce don kayan da suke jikin ta ko baka San tsadar Kaya ba zaka Gane nata masu tsada ne saboda tsabar kyawu da kyalkyali . Gashi in ta yarfa kwalliya Kai zaka Rantse da Allah kanwar Dr Anam ce saboda Babu Mai yarda itace Uwar sa...


Ya dube ta Yana Fadin
"Mummy fita zakiyi?
Ta dube shi tana Fadin

"Ko na fasa ne Uban Yan tsegumi? Halan yanzun ma karar ka kawo ? Kai Kam ka shiga uku wallahi mutum Babu hakuri Babu uzuri don dai takamar kana auren yarinya ka kwarzabi kanka ka addabi yarinya? To in ma tsegumin ka ka kwaso tashi sahun ka a likkafa ka wuce bani da muhallin karbar tsegumi na gaji Haka ladar ta Isa ....


"Ni ba tsegumi na kawo ba mummy yau dai ai Yar lelen Taki ce ta kawo tsegumin me tace Miki Nayi Mata ? Ni dai Babu abinda nayi Mata ....


"Wace kenan?
Ta tambaye shi da sauri...
"Nimra Mana mummy...

"Tana Ina ne yanzu?
"Yo Bata zo nan gidan ba?

Ta dube shi tana zaro idanu cike da tashin Tana Fadin...

"Ban Gane me kake nufi ba Anam? Fada min meye kake min kwana?....


Ta Zauna a Kan kujera cike da tashin Hankali don in aka tab'a Nimra tamkar an tab'a RUHIN ta ....

"Nifa tun asubahi Naga Bata gidan koma tun tsakar dare ne ta bar gidan ban sani ba Amma na San Nan zata zo ta kawo Miki Kara....

Bai Rufe baki ba mummy Nina ta faska wa Anam Mari jikin ta har kyarma Yake tana Fadin

"Kuma tun asubahi ko tsakiyar Dare bakama iya sanin yaushe ta bar gidan ba Kuma kaja Baki ka kulle sai yanzu kusan uku na Rana kake min zancen wofi? NA Shiga uku ina yarinyar Nan ta nufa? Na Sani Bata nufar gidan su da matsalar ka Amma me ya sa Bata zo Nan ba?
Anam yayi shiru Yana Jin zafin yadda mummy take zak'ewa a lamarin yarinyar tamkar itace tata ba shi ba...

Ta jawo wayar ta tana Fadin
"Ai da kunya na nufi gidan su neman ta Bari na Kira wayar ta naji Allah kadai ya San abinda kayi Mata...

Tayi ta Kiran wayar Nimra Amma a kashe Dole ta mike tana Fadin

"Sai ka tashi kaje gidan su ka gani idan tana can in Kuma Bata can sai ka San da kalar bakin da zakayi musu Bayanin abinda kayi Mata har ta gudu...

Ya mike ya fice inda yake ta tunanin wannan aure na Nimra da yadda yake gwagwatuwa Akan sa.

Hikima ta fado mishi ta Kiran mamar Nimra wacce zai gaisar ya Kuma bugi cikin ta yaji ko Nimra tazo in ma ya Kira din zata soma bashi hakuri in har tazo din don in ya zama batazo ba to yace musu Ina ta tafi?


Ya Kira wayar maman nimra suka gaisa a mutunce tana tambayar shi Nimra da hakurin da Yake tayi da ita? Karshe ta Dora da mishi nasiha Akan yayi ta hakuri da ita Amma Kar yayi hakurin da zai cutar da shi . Wannan nasiha ita ta nuna mishi Nimra Bata zo gidan su ba don Haka yayiwa maman sallama ya kashe wayar sa ya wuce gida da tabbaccin Nimra Bata gidan su


Mummy Nina kuwa da Hankali ya tashi ta Shiga zaga inda duk ta San Nimra na da alaka da su Amma Babu ita Babu labarin ta sai ma wani albishir da aka mata na cewa anga motar Nina a filing jirgin saman malam Umar Musa Yar adua Alamar da take nuna jirgi ta bi ta bar garin....


Nina tayi shiru cike d tashin Hankali kafin ta soma Fadin
"Nimra tana Abuja ta tafi Kuma bana ko shakka tana wurin Haj Haseena ....


