zubar? Ai ko Ni naji cikin Nan ya zube wallahi Zan Taya Anam neman hakkin sa Kuma ke da ita ne abun tuhuma Ni na Rasa dalilin wannan masifa ?
Yadda baffan Yake ta tijara ne yasa Nina tayi shiru don Bata San Hala baffan Yake da fada ba.
Baffan ne ya Kira wayar anam Yana fada mishi zuwan mahaifiyar sa da niyar daukar Nimra shi kuma yace Bai yarda ba .
"Baffa Kar ka Bari ta tafi da ita don in suka tafi zasu zubar da cikin ne a bar Nimra har ta haihu duk dawainiyar ta Zan dauke ta haihuwar kawai nake so tayi mu sake sabon Zama in ta yarda da sharudda na zamu koma in kuma bata yarda ba baffa kuyi min gafara Dole na hakura da Nimra...
Baffa ya dubi Nina Yana Fadin
"Ni na San yaron Nan hakuri Yake da halin yarinyar Nan to akwai magana a k'asa wacce ya lullube don Haka yace sai Nimra ta haihu zai fada don Haka kiyi hakuri haj a Bari ta haihu sai ayi magana ba Zan yarda na tauye mishi hakki ba shi kadai yasan yadda yake Rayuwar da yarinyar Nan to a aje magana kawai sai Nan da wata shida .
Bakin ciki kamar ya kashe Nina da Nimra Amma Dole Haka aka tafi Akan maganar baffa....
**** **** *****
Goggo Dubu tana Zaune a kofar dakin ta takaici goma da ashirin tana kallon yadda yara suke ta faman shige da ficen siyen abincin tara taliya ko gero da manja kun San yaro da son duk want Abu da aka sarrafa da shi da manja da yaji ku duba dai irin su taliya da manya teba da shasshaka alala da sauran su don Haka goggo jauhara take kasancewa cikin Aiki har sai an fashi makaranta
Ganin kwana kusan bakwai Dubu batayi Sana a ba taso ta tambaye ta in jarin ne Babu ta Ara Mata Amma Kuma tsoron abinda zai biyo Bayan hakan don ita da zuciyar ta guda zatayi Amma ta San Dubu zata iya juya maganar ta koma zance
Ganin dukkkan Kullin s Goggo Dubu tayi na son jazawa goggo jauhara asara Allah Bai Aiko Mata ba sai koma ba ta tashi kwance kanta ko na Ya'yan ta sai goggo jauhara ta soma kad'in taliya sai tayi ta figar gashi ga taliyar hausa da gashi kamar karfe da mayen karfe yanzu zaka ganshi ciki
Goggo jauhara tayi ta cirar gashi Amma Bata tab'a cewa Goggo Dubu komai ba sai ta Rika shanya kayan ta cikin dakin ta Wanda Yake ciki da falo Kuma ta gyara dakin da duk abinda take so na kawa kujeru da TV da kafet da labulaye don Goggo jauhara Kam biyan bukata yafi dogon buri a wurin ta har da Hakan yasa goggo Dubu Jin zafin ta Amma duk Bata kulawa harkar gaban ta kawai take tare da mayar da Hankalin ta Kan Sana ar ta
Sati uku cur Goggo Dubu Babu harka bare Sana a Ranar ne kuma Goggo jauhara ta kwashi adashen ta Dubu hansin cif ta siyi jarkar manja biyu Dubu talatin ta rage Dubu ashirin inda ta samu goggo Dubu tana fadin
"Dubu Naga kwana biyu bakiyi waina ba duk da nasan yau da gobe sai Allah idan Babu damuwa na kwashi adashe na damu manja nake son siya na Kuma siya to na Rage sauran kudi idan Zaki karba sai na baki ki koma Sana ar ki don gaskiya Zama ba zaiyi ba ...
