Ammar suna ta magana da turanci yaron Yana da saurin sabo har ya kwashe su a mota suka nufi sajuma ya hado su da kayan kwadayi suna ta mishi surutu Yana Jin kaunar su a ranshi
Kwanan Daddy uku wannan karon ma ya wuce da nufin sai lokacin tafiyar mu yayi zai dawo Nan katsina don ta Nan zamu tashi....
Tunda Daddy ya biya Mana kujerar Nan muke ta shige da ficen zuwa bitoci har tsawon watanni biyu yayin da ya rage saura kwana talatin da uku a soma tashi Daddy yazo shi kadai don ya baro su Ammar. Ranar da yazo saura kwana hudu mu tashi don Haka mukayi sallama da kowa yayin da na Kira Hakim ina sanar da shi a yau zamu tashi ya kuma zo yayi bankwana da Dada da baba na ya Kuma yi min Rakiya har sai da yaga tashin mu Yana Fadin zai Kira in mun sauka
Munyi Aiki lafiya mun Gama har muka soma Shirin dawowa yayin da Dada ke ta Fadin
"Kai Allah ya zuba Rahama a garin Madina Allah ni kam ko a yanzu ka dauki Rana na cika buri na Nazo mun gaisa da ma Aikin Allah . Kai Madina tafi aljanna Kam ANNABI ya zarce aljanna Allah ka Kira masoyan ANNABI suzo Suma suga inda ake Rabon gafara ba irin Nigeria ba da ake kwana da kuncin Rayuwa...
Ranar da muka dawo kuwa munga Yan Uwa da masoya Wanda suka zo tarbar mu
Kwanan Daddy biyu yace zai wuce kamaru Kuma tare Dani zai tafi don Nagano mahaifiya ta. Ya fuskance Dada da son zai wuce Dani kamaru Amma dada tayi tsallen tsinka tsumma tace Bata San zancen ba....
"Ka tafi da ita kamaru Hamza ? Kace itama ayi min irin na waccan? To ban yarda ba wallahi Babu inda Halimatu zata je ka bar maganar Nan Hamza don Halimatu ba zata Kuma duban hanyar kamaru ba tunda tabaro ta to yadda ta bar cikin tsohuwar ta Haka ta Barta kuma ko Bayan Rayuwa ta Kar ka yarda ka mayar da ita can Hamza in kayi hakan ba Zan yafe maka ba. Wanda suke can ma nake fatan su dawo Nan ba ta Nan ta koma can ba ..
Babu yadda Baba na ya iya Haka ya wuce kamaru Ni Kuma na soma Kuka da bak'in cikin Rashin ganin mahaifiya ta da son na ji wane irin Al Amari ne ya faru a tsakanin iyaye ne Haka?
Tsaraba ta sosai nayiwa Hakim na Kuma yiwa Ziyada da fiddausi da Goggo jauhara hatta goggo Dubu ma ban Barta s Baya ba bare kuma dangin mahaifi na Suma kowa ya samu tsarabar sa Amma ta masoyi daban take
Soyayyar mu taci gaba matuka Gaya tsakani na da Hakim muna Jin tamkar mu hadiye juna. Ni da kaina Zan so a ce mun mallaki juna Ni da shi don a yanzu Kan Ni da kaina na San na Kai mace duk da shekaru na Sha Tara Amma na San cikin Mata ma Ni sha kallo ce kuma son kowa
Tuni kuma Dada ta soma Tara kayan aure na Kuma kullum zakaji tana Fadin
"Ni fa na gaji da tsayuwar Nan gara in abin nayi ne a fito a yi shi yarinya kin Kai munzalin aure sai wani hayewa kike kamar fulawa Ni lokacin da akayi min aure ina na Kai shekarun ki? Ai ko Rabin su ban Kama ba in kuma nayi Rabin to da kad'an za a Dan Kara ...
