Lipton ba Kuma duk Ranar da ya Kuma yi min fyade wallahi zan tanadi kakkaifar wuka ta na sharbe shi kawai....
Ta mike a fusace ta bar gidan Nina ta bita da kallo don har ga Allah ta ji wani Abu Akan abinda tace zatayi wa Anam Kuma ta San da gaske nimra take yadda ta Fadi maganar har zuciyar ta.....
Bai zaci zai dawo gidan ya same ta ba don yayi zaton za a Bata yancin da ake maganar tana da shi Amma sai ya samu ta dawo tana wani cika tana batsewa tamkar dai ace shine ya kashe mata iyaye
Tun da ta dawo aka Shiga wani irin Zama Babu Mai Shiga harkar wani shima ya kwashe ta ya watsar in tana ganin kamar wata tsiya take a wurin shi to Bai so watsar da ita bane Amma a yanzun ya daura aniyar nuna Mata ba itace Rayuwar sa ba abinda yayi ma Ra ayi ne in ya so sai ya watsar da kayan banza
Haka yake ta koman shi inyaso yaci abincin masu Aiki in Kuma Bai so ba sai ya nufi restaurant yayi Oder abinda yake so yayin da ita Kuma Mai gidan take saka Yan aiki girka Mata abinda take so su Kuma gyara mata gida da dakin ta Kuma wata yayi anam ay biya su
Watanni biyu cur da faruwar wannan Al Amari da safe Dr anam ya fito da shirin ficewa Aiki ya Tara's da Nimra tana ta kwara amai tamkar zata shide har zai wuce ta don ba wani tanka shi take ba duk don Kar yace zai nemi wani Abu wurin ta
Tausayin ta ya Kama shi matuka Gaya don ko Babu komai a cikin ikon sa take Kuma a kallon da Yake Mata a yanzu take y fahimci matsalar ta da abinda Yake Shirin faruwa...
Ya Isa inda take tana murkususu ga Alama ciwon ciki ke damun ta ya Kama ta Yana faman jera Mata sannu kafin ya kaita bandaki ta wanke bakin ta da fuskar ta .
Tana Zaune dafe Kai tana Jin yanayin ta Sam Babu Dadi ga ciki da ya ishe ta da murdawa ya zauna da son ya taimake ta da agajin farko ya Kuma soma tab'a jikin ta da son yaji ko akwai zazzabi Amma take ganin kamar da wata manufa yayi hakan ..
Ya Gama duba ta kafin ya dube ta Yana murmushi Yana Fadin
"Congratulations my dear baby ne Yake son bayyana a Marar ki ....
Ta dube shi da wani duba na mamaki tsoro da firgici suka dirar Mata wane irin baby?
Tambayar ta subuce Mata ba tare da ta shirya ba...
"Baby dai namu ....
"Imporsible
Ta fada da tabbaccin Hakan...
Ya bita da kallo lokacin da take haurawa up stairs din bene yayin da ya dubi goggo yaga ya makara don Haka da sauri ya fice Yana Mamakin yahudancin nimra tana nufin ba zata haifi cikin ba ko kuwa bata shirya haihuwar ba?...
Lokacin da ya tashi daga Aiki ya Isa gidan su a can ya Tara's da Nimra kwance tana ta murkususun ta Alamar har yanzu ciwon Bai Barta ba yayin da mummy Nina duk ta tashi Hankalin ta Yana shigowa ta dube shi tana Fadin
"Kaita a fidda Mata cikin Nan Anam don Yana wahalar da ita gaskiya Kuma tace Bata shirya haihuwa yanzu ba gara ta fidda shi ta huta da wannan wahalar......
Ya fiddo idanu waje cike da mamaki Yake kallon mummy kafin yace
"A fidda mummy? Haba Haba don Allah mummy Wai Ni sai yaushe za a barni na Zama mutum kamar kowa ? Yanzu sai ace sai abinda yarinyar Nan take so zatayi Kuma tun yaushe nake ta fatan ganin hakan sai yanzu Kuma ace a fidda...
