x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - LINZAMI DA WUTA free pages

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 43517 words

Category: Tale Stories

Views 220

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Ni a komai na banbanta da sauran Mata...


"Saboda me?
"Saboda tsari na kenan....

Bata Bari ya sake magana ba ta mike ta wuce bedroom ya bita da kallo cike da son ta da Jin lallai da gaske Yake son ta....

Ya tashi bita dakin ya same ta tana Kara fesa turare komai nata Mai kyau ne.
Ta dube shi tana Fadin

"Na soma zargin kaina zaka Yankee tunda baka nuna kana da son mu kasance ba....

Tamkar ta Kara izashi ya Rungume ta Yana Fadin

"Ko masu yankan Kan ne suke Shirin Yankee naki Kan Zan fanshe ki da nawa Kan . Ina Jin Dadin kallon ki ne....

"Zaka biya kudi rib'i biyu kenan da na kallo da na wannan

"Ko rib'i nawa kike so Zan Baki my sweety Heeling...

Ta soma sauke Mishi Rigar da ke jikin shi yayin da gashin jikin shi ya soma fizgar ta . Ta soma Jin wani Abu a jikin ta a game da gayen Wanda ba kowa take Jin Hakan ba

Ta soma balle botiran Rigar ta Yana kallon ta kafin ta sauke komai gashin kanta ya watsu ta lafe a jikin shi.

Jiki da jini ya ji gaba Daya ta Rikita shi ya soma sauke Mata hot kis Yana Jin tamkar ya hadiye ta Amma me? Wata kakkarfar hamma da ya soma itace ta Zama shamaki domin kuwa Kan kace me? Bacci Mai nauyi ya soma kawo mishi Hari. Tana Rungume da shi taga baccin na Shirin sure shi har dai taga ya bingire...

Tayi murmushi ta Dora kanshi a filo ta sumbaci fuskar shi tana shafa ta kafin taja mishi blanket ta Rufa Mishi...

Ta sauko daga Kan gadon tana mayar da kayan ta ta duba inda taga ya ajiye brif case din wacce take dauke da kudaden tajawo ta ta Kuma dauki sayar sa Mai daraja wacce take dauke da layuka biyu sai ta fidda mishi layin glo don taga da shine Yake karbar alert Amma MTN din sai ta bar shi a cikin wayar ta Kuma saka ta a Jakarta ta ta dauko Jakar kudin ta fice daga dakin hotel din ....



***. **** ****



Goggo Dubu ta dubi wainar ta fall bokitin Roba kullum abin Kara lalacewa Yake . Kullum.sana a Babu Riba sai asara ga Dan Karen bashi da Yake ta Haye Mata don Rabon da tayi waina ta siyar tun kafin ta bar gidan Nan dawowar ta tamkar ta dawo da Rashin nasara da albarka. Amma Al Amarin kishiyar ta jauhara kullum kasuwar ta sai ci gaba take . A yanzu ma kusan sau uku take Dora tukunyar taliya Tana sauke wata take maida wata Al Amarin da ya Gama tabbatar Mata da an saka Mata Hannu....


"Asiya ke Asiya Wai Ina asiya take ne tana jina tayi min kunnen Uwar shegu?
Asiya ta fito daga Daki tana Fadin
"Gani goggo...

"Yau fa ba zanyi asarar wainar Nan ba Dole ke da fiddausi ku zaga min da ita tunda dama Haka aka shirya min da son lallai sai anga na kassara gashi kuma anyi nasara a kaina....

Goggo jauhara ta dago kanta tana duban Goggo Dubu da take auno Mata harara Amma sai tayi kamar Bata gani ba don ance maso habaici shine maso fada

Asiya tace
"Wai goggo talla kike nufi?
Goggo Dubu ta dube ta a fusace tana Fadin
"Talla nake nufi Mana ko kuwa don Uban ki gaku turus cikin Daki Zan ta jerawa kaina asara ....

"Haba goggo baban mu fa yace ko su abubakar Kar a Dora musu talla bare mu Mata Kuma fa ba a tashi makaranta ba...

"Idan na Dora Miki tallar kije ki Kai mishi kice talla na Dora Miki na soke makarantar in Kuma shi zaije min tallar sai ki bashi...