A Raina kuwa cewa nake to lokacin ku da namu ai ba Daya bane
Tun da baba na ya tafi Bai kuma waiwayowa gida ba abinda Kuma yayi matukar Tayar da Hankalin Dada wacce take ta fadin
"To ko Hamza fushi yayi don na Hana shi tafiya da Halimatu? Kai ba zaiyi fushi da Ni ba ka dai ji Kuma in dai lafiya to ba zai ki juyowa gida ba Allah kasa dai ba wani Abun bane ya faru. Sai ya Zama kullum Dada tana cikin damuwa motsi kad'an zakaji tace
Kai Allah ya tsare mini yaron Nan bana Jin shirun shi na lafiya ne Amma Allah shine mafi Sani kuma na San in Sha Allah kukan da nayi a gaban dakin ka abah da Rokon da nayi in Sha Allah Allah ba zai kunyata Ni ba sai dai kawai mu dage da ADDU A...
Nima Kam Hankali na a tashe Yake don hatta lambar Daddy da na karba a kashe take abinda ya tabbatar min da lallai ba lafiya ba....
Dole muka Dukufa ADDU A Dada ma ta saka malamai magada annabawa suna Mata ADDU A inda Kuma dangin mahaifi na suke ta fadar Wai Dada ta cika dorawa Ranta tashin Hankali Akan mahaifi na alhalin shi Yana can Hankalin sa kwance Yana morewwa Rayuwar sa da arna dama fa tunda ya Gane Dadin Rayuwa da arna yaushe zai Kuma waiwayar arewa? Kowa dai da abinda Yake fada akan shi kuma Marar Dadi abinda yayi matukar bani mamaki ganin lamarin Nasu Yana neman Zama Rashin adalci tunda shi komai zai fada Akan su na adalci ne Kuma na zumunci Amma su dubi abinda suke fada...
Dada bata sake bi ta kansu ba ta koma Kan ADDU AR ta da sadake sadake da Yake Allah shine arraheemu sai gashi kusan shekara baba na ya iso garin cikin wani irin Hali na ciwon kafa .
Nayi kuka lokacin da NA kalli kafar baba na Nagan ta tayi wani irin kumburi Mai ban tsoro don har kafar bata iya shiga cikin kafar wando sai dai datse wando akayi
Kuka nake Ina karawa yayin da Dada ma ta tasa shi a gaba tana kuka tana fadin
"Ni na San ba lafiya ba Hamza na San ba zakayi fushi da Ni ba don na Hana ka tafiya da Halimatu. Dama Raina da zuciya ta suna fada min ba lafiya ba Amma Ina ta Rokon Allah ya tsaya maka Hamza ciwo dawowa yayi ne?
Ya Duka agaban Dada Yana Fadin
"Ciwo dawowa yayi Dada Banda ADDU AR wata kila da sai dai ku samu Sak'on mutuwa ta Dada kin ga ciwo kamar ba za a Rayu ba in ya tashi Allah kadai ya San yadda nake kasancewa dubi kafa Dada kamar ana hura ta Wai Nan don ma na dage da tofa Mata ADDU A ne Al Amarin yayi sauki Haka Amma ai da bana iya daga ta yadda Kika San an daura min dutsi a kafar ai an godewa Allah komai yazo daga Allah ne kuma daga gareshi muke neman taimakon kulli Shai in lahu haddin illah mulkillah komai Yana da iyaka Banda mulkin Allah komai zai wuce fatan dai Ubangiji ya bamu ikon cin jarabawa duk wani Al Amari Mai sauki ne matukar baiyi Kan tafi da imani ba to Allah alhamdulillahi................
Ikon Ubangijin musulunci Hamza mu Kan mu fa muna cike da son Jin yadda wannan kullin naku Yake cike da sarkakkiya.. Allah ya baka lafiya yasa kaffara ......