"To ko in an cire a mayar maka kayan jikin ka tunda Kai kana so? Ta Yaya yarinya tana irin wannan Halin tin ciki bai Kai wani tsayin lokaci ba ana Shan wahala Haka don dai Rashin tausayi da adalci kace ba zata zubar ba? Kai Kam azzalumi ne wallahi Bayan ka danne ta ka Mata fyade tayi ciki Kuma kace wani ikon banza da wofi zaka nuna Mata ? .....
Ya zubawa Uwar tasa Ido Yana kallon ta da Mamakin wace Uwa ce ke daure katarar zubar da cikin jikan ta? Ya mutu daga Zaune ya kasa tsinkawa yayin da ya tabbatar da gaske mummyn Take Kuma hakikatan idan ya bar Nimra yadda take so zatayi don Haka sai Ubangiji ya kimsa mishi wata hikima ya kada kanshi Yana Fadin
"To shikenan mummy tunda Nimra tafi Ni ta Kuma fi ahali na duk yadda kuka so kuyi kawai ...
Yana Shirin ficewa ta tsayar da shi tana Fadin
"Ai kaci Uwar karya ka kwana da yunwa wallahi ka Barta a wanna Halin.. ok dare ne kake jya bi har in Bata yarda ba ka Mata fyade Amma ciwo ba naka bane? Dauke ta maza wallahi yadda ka Taya aka Samar da cikin haka Kuma zaka Taya a wurn sama mata lafiya Kai maza dai wallahi sai kun Shiga uku . In dai lamari na matan ku ne akwai ku da manuba da munafunci....
Yaja ya tsaya yayin da Nina ta tarairayo Nimra tana Rike da ita har motar Anam ya Shiga Yana Jin da ya San Haka wannan aure zai Zame mishi wallahi da sai dai kome zai faru sai dai ya faru Amma da Bai Karbe shi ba...
Ya shiga motar yaja ta suka fice daga gidan yayin da Nimra sai yunkurin amai take Amma Babu ko yawu sai kakari kawai take...
Kai tsaye ya wuce gidan su Nimra a maimakon asibitin da ake nufin ya kaita a zubar Mishu da gudan jini...
Mamaki ya cika Nimra wacce taga inda yazo wato gidan su a maimakon asibiti...
Ya bude ya futa itama ta samu da kyar fa fito tana mishi want shegen kallo Mai cike da neman ba asi Amma Bai Bata fuskar bin ba asi ba Dole ta shige gidan shima yabi Bayan ta ...
Maman Nimra tana gindin murhu tana tsintar shinkafar hausa taga shigowar Nimra ta bita da kallo kafin Kuma taga Anam ya shigo ta washe Baki tana mishi sannu da zuwa
Ta mike ta SHIMFIDA Mishi tabarma ya Zauna suna gaisawa Nimra Kuma ta shiga dakin maman ta kwanta don hajijiya ke neman kayar da ita..
Mahaifin Nimra ya shigo daga masallaci ya iske anam ya bashi hannu suka gaisa Yana tambayar shi Aiki da Rayuwa .
Anam Yana da mutunci a idon iyayen nimra Domin kuwa ya nuna musu shi Dan halal ne Wanda Yake taimakon su da nuna musu sun Zama iyayen sa shiyasa maman Nimra take matukar Jin kunyar shi musamman da ta San Halin yarta . Shima baffan Nata Yana matukar mutunta Anam don Haka yake Dan gida a wurin su fiye da Nimra...
Baffan ne ya dubi anam Yana Fadin
"Anam in ce dai ba wata tsiyar yarinyar Nan ta antaya maka ba....
"Eh baffa wani Abu ne dai tayi Wanda har naji ba Zan iya zuba Mata ido ba gara Nazo na sanar da ku don gaskiya Nimra tana neman kure hakuri na Amma nauyin ku da kunyar ku zai Hana na dauki hukunci da hannu na Amma don Allah kuyiwa tufkar hanci....
