x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - LINZAMI DA WUTA free pages

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 43517 words

Category: Tale Stories

Views 222

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ta hada Uban gumi Yana cije Baki Alamar Yana Jin wani Abu Akan maganin....

Tausayin shi yayi matukar Kama Ni ganin Yana ta hada gumi nace
"Dada ko za a barshi Haka ne ya huta?
Tace to Halimatu ai ga Alama magani yayi dama ayar Allah ai ba karya ba sai Kuma gobe Za a sake Allah ka taimaki bawan ka don darajar Uban Daki na sayyudyna Rasulullahi ...


A Ranar da aka fara maganin ma sai ga baba na Yana mikewa da kanshi Babu cije Baki Kuma Yan cewa Dada kafar ta rage nauyi .....

"Alhamdulillahi Hamza Allah abin godiya dama duk Wanda ya bar Allah ai wanin Allah zaije nema kuma duk Wanda yace ya zanyi hakika ya manta da Allah in Sha Allah maganin Nan na kwana bakwai ne kafin a Gama shi sai ka samu lafiya...

"Allah ya sa Haka Dada..

Baba na Yana daga Uwar Daki Ni Kuma da Dada muna falo yayin da kullum ake wankin kafa sau daya har na kwana bakwai za ayi amma da Yake Allah shine Al hayyu Kuma Al qayyum tun a kwana na uku kafar baba na ta soma sauka daga kumburin da tayi ciwo Kuma tun na Ranar da yazo har yau din Bai Kuma Jin sa ba. Haka muke zagewa Ni da Dada Amma su baba sa adu sai dai su leko su ce ya Mai jiki? Daga haka sai su fice Kuma har yau din Nan da ake cikin kwana na bakwai babu Wanda ya kawo ko da kanwa ce da Sunan magani

Baba na kafa ta sauka daga kumburi ciwo Kuma ya kau lafiya ta samu har Yana maganar komawa kamaru.

Dada ta dube shi tana Fadin
"Hamza komawa zakayi garin Nan? Ni Kam Allah ya Sani zuwa yanzu garin Nan ya fita Raina Amma na San Allah Yana tare da Kai Kuma da shi na barka....


"Kiyi hakuri Dada zanje na dauko Ya'ya na ne mu dawo Nan in Sophia ta yarda da gaske tana sona to ta karbi addini na mu taho tare da ita idan Kuma tace ba zata karbi addini na ba to Zan sauwake Mata Aure na na dauko Ya'ya na na dawo arewa....


Dada tace
"To Zan Taya ka ADDU AR Allah ya baka nasara ya Kuma tsare ka ya Kuma shirya maka zuriar ka cikin addinin musulunci...

Ya Amsa da ameen ameen Dada

Ba sai ya fada ba Ni da Dada mun San bashi da kudin motar komawa kamaru bare Kuma jirgi da ya Saba Hawa. Dada ta hankade adakar ta ta fito da tulin kudin na faransa wato cefa . Ta Miko mishi tana Fadin

"Rike wannan Hamza Amma don Allah kar ka Jima baka waigo gida ba Ni din yawan Rai ne ya kawoni yanzu to kar mu Dade bamu gaisa ba in son samu ne ma na cika a hannun ku Kuna masu nema min Rahama wurin Ubangiji don Allah in ka samu yadda kake so matar ka ta yarda ta karbi musulunci ku juyo gida idan Kuma Bata yarda ba to don Allah kwaso Ya'yan ka ka dawo gida Hamza...


Ya karbi kudin Yana Mai zubar da hawaye Yana Fadin
"In Sha Allah kuwa Dada Nagode kamar kin San bani da komai ba ko a can bani da komai ciwo ya cinye komai hatta dan albashin da ake biya saboda an ga na daina zuwa Aikin aka daina biya ....


"Kar ka damu Hamza ka dawo gida akwai kudi da kake bani suna Nan banyi komai da su ba kazo ka Karbe su ka fara Sana a ko kuwa?


Da Haka mukayi sallama da Baba na Wanda yabi Yan uwan sa gida gida yayi musu sallama ya wuce kasar kamaru...


