Kai sai Uban kishin kawai Kika iya Amma Baki da tuggu da makirci ....
"Ai wallahi yanzu Dole nake koyar su tabawa tunda na Gane kisan mummuke ake Shirin yi min macijin kaikayi sari ka noke kenan....
Goggo Dubu ta leka waje inda goggo jauhara take ta siyar da kayan sana ar ta ta waigo ta yafuci tabawa tana Fadin
"Duba ki gani hatta da manja yanzu jarka take siya Bata ma jiran Mai gidan in dai girki ne sai dai tayi nata dama Ni nace sai an Raba girkin an Kuma Raba kowa nashi Yake to Ni gashi yanzu ba harka ....
"Ai sai kiyi kokari ku dawo Daya itama ta Zama ba harkar Amma in ba Haka ba ai ita zata Rika digawa Ya'yan ki abinci a faranti Kuma ta Daki kirjin cewa itace take ciyar da gidan tunda har Mai gida Yana aron kudi hannun ta ai Kuma da gayya ma zata yanko magana..
Tabawa ta mike tana Fadin
"Ni Kam na wuce dama yau Haka muka tashi gidan Babu komai nace Bari na yo Nan ko waina na samarwa su Fati Ashe Rabon nayi mugun ji Amma dai kiyi kokari Dubu mu samu mu fiddo jaki daga Duma...
Suka fito tabawa tana Kara kallon Goggo jauhara da yaran ta Yan Tara. Bata Kuma duban inda take ba tayiwa goggo Dubu sallama
*** *** *** ****
Na dubi yaron da Yake sanar Dani Wai ana Kiran Halimatu a waje...
"Waye ?.
Na tambayi yaron yace
"Wani ne a cikin mota...
"Jeka kace Bata Nan
Na fada mishi don ban San Mai motar da Yake magana ba...
Dada ta tsayar da yaron tana Fadin
"Kai ce tana zuwa
Na dubi Dada wacce take duba na tana fadin
"Haba Hali Dubu Rai goma Kika Sani ko shine surukin nawa da nake ta fatan ya iso tunda kince Baki son yaron Nan balange Mai shago? Tashi kije ita mace da kike gani Allah ne kadai ya San mijin ta Kuma su maza ba a musu Haka ka Rabu da kowa lafia shi yafi...
Na mike Ina Jin Hakim Bai min adalci ba da ya faku tsawon wannan lokacin don Babu Ranar da zata fito ta komawa Ubangiji ban tuna bawan Allah Nan ba....
Ina fitowa Naga abunda ya saka Ni murmushin da ban shirya ba
Yana tsaye cikin Riga sheet da jins Wanda suka Kara fito da haibar sa...
Yana jingine jikin motar shi ya tako zuwa inda nake tsaye...
"Shikenan Babu cigiya Halimatu?
Na dube shi kamshin turaren shi Yana karade kofofin hanci na in Fadin
"Nayi cigiyar ka fa har a BBC Amma shiru bace ko baka Nigeria?
Yayi murmushi Yana kallon Ido na kafin yace
"To kalle Ni Mana sai muyi magana?
Na juya cikin gida na dayko FARAREN kujeru na kawo mishi a soron na Aje
Ya Zauna Yana Fadin
"Ina can ina ta fatan na Samu na kubuto Nazo Naga kyakkyawar fuskar ki Halimatu ai wannan Dan sanda ba Zan yafe mishi ba wallahi ...
Da sauri na dube shi Ina Fadin
"Me yayi maka?
Yaja tsaki kamar gaske ya soma Fadin
"Kama Ni yayi Wai don bani da lamba a motata Kuma bawan Allah Nan yaki Jin Rarrashi....
"Uhum ai Kai dai kaga Yan sanda ba kirki ne da su ba wallahi suna sane da gaskiya suke take ta in dai ba kudi gareka ba wurin Dan sanda duk gaskiyar ka Sai ya cuce ka shiyasa Ni ba wani son su nake ba Allah dai ya sa ba kulle ka sukayi ba?
Yayi murmushi Yana Fadin
"Kulle Ni sukayi tsawon wannan lokacin da Baki ganni ba sai jiya na fito....