Jikin su yayi sanyi kalau suka zuba mishi idanu ya soma Koro musu abinda Yake faruwa na ciki da Nimra tace ba zata iya Raina da haifewa ba sai dai a zubar Kuma mummy ta goya mata Baya har kawo yanzun da mummy ta hado su akan suje a zubar da cikin shi kuma baya Jin zai yarda idan har cikin Nan ya samu matsala...
"Shine baffa na dawo da ita Nan wurin ku don na kafa ku shaida Kuma na ke so na roki alfarmar zaman Nimra a Nan gidan har zuwa lokacin da zanga abinda ya Dace Nayi tukuna ....
Maman ta Rafka salati tana sanar da Ubangiji tana Fadin
"Ni hajara Allah kayi min jarabta ta yarinyar Nan wace irin bayahudar yarinya ce ne Wai ? To ko Ni Kuma wallahi matukar tazubr da cikin Nan Zan Mata Allah ya Isa tunda inda ana zubarwa da ita Bata budi ido a wannan duniyar ba ...
Baffan ya soma Bawa anam hakuri Yana Fadin
"Kayi hakuri don Allah don bani da bakin baka hakuri m tunda na San kana kan yi ma Amma kayi Hankali da ka nufo mu da maganar Nan Kuma in Sha Allah matukar dai tana son gamawa da mu lafiya to Dole tabi yadda kake so ni na San kana hakuri da yarinyar Nan wacce Bata aje kanta Nan kusa ba Kai ka ce Yar wani ce ta samu Allah ya Rufa Mata asiri shine take son yayewa kanta ...
Ya soma Kiran ta tana daga kwance tana Jin duk abinda Yake faruwa duk da tafi Jin ta mama akan baffa Wanda bashi da wani tsanani kamar mama Amma a yau sai gashi ta karyata kanta domin kuwa duk da ciwon da take ciki bai Hana ya saka mabugi ya Bata Kashi ba har sai da Anam ya kwacw ta
Tun daga wanna Rana zaman Nimra ya dawo Gidan su Abinda Kuma yayi matukar takura ta Domin kuwa ko da mahaifin ta Yake da Dan rufin asirin sa to gidan Anam yafi Nasu gashi Babu Shiga Babu fita
Mummy Nina Kuma da taji shirun Nimra yayi yawa ta tambaye anam Wanda ya ce Mata tana gidan su Kuma ya kafa iyayen ta shaida matukar ya nemi cikin sa yarasa to ba zai yarda ba ...
Ina wuta ta jefa shi ta soma auna mishi Ashar da tijara kala kala amma ya faske Yana Fadin
"Ni fa wallahi aure na zanyi mummy na huta da wannan Bala in dakika ja min Nimra Kuma jira kawai nake ta haihu na Karbe Dana ko Diya ta na sallame ta don Sam bamu da gami hanyar jirgi daban da ta mota...
A Ranar ne kuma mummy ta nufi gidan su Nimra da son ta mayar da ita dakin ta Amma baffan ta yace tayi hakuri mijin ta yace a Barta har zuwa lokacin da Yake ganin kamatar ta koma din .
Duk yadda taso tafiya da Nimra Amma baffan ya kafe Dole kuwa ta bar shi Amma fa cike take da takaicin anam akan wanna matakin da ya dauka Akan Nimra inda tayi nufin tata mishi Rashin kirki Mai daraja.....