Sai dai Bayan tafiyar sa dada take Fadin
"Nayi kuskure wallahi da na Bari Hamza ya koma garin can shi kadai da tare muka tafi don Kar aga ya koma lafiya Kuma ace ba a yarda ya taho da yarinyar Nan ba koma tunda ba son musulunci suke ba suce zasuyi mishi wani Abu musamman in suka ga ya samu lafiya?...


Nima Kuma sai Naga gaskiyar maganar Dada akwai ganganci ga barin Daddy ya koma bare yace zai taho da Ya'yan Nan . Amma sai na karfafe ta da cewa

"Ai Dada Allah Yana tare da shi kuma in Sha Allah ADDU AR mu ba zata Fadi ba .....


"Kwarai kuwa Halima tunda Ubangiji ya kunya ta su Bello to Hamza kafin Ubangiji ne in Sha Allah kuma Babu Mai yin nasara akan sa .....


Sai dai me? Ni da Dada Hankalin mu ya kasa kwanciya. Kullum Kuma muka kwanta bacci sai munyi mafarki da Baba na mafarkin da ba zai zamo Mai Dadi ba. Tun Bana fadawa Dada har dai Ranar na ce mata...

"Ni fa wallahi Dada kullum sai nayi mafarki da baba na.....

"Kema kina yin mugun mafarkin da shi? Me kike gani? Ta tare Ni. Sai nace Mata Ina dai ganin shi ne kawai don in nace Mata mugun mafarkin nake zata rude ne....

"Na soma Jin ba lafiya ba Halimatu. Amma Ina ta kaiwa Allah kuka na Kuma San shi sami uddu a ne komai ya tsara Akan Hamza Mai kyau ne wata Kil mune bamu San hikimar ba Amma fa mugayen mafarkan Nan sun ishe Ni Haka ...



Kwanaki sukayi ta tafiya Dada tana cikin tashin Hankali ga Kuma Babu Daddy Babu wayar sa kawai sai Dada tace min tafiya zatayi kamarun can tunda ta San inda Yake . Nayi maza nace tare zamu tafi? Ta kada kanta tana Fadin

"Ni kadai Zan tafi Kuma ba Zan fadawa kowa ba sai fa ke ....

"A a Dada wallahi ba Zan barki ki tafi ba ke daya in dai ba zamuje tare ba to kema ba Zaki je ba . Ta Yaya Zan barki ki tafi ke Daya ko Babu komai wannan yanayin da ake ciki ke Daya? ....

"Ke na fa San ko Ina tunda naje kamarun nan ba sau daya ba Kuma Babu komai sai alheri....

"Gaskiya Dada to sai dai ku tafi da yakumbo mariya ke Dayan ne fa Ban yarda ki tafi ba Bamu San abinda ya Rike Daddy ba kema kije su Rike ki na Shiga uku?...

Dada ta zuba min ido tana Fadin
"Ai na saka Allah Gaba Kuma shi zai tsare ni ba ke ko wata mariya ba..

Na kafe akan ban yarda ta tafi ba in Kuma tace sai taje to Zan fadawa Baba Headmaster. Abunda Kuma Bata so kenan har Al amarin ya kusa Zama bacin Rai tace Babu wanda zai Hana ta tafiya in ta so tafiyar ta abunda Kuma Ni ya Tayar min da Hankali kenan nayi ta Mata kuka har tace ta fasa kafin hankali na ya kwanta

Kwanaki da yawa Dada Bata kuma tada maganar tafiya ba Amma fa Bata fasa maganar shirun baba na ba. Ranar asabar Ina makarantar islamiya sai dawowa nayi na iske Dada Bata Nan . Na tambayi fiddausi wacce take bani Sak'on da Dada ta Bata ta aje min na kudi .....

"Ina ta tafi fiddausi?
Fiddausi ta dube Ni tana fadin
"Naga dai ta hada Kaya a Jakar ta Kuma ta gwada min wasu fakardu Wanda tace na duba Mata na Gaya Mata sunan wata unguwa da Naga Ni an Rubuta A kamaru.....