Haka kuwa ta Hana yarinyar komawa makaranta ta Dora Mata tallar
Sai dai fiddausi da Yake ita budurwa ce Bata zaga ba Amma dai tace ta zauna Mata kofar gida da ita


Tuni goggo jauhara ta siyar da taliyar ta tayi wankan ta fes ta kuma share kofar ta ta wanke kayan Sana ar ta . Yaran ta suka dawo makaranta ta Basu abinci kasancewar Yaran ta hudu Kuma duk maza. Abubakar sai Umar sai usmanu sai aliyu yayin da Goggo Dubu take da Ya'ya bakwai Kuma dukkan su Mata ne. Jummai da Maryam su suna gidan mizajen su . Sai fiddausi da asiya sai hadixa da salamatu sai karamar su hafsat. Har da Ya'ya maza da Goggo jauhara take da su suka Kara tsanar ta wurin Goggo Dubu don tana ganin tazo a Bayan ta Kuma zata amshe gida. Sai Kuma ta kula Mai gidan ya mutu a son jauhara wacce kaddara ce ta kawo ta gidan Domin kuwa ba sa adu take so ba Allah dai ne ya kaddara shine mijin nata Amma ba don tana son shi ba.
Wanda jauhara taso Aure Dan uwan ta ne da uwar sa da baban ta uwar su daya Uban su daya wato Ya'ya maza . Salisu ya tashi a gidan su jauhara don Nan gidan aka Rike shi har Allah ya hada zukatan salisu da jauhara. Direban mota ne Wanda Yake sufuri nijar da Nigeria. Mahaifin jauhara Kuma ya hada salisu da jauhara suka tabbatar mishi da sun aminta da juna don Babu irin maneman da Basu so jauhara ba smma tace sai salisu

Salisu Yana son jauhara matuka Gaya Amma kana taka Allah na tasa . Nasibin da salisu Yake da shi a tuki ne yasa wasu daga cikin direbobin da suke tare da shi Jin zafin sa alhalin Bai taka ba Bai zubar ba har dai sukayi mishi shune na ikon niger wata Rana da yayi Lodi Ashe an saka kayan laifin da ikon nijar basa so . Sai ga shi an sanar da ikon cewar motar salisu Mai lamba kaza ta dauko kayan laifi don Haka aka tare salisu aka Kuma ga kayan laifi don Haka ba a ko tsaitsaya ba aka Mika shi gidan kaso Wanda aka Yankee mishi wa adin shekara ashirin da biyar

Matukar tashin Hankali jauhara ta shige shi bare Kuma mahaifin ta Wanda shine Uban rikon salisu. Babu irin zarya da shige da fice da ba ayi ba Amma lamarin yaci tura. Duk sati jauhara tana hanyar gidan kaso kaiwa salisu kayan masrufi inda Kuma ta kudurce ba zata yi aure ba sai ta jira salisu ya fito.
Suna Zaune a benci tana ta kuka Yana Rarrashin ta har Yana Fadin ta Bawa masoyan ta dama tayi auren ta Amma ta tabbatar mishi da zata jira shi abinda ya tabbatar da ba me yuwuwa bane. Duk yadda yaso ta yarda Allah Bai zana aure a tsakanin su ba ta kafe zata jira shi har ya fito

Da ya Gane da gaske take sai ya Barta Amma da baffan Nasu yazo duba shi shine ya ke bashi shawarar a fiddawa jauhara miji Mai mutunci tunda Ni ga yadda Allah yayi baffa ba zai yuwu ace jauhara ta jira Ni har shekara ashirin da biyar ba Ni da ita zuwa lokacin ai Rayuwa ta tafi...


Haka akayi ta juyi da jauhara ta kafe akan zata jira salisu.
Sa adu malamin makarantar su ne tun a primary Yake son ta Amma Bata yarda ta bashi fuska don ta San tana sa salisu shine fa ya kafa naci musamman da ya samu labarin Halin da saurayin jauhara Yake ciki

Duk da Bata Boye mishi yadda take son salisu ba da Kuma jiran da take cewa zatayi mishi hakan Bai sarar mishi da gwiwa ba ya kafa naci har dai Allah ya kaddara shine mijin Kuma Uban su abubakar da Usman Umar da aliu.