_Kirkirarren labari ne da Bai shafi Rayuwar kowa ba kuskure ne babba danganta kai ko wani dashi babu mafi cancantar suyi suka akan labarin irin taurarun cikin labarin Wanda kuka San Babu su a zahiri to kar wanda ba cikin jaruman labarin Yake ba yace don shi ko don wani akayi Hakan jaruman cikin labarin ne kadai suke da damar sukar marubuci akan don me zai fallasaww duniya sirrin su_
_Fatan Aminci ne ga dukkan Al Ummar musulmi Wanda duk aka jarrabe shi da kaddara yayi hakuri ya jure in Sha Allah sakamakon Yana Nan zuwa ko da baizo a wannan gidan na duniya ba to Yana babban gidan LAHIRA Allah ka yafe Mana kayi Mana Rahama duniya da lahira_
_KADDARA TA RIGA FATA_
💖
.................Dada kuka take tana tausayawa Hamza Wanda Ubangiji ya dorawa kaddarori kala kala. Amma tana fatan su zame mishi kaffara da sanadi na shiga Aljanna....
Sai share HAWAYE da fyace majina dada take yi da gefen zanin ta tana Fadin
"Allah ga bawan ka Allah ga Bawan ka yadda ka suturta ciwon ANNABI ayuba Allah ka suturta na Hamza na...
Take Dada ta tashi yaro tace ya Kira Mata sa adu
Kan kace me ta Tara dukkkan Ya'yan ta tana Fadin
"Kunga ciwon Hamza ya dawo don Allah don ANNABI ku taimake Ni ku Taya Ni mu samu mu agaza Mishi ku Dubi kafar Hamza don Allan ku duba fa ku gani ku Dubi fa...
Ta fada tana tab'a kafar Mai ciwo sai Kuma ta Rushe da kuka yayin da Baba Bello Wanda Yake shi baba na Yake bi kafin yakumbo mariya Kuma shine yafi kowa Rashin kirki ya soma Fadin....
"To Dada ta Ina zamu iya taro ciwon Nan Bayan mun San ba warkewa zaiyi ba? Irin shi ne yayi shekarun Baya tunda har mun San ba warkewa zaiyi ba dada me zai Kai mu asarar kudi? Duk fa abunda ya samu Hamza bashi da kaico laifin sa ne shi fa kwadayi mabudin wahala ne yanzu me gari ya waya? Da yayi shawara da wani a cikin mu yaushe zamu yarda da Hakan ? Ni fa da ya nace da son tafiya kamarun Nan koyarwa a makarantar Yan Mata nace shikenan tsiya ta auku Aikin koyarwar a makarantar Yan Mata ai Babu abinda ba zai faru ba sai gashi Kuma komai ya farun har Yana Kan faruwa to ciwon shi shi da kanshi ya Sani ba warkewa zaiyi ba to ai hakuri kawai ya kamata yayi a saurari abinda Allah zaiyi....
Dada ta zubawa Bello Ido kafin tace
"Bello Kai kake ganin Hamza ba zai warke ba Amma Ni nayi tawassuli da Allah da manzon Allah tare da Al kur ani Mai tsarki Wanda Yake dauke da dukkan waraka Kuma gara da ka fada min abinda Yake cikin ka Amma Nasha mamaki da za ace wannan maganar zata fito daga bakin ka Zan Rantse na kasa Rantsewa ba dai Kai ba don na san daga Ni har Uban mu Mai mutuwa Babu Mai zuciya irin wannan Amma Babu komai Nagode....
Baba Headmaster ya muskuta Yana Fadin
"Dada Dole ne ma mu Taya ki nemawa Hamza lafiya Amma Kuma fa akwai kamshin gaskiya a maganar Bello mutanen Nan dama sun fada mishi tunda Kuma ya karya musu alkawari ai Kinga Dole komai ma ya faru Ni fa nafi Jin Ya'yan Hamza da dukiyar sa da take can don duk abinda kika San sun bashi ya karba to in dai zai karya musu alkawari ya fice daga addinin da Suke so yayi wato kiristanci to dole fa zai ta ganin abubuwa da yawa sun mishi ture gashi Nan Kuma Kinga ciwon na yanzu ma ai yafi na farko wannan kafar bana Jin akwai wani magani da zai dawo da ita Kan doka da Oder sai dai yankewa....