Shikenan Dada ta tafi kamaru.....























To Dada Allah ya Kai ki lafiya ya Kuma sa lafiya ta Boye hamzan Nan mu Kam mun Matsu a fiddo mu daga cikin duhu har yanzu Kam a lullube muke tafiya.....






Saura page daya mu kammala book one kuma book one din shine free amma 2 @3 4 paid ne mai bukatar su zai tura 1k ne account 1780003378 Eco banks ko kuma Katin MTN akan 08035191669


Gidan iko 08035191669






✍🏻 Alkalamin GIDAN IKO💖
[8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅





🧆 *_LINZAMI DA WUTA_*🧆







Pages
2️⃣9️⃣/30️⃣





NA
GIDAN IKO💖


_Hakkin mallakar littafin ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne kowane Abu Yana da mamallakin sa Babu Kuma Mai son a daukar mishi kayan sa ba tare da izinin sa ba mu kiyaye hakkin juna sai mu Zauna lafiya_




_ADDU A ne ga RUHIN dukkan musulmin duniya masu NUMFASHI da Wanda Ubangiji ya yanke NUMFASHIn su Allah ta ala da Kai mukai imani da Kai muke dogaro Allah ka Rahamtaww musulmi da Rahamar ka don Wanda ka k'agi duniya da lahira domin sa_



_TA FARU TA K'ARE_



💖



............... "Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un ! Ita nake ta fada ina maimaitawa cike da tashin Hankali kafin na fashe da kuka ina fadin

'Na shiga uku na fiddausi shikenan shikenan tawa ta same ni'


Fiddausi ta dube Ni a rikice cikin tashin hankali tana fadin
"Me Yake faruwa ne wai Halimatu? Me Dada ta tafi yi kamarun?...

Ban iya Gane abinda fiddausi take tambaya ta ba tamkar ba da hausa tayi tambayar ba . Babu abinda nake hangowa sai Dada a garin da ita kanta Bata yarda da kanta akan zuwan sa ba. Ban Manta ba Ni kaina da Baba na yace zai tafi Dani cewa tayi ba zanje ba. Haka Kuma tace tayi kuskure da ta Bari baba na ya tafi shi kadai gashi itama ta tafi Ni babban tashin Hankali na ma yadda Rayuwa ta Zama a yanzu da ake cike da tashe tashen Hankula da yadda in ka San wuri a da yanzy ba Haka Yake ba Kar taje ma ta bace shine damuwa ta....

"Me zatayo a kamarun?
Fiddausi ta kuma katse Ni da wannan tambayar...

"Wai baba na zata bi bayan shi gashi ma Ashe ko sunan inda Yake Bata Rike ba sai da ta tambaye ki na Kuma tabbatar da kafin ta Isa kamarun ta manta garin da tace duk arna ne waye ma ya iya hausar da zata tambaya?

Mukayi shiru Ni da fiddausi cike da tashin Hankali ga Dada ko waya Bata da ita bare na Kira ta naji inda ake ko Halin da take ciki


Wani matsiyacin tashin Hankali da ya mamaye Ni har na soma Jin zazzabi Yana kada Ni Dole na kwanta ina makyarkyata


Da yamma na nufi kofar Baba Headmaster na same shi ina gaishe shi ya Amsa min kamar yadda ya Saba amsa min ba yabo ba fallasa Don tun lokacin da Dada ta kora Goggo Dubu gida akan abinda tayi min na kula Baba Headmaster ya Kara tsana ta duk da dama can ba wani yi na Yake ba to Amma maganganun da ya fada ne suka nuna min ya ji haushin abun don ji nayi Yana Fadin

"Wannan yarinyar an shagwaba ta tana tatawa matan mu Rashin kirki kuma ace laifin su ne kana kallon idon ta kasan ja ira ce ...


Tunda naji wannan maganar na San yaji Haushi Amma ban yarda Dada ta Sani ba....