"Allah ya kyauta gaba ya tsare wallahi ban sani ba ai da na jajanta maka...
"Ba komai na gode Yaya maganar mu Halimatu?
Nayi shiru kunya Hana Ni nace mishi tun Ranar da ya furta min kalmar so naji a duniya Nima wata ABA ce Mai daraja Kuma gare shi ....
"Kar kice min bana daga cikin maxan da suke burge ki Halimatu Amma zanso ki sada Ni da Baba na fara gabatar mishi da kaina na fara neman izinin sa....
"Sai dai na fara kaika ga Dada ta don Baba na baya garin Nan...
Muka shiga Dada ta Karbe shi da karamci ya zube Yana gaishe ta ta Amsa tana ta saka mishi albarka kafin ya gabatar Mata da kanshi da son neman auren Halimatu...
Dada ta soma sanar dashi Halimatu jikar ta ce wacce ta haifi Uban ta Kuma ta yaba da tunanin shi da har ya iya fara neman auren sa irin yadda musulunci ya koyar da musulmi don Haka ta bashi Halimatu Babu wani ja tunda har Yana da Hankalin tsare Shari a to shine mijin Halimatu Allah ya Taya mishi
Godiya sosai yayiwa Dada kafin ya aje Mata kudi masu afki ya mike zuwa soro
"Allah Nagode maka Halima ni din ina da sa a daga kallo Daya Dada ta bani ke sai dai ban San yadda kike kallon kyautar Dada ba...
"Dada ta Isa tayi gaban Haka Dani don bani da Wanda yafi ta itace komai nawa ban tab'a sanin Dada kakata ce ba sai daga Bayan Nan don da ita na dube Ido na zaci ma itace mahaifiya ta don Haka Babu Mai Tayar da kyautar Dada....
"Alhamdulillahi Halimatu Amma naso naji irin matsayin da Kika bani don na San na Kai a so ...
"Kar ka damu Zan baka matsayi Mai GIRMA don Ni a gareni duk Wanda ya ce Yana Sona Ina bashi matsayi na musamman bare Kuma Kai...
Mun Jima muna fira Yana fada min yadda nake a zuciyar sa har zuwa Kiran sallaar magaruba inda yayi nufin tafiya ya Kuma aje min kwalin waya Yana Fadin
"Ban Sani ba ko Ra ayin ki ne ba kya son Rike waya Halimatu Amma dai ayi mini alfarma ko sau daya ne nake Kiran ki Ina Jin muryar ki Ina fatan ba dokar manya Zan karya ba?
Na kada kaina Ina Fadin
"Kawai dai nice bana son rikewa Amma in kana son hakan Zan yi ....
"Yauwa to Nagode akwai layi a ciki har da kati nayi karambanin sakawa Zan Kuma Kira anjima ...
Mukayi sallama ya tafi na Shiga gida da waya Ina nunawa Dada wacce take cewa
"To kin gani arzikin Yana Kira da tsiya zata Hana ki zuwa gashi Nan kin samo galleliyar wayar ai Ni wallahi yaron ya burge Ni tunda Yana da sanin auren musulunci ta sama ake fara neman sa ba taka Haye irin yadda yaran yanzu suke ba sai dai kawai kaga mutum a kofar gidan ka tsaye da yarka don Allah meye ba zai faru ba tunda ya san gidan su Babu Wanda ya San da shi?
Sai Naga maganar Dada gaskiya ce kuma Ni Kam yadda naji zuciya ta akan Hakim gaskiya in har Haka so Yake sai nace Babu abinda ya Kai so Dadi a duniya...
Da dare kuwa na kunna waya na saka chaji sai ga Kiran shi ya shigo n dauka.
Tun daga wannan Rana Hakim ya dasa min wani irin so Mai wahalar mantawa har nake Jin Babu Dadi idan Bai Kira ba.