Hauka Babu irin Wanda Dubu ba tayi ba lokacin auren jauhara don ta Gane sa adu ya mutu a Kan jauhara. Amma sai jauhara ta nuna Mata ita mace ce Mai ilimi Bata biye Mata Akan komai sai fa Ranar da Dubu ta Rufe kofa Wai zata baka Kashi inda jauhara ta lakada Mata dukan Shan gishiri har tayi barin ciki to daga Nan ne Bata Kuma gigin cewa zata dake ta ba.

Shekara daya da auren jauhara Allah ya wanke salisu ya Kuma fito gaskiya tayi Halin ta Al Amarin da ya gigita jauhara kenan ta Tayar da tsiyata ku kala kala don sa adu ya sau ta ta koma ga salisu Amma ina sa adu ya Kama igiyar ya Rike ya Kuma ji a duniya bashi da babban makiyi irin salisu da har gobe ya tabbatar da Bai bar mishi zuciyar jauhara ba .
Gane Bata da yadda zatayi yasa ta hakura shima salisun Bai jima ba yayi aure da wata matar wacce itama take cike da Jin zafin jauhara don salisu Bai Boye yadda yake son jauhara ba shiyasa matar salisu Bata yin jauhara ko sabga aka hadu Sai suwaiba matar salisu ta yadawa jauhara magana koma ta ganta ta dauke kanta. Yayin da Baba Headmaster Kuma Kuma ko sanga ake gidan salisu baya barin jauhara taje Wai Kar taje su hadu da salisun


Asiya Tasha yawon ta ta dawo babu cinikin kirki yayin da fiddausi dake waje ta Dan siyar Babu laifi

Goggo Dubu ta dubi dukan cinikin abun Haushi da takaici tamkar ta fashe da kuka cike da bak'in ciki...

Goggo jauhara tana ta kadin taliyar ta don injin gareta ita ke kada kayan ta

Usman ya dawo dauke da geron da goggo jauhara ta bashi ya surfo Mata don har da gero take son fara dafawa a gobe don yaran sunce take dafa musu zasu siya

Kamar Wasa ta fara dafa gero da manja shima yara suka dafe kowa ya shigo gero ko taliya yayin da Goggo Dubu Kuma waina Taki sai ma Dan Karen bashin da ya Haye Mata har ta Kai a cikin kwanaki biyar kacal Babu jarin da zata Dora har ta Kai wainar ta gagara

Tana Zaune bakin kofar dakin cike da bak'in ciki tana kallon yadda yara suka Rufe jauhara suna siyen gero da taliya yayin da hafsa karamar Yar goggo Dubu take kukan taliya take so goggo Dubu ta make Mata Baki saboda Jin Haushi ta Rufe yarinyar da sababi da tijara...

"Taliyar uwar ki yarinya sai cin tsiya ba yanzy Kika Sha Koko ba shine wani taliya? Uwar ki ke da Mai taliyarπŸ˜‚

Goggo jauhara tayi murmushi don tana Jin komai ta zuba taliya a Roba ta dago kanta tana Kiran hafsa..

"Taho ki Amsa kinji hafsa?
Da sauri hafsa tanufi Goggo jauhara ta karbi taliyar..

"Yauwa to Zauna Nan kici kinji..

Hafsa ta zauna tana cin taliyar yayin da Goggo Dubu taji bak'in ciki na Shirin shake ta ta mike ta fada Daki don ta gaji da ganin kayan takaici Kuma wani arashi a yau din da batayi wainar ba sai tambaya ake shine abinda ya Kara fusata ta...

Tabawa ta sheko sallama ta shigo inda taga bakin madafin Dubu babu ita bare tuyar waina sai madafin jauhara ne dankam da Yara suna siyen gero da taliya...

"Ikon Allah Haka abun ya Zama Kuma?
Cewar tabawa inda jauhara ta dago tana Mata Sanny da zuwa..

"Kai Amarya ludayin ki Akan dawo Masha Allah Ina Dubu ne Naga yau Babu waina?
Goggo jauhara tayi murmushi tana Fadin
"Allah dai tabawa Dubu tana Nan D'aka...