Goggo Dubu da take tankaden garin tuwo ta dubi Goggo jauhara tana Fadin
"Ba sai kin fada min kin kwashi adashe Zan San kin dauki kudi ba jauhara. Na gani Allah ya Rike Amma Ni kike nufin ki arawa ko kudi ko ki bani nayi jari? Allah ya tsare tsautsayi da asara ai ban yi wannan tsiyar ba da har kishiya zata Ara min kudi ko ta tada min jari in na yarda na karbi kudin ki Ina ne ba Zaki Kai Ni ba kice kece ke min zanin daurawa ko ke ke ciyar damu Ni da Ya'ya na? Ai kema bakiyi tunani ba ....
"To Dubu Ni Kam na fita hakkin makotaka Amma ke Baki fita ba tinda gashi har kina tunanin Zan je gaba na fada Kuma Ni Allah yaga zuciya ta da niyar da nayi dama tuni nake son nayi wannan bajintar Amma zuciya tana Hana Ni don nasan Sai kin fassara Ni to Babu damuwa.....
"Ni kuwa wace bajinta zakiyi a Ido na? Ai dama da manufa kikayi in ma bugun ciki na kike son yi to zuba ido kisha mamaki ba barin waina nayi ba ja da baya ga Rago ba tsoro bane takon fada ne Ashe Ni duk kallon matsiyaciya ake min a gidan Nan ban sani ba har da aka ga ban Gane ba aka fito fili aka sanar Dani to a saurara za a ga fita ta wallahi duk da Ina sane da Dariyar da ake mini Babu komai lokaci ne ....
Goggo jauhara Bata tanka Mata ba ta wuce da kudin ta Daki taci gaba da harkokin ta Goggo Dubu Kuma tayi ta Arashi da yada habaici
Washe gari hafsa da salamatu suka nufi goggo jauhara Kai wuri suna Fadin
"Goggo a zuba Mana gero da yaji
Ta karba tana Fadin
"To hafsa yau ba a son taliya sai gero? Yarinyar tayi murmushi tana kada kanta. Ta zuba musu geron Mai yawa a wuraren su ta Kuma kwalala musu Mai hafsa Bata son yaji sai Bata zuba Mata ba amma salamatu ta zuba Mata Duka har yajin
Ta dubi salamatu tana Fadin
"Ina su fiddausi ne salamatu Basu zo sun karbi abin Kari ba?
Salamatu tace suna Daki..
"To ce musu suzo su karba Kar ta Kare kicewa Dubu ma ta bada wuri a zuba Mata geron ko taliyar...
Fadar hakan kawai Ina wuta Goggo Dubu ta jefa Goggo jauhara Wai shikenan ta Shiga uku ta lalace ana can ana ta Sheelar an Bawa Ya'yan ta abinci har itama ana cewa ta kawo kwano....
Tayi ta masifa tana sakin maganganu Amma goggo jauhara Bata sake bi ta kanta Don yanzu a Kam ta soma tambayar kanta Anya Kan Dubu Daya kuwa? Amma ta San har da jahilci a cikin abinda Yake wahalar da ita lafiyar ta Lau
Kwana biyu da yin hakan sai ga sa ade kanwar Goggo Dubu ta iso gidan daga jibiya .
Ta Shigo daidai lokacin da Yara ke ta haya hayar siyen gero da Talia ...
Goggo Dubu tana Zaune bakin kofar dakin ta cike da takaici da Jin Haushi taga zuwan sa aden.....
"Kai sa a yanzu kike tafe?
"Wallahi kuwa Yaya Dubu yau ba a wainar ne?
Bata tsaya zaman da Dubu take aje mata filo ba ta wuce wurin jauhara Tana Fadin
"Jauhara sannu da Yara ya kuke ya Yara?
Goggo jauhara wacce ta ga sa ade Kai ba zaka ce tarbiya daya dubu da sa ade suka Samu ba . Sa ade mace Mai kirki da sanin ya kamata Kuma babu komai a Ranta ....
"Kai sa ade yanzu kika zo? Ya kika baro mutanen jibia?
"Wallahi kowa lafiya Ina headmastern ku? Ta Dora da zolayar Goggo jauhara wacce tayi Dariya tana fadin Yana gaishe ki sa a....