Na gaishe shi Ina Fadin
"Baba Dada fa ta tafi kamaru ita Daya Ni kuma Ina Jin tsoron Kar wani Abu ya faru don Naga ita da kanta Bata yarda da wani ya tafi ba Amma ita fa ko sunan unguwar da zataje Bata Sani ba sai da ta tambaye fiddausi......

"Me ta tafi yi kamarun? Ko ance wani Abu ya sake faruwa ne?...

"Wai bin Bayan baba na tayi taji shirun shi yayi yawa shine tabi Bayan shi .....

"Yanzu har Dada ta iya tafiya kamarun Amma Bata sanar da Dayan mu ba?
Ya fada Yana Mai nuna fushi inda na Gane Kai dangin mahaifi na dai mutuncin su ba wani yawan kirki ne da shi ba....

"Ni yanzu da kika zo kika fada min me kike nufin nayi?
Ya tambaya Yana tsattsare Ni da manyan idanun shi cike da masifa...


"Baba don Abi bayan ta tunda ba Sanin inda zataje tayi ba ita da kanta fa a tsorace take da garin Nan Baba gara abi Bayan ta a dawo da ita kamaru fa ba Nan bace....


"Ni dai ba zanbi Bayan ta ba tunda har ta tafi ban sani ba zanyi Mata ADDU AR Allah ya tsare hanya Amma Ni Ina Naga kudin da Zan bi hanyar kamaru a yanzu ? Allah ya maido ta lafiya ai Ina ganin cikin mu ya kamata ta tada wani ko Ni ko Bello tace mubi Mata Bayan hamzan tunda Kuma ta fidda mu daga cikin lamarin me zai kai mu Shiga? Dama ta fara Fadin saaboda munga yadda ya Zama . Tun yaushe Dada take nuna Mana Hamza ne kawai Dan ta ko wanda take so? Inda ta dauke mu kamar shi yaushe zata tafi bamu Sani ba? Ni ko kudin zuwan ma ne da Ni ba zanje ba tunda ba a saka Dani ba ....


Na mike ina Jin Ashe ba Rashin kirki ne da su Baba Headmaster ba Rashin mutunci ne . To Rashin mutunci Mana? In sunyiwa Baba na bakin Hali shine Rashin kirki Amma tunda abun Nasu Bai bar Uwar su ba ya je ga Dada Rashin mutunci ne....

Na mike ban iya ce mishi komai ba Yana ta sababi Yana tijara yayin da Goggo jauhara tace

"Amma kuwa in kace Haka kamar Babu GIRMA da biyayya ai Dada ko makotaka take da ku ta wuce abinda kake fada Mata gaskiya Babu D'a A acikin abinda kayi Amma kayi hakuri in tawa tayi zafi....


Ban iya tsayawa naji karshen abinda Goggo jauhara take fada mishi ba na wuce na barshi Yana ta tijara har Goggo Dubu na Fadin

"Ai kuwa a makotakar akace ka sanar da makocinka Halin tafiya ko ciwo don shine Wanda zai fara taimakon ka kafin wani naka yazo ma Amma sai fa yanzu muke Jin ta tafi kamaru....

Na wuce ban tssya ba inda koma kofar mu na Rufe na nufi gidan yakumbo mariya wacce na Zayyanewa komai akan tafiyar Dada kamaru Amma itama yadda kuka San sun hada Baki da Baba Headmaster itama tace ai Dada ta Gama mutuwa Akan son Hamza fiye da su don Haka ADDU A zasu Mata Allah ya tsare hanya

Na fito ina cike da tashin Hankali Anya kuwa Dada ce uwar su Yakumbo mariya da Baba Headmaster? Kai ban zaci hakan ba Amma Kuma ko Rukon su tayi ai ta zarta wannan wulakancin a gare su...


Na iso bakin titi don na tsayar da Napep amma fetal Babu su na kafa tsayuwar jira....


Dr Anam da ya taho daga asibiti zuwa gida ya soma hango ta tsaye cikin hijabi da kyakkyawar Shiga ta Kamala Amma ya cika da mamaki me ya kawo ta garin Nan? Kuma duk cikin salon barikin ne ya ganta da hijabi?...