Tabawa ta afka dakin goggo Dubu tana Fadin
"Lafiya dai Dubu zaman D'aka ana wannan kakar ta Yan makaranta? Ina wainar ne? Meye ya faru Naga ban ganki a madafi ba?.....



















To munji wanna Bari muji meye next chapter? Amma tabawar Nan anyi munahika duk da ban Gano ta ba Amma bakin ta fall Yake da tsegumi.....














✍🏻 Alkalamin GIDAN IKOπŸ’–
[8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»πŸ’…πŸ»








πŸ§† _LINZAMI DA WUTAπŸ§†_





Pages
1️⃣3️⃣/1️⃣4️⃣






GIDAN IKOπŸ’–








_Kirkirarren labari ne da Bai shafi Rayuwar kowa ba kuskure ne babba danganta kai ko wani dashi babu mafi cancantar suyi suka akan labarin irin taurarun cikin labarin Wanda kuka San Babu su a zahiri to kar wanda ba cikin jaruman labarin Yake ba yace don shi ko don wani akayi Hakan jaruman cikin labarin ne kadai suke da damar sukar marubuci akan don me zai fallasaww duniya sirrin su?_






_Sadaukarwa ne ga dukkan Al ummar musulmi da suke Rayuwa a wannan yanayin Ubangiji Allah ka shiga cikin Al Amarin musulmi ka Hana cewa ya zamuyi a Raye ko a kwance._





_Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da Aminci mara yankewa zuwa ga shugaban mu fiyayyen halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam da ahalin gidan sa madaukaka da masu bin su da kyautatawa har izuwa Ranar Alkiyama_




_MUNAFUNCI_

πŸ’–
..............."Me nake Shirin gani Haka Dubu? In dai lafiya ma ai da sauki....

Cewar tabawa wacce take Raba idon duban aminiyar tata Dubu...


Goggo Dubu da ta tashi daga kwancen da take tana daura Dan kwalin ta tana Fadin

"Ina fa lafiya tabawa? Wace lafiya ce zata kunshe Ni a Daki a irin wannan lokacin ....

"Ince dai ba zazzabin Nan bane ba?
"Ai Ni ko zazzabi baya Hana Ni tuya tabawa nayi sake ne dai kawai har anyi nasara a kaina kasuwa ta k'i Ni tamkar Mai bakin iyaye Sana a Babu ci gaba kullum cikin asara nake waina kullum nayi ta sai dai su salamatu suyi ta watanda da ita maganar na siyar Bata taso ba bare na ga haske ko wata Riba. Ba ma wannan ne abinda yafi Tayar Min da Hankali ba sai bashin hatsin duduwa da ya taru ya Haye min yanzu Haka kudin duduwa sun Tasar ma Dubu Sha biyu Kuma Ni bani da Dubu biyu cikakkiya tabawa....


"An kuwa yi nasara Akan ki Dubu Amma banji Miki zafi ba Baki da kaico tunda tuni nake fada Miki duk Ranar da aka tashi saka Miki hannu Zaki ga abinda zai faru gashi Kuma kina Kan gani yanzu jarin ya lalace kenan?

Tabawa ta tambaya...

"Ya Rasa lalacewa tabawa? Kullum nayi waina kwantai nake sai dai na Bawa Yara Amma ita har da gero ta ke hadawa yanzu Dubu kiga yadda gidan Yake cike da Yara da ta siyar ta sake maida tukunya Ni Kuma gani makure a kuryar Daki na Kame hannu na Rungume Ni ba salati ba ba istigifari ba sai bak'in ciki ke ta nanuka ta ...


"To kuma Haka Zaki ci Gaba da zaman D'aka kamar wata Mai danyen jego ko amaryar mugun Abu? ...

"To Yaya Zanyi tabawa?
"Ai Ni kinji abunda Yake bani takaici da ke wallahi Dubu Baki da dabara bare fiddawa Kai mafita. A wannan Halin da in Allah ya kawowa fiddausi da hadiza miji za a ce fito shine har kike tambayar ya zakiyi?...