Da sauri Nina ta jawo wayar ta tana lalubar lambar layin Haj Haseena ta Kira Amma wayar a kashe abinda ya darsa Mata tarin zargi Mai yawa


Kwana biyu Babu labarin nimra wayar ta ma a kashe yayin da wayar haj Haseena ma a kashe inda mummy Nina ta yanke shawarar zuwa Abuja gidan Haj Haseena don zuciyar ta ta kasa yarda da Nimra ba can ta tafi ba

Tuni tayi shiri ta yanki tikiti ta wuce Abuja da fatan ta samo Nimra a gidan Haj Haseena....



Fitar Nimra da asubahin farko Kai tsaye ta wuce filin sauka da tashi na malam Umar Musa Yar adua ta yanki tikitin zuwa Abuja kafin karfe takwas na safiyar ta sauka a garin Abuja Kai tsaye mota tazo daga gidan gwamnati ta dayki Nimra zuwa gidan gwamnatin inda sashi sashi na gidajen Yan majalissu Yake da sanatoci

Haj Haseena wacce take cike da murnar ganin Nimrata tarbe ta tare da kayan tarba na garari ...


Bata iya taba komai ba Banda wanka da tayi da Ruwan zafi ta kashe wayar ta tace bacci ne a idon ta don Haka ta kwanta

Sai karfe biyu na Rana ta farka aka sake dire Mata kayan sauka na garari ta karya ta sake yin wanka ta shirya cikin sabbin kayan da aka marabce ta da su

Sun jima suna fira da Haseena wacce take ta tambayar ta Nina da Anam. Bata sanar da ita komai ba ta dai smsa da Duka suna lafiya

Ba karamin farin ciki Haseena tayi da zuwan Nimra ba don Haka ta shiga yi mata barin kudade da famfa ta akan ta yakice auren anam. A ranar gayyaci Nimra rakiya zuwa London don a neme ta a rasa Haka kuwa a Ranar akayi musu komai suka Kuma wuce London don Haseena ta mayar da abroad kamar zuwa kasuwa kasancewar ta matar wani k'usa a gwamnatin Nigeria hatta da maxanin su ma Yana Nan cikin mazaynin shuguban k'asa wato Villa a rukunin gidajen madafun ikon


Sai da su Nimra suka kwana biyu a London ne ita da Haseena kafin mummy Nina ta iso Abuja duk da nata mijin ma a Nan Yake da nashi gidan rukunin gidajen madafun ikon Amma Bata ko kawo shi a Ranta ba bare taje gidan Haseena kawai tayi wa tsinke


Ma aikatan gidan ne suka karbi Nina kasancewar sun San kawancen su da Haseena. Itama ta samu tarba ta karimci Amma sai suka sanar da ita Haseena Bata gari tana London yau kwanan ta biyu

Tayi shiru don tana tunanin akwai wani kulli don Haka sai Bata ce komai ba bare ta tambayi zuwan Nimra

A Ranar ta yanki tikitin zuwa London ba tare da ko gidan Mai gidan nata ta leka ba

Jirgin saman Azman ya sauke ta a London don Haka ta San inda zata samu Nimra da Haseena ....


Kamar daga sama Nimra da Haseena suka ga Nina wacce aka shiga kallon kallo tsakanin Nina da haseena kallon da zai nuna maka wani Abu a kasan zukata. Bata nuna musu komai ba Amma Kuma sun firgita da ganin ta Amma Nina Bata ja ba ta umurci Nimra da ta taro kayan ta su wuce Nigeria

Duk da Bata so ba haka ta biyo Bayan Nina suka sake hawo jirgi suka sauka Nigeria


Ba karamin bak'in ciki Nina taji ba da ta tabbatar da Nimra gun Haseena taje ba Amma Bata nuna musu komai ba abinda ta yarda ma shine Anam yayiwa Nimra laifi Mai GIRMA ne har ta zabi guje musu tunda Bata tab'a hakan ba...


Da safe Dr Anam ya iso gidan Nasu Bayan Kiran da Nina tayi mishi ya iso yayi Karo da Nimra wacce take fidda hawaye Wanda Allah ne kadai ya San dalilin hawayen nata a yanzu


Nina ta dubi Anam tana Fadin
"Gata na samo ta a London kace mini Babu abinda kayi Mata Ni Kuma na San Bata tab'a wuce Ni Akan matsalar ka ba don Haka gaka ga ta sai ka fada min abinda kayi Mata ...


Ya dubi Nina Yana Fadin
"To mummy Ni ai nace Miki ban mata komai ba in nayi Mata ai gata sai ta fada...


