lamarin Dan ta sai ta ganni a kamarun? Ai kawai muyi Mata ADDU AR Allah ya tsare ya maido ta lafiya....
"A a Bello tafiya fa ta Kama ka tun yanzu an soma ga zance ga magana ina ga Kuma wani Abu ya faru? Ai duk shiyyar Nan Babu mu Babu sauran zaman lafiya Ni in ka dawo nace Zan mayar maka da kudin zuwa Amma ai kaima ka San in suka ga zuwan ta garin Nan wallahi Rike Dada zasuyi kaga wata Shiga ukun ce ta same mu in bamu bi Bayan Hamza ba ai zamu Bayan dada .....
A Haka dai Baba Headmaster ya ci karfin baba Bello har ya shirya tafiya kamarun. Kwana biyu da yin hakan Baba Bello ya dauki hanyar kamaru...
Tunda Baba Bello ya tafi na Samu Dan sauki sauki don na San ba Zai dawo ba sai da Dada Kuma ko ba komai duk Rashin mutuncin sa dai ba zai Bari Dada tayi mishi Bataan dabo ba
Na samu sauki kad'an Amma Kuma zuwa yanzy ji nake Babu abinda nake so irin sanin ta yadda kaddarorin Baba na suka fara har kaddarar ta Kara Hawa da mahaifiya ta
Kwanaki bakwai cur kafin baba Bello ya iso garin katsina Amma Kuma shi kadai ya taho Babu Dada Babu wani labarin ta...
Na tarbe shi ina mishi sannu da zuwa Bai Amsa ba sai faman Jan tsaki Yake tamkar zai tsinke hsrshen sa
Ban Isa na tambayi damuwar shi ba bare nabi kadin tsakin bare kuma nace Dada zan tambaya ...
Ina makure naji Baba Headmaster ya shigo Yana Fadin
"Yo Bello ya Nagan ka Kai Daya? Ina dadar ne ko tace ba zata taho bane?
Baba Bello ya Kuma Jan tsaki Yana Fadin
" Sai da nace ba zanje garin Nan ba sa adu ka matsa min kaja nayi asarar kudin mota ta to gashi Nan naje da kyar na iya lalubo muhallin Hamza Wanda nasha da kyar dock nima da kafuran nan sun kula dani da ban tsira ba sai kuma gashi wai Amma Dada Bata je can ba matar sa kahira kawai na Samu a gidan Amma shi hamzan Yana can wurin iyayen matar sa wai ana mishi magani ciwon kafar sa ne ya dawo Amma kuma Wai Dada Bata je ba Ni kuma na san iyayen matar Hamza ne zasu hada da Dada da Hamza su Rike kuma kunga dole suyi hakan tunda namu ne ya jawo mana. Wannan bala in Allah kadai ya San Halin da suke ciki a yanzu....
Na mike tsaye cike da wani matsiyacin tashin Hankali na Dora hannaye na saman kaina ina Shirin kwarara ihu Amma tamkar wacce aka sakawa padlock aka datsewa Baki Haka na kasa ko motsi....
Kan kace me?. Sai ga Yakumbo mariya ta iso tana kuka tana fadin
"Ni Kam Hamza ne ya cuce Ni wallahi kuma ba zan taba yafe mishi ba gashi Nan ina Shirin Rasa Uwa ta
Gida ya rude ana ta koke koke yayin da Baba Headmaster shi da Yakumbo mariya sukayi Shirin wucewa kamarun Don a yanzu kam Basu ga ta Zama ba
Washe gari kuwa Baba Headmaster da Yakumbo mariya suka dauki hanyar kamaru duk da Baba Headmaster yaso su koma da baba Bello Amma yace ba zai je ba su dai suje
Isar su Baba Headmaster da Yakumbo mariya kamarun Kai tsaye Suka Isa gidan Hamza inda Suka same shi kwance karkashin cikin ciwo yayin da dayar kafar da batayi ciwon ba itace ta kamu da ciwon ga Kuma Halin Rashi Hamza Yana cikin jinya matuka Gaya Amma da Yake ba ta shi din suke ba sai suka shiga tuhumar Dada da son Sanin inda ta lakafe...
Sophia wacce take ta kuka musamman da taga Halin da mijin nata Yake sai Kuma tsoro yayi matukar Kama ta tunda taga zuwan baba Bello taji tashin Hankali Mai tsanani ya kamata don in har akwai abinda take tsoro to Bai wuce Yan Uwan Hamza ba don gani take kashe ta zasuyi sai Kuma gashi yanzu taga wasu daga cikin dangin nashi sun Kuma zuwa kwanaki kad'an da zuwan wancan ta tabbatar da ba lafiya ba
Hamza da Yake cikin Halin jinya ya Rame sosai ga Halin Babu ga ciwo ga Kuma wani tashin Hankalin na tahowar Dada Kuma Bata zo ba sai Al Amarin ya dugunzuma shi yaji ina ma Yana da lafiya? Da a yau duk inda dada take sai ya Nemo ta a cikin garin kamarun Amma ina ! Kafa Bata takuwa sai da hikima sai da dabara ...
Sophia kuwa tunda taga fadan da Yakumbo mariya ta iso take ta lafe ta kasa ko motsi Mai karfi don tsoro gare ta matuka Gaya
Wani makocin Hamza ne da Yake da tsananin kirki shi ya Shiga gaba da su baba sa adu aka shiga cigiyar Dada har a kafafen yada labarai na babban birnin yawunde aka Shiga cigiya Babu ji Babu gani Amma shiru Wai Mai kalangu ya fada Ruwa
Kwanaki goma Sha hudu su Baba Headmaster da Yakumbo mariya sukayi a kamaru Babu wani labari Dole suka juyo gida Nigeria suka Kuma baro Hamza bawan Allah cikin Halin jinya Kuma Babu wani tartabin taimako ko saka lalurar shi ta Zama ta su Babu ma Wanda ya Kuma bi ta Kan shi bare tuna Yaya zai Kare ?
Yakumbo mariya kam kuka ta iso gidan tana Fadin
"Na Shiga uku na lalace Hamza yaja Mana janhurun masifa Dada na can ta bace a garin kamarun Kuma Babu ko shakka siddabarun arnan Nan ne da ya dafewa Yar su
Kan kace me ? Gida ya cika dankam da mutane ana ta faman jajantawa juna dada ta b'ace Dada ta b'ace shine kawai abinda ake ta shelantawa Amma maganar su tuna da Halin da bawan Allah baba na Hamza Yake ciki ma Babu don suna ganin shine ma yaja musu hakan don Haka Babu tausayin Halin da Yake ciki bare ayi nufin taimakon sa sai ma kullata da Jin ciwon batan dada da abinda zai faru Kuma da ita .........
Ikon Ubangijin musulunci Kuma Haka kuke? To Allah na Nan Hamza Allah ya kawo maka sauki don alfarmar ANNABI da Al kur ani Amma zumunci Kam ya Zama abinda ya Zama a wannan marrar Dada ina kika makale ke kuwa?
Wannan shine karshen book one kuma karshen free Page sai dai mai bukatar ci gaban 2 3 @ 4 zai tura 1k akan wannan account din 1780003378 Eco bank ko kuma katin MTN akan wannan layin 08035191669
Gidan iko 08035191669
✍🏻 Alkalamin GIDAN IKO💖
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng