na Gane yadda yarinyar Nan ta dauki aure ba Haka Yake ba a zahiri . A wurin ta aure Bai barranta da Rayuwar ta a gidan su ba bare ta San farali ko mustahabbi. Da na nutsu ma sai na Gane yarinyar Nan so take ta saka Ni a Rayuwar bariki don Sam Bata son nace Zan tab'a ta Ni Kuma gani Allah yayi Ni Mai son kulawa da tarairaya. Amma da nacewa mummy ga Halin da yarinyar Nan take ciki sai tace shifa aure kowa Yana da yanci Kuma don takamar Kaine Mai gida ba Yana nufin ka tursasawa Nimra abinda Bata bukata ba yaya zanyi Hakim? Yanzu Haka yunwa nake ji Amma na tabbatar da Bata iya girka min ko Ruwan shayi in dai ba Ni Zan girka ba sai dai na sa Mai Aiki....
"Gaskiya Babu kyautawa Yaya Amma kayi hakuri gaskiya Ni shawarar da Zan baka kawai tunda mummy tana goyawa yarinyar Nan baya to Rabu da su ka nemi yarinya Mai mutunci wacce zata tssre maka mutunci sai dai aji kayi auren ka ka manta da su...
Dr Anam ya dubi hakim Yana Fadin
"Good idea my brother wallahi na gamsu da wannan shawarar Amma Nima Zan baka wata shawara Hakim wallahi Kar ka yarda mummy ta Shiga cikin lamarin auren ka don wallahi in ka Bari ta ce irin yadda ta zaba min Nimra kaima itace zata zaba maka to gidan jiya ne za ayi Ni na Rasa hikimar ta da Hakan ...
"Ya zamuyi da mummy Dr? Sai hakuri Amma gaskiya Ni bakin Nan nata ne suke Bata min Rai kullum ka Shigo gida sai ka iske bakin mummy wasu ma ka Rasa ta inda ta San su ....
"Ta na wurin Hakim Banga laifin ta ba laifin Daddy ne da Yake tafiyar shi Abuja ya Barta sai ya share watanni shida bai zo katsina ba inda Yana Nan za ayi hakan ne?....
"Daddy bashi da laifi Yaya Dr Babu yadda baiyi ba Akan ta Bishi su tafi Amma tace ba zata Bishi ba....
"Wallahi laifin nashi ne Hakim in mace tace ba zata bi Ra ayin miji ba mataki ya kamata ya dauka don ya nuna Mata shine shugaba Kuma jagora ko Ni da kaga Ina bin yarinyar Nan a sannu don nabi hanyoyin da zata gyara in Bata gyara ba wallahi Zan fidda ta a Rayuwa ta ta tafi ta bar min gida na don Haka laifin Daddy ne duk abinda mummy takeyi kana auren mace Amma kayi wata shida baka San me take ciki ba?...
"To muyi musu ADDU A kawai muje kaci abinci tunda kace yunwa kake ji...
Suka fito daga motar suka jera suna tafe suna Kara tauna matsalar mummyn tasu .
Suna shiga falon kuwa sukayi kicibus da abinda basa kauna wato bakin mummy kusan su biyar Zaune kowace da Shiga ta tashin kirki wata kirji a bayyane wata Babu Dan kwali to baza gashi kowace dai da kalar shigar ta....
Suka soma rige rigen Rufe jikin su yayin da Mayra ta zubawa Hakim ido shine gayen da take fadawa anty Nina Amma Bata Gane ba . Tun da tayi mishi kallo Daya ya sace zuciyar ta ta Kuma kasa zama lafiya sai a yau da ta Kuma Kare mishi kallo ta Gane Ashe Bata ga komai a tsarin kyan sa ba....
Suka soma ficewa daga falon daya Bayan Daya Amma Mayra Bata ko motsa ba inda Dr Anam ya soma fada Yana Fadin
"Dubi ka gani hakim ? Don Allah dubi wanna abun meye Haka ?
Nina da take can uwar Daki ta soma jiyo muryar Anam Wanda ta San sai shi din..