Wani irin Abu ya Daki Kirji na Wanda har naji zuciya ta tana harbawa da sauri da sauri Jin mugun fatan da Baba Headmaster yakewa Baba na Kuma Dan Uwan sa . Na Rintse idanu na Ina Jin wani Abu Yana min yawo a kwanya ta haka dama dangin mahaifi na suke ? Haka zumunci ya koma ko kuwa dai Yan Uwan mahaifi na ne suke neman komawa haka tunda sun ganshi ba kamar yadda suka Saba ganin shi ba ? Hakikatan Ni da kaina na San Rayuwa ta sauyawa Baba na duk da bana Raba Daya biyu cewa ciwo ne ya cinye komai wurin magani. Amma a yau saboda Babu ta same shi Yan Uwan sa suke neman tozarta shi. Ban manta ba zuwan da yayi kafin na tafiyar mu Saudi Arabia Baba Bello Napep yace baba na ya siya mishi ya Kuma siya mishi . Shi kuwa Baba Headmaster jari ya nema yace zai Kara a kasuwar sa don ba zai yuwu ya tsaya jiran albashi ba. Ita kuwa yakumbo mariya fridge tace ya siya Mata ya kuma siya Mata har da gen na tadawa ......
Dada ta Dubi Baba Headmaster tana fadin
"Haka ne sa adu kunyi gaskiya Amma ban zaci Zaku ce Haka ba to ku Kam ku kawo idanu ku zubawa Hamza Amma Ni ba Zan iya hakan ba ko ba zai warke ba Zan nema har na Dace bare Kuma na San Babu abinda yafi karfin Ubangiji....
Yakumbo mariya ta soma Fadin
"Dada gaskiya fa su Yaya Bello suka fada ciwon Yaya Hamza sai dai mu Taya shi da ADDU A kawai Amma neman magani wahal da Kaine karshe ma mutum yazo ya kamu da irin ciwon nasa tunda masu turo mishi ciwon ba musulmai bane ba Kuma I'mani ne da su ba . Yanzu in kace wurin Mai magani zaka in aka soma yanko maka uwayen kudade sai kaji kamar ka antaya da gudy....
"Haka ne mariya kuje kuyi mishi ADDU AR Nagode da ADDU AR ma kudi Kuma da kuke magana ai Ina da su Ni Kam ba zanci na goge baki ba ko da kudin Hamza ko Babu in Sha Allah Allah ba zai Hana Ni abinda Zan nema mishi taimakon ba. Na San duk abinda yasa ku nunawa bawan Allah nan wannan bak'in Halin saboda kunga Babu komai a tare da shi Amma ai lokacin da kuka tabbatar da Yana mamora kowanen ku Babu Wanda baya kawo mishi lalurar shi amma ya yi muku to shi Kam ya fita hakkin zumunci ku ya ragewa...
Baba na Yana sunkuye da kanshi Yana Jin duk abinda Yan uwan sa suke fada Bai dago ba bare ya tofa ba mamaki Yake da mutunci ya Zama na kudi a wannan Rayuwar. Ko a mafarki Bai zaci ji da ganin abinda Yan Uwan sa suke son nuna mishi ba....
"Kiyi hakuri Dada ba fa Haka muke nufi ba ta Yaya zamu guji Hamza? Kawai dai Baki fahimci lamarin ciwon nashi bane kawai Amma zamu laluba Mai maganin ciwon kafar . Matsalar ma in kaje tambayar maganin Dada kace meye silar ciwon ? ....
Dada ta mike Bata Kuma tanka musu ba ta wuce Uwar dakin ta ta fito da wata jaka wacce take ajiye ajiyen ta ta soma fito da kullin magunguna tana neman ganyen magarya har tayi nasarar lalubo shi ta fito da shi tana Fadin
"Karbi wannan Halimatu ki Daka min shi yanzu Bari na Nemo lemun tsami
Na mike idanu na cike da hawayen tausayawa baba na
Tuni na hau dakan ganyen magarya Wanda har kayoyin dada tace na dake Kar n fidda Kaya ko daya
Ta fice daga gidan Bata sake tankawa su Baba Bello ba .
Suka mike suna Fadin
"Allah ya Kara lafiya Hamza zamu laluba Mai maganin In Sha Allah
Suka mike su Duka har yakumbo mariya suna ta fadin Allan ya Koro sauki na Amsa da ameen baba ku gaida gida..
Na matse hawayen da suka ciko Ido na na sharce su naci gaba da dakan ganyen magarya yayin da Naga Baba na Yana son mikewa Amma ya kasa sai cije Baki Yake....
Da sauri na saki tabaryar na nufo shi Ina Fadin
"Daddy zaka tashi ne?
Ya kada min kanshi Yana Fadin
"Ina son na daura alawala ne Halimatu Amma tashi Yana neman gagara....
Na Kama shi na taimaka mishi ya mike yaja kafar da kyar don ta Zama kamar turmi komai a wahale Yake yin sa ga nauyin kafa ga Kuma azabar ciwo da zogi...
Dada ta dawo gida dauke da tarin lemun tsami tsanwa Shar Babu nunanne ko daya kuma ya Kai guda dari .ta aje tana Fadin
"Kin Gama dakan ganyen magaryar ?
Na kawo Mata shi ta karba tana fito da zam zam din ta Wanda ta aje tun na zuwan Saudi Taki Sha Wai in ta mutu da shi za ayi Mata wanka sai gashi ta dauko shi galan guda Kuma na gasken ne Wanda Babu gami don galan din ma sai da wuka aka Yankee bakin sa.
Dada ta ce na yanka Mata lemun tsamin Nan yanka biyu a Raba shi ta tsakiya
Haka na soma yanka lemun tsamin Nan ita Kuma tana zuba Ruwan zam zam din nan a cikin garin ganyen magarya ta Kuma hade da lemun tsamin Duka a wuri daya kafin ta ce na dauko Mata Al kur ani na dauko ta bude tana neman wasu ayoyin da akayi magana Akan suna karya sihiri
Ina kallon dada wacce tace na Shiga Uwar dakin ta na saukewa Baba na katifar gadon ta na Kuma cire gadon na jingine inyaso sauran tarkacen mu Ni da ita na dawo dashi falon ta shi kuma mu bar mishi cikin...
Hakikatan naji tausayin baba na na Kuma ji tausayin Dada wacce ta Kara tabbatar min da maganar da Baba na ya fada Akan alfarmar mahaifiya . Yau da ace Babu Dada yaya su Baba Bello zasu tarbi Baba na bare kulawar da Yake tsananin bukata a yanzu?...
Tuni na gyara wurin na ajewa baba na katifa da shimfida a sama inda na dawo na dauko mishi abinci na kawo mishi na zuba na kawo mishi Ruwa ya soma Fadin
"Nagode Yana Fadin ya goden Kuma hawaye a idon shi.....
"Daina kuka Baba don Allah kaga ka saka Dada itama
Yayi maza ya share hawayen Yana Bawa Dada hakuri Ni Kuma na kure kuryar Daki Ina kuka na
Na futo ne saboda Kiran da Dada tayi min na fito Naga tana Karanta ayoyin karya sihiri tana tofawa a cikin Ruwan zam zam din Nan da ganyen magarya har ta Gama lokacin baba na ya Gama cin abincin har ya kwanta akan sallayar da yayi salla Dada ta Gama hada maganin ta ta Kuma ce na Kama Mata ta wanke mishi kafar
Ai kuwa tana soma zuba Ruwan maganin baba na ya farka a gigice Yana hada Uban gumi Amma duk da Haka Dada Bata fasa zubawa kafar Ruwan maganin tana wankawa ba ta soma wanke kafar wacce take fidda wani huci Mai zafi yayin da Baba na kuma Yake