Nina ta Dubi Nimra wacce Ruwan hawaye yayiwa kaca kaca a fuska
Cikin wata murya Mai Sanyi da Rarrashi take Fadin

"Fada min abinda yayi Miki Nimra matukar ya take Miki hakki nice Mai karba Miki shi . Kuma me yasa Kika tsallake ni Kika bi Haseena har London? Ko kin San wannan shine laifi Mafi girma da Kika yi mini? Kar ki yarda ki jawo wa Haseena abinda zai Dame ta kin Sani bani da sauki Akan komai in nace komai to Ina nufin komai ki fidda ta Daga cikin abinda ka iya Zama ajalin ta wallahi...


Nimra ta harari Nina tamkar idanun ta zasu fado don ji take Nina ta cuce ta anzo kuna zo gabar da ba zata sake yarda ba.taja tsaki tana yiwa Nina wani shegen kallo tana cije lebe . Nina wacce ke maganar da tabbaccin hakan sai Kuma tayi Mata nuni da Anam da Yake Zaune Yana Jin su....


"Bana shakkar kowa Nimra ki Gane Hakan Zan iya fadar abinda yafi hakan don bana rufi kema Kar ki yarda na Gane akwai lauje cikin nadi a cikin Al Amarin Nan gara ki saba da bude min gaskiya da gaskiya kawai shine rufi asiri don Haka fada min abinda yayi dalilin da Kika bar gida Kika bar gari zuwa wurin wacce zata ga kasawa ta da yi min kallon k'askantacciya...........
























Me ake nuhi da maganar ga? Ni fa kaina a duhu take duk don wanna abun da akayi ne ya jawo wannan Jaye Jayen? Kai lamarin fa ya fara zuwa DA MAMAKI..........
















✍🏻 Alkalamin GIDAN IKO💖
[8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻







🧆 *_LINZAMI DA WUTA_*🧆






Pages
1️⃣9️⃣/2️⃣0️⃣






NA
GIDAN IKO💖









_Kirkirarren labari ne da Bai shafi Rayuwar kowa ba kuskure ne babba danganta kai ko wani dashi babu mafi cancantar suyi suka akan labarin irin taurarun cikin labarin Wanda kuka San Babu su a zahiri to kar wanda ba cikin jaruman labarin Yake ba yace don shi ko don wani akayi Hakan jaruman cikin labarin ne kadai suke da damar sukar marubuci akan don me zai fallasaww duniya sirrin su_





_ADDU AR fatan Aminci ga iyaye na guda biyu Uwa da Uba Wanda nakewa fatan Ubangiji ya tsaya musu a kowane Hali Rayuwa da mutuwa ya yafe musu ya tallafa musu ya amintar da su day Amincin sa_






_DA MAMAKI_

💖

............."Wallahi Zan iya yin komai in nace komai to Ina nufin komai ki Gane ki Kuma kiyaye wacece Haseena ma da har zata shigo cikin Al Amarin Nan? To Kar ki sake bana so bana so....


Nina ta Kare da bayyanannen bacin A fuskar ta

Nimra taja tsaki tana fadin

'Sai kuma a dake ni a hanani kuka kenan? Ke nifa kun ishe ni wallahi nace bana yin auren nan dole ne? Ok dama baki fada mishi akwai sharadi ba auren namu ? To zanyi fallasa wallahi kuma ki fada mishi babu wannan rayuwar a cikin auren nan kuma fa ba son sa nake ba kece kika hada ni da aikin auren sa to banayin auren a sauwake min. Haka kawai katon banza katon wofi zai rika danne ni ta karfi yana rapping dina ke haka uban sa yake miki? To in har zan zauna da shi sai ya yarda ba xai kuma Neman komai wuri na ba...ta share hawayen ta da tissue paper

'Idan kuma ba haka ba wallahi nima zan iya yin komai in nace komai to ina nufin komai wallahi. Kuma in dai Haka auren Yake cike da keta alfarma da Rashin yanci to wallahi na Gama shi dama ke Kika hada shi to kawai ki karba min takardar sakin don na Gane in nace Zan Zauna Aure da Anam to shine Ajali na wata Rana gawa ta kawai za a dauko .....


"Fada min abinda ya faru kawai Kai tsaye Don na fahimci matsalar Amma ai ke da kanki kin San ba Zan tab'a Bari ya cuce ki ba bare har yayi Ajalin ki kin San Zan iya yin komai don ganin Bai danne miki hakki ba.....

Wata shegiyar harara nimra ta watsawa Nina tana fadin
"Sau nawa Yana danne min hakkin me kikayi? Ko sai yanzu ne zakiyi wani abin ? To na rantse mkki da Allah Idan shegen danki ya kuma yi min fyade nice ajalin sa don wallahi wuka zan saka kakkaifar wuka ne na shsrbe wuyan sa.
Cewar Nimra wacce tayi maganar Babu ladabi bare sanin da wa take maganar....