Ta fito da sauri inda ta ganshi sai masifa Yake yayin da su Asma suka fice sai da Mayra wacce idon ta Yake Kan Hakim....
"Kai fitinanne meye Kuma kake min kwakwazo?
Kyakkyawa ce fara tas Mai tsarin jiki Mai kyau don ba zakace itace ta haifi Dr Anam ba . Tsab shekarun ta suka buya a jikin ta komai nata mai kyau ne tun daga dogon gashin ta zuwa murjajjen jikin ta da kirjin ta Wanda har yanzu Yake kyam ga Kuma hutu da kulawa da jikin Yake samu sai tayi nasarar lashe shekarun ta kai ba zaka ce itace Uwar Dr Anam ba sai dai ko yayar sa ....
Ta dubi Mayra tana Fadin
"Ina suka tafi ba dai sun tafi ba?
Mayra ta sauke ajiyar zuciya tana Fadin
"Ina Jin fa sun tafi....
Ta dubi hakim da Anam tana Fadin
"Ku kuma daga Ina kuke Haka kamar Wanda aka aikawa katin gayya? Ko kuwa yauma karar ka kawo Kai sarkin tsegumi? In ma karar ce Nimra ta tafi Egypt duba marar lafiya....
"Kuma yanzu saboda Allah mummy in har nayi magana akan hakan ace tsegumi? Dama Haka ake Ni ban Isa ta fada min zata je wani wuri ba sai dai naji daga bakin ki?....
"To ba gashi Ni na fada maka ba? Kai dai tsegumi baya maka wahala wallahi akuri sarkin aure takobi sarkin gida...
"Amma mummy har zata tafi bata sanar mishi ba? Cewar Hakim
"Kai tana da fa yancin ta a hannun ta Kar ka Taya mishi ku tauye yarinya tashi kuje abinci na Nan a darning na San dai shine matsalar ku kuje na gaji da magana...
Anam ya mike ko uhum Bai sake cewa ba ya fice inda shima Hakim din ya mara mishi baya . Amma sai yaga Anam ya fice daga gidan Bai iya tsayawa yaci abincin ba....
"Kayi hakuri Yaya Dr ka tsaya kaci abinci....
"Na koshi ne Hakim Bari kawai na wuce gida Ruwan shayi kawai Zan iya Sha ....
Ya figi motar a guje ya fice daga gidan inda shima Hakim din Bai Kuma bi ta Kan abincin ba ya wuce part din sa....
Da sauri Mayra ta Isa ga Nina tana Fadin
"Anty waye wannan ? Waye shi? Shine fa Wanda nake fada Miki?...
Nina t kalle ta tana Fadin
"Anam ko Hakim?
"FARIN dai Mai sumar Kai ....
"Hakim ne....
"Wallahi shine Wanda na fada Miki nayi tuntube da son shi ni wallahi wannan ce kawai alfarmar da zakiyi min kin sallame Ni ....
"Amma tsaya tsaya me kike nufi Mayra? Son aure kike mishi ?...
"Sosai anty Nina wallahi ban tab'a sanin bature Yana da gaskiya ba da yace love at first sight ba sai akan Hakim ...
"Kar ki damu Mayra inadai Hakim ne damuwar ki to an Gama da ita . Hakim ba Ni na Haife shi ba matar da honorable ya auro ce ta Haifa mishi shi ta Kuma mutu . Ni na Rike shi har ya girma duk da ya Gane ba nice mahaifiyar sa ba wani lokaci yana son bani ciwon Kai Amma yadda nake iko da Anam Haka nake da iko da shi tunda Uban su ma sai yadda nace dashi bare su in dai hakim kike so to na Baki shi daga yau kike kallon shi a mijin ki mallakin ki don Babu Mai ja da Hakan...
Kwanaki kusan bakwai Hakim Yana son zuwa wurin Halima Amma Aiki ya saka su a gaba musamman ma yanzu da suke Shiga kananun hukumomin jihar katsina Wanda suke fama da matsalar Rashin tsoro. Halima na makale a Ransa bashi da fatan da ya wuce ya Sami kanshi yaje gareta yaji matsayar da ta sama mishi
Makonni uku cur Nimra ta kwashe a Egypt kafin ta dawo Kuma ta dawo gidan ta Lau lafiya Babu kuma wani Bayani bare tacewa Dr Anam kaji kaji.
