Safiya don wallahi ba zanyi rantsuwar banza tunda Dubu Bata ji kashedin da nayi Mata ba to kun kaini kwano ...
Baba Headmaster ya juya inda goggo Dubu take tana kallon Dada cike da Haushi da takaici....
"Wato Dubu na Gama Gane kece ke son Shiga tsakani na da mahaifiya ta ko? Dukkan wani Abu da Ranta zai baci kece ke jswo min shi . To bari kiji Akan ki ba Zan yarda na fusata mahaifiya ta ba wallahi Duka ki bata hakuri ki Kuma tabbatar Mata da wannan shine karon karshe da Zaki sake tofa wani Abu akan Halima....
Goggo Dubu ta motse Baki tana fadin
"Ikon Allah Ni fa Babu abinda nace daga ta kawo Allon Zayyana nace Anya Babu Zuk'u a cikin wanna sauka shikenan fa cibi ya Zama Kari Kari Kuma ya Zama kababa Allah ya Baki hakuri ...
Tana fadar hakan ta juya Bata Kuma sauraren su ba.
Baba Headmaster ya dubi Dada Yana Fadin
"Kiyi hakuri don Allah Dada nayi Miki Alkawarin daga wannan ba zata sake ba....
Dada ta dube shi ba tare da ta tanka ba ya Gama jera Mata kalaman Rarrashi ya mike Yana Mata sallama ta dube shi tana fadin
"Iyakar matakin da zaka dauka kenan sa adu?....
"Zan Kara wani Dada musamman idan Dubu ta Kuma Shiga harkar Halima....
Dada ta shigo dakin ta same Ni don naji duk abinda ya faru inda Kuma na Gane Tayar da Hankalin da nayi to tamkar Tayar da Hankalin Dada ne nata ma yafi nawa ....
"Kiyi hakuri Dada ki rabu da goggo Dubu abinda ya faru Kuma ya wuce....
"Kinci abincin?
Ta tambaya nace Mata eh duk da kuwa ko bude shi banyi ba don Sam bana Jin yunwar...
Ina Gama sallar isha I na kwanta don kaina sai ciwo Yake ga zazzabi da nake ji
Kafin wayewar gari sai gani Sharkaf cikin Rashin lafiya zazzabi da ciwon Kai har da haraswa
Dada ta Rikice tana ta jawo min magunguna na samu paracetamol na Sha na koma na kwanta....
Dada ta nufi wurin jauhara ta samo min maganin ciwon Kai inda ta ci Karo da goggo Dubu tana hada kullun wainar ta ...
"Kai Usman maza Shiga makaranta ka kiro min sa adu kace maza maza yazo
Yaron ya fice Kiran baban su sai ga su a tare da Baba Headmaster....
"Wannan shine matakin da ka dauka Akan matar Nan? To in ma baka Gane abinda nake nufi Bari in bude maka bana son ganin matar Nan a yanzu ta matsa daga Nan har zuwa lokacin da Zan huce in Kuma ba Haka ba Ni zan matsa...
Baba Headmaster ya dubi goggo Dubu Yana Fadin
"Zo ki shige Dubu kije sai lokacin da Dada ta huce ...
Dada ta wuce wurin jauhara tana Fadin
"Jauhara don Allah bani maganin ciwon Kai in kina da shi Halima ce kwance riris...
Goggo Dubu ta mike ta tsallake kullun wainar ta ta wuce Uwar Daki duk da batayi zaton wannan hukuncin ba Amma Dole ta tsallake ta bar gidan zuwa Nasu gidan da Yake can karamar hukumar jibia...
Goggo jauhara ta karasa kwabin kullun wainar goggo Dubu ta Kuma toya Mata don gudun Kar ayi asara . Ta toya Mata ta Kuma siyar Mata t Adana Mata kudin ta ....