"Ai wallahi tabawa na Gama tayarwa kaina hankali akan sabgar aure tabawa. Abinda Uban su yayi ya wadatar Dubu bataliyat da take gaba na in ma wasu sun tafi ga wasu Nan to abunda ya samu da shi za ayi amfani wallahi Yar Sana ar da Zan tattali wani Abu an kassara Ni...

"Tashi kawai zakiyi mu nufi wurin malam Mai gafukka ki samo Dan dafa I ko kya Dan Rika motsawa Amma yaushe matar malamin makaranta irin ki Mai Ya'ya Mata turus har biyar a gaban ki Zaki ja ki Zauna ko kudin Jan Baki da hoda da Dan man shafawa sun ishe ki ba?....

"Tabawa in munje wurin malam Mai gafukkar shekaru na Zan zube mishi yayi mini Aikin? Tuni nake ta auna zuwa wurin nashi Amma sai na tuna kudin motar zuwa da dawowa kadai na mallaka gashi Kuma kince Aikin shi tsadar tsiya ne da shi ga bashin da ke kaina na tabbatar da duduwa ta tabbatar da Babu kudin Nan a k'asa sai tayi kamar ta tura wuta da Raina....

"Kuma ke Baki da Dan Kama sayar Wanda za a Kama wasu Yan kudi Nan?
Cewar tabawa da ta katse Dubu...

"Adashe Kuma Ni ake bi bashin zubi bare nace ina jiran kwasa na dauki ta takwas duk na zuba cikin Sana ar Nan Amma duk a wofi aka ce kad'an ma kenan ai na tsinewa Ranar da sa adu ya kyallo min matar can har yaji Yana son ta wallahi nayi Allah ya Isa yafi sau Dubu....

Tabawa ta kyalkyale da Dariya tana Fadin
"Kya ma Kara wata dubun dubulliya Amma dai yanzu ki San abunyi Amma Zama Kam Bai Kama ki ba...


"Ni yanzu in akwai kudi a wurin ki tabawa ki aro min na koma waina na gani....

"Au wainar Zaki koma ba zuwa wurin malam Mai gafukkar ba? Lallai Baki ji wuta ba to Ni Ina Zan ga kudin Baki Dubu ? Ba fa wata Sana a nake ba miji ba wata Gama ba bare na kwantalo Miki a jikin shi ....

"Duk ba wannan ne damuwar ba tabawa Wai kin San fa duk jarin shegiyar matar can sa adu ne ya Bata har da na gero Amma Ni na tambayi aro ma yace tun kafin albashin yaxo Wai mun cinye shi shima wurin jauhara Yake aro Wai nayi Mata magana ta Ara mini?...

"Ta Ara Miki ? Ai kuwa da kinci baya wallahi ace jarin da kake juyawa kishiya ce silar sa ai ko albarka ma ba zaiyi ba ...

"Yo ko nayi hauka tabawa yaushe Zan kalli kudin jauhara bare nace ta Ara mini? Ni fa duk gidan Nan ya fita a Raina wallahi ji nake kamar nayi tafiya ta jibia...

"In Kika tafi jibia ko ai Aikin malami yayi Dole a biya shi. Ni fa ina ganin idan babu kudin da kema Zaki motsa to Ina ganin ta Bayan gida kawai Zaki fito ma ana ki nemi hanyar kassara sa ar tata da tuggu da makirci kiyi ta lalata kayan Sana ar har itama ta Rasa in yaso ku taru ku Rungume Hannuwan Baki daya....

"Kamar Yaya tabawa?
Goggo Dubu ta tambaya a zak'e don taji tafi yarda da Hakan ...

"Ai idanu Zaki fakaita ki samu wani Abu da zai lalata kayan Sana ar Kamar in ta Dora geron ko taliyar sai ki ambama Mata wani Abu da Dole zata zubar da shi Rariya Kinga Dole ba zai ciwu ba sai dai a Kai tsari a Kai kwatami....

Goggo ta kyalkyale da Dariya suna tafawa ita da tabawa...

"Shikenan kalas Kinga daga Nan sai jari yayi kasa in Kuma Yara sunci sunji Babu Dadi gobe ba sa komo ba...

"Yo Eh Mana in an Hana ihu ai ba za a Hana aha ba shiyasa nake ganin wautar ki Dubu Baki da hikimar kwatar
End Ads