Ta juyo ta dawo wurin Goggo Dubu wacce ta cika ta batse da wannan neman gindin zaman na kanwar ta duk lokacin da ta zo gidan sai ta gaishe da jauhara....
Goggo Dubu ta auna wa sa ade harara tana Fadin
"Kin gaishe da kanwar Uwar Taki ko? Ai nasan Yar taliyar da take Baki itace matsalar ki....
Bata ko Rufe baki ba Umar Dan Goggo jauhara ya direwa sa ade taliyar fall Samira ta ce
"An gode kaji umari kace na gode Allah ya Karo kasuwa Mai albarka...
Goggo Dubu taja tsaki tana fadin
"Halin ki dai baiyi ba har yanzu kina Nan da shegen kwadayin tsiya..
"Ai kuwa ba a ce min ins da kwadayi Yaya Dubu don Allah ki sakawa zuciyar ki Aminci Akan matar Nan ko kema kya ga Aminci. Ni wallahi banga aibun matar Nan ba duk kin ishi kanki da zancen ta alhalin ita Baki gaban ta ma bare ki Zane Mata damuwa....
"Kinzo ki zage Ni ko kuwa kinzo ne ki fada min jauhara Yar aljanna ce?
Sa ade ta zuge Jakarta ta fito da kudi tana Fadin
"Kudin hayar gonar mu ne aka kawo shine na kawo Miki naki Ni ba wani takulo aibun wani ya kawo Ni ba....
Da sauri Goggo Dubu ta warce kudin tana lissafa su Dubu ashirin cif ta rangada guda Mai karfi tana Fadin
"Allah na gode maka sannu da kokari sa aden sa a sa adatu sa ar mata gidan da ba sa a ba sa a Wanda bai da sa adaty yaje ya nemo sa a yanzu Naga zuwan ki sa Ade ta abinda kikayi ma na yafe Miki Allah ya yafe miki maza ki hauda taliyar ki Bari na sa salamatu ta samo Miki madarar suya milik ki taushe...
Ta kwalawa salamatu Kira tazo ta siyowa sa aden Madarar waken suya duk murna ta cika goggo Dubu Babu abinda zuciyar ta ke Raya Mata sai malm Mai gafukka...
Sun jima tare da sa ade tana fada Mata dama jarin waina ya mutu Amma yanzu Samun kudin Nan za a Tayar da shi
Sa ade ta tafi Goggo Dubu Kuma ta figi mayafi ta nufi gidan tabawa tana fadin
"Ke tabawa albushirin ki? tabawa ta fito tana daura Dan kwalin ta tana Fadin
"Goro fari kwalele bani Nasha Kar na margaya...
"Kudi ne kin gan su yanzu sa ade taxo daga jibia ta kawo min su kudin hayar gonar mu ta gado ne Dubu ashirin kin gan su . Kin San me? Wallahi gobe goben Nan zamu fasa wurin malam Mai gafukka Dubu biyar kawai zan cire na Tayar da jarin waina ta sauran kuwa zan zube mishi su Duka ayi min Aiki akan matar Nan da Sana ar ta ...
Tabawa ma ta rangada guda tana Fadin
"Yanzy Zaki dawo dubun ki ta ainafi Amma fa ki cire tsoro da shakka don duk abinda Kika cewa malam Mai gafukka kina so shi zai Miki Kuma yadda Kika San yankan Reza don yafi wuka kaifi..
"Ai ke dai Allah ya kaimu goben tabawa yadda naji wutar Nan ai Ni kadai na San gubalar da na Sha ke dai kamar karfe nawa Zan zo muje?...
"Ai in za aje wurin malam Mai gafukka sammako akeyi don wasu fa a can suke assalatu Kuma Yana da adadin mutanen da Yake gani idan akayi Rana ba zaka samu ganin shi ba. kawai dai da an sallame sallar asubahi ki fito muje mu Dasa layi Kuma duk sammakon sai mun iske Wanda suka Riga mu....
"Ai ko kwana ake tabawa na shirya ke dai Allah ya kaimu da Rai da lafiya........
