x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - LINZAMI DA WUTA free pages

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 43517 words

Category: Tale Stories

Views 226

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
hakuri kin San me na tuna?
Nace
"A a
Tace
"Balange Mai shago Anya in ya ganki zai Gane ki kuwa?
Naja tsaki Ina Fadin

"Mun kusa mu Bata Ziyada Ni Ina wani tunawa da wani balange ne? Don Allah tashi muje in kaiwa mama Allo na ta gani ...

Dada ta kamo Hannu na tana Fadin
"Baki fesa turare ba Halima ai kin ragewa kwalliyar armashi...

Ta fito min da turaren ta tana fesa min kafin tace
"Ki fara kaiwa mutanen gida Allon Zayyanar ki Kuma Karanta musu ko sa yi zuciya suke matsawa Ya'yan su zuwa islamiya Kuma duk Wanda ya Baki sadaka ki Amsa Nima kafin ki dawo Zan samu abinda Zaki kaiwa sayyadin sadaka yanzu Kuma Zan Kama kaza guda in Miki ragadada....

"Kai dada kina shagwaba Halima da yawa ai kuwa Zan dawo aci kazar Nan Dani. Cewar Ziyada.
Na Rungume Dada Ina Fadin
"Allah ka bar mini Dada ta ka Kara Mata lafiya da nisan kwana....

Muka fito kofar dada na nufi madafi inda goggo Dubu take tana tuyar waina goggo jauhara Kuma tana can Yara Yan makaranta sun yanyame ta kasancewar Yan Tara masu siyen abincin tara. Idanun goggo Dubu Yana Kan goggo jauhara da Yara suka Rufe kasancewar ita goggo jauhara taliya da manja take yi ita Kuma goggo Dubu waina da miya da Kuma Yar tsala da yaji duk da itama akwai yaran a wurin ta Amma na goggo jauhara sunfi yawa don Haka sai idon ta Yake Kan kishiyar ta goggo jauhara don ba wani zaman Dadi akeyi ba duk goggo Dubu ce Bata da son zaman lafiya ga tsegumi da neman fitina Amma sai tayi sa a goggo jauhara wayayyiyar mace ce Mai kawai ci da alkunya da Kuma nuna harkar ilimi a komai nata....

"Sannu da Aiki goggo Dubu.
Na fada Ina rusunawa ta waigo tana min wani shege shegen kallo musamman da ta ganni cikin sabuwar Riga don Bata Boye Jin haushin ta Kuma Bata son ace Anfi ta komai ko Anfi Ya'yan ta don Haka a sheke ta amsa tana Kare min kallo tun daga sama har k'asa.....


"Goggo ga Allo na karbo ku saka mini albarka....

"Wai na sauka?
Ta tambaya da mamaki nace Mata eh...


"Saukar izifi biyar ko na goma?

"Izifi sittin dai goggo....

Ta kada kanta tana Fadin
"Shararrar fayif ! Wai ke Nan izifi sittin Kika sauke? To madalla dama sai da asiya ta fada min karatun naki duk Zuk'u ne gashi Kuma na gani ...


"Wallahi Babu Zuk'u goggo Allah ma shaida ne Kuma Bari na Karanta Miki kiji in Zuk'u ne.....

Na soma Karanta Mata har na Kare Bata ma sake bi ta kaina ba tana ta hidimar sallamar Yara Yan siyen waina .
Ziyada ta Kama hannu na mike
Muka wuce zuwa wurin goggo jauhara wadda Yara suka yiwa sauki ta dube Ni tana murmushi tana Fadin
"Kai Halimatu ba dai an kawo Allon ba?
Na Duka Ina Fadin

"Wallahi an karbo goggo sannu da Aiki ....

Masha Allah Halimatu Ubangiji yasa anyi na tsoron Allah ya Kuma saka albarka kiji. Na Amsa da sauri abinda ke burge Ni da goggo jauhara kenan mace ce Mai fahimta da sanin Rayuwa akasin goggo Dubu...


Ta bude bokitin da take zuba kudin cinikin ta ta dauko dari biyu tana Fadin
"Karbi Halimatu Allah ya Rika ....


"A a goggo ki bar kudin ki wallahi Nagode da ADDU A ma....