Goggo jauhara tun asubahi take tashi ta soma Dora sanwar kayan Sana ar ta musamman gero da Yake yafi taliya wuyar dahuwa. Kuma a cikin gidajen Makota ma Akan shigo siya don Haka manyan tukwanen ta masu lamba 20 da Mai 25 sune take dorawa kafin garin ya waye ta Gama sai dai dakan yaji da Kona manja da albasa
Kamar kullm yauma bayan an sallame sallar asubahi ta Dora sanwar ta ta tada wuta ta Shiga bandaki tayi wanka yayin da Goggo Dubu take ta faman fakaitar idanu harta samu jauhara ta Kandami Ruwa ta Shiga bandaki sai kawai goggo Dubu ta soma waige da neman abinda zata gani a dakin taje ta zuba a tukunyar gero ko taliya. Idon ta ya fada Akan omon kilin irin na aune din Nan sai kawai Goggo Dubu ta figi ledar ta sadada ta ambamawa goggo Dubu shi a cikin tukunyar taliya ta koma Daki abinta...
Goggo jauhara ta fito ta shirya har ta soma dakan yaji taga tukunyar taliya Tana ta kumfa da sauri ta matsa ta bude inda kumfa sai fita Yake abinda ya Bata mamaki Bata kawo komai ba in ma da akwai abinda ta kawowa Ranta to Bai wuce fulawar ce bata da kyau ba don tun a wurin kadi taga Bata son Ruwa...
Da sauri ta sauke tukunyar daga wuta ta dauko matsami ta soma fidda taliyar tana zuba ta cikin Ruwa duk Bata kula da abinda Yake k'asa ya cure ba.
Ta wanke taliya tas ba tare da ta San asara aka so jaza Mata ba Amma da Yake Al Amarin Yana Nan cikin kaulasan Allah Bai zana Mata wannan asarar ba sai ga taliya ta shige tas Babu Mai cewa akwai wani abu a ciki sai dai Dan gishir gishiri shima sai ya hade da yaji
Goggo Dubu da ta fito bakin kofar dakin ta tana jiran taga ana Kai taliya Rariya sai taga ana Shirin mayar da tukunya Kan murhu hatta da geron ya Kare sai an sake dafawa
Wurin wankin tukunyar ne jauhara taga abu ya taru gefe daya ya dunkule Bata kawo komai ba ta wanke ta zubar ta mayar da tukunya...
Wannan ta wuce goggo Dubu Bata samu yadda take so ba inda ta Kuma kulla makircin ambama kalanzir
Shima kamar waccan lokacin da asubahi ta fakaici Ido ta auna Uba kalanzir a cikin Ruwan sanwar
Shi ma da Yake Allah Bai dorawa jauhara wanna asarar ba kafin ta zuba geron ta taga kyallin maiko a saman Ruwan inda ta soma yad'ewa Amma tuni zarnin kalanzir yaje hancin ta ta kuwa sunsuna sai ga Abu zau Dole ta zubar da wannan Ruwan ta Kuma sake tukunyar sanwar
Sai da Goggo Dubu tayi Karo uku Duka Babu nasara Amma Kuma zuciyar ta Bata rusuna ba
A cikin Karo na hudu ne Kuma Allah ya tona asirin ta dama Rana Dubu ta barawo Rana guda ta Mai Kaya inda Baba Headmaster ne ya kamata tana madacin da Dole ya haramtawa Al Umma abincin. ....
"MENENE Kika zuba Mata Haka Dubu?
Yayi tambayar a lokacin da Goggo Dubu tayi zaton a cikin duhu Babu Mai ganin ta tayi muguntar ta ..
Goggo jauhara ta fito tana kallon su inda Baba Headmaster ya tsare Dubu Yana tambayar ta...
"Ban Gane me nake zubawa ba? Kai ma SHARRIN zaka ja min?...
Ya juyo Yana duban jauhara Yana Fadin
"Duba kigani meye ta zuba a cikin tukunyar can ta farko?
Da sauri Goggo jauhara ta bude tukunyar sai ga Ruwa ya rune da kalar Abu....
"Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un menene wannan din?
Cewar Goggo jauhara Allah ya kiyaye shima Bata Kai ga zuba hatsin ba....
"Wai Dubu me kike daukar Rayuwa ne? Yanzu ke hakan shine yayi Miki daidai ki cutar da abokiyar zaman ki...