To Dubu ta shirya kenan Bari mu saurare su muga irin Shirin da tayi. Shin na kashe jauhara ne ko kuwa na kashe Mata kasuwa? Amma dai Ni na San kasuwa ta na hannun Allah har na mutu Ina tare da wanna tauhidin Amma dai Bari mu saurari Dubu da aminiyar ta tabawa.........
_Hakkin mallakar ma na GIDAN IKO ne Kuma abin kiyayewa ne kowane Abu Yana da mamallakin sa Babu Kuma Mai son a daukar mishi kayan sa ba tare da izinin sa ba mu kiyaye hakkin juna sai mu Zauna lafiya_
_ADDU AR har kullum ga kimar iyaye nace guda biyu Uwa da Uba Wanda nakewa fatan Aminci mara yankewa da Rahama da gafara garesu tare da dukkan mumunai bayin Allah_
_ZANEN KADDARA_
💖
..................Dada ta dage da ADDU A akan mahaifi na kullum tana tsayuwar Dare tare da yi mishi fatan alheri da kiyayewar Ubangiji. Haka kullum cikin sadake sadake take .
Allah Arrahamanu sai gashi ba a Rufa shekara Daya da zuwan Baba na ba sai gashi ya sake dawowa. A wannan karon ma tare da Ameer har da Ammar kanin Ameer din Amma Kuma babu mahaifiya ta .
Murna sosai Dada tayi har da hawayen FARIN CIKI. Yayin da Ni Kuma nake Rungume da Ameer da Ammar Wanda kamannin su da Ni Basu buya ba. Kyawawan Yara farare tas masu tsabta da gayu Alamar suna cikin afuwa da hutu Mai yawa
Yana durkushe a gaban Dada tana kallon Ammar yaro Mai kyau da kwarjini tana Fadin
"Ikon Ubangijin musulunci Hamza wannan ma naka ne?
Ya Amsa da
"Eh Dada Ammar kenan shike bin Ameer ...
"Masha Allah Hamza kaddarar ka ce haka Kullum Ina nema maka Aminci da Rahamar Ubangiji Allah ya sa masu yiwa musulunci hiduma ne Kai Kuma ya Shiga cikin Al amarin ka ko Ina Raye ko na mutu in Sha Allah Kuna cikin Aminci
Yana Duke gaban ta Yana fada Mata cewa
"Dada dama Nazo ne don na sanar dake na biya Miki hajji bana zamuje har Dani da Halimatu ...
Dada ta Rike Hannun shi tana Fadin
"Allahu Akbar Hamza yau wannan buri ya cika ? Allah ya cika maka naka burin na duniya da lahira Allah ya yafe maka ...
Ina Zaune tare da su Ameer da Ammar wanda na jerawa kayan makulashe suna ta min surutu duk da na kula na Kuma Gane turanci ne abinda suka fi ji duk da akwai hausa a bakin su Amma Basu iyata irin yadda suka iya turanci ba
Babu abinda ke Raina da zuciya ta irin son na tambayi Baba na ina mahaifiya ta? Amma Dole na barshi suna ganawa da tashi mahaifiyar
Naji Dadi kwarai da Jin zamuje Saudi Arabia Ni da baba na da Dada. Dada buri ya cika kullum maganar ta kenan Allah ka nufe mu da zuwa ziyarar Dan Aminatu da Abdullahi Uban Daki na Uban dakin kowa ko an Kiya bare an yarda ...
Mutanen gida sukayi ta shigowa gaida baba na duk Kuma Wanda ya shigo sai Dada ta fada mishi Hamza ya biya Mata kujerar hajji ita da Halimatu Sai a Taya ta murna da fatan alheri
Yan uwan Baba na su Baba Headmaster da baba Bello sai yakumbo mariya duk sunzo kuma duk Wanda yazo sai ya kawowa Baba na bukatar abinda Yake so yayi mishi Kuma a take baba na zai Basu duk abinda suka bukata
Sai dare na Samu Zama da baba na ina gaishe shi Ina Fadin
"Baba ka cikawa Dada burin ta kullum Fadi take Allah kar kasa Zan mutu banje na ziyarci dakin Allah da kabarin manzo sallalahu alaihi wassalam ba na gode maka da wannan burin da ka cikawa Dada wanda Naso ace nice na cika mata shi...