"Ke karbi kinji duk Wanda ya Baki karbi albarkacin Al kur ani ne Kuma ko A LAHIRA albarkar ANNABI da Al kur ani muke fatan samu duk Wanda ya Baki karbi abinki Kar ki ki karba...

Na karba Ina godiya nace
"Goggo Bari na biya Miki bak'ara da fatihatul kitabi..

"Ai kuwa Karanta mini Halimatu naji...

Na Karanta Mata gaban Allon da Baya tana ta fadin
"Masha Allah shukaran tabarakallah kinji .
Na mike Ina Mata godiya muka fice daga gidan Ziyada na Fadin

"Wallahi matar Nan tana burge Ni ta San Rayuwa ba kamar goggo Dubu ba Sam kamar Bata je makaranta ba Babu lissafi a lamarin ta...

"Uhum
Shi kadai na iya fada don ma Ziyada Bata San goggo Dubu bane Ni Kam na San ta Sani na hakika.....


"Halimatu
Aka Kira sunan muka juya tare da Ziyada saboda shaida Mai muryar wato balange..

"Muje Halimatu don Allah kar ki share shi yau fa Ranar farin ciki ce Ni fa banga aibun balange ba Halimatu Mai sonka kamar Bai kamaci wulakanci ba don Allah ki daina nunawa bawan Allah Nan Baki yin sa ki rabu da kowa lafiya ....

Na kada kaina don na yarda da maganar Ziyada kwarai...

"Kai masoyiya ta sauka kikayi?
"Eh na bashi Amsa cike da wani irin Sanyi..

"Masha Allah Allah ya sa albarka biya min naji in dai ba Zuk'u kikayi ba ...

Na kalle shi Ina Fadin
"In ma Zuk'un nayi ai Allah shaida ne mala ikun Allah ma shaida ...

Na soma Karanta mishi cikin murya ta har na kare shi Kuma ya Amsa da takbeeri Yana Fadin

"Takbeer Sadak'ta masoyiya na yarda Allah yasa anyi na tsoron Allah ga wannan sai na kawo abin sadaka ko?
Ya Miko min naira Dubu Amma na kawar da kaina Ina Fadin

"Nagode ma da ADDU AR da kayi min...

Ya mikawa Ziyada Yana Fadin
"Rike Mata Ziyada sai Nazo har gida wurin Dada na kwashi gaisuwa Kuma na kawo wani Abu....

Muna Shirin wucewa ne na kula da shi tsaye gefen mu Yana sanye da hannayen sa cikin aljihun wandon sa ga Alama Kuma yaji abinda muke ...

Idanun mu suka hadu a lokaci Daya yayin da naji wani Abu ya fizge Ni kamar Jan wutar lantarki. Fari ne tas Mai tsawo Kuma Mai Fadin kirji. Yana da manyan idanu da dogon hanci sai gashin Kansa Mai tsananin kyalli da sheki.....

"Nima Azo a biya min karatun naji in Babu damuwa.
Ya fada da wani Amon sauti Wanda ya Hana nayi mishi gardama....

"Babu ma wata damuwa
Cewar Ziyada
Na juyo Ina Jin idon shi a kaina Yana zagaye Ni Amma kamar ance dago muka sake kallon kuda ya saki murmushi Yana Fadin

"Kece kikayi saukar ?
Na amsa da gyada mishi Kai...
"Ok to Allah yasa albarka malama Amma sunan malamar?..

"Halimatu na Samu kaina Ina Mai fada mishi sunan Kai tsaye Babu kwana abinda na tabbatar ban tab'a yi ga wani irin shi ba...

"Babban suna ne a wuri na ba na iya fadar sunan ...

Na soma Karanta mishi Ina Jin kamar Zan daburce don idon shi a kaina har na Gama shima yayi kabbara Yana min ADDU AR Allah yasa Al kur ani ya CeCe Ni . ADDU AR shi tayi min Dadi matuka Gaya na Kuma Amsa da ameen ya Rabbi

Ya sa fito da kudi daga aljuhu Yana Fadin
"Nima ga tawa sadakar...

Na kasa Musa mishi na karba Ina godiya muka wuce Ina Jin idanun sa a kaina .
Sai da muka Shiga gidan su Ziyada ne Naga Ashe Dubu biyar ce farin mutumin Nan ya bani . Na nunawa Ziyada wacce take cewa

"Gaskiya gayen Nan ya iya wanka Halimatu....

Naja tsaki na wuce zuwa dakin mama wacce take ta min ADDU A Bayan na Karanta Mata Allo itama Dubu biyu ta bani kafin muka Shiga zaga gidajen Yan Uwa da abokan arziki sai gani da kudi masu yawa. Wanda ake ta bani.

Sai kusan la asar muka dawo gida Ina gaban Dada Ina Karanta Mata adadin mutanen da suka bani kudi da masu yi min fatan alheri har na Kare kafin Dada tace

"Banji abinda Dubu ta Baki ba ?
Na dubi Dada Ina Fadin
"Bata bani komai ba Dada sai ma cewa da tayi Wai nayi Zuk'u....


"Ahaf ai Ni na San jauhara tana iya Baki komai ma Amma Dubu fatan alheri ma bakin ciki ba zai Bari ta iya ba....


"Kyale ta kawai Dada Allah ai shaida ne Kuma ba gashi ba Wanda ban sani ba ma yabani Dubu biyar.
Dada ta jawo langar wacce ta dafe kazar Nan da daddawa da albasa Tasha attarugu ta Miko min tana Fadin

"Ga kazar ki Ziyada Taya ta ku cinye ta ....

Nace
"Ai tare dake Dada zamu ci ....

"Kuci in kun rage zanci in Kuma kun cinye ba komai Bari na yiwa jauhara godiyar alherin da tayi Miki...


Ta fice zuwa kofar su goggo Dubu
"Jauhara kun cika Halima da abin arziki allah ya biya ya saka da alheri....


Goggo Dubu tace
"Wai Dada Anya karatun Nan na Halima Babu Zuk'u a ciki? ....

"To Dubu in ma da Zuk'un ai ta dai yi duk gidan Nan waye yayi Zuk'un Nan irin na Halima? Ina ce har su jummai sukayi aure ko saukar Zuk'un basuyi ba? Ashe ko ko Babu komai Halima ta kafa tarihin sauka Koda ta Zuk'u ce ....


"A a dada kice magana dama Kika kullo tunda har da gori da Gaya magana Amma Ina ce saukar kawai Halima zata nunawa su jummai Amma ba nagarta ba tunda su har gobe Basu da wani bakin fenti bari mugun tabon da in magana ta bugi magana za ayi Indo ina Ai....


Wannan maganar ta sauka akan kunne na na bakin fenti da mugun tabon da in ya bayyana....

"Dubu nafi karfin na kullo magana Akan ki . Mijin ki ma Dole yayi abinda nake so bare har na kullawa suruka magana. Kuma kin yi na farko kinyi na karshe Akan wannan maganar na Rantse Miki da Allah duk Ranar da Kika Kuma kwata irin ta Zaki hadu da fishi na ....

Goggo jauhara ta taso tana Fadin
"Gaskiya Dubu babu tsinkaye a cikin abinda kikeyi . Dada ba tsarar ki bace tunda Wanda ya San darajar manyan sa shine Yake mutunta na wani....

"Barta jauhara in ita ban Isa da ita ba ai na Isa da mijin ta....


"Kiyi hakuri don Allah Dada....
Na kamo Hannun Dada Ina Fadin
"Yi hakuri Dada ta taho muje....

Muka wuce inda Kuma goggo Dubu ta mayar da tijarar ta Kan goggo jauhara tana Fadin

"Ni fa in ban kasa da mutum ba Banga dalilin da zai dauka ba in ba munafunci ba sai a zage Ni a dake Ni kuma ace ba zan koka ba? In takamar ta haifi miji na sai ta gayan zancen banza na kyale ta? In ta zubar da girman ta sai na kasa saka kafa na murje shi ?to bana gayyar munafunci ban kasa da mutum ba bare ya dauka Kuma tsohuwar can tace min kulle Zan ce Mata casss ta Rike girman ta ta daina yada min magana da arashi har tana neman zagin Ya'ya na akan wata karere can Marar tsarki? To in ta haifi Mai gidan sai akace Nima ta Haife Ni?