To Kai Kuma anam kaga ta Kan ka wane irin Rashin daraja ne wanna ? Wallahi ka samu wata kawai kayi ciki da ita ka rabu da su mace Babu kula yaushe ta Zama mace? Nimra Kam tsautsayi ne ya Kai ka dauko ta duk da mun fahimci Dole akayi maka to samawa kanka mafita Yasin 🙄
_Kirkirarren labari ne da Bai shafi Rayuwar kowa ba kuskure ne babba danganta kai ko wani dashi babu mafi cancantar suyi suka akan labarin irin taurarun cikin labarin Wanda kuka San Babu su a zahiri to kar wanda ba cikin jaruman labarin Yake ba yace don shi ko don wani akayi Hakan jaruman cikin labarin ne kadai suke da damar sukar marubuci akan don me zai fallasaww duniya sirrin su_
_Fatan Aminci ne ga Amina baiwar Allah wacce Allah ya jarrabe ta da bauta Kashi Kashi Ubangiji ya jikan ki ya Baki ladar jinya Hawa Hawa_
_Gaisuwa ne ga dukkan masoyan Rubutun gidan iko musamman Wanda suka fahimci manufar Rubutun nawa Ubangiji ya amfanar damu alherin Rubutun kuskuren ciki Kuma Ubangiji ya yafe Mana_
_MUGUNTA_
💖
.................Mayra ta iso gidan cikin hadaddiyar motar ta wacce kallo Daya zakayi Mata ka yarda kudi suna magana sai dai ga Wanda Bai fahimci ta yadda suke maganar ba.
Mayra fara ce kyakkyawar gaske wacce ta kallo daya zaka yarda Mayra Mai kyau ce . Fara ce Mai kyakkyawar fuska Mai dauke da idanu masu kyawun zubi ga dogon hanci da giraren idanu masu tsari sai Ramin kyau a gefen fuskar ta wato dumful sai Dan karamin Baki Mai dauke da jajayen labba tamkar ta shafa musu Jan Baki Amma Haka Halittar ta ce .
Mayra ba Yar garin katsina bace Yar garin kaduna ce kuma Diya ce ga tsohon gwamnan kaduna saukakke. Iyayen ta suna can kaduna Amma suna da gida a Nan katsina don Haka in Mayra ta zo katsina gidan su take sauka
Tun lokacin da Mayra taga Hakim ta Rikice duk da tarin maneman ta Ya'yan wasu masu Rike da madafun iko Amma Mayra babu ajandar aure a tare a tare da ita duk da ma tarin maneman Nata Bata ga Wanda yayi Mata ba Amma ganin Hakim ya tarwatse Mata tanadi taji duk duniya Babu wani in ba shi ba har ta Kai ta sanar wa anty Nina ta Kuma Bata tabbaccin in dai hakim ne damuwar ta to anyi an gama Amma har yau da ake shirin Shiga watanni uku cur Babu wani gamsasshen Bayani shine ta iso da son Jin inda aka kwana...
Ta faka motar ta fito cikin shigar doguwar Riga wacce Bata Boye Mata tsarin Halittar ta ba don in ka zuba Mata ido da kyau ma gaban Rigar Wanda Yake da raga raga zaka iya hango kirjin ta Wanda Yake saye da farar bra da sashi sashi na jikin ta Banda bra din ma da tsab zaka ga tsayuwar kirjin nata...
Sanye take da takalmi high Hil Mai madauri silver color sai Yar karamar jaka itama silver color sai siririn agogo Mai hannun sarka da Yake a farin hannun ta yayin da ta yiwa gashin ta dauri Mai burgewa duk Bata daura Dan kwalin ba yafa shi tayi kamar gyale hakan zai baka damar ganin gashin nata soasai
Kamshin turaren ta kuwa tamkar wacce akayi barin turaren a kanta don tun daga parking space na cikin gidan ya jiyo shi
Hakim Yana dakin sa Wanda Yake Dan da parking space din yajiyo kamshin wanda ya sa shi ya mike Yana dage labulen tagar dakin nashi da son yaga waye ? Duk da ya San ba Zai wuce shegun bak'in mummy ba Wanda ya tsana fiye da zaton Mai zato don ya Rasa makasudin zuwan Nasu tunda ya San ba wani kasuwanci take ba bare ace ko hajar ta suke zuwa siye
Yana dage labulen ya hangi Mayra wacce shigar ta ta Kara darsa Mishi tsanar ta....
"Don Allah dubi shigar yarinyar Nan Bata da maraba da tsirara
Ya fada ba tare da ya Shirya magana Akan ta ba don Allah yayi shi da tsanar mace Mai nuna tsiraici . Yana son ganin mace cikin shiga ta mutunci da kamewa . Mace wacce ta San ita mace ce Mai daraja sai yaji lallai duk Wanda ya Dace da mace kamammiya lallai yayiwa Ya'yan sa Uwa ta gari shiyasa yake tausayin brothe din sa anam Wanda ya Gama fahimtar mummy Kam sai a Hankali....