Ya taka burki a gaban ta Yana sauke gilas din motar....

Na ja da baya da sauri ganin mota ta faka a gaba na ya sauke gilas din Yana kallo na cike da mamaki har Yana murmushi...

"Kai Ranki ya Dade helengabros yau kece a garin namu ?
Na dube shi cike da Mamakin sunan da ya Kira mini Wai Helen gabros....

"Wace Haka Kuma Helen gabros?...
Yayi murmushi Yana Fadin

"Oh Sorry Queen nake so tunda Haka kowa ya San sunan ko?
Na Kuma duban shi ina Fadin

"Don Allah kayi hakuri ina Jin ba wacce ka Sani ba ce kace Helen kace Queen in ma cinke kake to Duka Babu suna na a ciki wallahi....

Kafin ya tanka nayi maza na tsayar da Napep da Hannu na Mai dauke da waya ta inda yabi hannun da wayar shi da ya gani wacce ta nuna mishi Halin bariki kawai ake son nuna mishi....

Yana kokarin fitowa Daga motar na fada Napep ya ja muka shilla a guje kamar Mai Napep din ya San hakan nake bukata. Ga Alama Kuma Dan arufta ne wanda Yake Aikin a Haka....

Dr Anam ya koma motar da sauri ya tashi motar ya marawa Napep din baya don Bai tab'a Jin Yana son Helen ba sai yanzu da ya ganta cikin shiga ta mutunci wacce yake fatan ace ta musulunta Kuma ta Kame kanta shi Kam da yafi kowa murna ....

Yadda yake gudu da son ya cimma su inda Kuma Mai Napep ya wuce mishi fintinkau Amma tabbacci da hakika Yana nuna mishi zai iya taddo su.

Sai dai ina ! Ko kyallin su bai hango ba har ya iso bakin traffic light Amma Babu wata Napep ma bare yayi zaton tana ciki...

Ya koma baya Yana dukan sitiyarin motar Yana cizon lebe da Jin wani irin so da bege ga yarinya Helen gabros...


Ko da na iso gida Ni tuni ma na manta da babin wani Mai mota don tun a can na Gane Yan latsi ne Ni Kuma basa gaba na. Abinda kawai Yake a Raina shine yadda su Baba Headmaster da Yakumbo mariya suka nuna min akan Dada ko Rukon su tayi ai ta wuce da wannan wulakancin Daga gare su. Na San Baba Bello yafi su Rashin kirki shiyasa ma ban nufe shi ba na fara da babban Nasu Baba Headmaster to karamar tasu ma ba kirkin gare ta ba ga abunda tayi min .

Da dare sai ga Baba Bello ya iso nan suka shigo shi da Baba Headmaster Yana Fadin

"Ai Ni Bata zo gida na ba Allah ne ma ya kure ta da Bata zo ba don da sai na Zane kafira saboda Uban ta ne zata tsoma mu cikin balaki? Mutanen can ita Dada da kanta ta San yadda suka Rabu wurin tahowa da Yar Nan Kuma ta San ba ta Dadi za a kwashe ba meye ya kaita kwasar jiki ta tafi? Ai don ta San in ta fada Mana gaskiya zamu fada Mata shiyasa Ai Bata fada Mana ba ....


"To ai Ni da nace Kai Bello kabi Bayan ta tunda har jauhara ta soma nuna min dacewa da Rashin dacewa sai kace Uwar ta ce ba tawa ba sai gashi dazu ma ana cewa Wai munyi abun kunya Uwar mu ta gudu Amma bamu damu ba to tunda duniya ta soma zagin mu kawai ka Rufe ido ka bi Bayan ta na San Kai ba zaka yarda ka kwana ciki ba in yaso in na Samu kudi Zan mayar maka da na zuwa sai kayi na dawowa tunda Kai dai kana da kudi a yanzu Napep din ka uku Kuma kowace tana kawo wuta ....


"Yo in don zagin duniya ne sa adu ai baka iyawa Dan Adam Kuma Dada Bata son mu Shiga
End Ads