Goggo Dubu tayi ta tijara tana sakin maganganu Amma goggo jauhara ko Tak Bata ce Mata ba sai ma Kira ar karatun Al kur ani da ta saka wayar ta ya soma karade tsakiyar gidan abinda ya Kuma fusata goggo Dubu kenan Amma iyakar abinda zata iya kenan don jauhara dai ba zata daku ba don ta taba Rufe gida Wai zata Bata Kashi sai gashi reshe ya juye da mujiya jauhara ta lakada Mata dukan da har sai da tayi barin ciki tun daga wannan Rana Bata Kuma gigin cewa zata dake ta ba.......










To fa kaji wani Abu. Bari muji Yaya wannan tafiyar take Mai taken _*LINZAMI DA WUTA*_



✍🏻 Alkalamin GIDAN IKO
[8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻







🧆 *_LINZMI DA WUTA_*🧆





Pages
3️⃣//4️⃣






NA
GIDAN IKO💖







*_Kirkirarren labari ne da Bai shafi Rayuwar kowa ba kuskure ne babba danganta kai ko wani dashi babu mafi cancantar suyi suka akan labarin irin taurarun cikin labarin Wanda kuka San Babu su a zahiri to kar wanda ba cikin jaruman labarin Yake ba yace don shi ko don wani akayi Hakan jaruman cikin labarin ne kadai suke da damar sukar marubuci akan don me zai fallasaww duniya sirrin_.*





_WULAKANCI_




...............Babu abinda Yake Amsa kuwwa a kunnuwa na da zuciya ta face kalaman goggo Dubu. Meye bak'in fentin da Yake gareni ? Wane irin mugun tabo ne Dani Wanda har in magana ta bugi magana za ayi Indo ina A i?


Kaina ya shiga wani irin mugun duhu duk da ba yau ne Ranar farko da na soma Jin hakan a bakin goggo Dubu ba Amma a yau din naji Ina son sanin ma anar kalaman nata gareni.


Dada da take ta tijara da masifa Akan dai kalaman goggo Dubu ban iya ce Mata Tak ba bare na Bata hakuri har aka Kira sallar magaruba Dada Bata yi shiru ba .

Na mike na figi buta na Shiga bandaki na fito na jawo kujera Yar tsuguno na Zauna ina alwala Ina Jin zafin kalaman goggo Dubu Wanda nake son a yau na tambayi Dada meye bak'in fentin da Yake jiki na ? Meye Kuma mugun tabo a tare Dani?


Na Gama daura alwala na mike na wuce Dada tana ta fadan ta duk dai akan goggo Dubu da abinda tayi mini...

Duk da ban juyo ba Amma naji kallon dada a jikina Wanda bana ko tantama na shirun da nayi ne ban kuma tankawa ba har kawo yanzu.


Ina salla zuciya ta cike fall da tunanin Al Amarin da ya Zama bak'in fentin a gareni.
Hakika gata da kulawar Dada ta Bai iya bude min kofar da Zan tuhumi Ni wacece ba . Tunda kaf ahalin da suke gidan mu Ni din Yar gata ce ta nunawa a jarida . Dada ta kore min dukkan wani Abu da zai nuna Ni din na tawaya ko a nakashe nake. Amma a yau kalaman goggo Dubu sun nuna min Ni din wata musaka ce ko tauyayyiya wacce ta Rasa wani Abu da zatayi dukan kirjin da cikakkun Ya'ya sukeyi....


Ban San nayi zurfi a tunani ba har idaniya ta Bata iya Boye zafin da zuciyar tawa take ciki ba har na soma zubar da hawayen tausayawa Kai sai dai ji nayi Dada tana Fadin....

"Subhanallahi me ya faru ne Halima?
Na dago da sauri ina goge hawaye na nace Mata
"Ba komai.

Ta bi Ni da kallon tuhuma na mike na wuce Uwar dakin na Zauna a gefen gado Ina Kara jin zafin kaddarar da ta hau Ni har abin ya Zama abin gori gareni wurin goggo Dubu. Shin MENENE? Me ya faru har Al Amari na ya Zama a goranta min don Raina ya baci a ji Dadi?


Ina jin lokacin da goggo Dubu ta kawowa Dada abinci har Dada tana Kuma Rufe ta da masifa duk dai akan abinda ya farun Amma banji goggo Dubu ta tanka ba me yuwuwa tayi nadamar abinda tayi Amma Kuma banji ta bayar da hakuri ba.