A cikin Satin da ta dawo ne Kuma ya samu takardar gayyata daga asibitin garin Lagos akan duba wani Marar lafiya kasancewar shi kwararre akan abinda ya shafi cikin Dan Adam da abinda ya shafi k'oda da hanji hanta da kuma hunhu don haka suka gayyace shi don sun hada masu wannan cutar da dama a asibitin gashi Kuma Basu da masana wannan fannin
A Ranar yayi shiri ya wuce Lagos duk da Bai San adadin kwanakin da ayyukan zasu ja shi ba.
Saukar shi garin Lagos misalin bakwai na dare ya wuce a motar sa a agege inda ya wuce wani park na Mata kyawawa Yan good evening....
Abin ya bashi mamaki don duk da Yake Jin ana fadar akwai ire iren wadan Nan wuraren na Yan good evening Bai tab'a zaton da gaske bane sai a yau da ya gani da idon sa.
Ya soma karewa matan kallo sunci Uban ado da daukar wanka na sukari da son a samu Mai tayawa .
Ya faka motar a gefe yana kallon motocin da suke tsaya su darji matan da sukayi musu yayin da idon shi ya sauka Akan ta . Take komai nashi ya tsaya cikk
Ya zuba Mata ido Yana kallon ta shigar ta da kyawun ta ya haske sauran matan da suke wurin tamkar ma Zara ce a cikin taurari...
Yana kallon mazan bariki da suke ta kawo Mata Hari Amma ABIN MAMAKI ko ta tada Kai ta dube su sai fa dannar wayar ta da take
Dole suke kyale ta suna matsawa birnin gaba..
Take yaji mood din sa ya motsa mutum ne Mai son hutawa don Haka yarinyar ta cije shi duk da ya kula tana da aji ba kamar sauran ba.
Ya fito daga motar Yana Jin a yau Kam zai zuba ya kwashe Akan harkar ...
Ya tunkare ta da tabbaccin zai Shawo kanta....
"Hey beautiful beb...
Ya fada da son ya zabaro hankalin ta gare shi ya Kuma yi sa ar hakan cikin mamaki yaga ta dago kanta tana sauke idanun ta Akan shi inda yaji wutar lantarki taja shi ...
Ta dube shi tana Kare mishi kallo a nata bangaren ma wani Abu taji yaja ta har ta zuba mishi ido cike da Jin wani Abu...
"Ya Mika Mata hannu Yana Fadin
"Kina da kyau yarinya ina son na siyi wannan Daren dukkan shi da duk irin kudin da Kika tssgawa kanki....
"Anya kuwa za ka ya siyen Daren Nan gareni?..
"Sosai kuwa muje mota na nuna Miki zahiri...
Babu musu ta mike ta Bishi zuwa motar tashi Mai daraja ta land Rober . Suka shiga Yana Kare Mata kallo musamman kirjin ta Wanda ya tafi da dukkan nutsuwar sa . Ya jawo brift case din sa ya Dora Mata Akan cinyar ta ya zuge zuf din sai ga tarin kudaden kwance a ciki..
Ta dube shi tana murmushi....
"Kana zaton wannan kudin zai Isa ya siyi Daren kyakkyawa kamata Anya banyi arha da yawa ba?....
Shima yayi murmushi Yana Fadin
"I have my account I will send any more...
"Ok last go...
Ya tashi motar suka wuce ya Kama hotel Mai kyau da tsada sukayi masauki ya Zauna Yana Kare Mata kallo....
Sanye take da Riga wacce ta fito da duk Surar jikin ta musamman ma kirjin ta da shafaffen cikin ta kanta Yana dauke da kitso Wanda Yake na zallar gashin ta ne ba na Kari ba . Dogon gashin ya watsu a kafadun ta Babu abinda Yake sai kyalli. Wandon jins ne a jikin ta Wanda ya taimaka wurin fito da kuturin ta ya kamata Tak dirin ta ya fito sosai ta yadda Mai kallo zai ganshi
Bakin ta dauke da cingam tana tauna cikin salo Mai daukar hankali . Ya shagala da kallon ta zuciya na kitsa mishi ina ma ba a wurin Nan ya ganta ba da hakika auren ta zai fito nema Amma duk da Hakan baiji ya fasa daga kudirin auren ba....