"Ina aure Amma bani da cikakken Yanci sai ace ko fita Wai sai na tsaya na tambaya kamar Uba na? Banda Ban yarda da ikon da ya ke nuna min ba har bautar Ni da yaso yi da girke girken abinci kullum na Kare a kitchen Ina dafa mishi abinci da kayan shayi. Kuma duk hakan Bai Isa ba sai dare yayi ace wani Abu zanyi ko da kuwa Ni din bana Ra ayin hakan ace ta karfi za ayi min ? Duk wannan Bai Zama abin duba ba har in na ki yarda a tadiye Ni a harde Ni ace da tsiya sai nayi abunda bana muradi? To wallahi anzo karshe a shekaran jiya rapping nawa yayi kamar Ni ayi rapping dina don dai ana takamar an aure Ni kamar wacce aka Kai kudi kasuwa aka siyo? Ke anty Haka uban su Yake Miki in Baki yarda da shi ba yayi rapping din ki? To Ni ba zan iya ba in ma haka uban su yake miki wannan larurar ki ce amma ni wallahi na gaji da auren Nan ya sallame Ni ....

Anty Nina ta sauke ajiyar zuciya a rikice da jin kalaman nimra tana kallon Anam cike da fusata take Fadin

"Don uban ka haka ka zama Anam? Har lamarin ya Kai ka ketawa Yar mutane haddi kana Mata fyade kana hayuka ne ko kasha giya?....


"Haba mummy fyade dai sai kace wata Yar jaririya? Duk tsawon zaman mu ban Mata fyade ba sai yanzu ? Ina ce tun kafin na aure ta na Isa Zama namiji Amma ban Mata fyade ba sai da ta Zama matata ? Kuma mace da mijin ta ace an Mata fyade? Kuma mummy ai ta aje Miki tambaya sai ki Bata amsa da tace Haka kikewa Daddy? Sai ki fada Mata yiwa miji biyayya wajibun ne haka girmama Kiran sa da SHIMFIDAR sa....


Bai dire zancen sa ba Nina ta kifa mishi Mari tana huci tana Fadin

"Da Allah Rufe min Baki nonsense kana hauka ne ? Ko kuwa da ka auro ta an ce maka baiwa ce aka baka? ...

"Ba baiwa aka bani ba mummy Amma matar aure aka bani. Shin meye auren? Ko kuwa na auro ta na kawo gida na ne don ta tsara min abin da take so da Wanda Bata so har da haramta abinda shine ginshikin auren? Mummy in fa ana maganar gaskiya to maganar gaskiya ake. Saboda Allah don na zuba Mata ido na kalle ta Kika tursasani auren ta? Meye ma auren tukuna idan Bata biya bukatu na na biya nata ba? In kuwa ba wannan ne aure a gare ku ba mummy to kawai ki tabbatar Mata da yancin da kike fadar tana da shi Ni Kuma a yanzu Zan sauwake Mata wallahi don Bata da wani amfani matukar dai ban Isa nace Mata tayi ko ta Bari ba ko Kuma ta girmama bukatun juna to gara zaman ta gidan Uban ta Ni Kuma a shirye nake da na tabbatar Mata da ba wata tsiya take a wuri na ba dama ke Kika saka Ni a cikin lamarin ta to a Bawa kowa yancin sa...


"Kai Kar fa kace zaka kawo min wulakanci a Nan Dole ne kabi Ra ayin ta ka kuma kiyaye dukkan abinda bata bukata....

"Gaskiya ban yarda da wannan tsarin ba Dole ne ta zama cikakkiyar matar aure irin wacce na Sani tayi min girki ta Kuma gyara gida da shimfida in Kuma bukace ta ta Amsa Kira Na in tayi min Haka Nima Kuma Zan cike dukkan muradun ta Amma wallahi idan tace sai yadda take so ne zanyi to kawai ta wuce gidan su don Banga amfanin zaman ta ba gara na San Ni kadai nake Rayuwa ta....

Ya mike a fusace ya fice don ya gaji da hukuncin son zuciyar da mummyn take Yankee mishi ...


Ta dubi Nimra tana Fadin
"Kiyi hakuri ki koma Nimra don zaman ki a can yafi Miki ko Ina ke kin Sani Nima Kuma kin nema min zaman lafiya ....

"Wai anty na koma nayi mishi duk wannan bautar da ya zano? Wallahi tallahi ba zanyi mishi ko Mika Ruwan
End Ads