"A a Kar fa kace zakayi min sharri sa adu. Wace burgewa kake sonyi wurin matar ka da kake neman b'ata Ni a idon ta don kayi bajinta? Kai Kuma Haka naka salon Yake ? Yau ga wani ikon Allah Mai gida da haddasa husuma a gidan sa. ai ba sai kayi Haka ne Zan gane kana neman Shiga ba ....
Goggo jauhara ta dubi Baba Headmaster tana Fadin
"Don Allah kaje ka shirya kana Shirin makara fa...
Ya juya Bai cewa Dubu komai ba abinda Kuma yayi matukar Kona Ran goggo Dubu akan yadda jauhara tayiwa sa adu magana cike da kinaya da kissa ya Kuma bi Babu musu to wannan yafi komai bak'in ciki a wurin ta ....
Goggo jauhara ta zubar da Ruwan sanwar ta sake wasu ta mayar a wuta
Tun daga Ranar goggo jauhara in zata Dora girkin ta zata Zauna a wurin har sai ta sauke . Sai ya Zama komai nata ma ta daina barin sa Haka nan tana ta kaffa kaffa da koman ta yayin da kasuwar ta Kuma take ta hab'aka tana ci gaba tana ta Samun Yan kudaden ta . Kuma Bata fasa zubawa Ya'yan Goggo Dubu kayan Sana ar ta ba. Sai ma ta tambaye su abinda suke so taliya ko gero Kuma in zata zuba batayin na kwauro yadda zai ishe ka don Bata yarda kyauta na Hana samu ba. Kuma ita a gareta biyan bukata yafi dogon buri . Shiyasa Allan ya Daga Al Amarin ta hatta da sutura siyen abinda take so take ita da Ya'yan ta shiyasa tafita daban a gidan mu Kai ba zaka ce goggo jauhara da Ya'yan ta ahalin gidan mu bane don kudin goggo jauhara Kam sun biya Mata bukata yayin da Goggo Dubu Kuma kullum take cikin bak'in ciki da huzuni tamkar wacce aka aikowa mutuwar iyaye. Abu kad'an zai hada ta da Ya'yan ta ta Kama su tayi ta jibga tana antaya musu Ashar ko da kuwa laifin Bai Kai ya kawo ba ..
Fiddausi ta shigo gidan ta iske Goggo jauhara tana wanke kayan Sana ar ta inda ta Duka tana Fadin
"Goggo kawo na wanke Miki ..
Ta karba tana wanke Mata Goggon na Fadin
"Na kuwa gode Miki fiddausi Bari na koma Kan fulawa ..
Fiddausi tana matukar girmama Goggo jauhara don Bata nuna musu mugunta ita a wautar ta ma Goggo Dubu da take kullatar Goggo jauhara Bata godewa Allah ne shiyasa fiddausi Bata daga cikin Wanda ake adawa da Goggo jauhara akasin Salamatu da Asiya Wanda Goggo Dubu ta Dora su a kiyayyar Goggo jauhara Kuma basa Jin kunyar yi Mata Rashin kunya Amma Goggon Bata ko biye wa bare ta fadawa Uban su tausayi ma suke Bata ..
Wannan wanke wanke da fiddausi ta karbawa Goggo jauhara ya tsayawa goggo Dubu har da ta shigo dakin ta Rufe ta da masifa tana Fadin
"Ni Kam da a asibiti na Haife ki fiddausi da na Sha aradu sauya min ke akayi .waccan matar ko kanwar Uwar ki ce ita sai Haka ko kuwa Yar taliyar da take lika Miki a faranti ne kikewa kulafuci ? Kai tur da Halin Rashin zuciya....
"Goggo don Allah ki Gane Goggo jauhara ba makiyar ki bace wallahi in da matar Nan tana kin ki wallahi da Bata kalli Ya'yan ki ba bare ta basu abun ta. Ki Dubi yadda kike Mata Amma ta kawar da kanta Bata tab'a biye Miki harkar gaban ta kawai take don Allah ki fidda ta a ranki ko zaki huta...