Kwana na uku a kwance kafin na warware na shiga harkokina inda Kuma goggo Dubu sai da tayi wata biyu a gidan su Inda iyayen ta suka shiga zaryar zuwa Bawa Dada hakuri Amma Dada tace Bata huce su Mara hakuri har zuwa lokacin da zata huce
Sai da goggo Dubu tayi wata hudu cur Bata gidan kafin goggo jauhara ta iso wurin Dada tana fadin
"Dada don Allah Nazo kiyi mini wata alfarma don ANNABI. ....
"S A W jauhara nayi Miki ita tun kafin naji ta tunda Kika ce ANNABI ai karshen magana ne...
"Yauwa dada Nagode . Don Allah dama cewa zanyi kiyi hakuri dubu ta dawo ko ba don komai sai don Yan yaran ta Kuma kuskure ne abinda tayi yanzu in ta dawo tunda kin hora ta ba zata yarda ta sake ba. Na duba yaran ta ne suna bani tausayi wallahi ga Kuma iyayen ta da suke ta Zarya kin san shi zaman gida in mutum ya wuce shi to ya wuce shi Babu Kuma uwar da take so ta Kai yarta dakin aure ta dawo Mata bare Dubu da har suruki gareta abun Babu Dadi surukin ta yayi ta zuwa Yana Tara's da Bata Nan tun Bai Gane ba zai Gane shine Nazo kiyi min alfarma don Allah kiyi hakuri ta dawo dakin ta...
"To jauhara na yarda Amma ba don ita ba sai don ke da na Gane ba irin Dubu bace zuciyar ki tana da kyau in sa adun ya dawo ki fada mishi na huce ya dawo da matar sa...
"To Nagode Dada Allah ya Kara sutura da lafiya...
Washe gari sai ga goggo Dubu ta dawo goggo jauhara ta Bata kudin cinikin wainar ta ta Kuma Bata shawarar ta kawar da idon ta daga Halimatu Kuma Yana da kyau taje ta Kara Bawa Dada hakuri don komai ya wuce....
Wani mugun kallo da goggo Dubu ta jefawa goggo jauhara tare da Jan tsaki shi ya nunawa goggo jauhara Dubu Bata rusuna ba don Haka Bata Kuma bi ta kanta ba tayi mata ADDU AR shiriya kawai
Kwana biyu da dawowar goggo Dubu sai ga kawar ta goggo tabawa ta iso gidan tana Fadin
"Kai barka barka aminiya ta hasken gidan headmaster duk sadda zanzo gidan Nan na Tara's da dakin ki a Rufe sai naji wani Abu har Mai gidan na Samu Ina Rokon alfarma yace min Babu yadda zaiyi ne a Nan na Gane yafi kowa damuwa da Rashin ki a gidan ............
To ke kuma Haka kike tabawa? Anya kuwa za a kulla abin arziki? Muje zuwa tukuna
..............Goggo jauhara ta dago kanta saboda Jin Arashin da tabawa take saki Wanda ta tabbatar da ita take.
Goggo ta mike tana fadin
"Yar Halak kink'i ambato yanzu nake zancen ki a Raina Ashe kina tafe. Muje daki akwai magana dama ko Baki zo ba Ni Zan zo shiyyar ta ku...
Ta figi hannun tabawa suka nufi Daki yayin da Goggo jauhara tace da tabawar
"Tabawa Ina yini ya gida?
Tabawa ta juyo tana yamutsa fuska tamkar taga tutun da yasha kashin Ruwa tana Fadin
"Lafiya Lau Amarya ya kasuwa?
Ta shige Daki ta zauna tana Fadin
"Kai Dubu kina ganin lukutar masifa wannan Mata akwai kisisina da son iyawa....
Goggo Dubu ta katse ta tana fadin
"Ke me kika gani a Kan kisisina? Wai fa shegiyar tsohuwar can har arashi tazo ta yada min wai jauhara ba kishiya ta bace Yar Uwa ce wai ita ta bayar da hakurin da aka dawo Dani.?.....
"Tasa aka dawo da ke ko dai tasa aka fidda ke? Tuni nake fada Miki matar Nan asiri take tana hayewa tana barin ki Amma kina ganin kamar Zaki iya da ita ....
"Na yarda wallahi tabawa don in ban yarda tayi min asiri Akan miji ba yanzu Dole na yarda tayi min Akan Sana a ta....
"To Bari ma kiji in fito miki a mutum Dubu Ranar da sa adu ya Kora ki gida ai wani tarkon ne ya Kama meye don kin zagi waccan lauyayyar tsohuwar? Ina Abun Kora a Nan? To don ma in Kara fita daga zargi wurin malam Mai gafukka naje na Zayyana mishi komai sai ga magana ta fito asirin dai ne Kuma daga kishiya....
Goggo Dubu ta zubawa tabawa idanu cike da tsoro don Allah yayi Mata mugun tsoron asiri shiyasa ma Bata tab'a taka wurin wani malami ko Dan tsubbu ba don gudun Kar ta jawo abinda zai ishe ta duk da aminiyar tata tabawa Tasha fada Mata akwai asirin da kishiyar ta jauhara ke auno Mata Amma Bata tab'a Jin zata mayar da martani ba...
"To in da ban yarda ba tabawa yanzu ai na yarda wallahi . Tunda na dawo gidan Nan tabawa komai na Sana a ta yaja baya kullum sai nayi kwantan waina tamkar wacce take siyar da mugun Abu Amma ita sau biyu ma kwanan nan take dafa taliya Yara kuwa Yan Tara Babu Mai duban inda nake bare ace waccan shegiyar Mai take kasawa? Kowa ya shigo zakiji yace a bashi taliya abada taliya dai har na yanke shawarar Nima taliyar Nan Zan koma tun abin saidawa Bai gagareni ba tunda kullum cikin asara nake sai dai na Bawa Yara da almajirai kayan kudi na Ina ji Ina gani...
"Ahab ai wannan tafiyar da kikayi Dubu Nan aka samu damar binne binnen da akayi Miki . Ba kince har da wata kinaya akayi Miki ba Wai an Toya Miki kullun wainar ki don Kar ya lalace an siyar Miki ba? To da Zaki lalube inda kike kafa kayan Sana ar ki da kinsha mamaki don Babu abinda ba Zaki gani ba ....
"To yanzu dai ga wainar can bokiti fall Ina Jin Duka dukan cinikin da nayi Bai wuce dari takwas ba ita Kam har sake dafa taliyar tayi ta Kuma siyar.....
"Ai wannan karon Dubu Dole ki aje tsoron ki gefe mu je gun malam Mai gafukka wallahi in ba fidda matar Nan kikayi a gidan Nan ba to itace zata fidda ki don shi macuci kafin ya cuce ka ne ya kamata ka fara cutar shege don shima burin da Yake da shi kenan Akan ka. To in har kin ji kin gani Zaki iya Zama da ita to sai ki kasa a kassara Mata Sana ar ta ko a kassara Mata lafiyar da zata yi Sana ar da ita Amma in nice ke wallahi da tsiya Zan sa Mai gafukkar ya fidda min ita in yaso Ni nake yin Sana ar tata Duka na hade ita Kuma Allah ya hada ta da mijin Mai tsautsayi Amma yaushe kana da kishiya ka Kama hannu ka Rungume? Ai Dole sai kana Dan motsawa....
"Ya zama Dole wannan karon nayi motsi tabawa musamman da na Gane yadda ake so na Zama . Na Gane anyi nufin yi min kisan mummuke ta yadda Zan ta narka kudi na wurin Sana suna narkewa Kinga idan na Zama bani da komai to burin ya cika ayi mini homa da barazana har ma ya Zama Ya'ya na ma sai abinda aka Basu sai dai Allah ya Sani Ina tsoron dakin Nan na malam Mai gafukka tabawa yadda kike fada cewa har Kan Rauhanai ake gani da yadda macizai suke kawo magani shine abinda Yake tsorata Ni wallahi ....
"Kinji matsalar ki wallahi Dubu . Ban fada Miki Aikin malam Mai gafukka Sha yanzu ne magani yanzu ba? Shi fa da kinje kafin kice mishi komai shine zai ce sunan ki wance Kuma akan Abu kaza Kika zo . Kan kice me? Sai dai kiga Mai kawo magani tsakanin Rauhani ko bakin aljani ko macizai ko wani Abu daban....
"Yanzu Babu yadda za ayi tabawa ba bada Sak'o ki isar mishi ba sai naje ba?....
"Ai shi baya karbar Sak'on wane yaji ga wane? Yafi son kazo da kanka in kace sako ne aka Aiko ka zai ce koma in Mai Sak'on Yana son biyan bukatar sa yazo da kanshi . Ai da Yana karbar Sak'on Dubu ai da tuni na zube kudi na na karbo Miki magani sai sai dai ki gan shi kawai....
"Wallahi Ina tsoron ganowa kaina janhurun masifa ne tabawa.....
"To sai ki Zauna in aka mayar da ke yadda ake so ai bukatar ki ta biya ko?
Cewar tabawa wacce ta dankara baka...
"Ba ma za ayi haka ba Zan Rufe Ido muje sai dai yanzu Babu wasu kudin kirki wuri na sai na Dan tattale su tukuna ...
*** *** ***
"This is love at first sight?
Ya fada da karamin sauti tamkar Mai yin rad'a...
Ya mike daga kwancen da yake ya dubi agogon wayar sa da take nuni da karfe biyu saura kwata na Daren.
Ya shafi sumar da take kwance a kanshi Yana Rintse idanu Babu abinda Yake hangowa face kyakkyawar fuskar ta da Kuma sassanyar muryar ta da take rero Kira ar ...
Ya jima cikin shiru kafin ya mike saboda ya Gane ba zai iya Samun bacci a yanzu ba.
Ya kawo farar jallabiya ya saka ya nufi kofar toilet ya tura ya shiga ya dauro alwala ya fito ya shimfida sallaya ya Tayar da salla
Raka a hudu yayi ya Zauna tasbihi ya jima kafin ya Daga Hannu sama Yana ADDU A Mai tsayi kafin ya shafa tare da bude alkur Ani Yana karatu.
Sai dab da asubahi ya ji BACCI na fizgar shi Amma sai da yayi salla kafin ya kwanta...
Yana kwanciya kuwa bacci ya fige shi cike da mafarkai akan ta...
Wayar sa ce ta Tayar da shi ya bude Ido cike da bacci inda yaga sunan mai Kiran abinda ya tuna mishi da Aikin da Yake hannun shi Dole ya mike ya shiga toilet yayi wanka. Ya fito ya shirya cikin Kayan Aiki Yana tsaye a gaban mirror Yana sharce sumar sa inda ta cikin mirror din Yake hango gizon yarinyar abinda yasa shi juyowa Yana kallon dakin Amma Bai ga komai ba.
Ya Zauna cikin shiru kafin Kuma ya jawo farar takarda tare da kaloli irin na art ya soma zana fuskar ta har da kalar Rigar da ya ganta Mai stone.
Kan kace me? Ya Gama zanen ya daga takardar Sama Yana kallo yayi murmushi ya sumbaci fuskar ta ya linke ya nufi fita ko kofar mummy din Bai duba ba ya fice ya Shiga motar shi ya fice daga gidan...
Mummy din Ashe jiran shigowar shi take Amma sai Jin fitar motar shi tayi.
Taja tsaki tana Fadin
"Wannan yaron fa in banyi sannu ba zai bani ciwon Kai kamar yadda uwar sa ta bani.....
Ina Zaune akan kujera tree seater a dakin Dada nayi shiru don tun lokacin da Goggo Dubu tayi min maganar Nan na Zama wata lazzy magana ma sai ta Zama Dole nake yin ta. Babu abinda nake tunani irin shin tsakanin Uwa da Uba na wanne ne Wanda yaja min bakin fenti da mugun tabon? Shin su waye ma iyayen nawa? Kuma Ina suke da har suka barni hannun dada wacce na jima da Gane kakata ce don Nasha Jin tana cewa mutanen da suke tambayar ta Ni din ta wurin waye? Sai tace ta wurin Hamza ce. Sunan hamzan kawai na Sani Amma ba Zan iya nuna shi ba. Cike nake da tarin tambayoyi Amma Kuma na San furta su daidai Yake da bacin Ran Dada shiyasa na hadiye kayana.
Na mike da nufin na tafi gidan anty sa a yayar Ziyada wacce tace nayi Mata laifi ban Kai Mata Allon sauka ba shine nace zanje na Bata hakuri
Na dubi Dada Ina cewa
"Dada zanje gidan anty sa a Ziyada tace min wai nayi mata laifi ban Kai Mata Allo ba....
"To maza ki Shirya kizo ka kudin Napep ki tafi Kuma don Allah ki saki ranki bana son Ina ganin ki kinyi shirun Nan ....
Na wuce bandaki na bar Dada tana magana akan shirun nawa. A Raina Kuma cewa nake to me Zan ce? Ai gara na koyi kame Baki na tunda in nayi magana ne ake neman mayar min da aibu na ko na Uwa ta ko na Uba na Wanda ban San me sukayi ba...
Ina cikin makewayin ne naji zuwa wani mutum Wanda kamshin turaren shi ya iso har cikin ban dakin inda naji Dada na Fadin
"Iko sai Allah Hamza Kaine?
Gaba na ya Amsa da karfi duk da ban San dalilin hakan ba.
Sai naji Ina son nayi na Gama na fito don Naga waye wannan bakon na Dada...
Na Gama wankan na fito inda Naga sai shigowa ake da kayayyaki dangin kayan abinci buhuhuawa ana ta saukewa a kofar Dada
Wani kyakkyawan yaro Dan kimanin shekara biyar na gani fari tas Yana tsaye bakin kofar dakin Dada da kwalbar lemu Yana Wasa da ita . Na samu kaina da zuba mishi ido Ina Jin wani Abu Yana fizgata zuwa gareshi har na kamo hannun shi ya dago Yana kallo na kallo irin na neman ba asi...
Kukan dada shi ya saka Ni ajiye yaron na nufi kofar dakin Ina sallama ban jira an bani izinin Shiga ba na shige don inga abinda ya saka Dada ta kuka....
Wani kyakkyawan mutum ne fari tas Mai Kama da yaron Nan Yana durkushe a gaban Dada Yana Rike da Hannun ta shima Yana kuka fuskar shi Sharkaf da hawaye....
Ina shigowa Dada ta daina kuka shima ya zuba min Ido Yana kallo na inda Naga kamar na tab'a ganin shi Amma Kuma ba Zan iya tunawa ba....
"Kiyi min gafara dada Ni Mai laifi ne a wurin ki Amma Allah ya Sani ban San abinda ya ke dauke min Hankali da gida ba har dai na Gane mutanen Nan ba Haka suka barni ba don Allah kiyi hakuri Dada ki yafe mini ki saka Ni ADDU AR ki Allah ya yaye min abinda Yake kaina....
"Na yafe maka Hamza na Sani ba Haka mutanen Nan suka barka ba Kuma Ina ADDU A gashi Kuma Allah ya nuna min Yana karba mini tunda yau gaka gaba na Ina fatan dai kana Nan a musulmin ka Basu kafurta mini Kai ba kamar wancan lokacin?
Ya gyada kanshi Yana Fadin
"Ina Nan a Muslim dada Ya'ya na ma Haka itace dai nake ta kokarin jawo ta Amma mamar ta tana hanawa...
"To alhamdulillahi Hamza wannan shima naka ne?
Ya Amsa Yana Mai jawo yaron Yana Fadin
"Ameer come great my mother....
Yaron ya jiyo Yana kallon dada Yana Fadin
"Sweet Daddy this is your mother?
Ya fada Yana nuna dada shi kuma ya kada mishi Kai sai yaron ya taho Yana mikawa Dada hannu Wai suyi Musabaha. Dada ta karba tana fadin
"Yanzu Baku koyawa yaron Nan hausa ba sai yaren uwar sa?
Yayi murmushi Yana Fadin
"Ba yaren Uwar sa bane dada turanci ne Kuma ya iya hausa can inda muke ne galibi da turancin ake komai ....