Ta dago kanta taga ya zuba Mata ido
Tayi murmushi tana Fadin
"Me yake burge ka da kallo na? Ba ka siyi komai nawa na wannan Daren ba?
Ya mayar Mata da murmushin Yana Fadin
"Zuciya ta ta soma tunanin na aure ki don ba da wasa son ki ya Kama Ni ba....
Tayi maza ta toshe bakin ta da Hannun ta biyu kafin tace
"I can't not married you
Ya lura ba sosai take Jin hausa ba tafi Jin turanci akan hausar don mafi yawan maganar da turancin suke yin ta ...
"Me yasa ba Zaki iya aure na ba? Bani da tsarin da kike so ne?
Ta kada kanta
"Kawai dai Babu tsarin aure a Rayuwa ta wannan Rayuwar tafi min Dadi....
"Ni Kuma nayi Miki alkawarin in don kudi ne zanyi ta Baki su matukar dai Zaki yarda ki aure Ni.. tukuna ma shekarun ki nawa?
Tayi Jim kafin tace mishi 17.
Ya yarda da maganar ta don yarinya ce wacce take cikin kuruciyar ta....
"Ina iyayen ki ne da suka barki kina wannan Rayuwar duk da na kula a addinin ku kamar...
Ta dube shi tana Fadin
"Ka duba lokaci fa Yana tafiya alhalin Ni kudi na zaka biyani ko da baka tab'a Ni ba har gari ya waye...
Ya mike Yana Fadin
"Bari nayi Mana Oder abinci kafin nayi wanka don ina da gajiya don ni ba Dan Nan garin bane...
"Daga wane gari kake?
Ta jefa mishi tambayar
Ya Bata amsa da cewa
"Katsina!
Tayi shiru tana Kara maimaita sunan garin
"Ina son garin Nan
Ta fada cike da alhini..
"In Zaki yarda ki aure Ni can Zaki Zauna...
"Mu bar maganar Nan ta fada tana mikewa akan kujerar tree seater tana danna wayar ta...
Ya Kira layin restaurant yayi musu Oder abinci da abin Sha kafin ya Shiga wanka
Yana cikin toilet din ne Mai kawo abincin ya iso ta karba ta mayar da kyauren ta Rufe.
Da sauri ta jawo Jakarta ta zuge ta fito da wani a cikin leda ta kwance ta bude abincin ta marmasa kafin ta mayar ta Rufe ta mayar da ledar a cikin Jakarta ta zuge
Ta koma ta kwanta tana danna wayar ta har ya fito daga wankan itama tace zata yi duk da a cikin kwalliyar ta take
Ta fito wankan ta bude Jakarta ta fito da kayan shafa ta soma shafa yayin Dr Anam ya Gama sallar sa ya Zauna Yana kallon ta sanye da wata Riga wacce Bata Boye koman ta ba abinda ya Kuma ruda shi har ta Gama inda yaga sarkar da take makale a wuyan ta ta cross wacce ta cire ta saka cikin Jakarta
Ya bude abincin don ya Gane manufar ta ba zata kwanta da sarkar cross din ba Wai don ta girmama shi ...
Ya turo Mata abinci ya Kuma zauna dab da ita Yana kallon ta tayi maza ta kada mishi kanta kafin tace mishi Bata cin abinci Mai nauyi yayin kwanciya don Haka sai ta soma Shan Madarar da aka hado tare da fruit din dake cikin Kayan...
Ya yarda da abinda ta fada don Haka shi ya soma cin abincin Yana kallon ta tana taunar tuffa komai nata burge shi Yake....
"Baki fada min sunan ki ba fa?
Ya jefo Mata tambayar...
Ta dube shi tana Fadin
"Heeling gabros...