Fadar hakan ke da wuya Goggo Dubu ta Rufe fiddausi da Duka tana fadin
"Ni Kam in ma nema na akayi an same Ni Allah ya tsayar kanki Kar sauran dangi su zama kamar ke ...........
To Allah ya kyauta dai Amma Dubu kina Ruwa kusa da kada wallahi shiyasa Mana Kika kasa ci Gaba. Abinda kike son gani ne ga wanin ki ya fara sauka a Kan ki Allah ya ganar da ke.....
_Kirkirarren labari ne da Bai shafi Rayuwar kowa ba kuskure ne babba danganta kai ko wani dashi babu mafi cancantar suyi suka akan labarin irin taurarun cikin labarin Wanda kuka San Babu su a zahiri to kar wanda ba cikin jaruman labarin Yake ba yace don shi ko don wani akayi Hakan jaruman cikin labarin ne kadai suke da damar sukar marubuci akan don me zai fallasaww duniya sirrin su_
_Fatan alheri ne ga dukkan ma Aura ta sabon aure dama tsofaffin auren Allah ta ala ya kawar da fitina da gidajen auren musulmi da auren su . Amare da angwaye Kuma fatan Aminci a cikin auren ku har muddun Rayuwa_
_Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da Aminci mara yankewa zuwa ga shugaban mu fiyayyen halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam da ahalin gidan sa madaukaka da masu bin su da kyautatawa har izuwa Ranar Alkiyama_
_MUGUN KULLI_
💖
...............Rana ta kwalle tarwai har hannnun agogo na Shirin nuna Sha biyu da Rabi na Rana Amma Dr Anam Yana kwance Yana bacci sakamakon wani nannauyan bacci da ya dauke shi Mai kama da na ya Kora kayan karawa sama hazo....
Yayi juyi Akan faffadan gadon irin na hotel Wanda ya Ni imtu da Sanyin AC da Kuma lafiyayyan gado da shimfida irin ta more kudin ka...
Ya Kuma juyawa da cike da wani irin Dadi da Nishadi musamman Akan mafarkin da Yake yi da kyakkyawar yarinyar da tayi nasarar shiga zuciyar sa ta farat Daya wato heeling gabros...
Ya bude idon shi da kyar saboda har yanzu baccin Bai sake shi ba Don ji yake tamkar an watsa mishi k'asa a cikin idon....
Yayi Mika tare da yaye blanket din da Yake jikin shi Yana wara idanu da son ya hango Heeling agefen shi Amma sai ya ga wayam
Ya mike Zaune yana Kara caje dakin da idanu da son ya hango Heeling Amma Babu ko burbushin sawayen ta...
Tunanin sa ya bashi ko tana toilet ne Amma da ya Dubi agogon dakin wacce take nuna mishi lokaci ya Kuma hango Ranar da ta kwalle sai ya soma tunanin Heeling Bata cikin dakin Amma duk da Haka Bai yankw tsammanin Tana toilet ba...
Ya mike daga Kan gadon ya sauko Yana tunanin baccin da yayi Mai nauyi Haka yayin da jikin shi kuma Yake Jin shi ba daidai ba abinda ya kasa gasgatawa duk da zuciyar sa na Ray's mishi akwai dalilin baccin shi.....
Layin wayar shi na network din glo da idon shi ya hango mishi a saman center table yashe shi ya haska mishi cewa Heeling Tana da manufa tunda shi ya San layin Nashi a cikin waya Yake...
Sai ya soma waige waige da son ya lalubo wayar shi Amma waya tayi batan dabo....
Ya tura kofar toilet din Yana wara idanu Amma Babu kowa bare Heeling da yake zaton tana ciki...
Ya dawo baya Yana nufar inda ya ajiye key din motar sa da kudaden sa dake cikin brife case Nan ma ya Tara's da Jakar kudin tayi batan dabo...
Bai ja da nisa ba ya Gane Heeling tayi mishi Halin Yan bariki.
Ya Shiga wanka a gaggauce ya fito duk har yanzu baccin Bai sake shi ba Amma Bai koma ba sai ya sauya Kaya Yana mamakin yarinyar. Baiji haushin satar da tayi mishi ba irin yadda ta gujewa ganin shi da