Yayi murmushi Yana Fadin
"Halimatu bani da kamar dada a duniya. Dada ce dukkan wata alfarma ta a duniya Kuma Banda Dada da yanzu ban San a wane Hali ko wace duniya nake ciki ba. Halimatu Uwa mahaifiya da kike gani ba karamar alfarma bace a duniya. Ko da mutum Bai iya kukan mutuwa ba duk Ranar da Uwar sa ta mutu sai ya koye shi sai ya iya shi. Ke duniya ma har habaici takewa wanda ya Rasa Uwa mahaifiya cewa yanzu nee komai ma zai same ka tunda ka Rasa Mai Rufa maka asiri Nima yanzy Zan nuna maka ba ka da sauran gata....
Babu abinda yazo zuciya ta sai taww mahaifiyar wacce Rashin kusantar ta kadai ya kawo har ana min gorin bak'in fentin da mugun tabo Ashe kuwa maganar baba na gaskiya ce !
"Haka ne Baba Amma ya akayi kuka zo da su Ameer da Ammar baba Amma Banda mahaifiya ta? ....
Baba na yayi maza ya dawo nutsuwar sa don shi da kanshi ya gane maganar da yayi akan mahaifiya Nima naji Ina son na kusanci taww mahaifiyar har ta Kai yayi dakacen fadar abinda ya fada....
"Mahaifiyar ki Halimatu kullum cikin maganar ki take sai dai tace ba zata zo cikk Yan Uwa na da dangi na ba saboda tana tsoron su kashe ta....
Nayi maza na toshe baki na ina zaro idanu ina Fadin
"Su kashe ta Daddy? To me tayi musu da zasu kashe ta?....
"Mu bar wannan maganar Halimatu ba Zaki ji komai Baki na ba Amma nayi Miki alkawarin in muka dawo daga Saudi Arabia Zan kaiki kamarun ki ga mahaifiyar ki itama ta ganki abinda kawai Zan fada Miki shine mahaifiyar ki tana kaunar ki yanzu ma da Zan taho ta bada Sak'o na kawo Miki...
Kayan da mahaifiya ta ta bada Sak'o a kawo min sun bani mamaki Domin kuwa wannan karon ma Kaya ne masu daraja Kuma abin Mamakin ba irin Wanda ta Aiko min wancan karon ba wato English Wear duk da na San Daddy ne zaice Mata ta siya min Kaya irin na muslim religion ...
Kaya sosai har da kananun sarkoki na gold har uku da kayan cosmetic masu daraja Wanda suke gyara fata da fito da martabar mace
Kaunar mahaifiya ta ta Karu a Raina da zuciya ta duk yadda take Ina son Kaya na nayi Mata ADDU A nayi kewa nayi begen irin na Uwa da danta
Yan kanne na suka nane min musamman Ammar dama shi Ameer shine Mai cewa Daddy a kawo shi wurin sweet anty da mother Daddy shi dama muna jone to shima Ammar din ya Dafe min abinda nake cewa a Raina jini ba karya ba..
Duk Wanda ya kalli yaran Nan sai yace Kai Kuna Kama da yaran Nan Halimatu yan Uwan ki ne halan?? Nace kanne nane
Hakim ya iso don gaishe da mahaifi na saboda na sanar da shi zuwan Daddy na ya Kuma zo ya gaishe shi gaisuwa irin ta mutunci ya Kuma sanar da shi shine Mai sona ya zo don ya nemi izini kamar yadda musulunci ya shardanta Amma sai Dada ya gani....
"In ka ga Dada Hakim kamar Ni ka gani in Dada ta baka Halimatu to ta bayu komai m zai tafi ne da cewar dada Nagode sosai da mutuntawa Allah ya tabbatar da alheri a tsakanin ku...
Hakim yayi ta amsawa da ameen ameen Daddy Nagode
Sun jima suna magana kafin yayi mishi sallama Bayan ya aje mishi turare designer