Yaja tsaki ya saki labulen ya koma Yana karbar Ruwan coffee Mai zafi ya soma Danna wayar shi wacce katon hoton Halimatu ya mamaye screen din wayar ya zuba Mata ido kafin ya sumbaci hoton ya Kuma Danna Mata Kira ....
Mayra ta shiga gidan tana taku irin na Mata masu aji..kamshin ta ne ya sanar da mummy zuwan ta ta Kuma fito tana Fadin
"Wannan kamshin Mayra Aisha ne Yar Halak kink'i ambato yanzu nake maganar ki a Raina Ashe kina tafe .....
"Kar dai har an kashe Boos anty?
Mayra ta tambaya cike da doki da ci da zuci ...
"Me kike ci na baka na zuba ne Mayra ? Ni fa nace Miki anyi an Gama ....
"Na kasa nutsuwa ne anty tun daga Ranar Nan na kasa Zama lafiya gayen ya tsaye min A Rai ne ko Babu komai yanzu Nazo muga juna naji Kuma irin yadda yake Sona....
"Uban yaron Nan fa a hannu na Yake Mayra sai abinda nace da shi bare Hakim da baya tsallake maganar Uban sa don Haka Bari na Kira shi yazo Nan ku gana tunda na kula dai Mayra kina Dab da zautuwa...
Mayra ta zauna akan kujera tree seater tana Dora kafar ta Daya Kan Daya tana kada su tana aje key din motar ta da Jakar ta s saman center table tana Fadin
"Ai anty bature yayi gaskiya da yace love at first sight wallahi Naga hakan don Allah Kira min shi ko kollon sa nayi na Rage radadin da Yake zuciya ta ....
Nina taja wayar ta tana kiran wayar hakim Wanda ta samu laying nashi Yana busy sai waiting Yake nuna Mata ..
Fiye da mintuna talatin Nina tana Kiran wayar hakim Yana ta busy...
"Yau dai bashi da Aiki to wayar ta mecece Haka ?
Ta mike tana Kiran Dan ladi Mai wanki tace ya Kira Mata Hakim a dakin sa
Hakim Yana Zaune Yana waya da Halimatu Wayar da ake kona kudi b kad'an ba wacce ake kwashe fiye da minti sitting ana yin ta Kai har wucewa ma...
Dan ladi ya sallama a kofar Yana Kara sallama
Hakim ya mike ya fito Yana duban Dan ladi wanda ya isar da Sak'on mummy na Kiran shi da take
Ya jawo kofar ya na Kare da wayar shi suna ta misayar Kalamai shi da Halimatu
Yana shiga ne yace ta Bari zai Kira in ya fito.
Ya shigo da sallama ya zauna Yana Fadin
"Mummy kina Kira?
Ya fada fuskar shi Babu yalwa don irin yadda yaga Mayra ta tsare shi da idanu shi kuma tun Ranar da ya iske su ya Kuma ga irin kallon da take mishi Yaji ya tsane ta matuka Gaya don Sam bai ji mutuniyar kirki bace bare Kuma shigar ta da irin adon ta na nuna tsiraici....
"Eh Hakim dama Mayra ce Zaku gaisa gata nan ...
Ya juyo ya kalli Mayrar da tsukakkiyar fuska Babu sassauci kafin ya mayar da kallon shi ga mummy Yana Fadin
"Wace irn gaisuwa Kuma mummy? Ya sake kallon Mayra Yana Fadin
"Ya kike?
Tayi murmushi tana Fadin
"Lafiya Lau ya kake,?.
Yana Gama fadar hakan ya mike zai wuce Nina ta tsayar da shi tana Fadin
"Kai bana son hauka kaji. Gaisuwa irin ta fahimta nake so kuyi don tuni