Ikon Allah Dr Anam? Amma dai Bari muga meye heeling ta zuba maka a cikin abincin? Allah ya sa ba guba bace wacce zaka haure. ABIN DA MAMAKI Haka salon nashi ya taho Amma mu nutsa don gsno Mamakin....
_Hakkin mallakar ma abin kiyayewa ne kowane Abu Yana da mamallakin sa Babu Kuma Mai son a daukar mishi kayan sa ba tare da izinin sa ba mu kiyaye hakkin juna sai mu Zauna lafiya_
_Fatan alheri ne ga dukkan Al Ummar musulmi musamman Wanda suke kwance Babu lafiya gida da asibiti birni da karkara Allah ka basu lafiya_
*_GAMO_*
💖
.............."Heeling gabros? Ya maimaita sunan Yana Mai zuba mata idanu da Jin hakikatan Bai tab'a Jin son wata mace kamar wannan kyakkyawar yarinyar da yayi tuntube da son ta a garin Lagos wacce baya ko tantamar kaddarar haduwar su ce ta sa shi tako garin Lagos...
"Sunan ki ya Dace da kyakkyawa irin ki ban San me yasa kike burge Ni ba komai naki yayi min daidai da tsari na ....
"Ban tab'a fadawa kowa cikakken sunana ba saboda Kar yace zai neme Ni . Amma why Kai na sanar da Kai ? Ban tab'a siyar wa kowane namiji dare gaba Daya sukutum ba Amma why Kai na yarje maka? Ka Sani ba kowane namiji nake kulawa ba Amma why Kai naji Ina son na saurare ka?...
Yayi murmushi Yana Mai Kara matsar inda take ya ture abincin Yana Mai Rike Hannun ta Yana kallon tsakiyar idon ta itama ta zuba mishi ido suna kallon kallo...
"Babu mamaki zukatan mu ne suka yarda da juna. Babu Mamaki Kuma Ni din Nasha banban da sauran mazan ne. Ki yarda Dani Ina Miki wani irin son da ban tab'a yiwa wata mace ba. Kiyi min alkawarin na Raba ki da wannan Rayuwar muyi aure....
"Wannan Rayuwar da kake magana Ra ayi na ne ba komai ba. Ina son kudi ne shine kawai yasa na ke yin ta. Na Saba da Rayuwa Mai Dadi ne sai Kuma na Sami Kai a Halin Rashi shiyasa kawai nake wannan Rayuwar....
"Ina da kudi Kuma Zan wadataki da duk abinda kike so ke dai ki yarda na Aure ki....
"Mu bar wannan maganar my parents ba zasu Bawa Muslim aure na ba Kuma Nima ba Zan aure ka ba ....
Ya Rike Hannun ta Yana Kare Mata kallo musamman Rigar jikin ta wacce ta fito Mata da koman ta ...
"Kina da tausayi kuwa?
Ya tambaye ta tayi saurin girgiza mishi kanta...
"Zaki barni cikin kewa da alhini idan Kika nisanta kanki Dani. Ban taba yarda love at first sight ba sai a kanki ....
"So fa karya ne tuni na yarda da Hakan. Da so gaskiya ne da masoya Basu Sha wahala ba.da ba a ci amanar soyayya ba....
"Wannan Kuma daga masoyan ne wani ne bai dauki soyayyar da gaskiya ba Amma Ni ki gwada Ni Zaki Gane ba irin sauran bane...
"Nace maka mu bar maganar Nan bacci nake ji ...
Ya fada tana kwance Banda din da ya daure Mata dogayen kitson ta kafin ta dube shi tana nuna mishi agogon wayar ta....
"Gaskiya na yarda kana da kudi tunda gashi har kusan 12:00 Amma baka nemi ka fanshe kudin ka ba abinda mazan bariki Basu yarda da shi ba kensn. suna yin komai da wuri don su more kudin su....
"Zan iya karar da wannan dare muna fira in Kuma biya ki kudin ki kafin na sake siyen wani Daren na biya ki....
"Ba zan iya baka darare biyu ba don a tarihi na ma bana iya bada dare duka Don