Dada ta dauko kwanon abincin ta biyo Ni Uwar dakin tana kallo na ta aje abincin tana Zama kusa Dani ganin idanu na da Ruwan hawaye kaca kace yasa ta jawo Ni tana Fadin

"Halima yanzu akwai wani Abu da zai same ki Amma ki Boye min ki kasa sanar Dani? Don Allah ci abinci ki fada min abinda ya Dame ki....


"Na koshi Dada. Babu Kuma abinda Yake damu na sai kalaman goggo Dubu. Meye bak'in fentin da nake dashi Dada? Meye mugun tabon da ake tsoron ya fito mini?....

Sai kawai Naga Dada ta fashe da kuka tana Fadin

"Ni Dubu zata wulakanta? Ni zakiyiwa wannan wulakancin? Sai Kuma ta mike da Sauri har zanin ta Yana Shirin faduwa ta fice daga dakin Ina kallon ta fice zuwa kofar su goggo Dubu. Ina ji tana Fadin


"Jauhara sa adu na Nan?
Banji abinda goggo jauhara ta fada ba sai Naga Dada ta wuce cikin gidan

Baba sa adu Wanda suke cewa Baba Headmaster Yana Zaune saman kujerar sa da redio Yana sauraren Shirin idon mikiya ya Rage karar Radio Yana mikewa don Jin Kiran mahaifiyar sa inda Kuma goggo Dubu gaba ya fara Mata balli balli....


"Gani Nan Dada lafiya dai ko?..

"Ina fa lafiya? Ba nice nace kayiwa matar ka iyaka da Halima ba? Shin a me kuka dauke Ni ne Kai da ita? Raining da kayi min ne har ka Bawa matar ka damar ta Raina Ni? To zan Kai karar ka ga Ubangiji don Allah ya sani Kuna cutar Dani kuna kunsa min bakin ciki...

Sai ta Kuma fashewa da kuka ta koma kofar ta....

Goggo jauhara ce ta ta biyo ta tana fadin
"Kiyi hakuri don girman Allah Dada ayi hakuri in Sha Allah ba zata sake ba....

"Za a sake Mana jauhara? Ba shi ya Bata kofar da ta Raina Ni ba? Inda Ina da mutunci a wurin shi yaushe Dubu zata kalli idona tayi min Rashin kunya? Ni da kaina nace mishi ya jawa matar shi kunne ta fita harkar Halima tunda ba kishiyar ta bace Ni Banga abinda yarinyar Nan tayi mata ba.....


Baba Headmaster ya biyo Bayan dada Hankalin say tashe yana Fadin
"Kiyi hakuri Dada wallahi ban San abinda Yake faruwa ba....


Dada ta soma share hawayen ta tana fadin
"Ai Ni na Gama magana sa adu saura kiris na hada kayana na bar maku gidan Nan ....


"Kiyi hakuri don girman Allah
Ya dubi goggo jauhara Yana Fadin
"Jauhara Kira min Dubu taxo...

Goggo jauhara ta fice Kiran goggo Dubu inda Baba Headmaster Yake ta rarrashi da ban hakuri har goggo Dubu ta iso....


"Me kikayiwa Dada?
Ya watsa Mata tambayar ta dube shi tana duban Dada....

"Me fa tayi Banda son ketawa Halimatu Rigar mutunci? Ni na Rasa abinda yarinyar Nan ta tsarewa baiwar Allah Nan tamkar taji ance kana Shirin auren ta ta Zama kishiyar ta. To a yau na gaji da hakuri wallahi yadda ta saka Halimatu kuka itama sai tayi nata kukan. Dama na fada Miki tab'a mutuncin Halima daidai Yake da tab'a mutuncin igiyar auren ki don wallahi kinji na Rantse matukar dai Kika ce Halima ce kishiyar ki fiye da jauhara to ina Mai tabbatar miki da wallahi zaman ki ya zo karshe a gidan Nan don sa adu ma yace zai tab'a mutuncin Halima to zai ga abinda zanyi mishi bare ke da aure ya kawo . Tun yarinyar Nan Bata kula da kalaman ki ba har a yau tana neman sanin meye abinda Kika fada Mata? Sai Kuma Dada ta Kuma rushewa da kuka .....


"Don girman Allah kiyi hakuri Dada....

"Ba inyi hakuri nake son ji ba sa adu. Mataki kawai nake so ka dauka akan matar ka kafin nan da zuwa
End Ads