x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - LINZAMI DA WUTA free pages

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 43517 words

Category: Tale Stories

Views 216

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
muka magana da Daddyn ku ya ce na zaba maka Mata kamar yadda nayiwa anam shine na ce mishi ga Mayra nan ya San Uban ta tsohon gwamnan kaduna ne Kuma ta Dace da Kai shine nace tazo ku zanta na San dai irin choice din ka ce don Babu inda ba za a nuna Mayra ba ba tare da anji kunya ba dube ta da kyau zaka Gane ta Dace da Kai matuka Gaya don na San Kai Dan gayu ne shiyasa ma na zabo maka wacce zata Dace da Kai.....

Yayi murmushi Yana Fadin

"Ni mummy ai ba Dan gayu bane Dan islamiya dai ne Wanda Yake son yayi komai irin na islam don na Gane musulunci shine kawai karbabben addini wurin Ubangiji Amma wannan matar da kike magana ai matar Yan boko ce dube ta fa ?
Ya fada Yana nuna Mayra wacce ta kasa dauke idon ta daga Kan Hakim....

"Ni fa ban Kira ka don ka nuna min boko da Islam ba Mayra na Kira ka ka gani don na fita hakkin ka Kai da ba iya maka ake ba yanzu meye aibun ta to?....

"Ga aibu Nan kina kallo mummy dubi yadda ake iya ganin under din ciki Mana. A Haka kike so na aure ta tana yawo tsirara? Sam Ni ba na son irin wannan matan Wanda mazan duniya suka gama kalle su sai kace dai wani jaki na dauki abinda kowa ya Sani ? ....


"Zage Ni kawai Mana Hakim saboda nayi maka abin alheri...

"Ba abin alheri bane wannan mummy Ni fa ba Zan yarda ayi min auren da akayiwa Yaya Hakim ba tunda akan idona komai Yake faruwa Kiri Kiri shi da gidan sa an Hana shi yayi komai bare a bar shi yayi iko da gidan shi Ni Kan wallahi bana so mummy ki ma fadawa Daddy Ni bana son irin wannan auren a barni na zabi kalar macen da nake so Mai hjabi Yar islamiya iri na wacce Kuma zata yarda nine mijin ta ba Mai cikakken Yanci a hannun ta ba .....


"Ai kuwa ka San kayi karya wallahi ayi magana da iyayen yarinyar Nan Kai Kuma kace zaka mayar da Uban ka karamin mutum ba.....

"Ai ban ce a nema min auren Nan ba mummy Ni fa ina da wacce nake so wacce ta Zama irin yadda nake so Yar islamiya ba Yar boko ba wacce Bata bayyana jikin ta ga Kare da doki ko Ni sai nayi da gaske na iya ganin fatar jikin ta bare Kuma wurare masu daraja don Haka mummy ayi hakuri ba Ni ba wallahi ko brother ba Zan sake Bari ayi mishi irin auren Yan iskan can da akayi mishi ba Wanda Bai Kara mishi komai ba sai bak'in ciki Ni da na San hakan ma ai da ban yarda ya Karbe shi ba wallahi ....


Dr Anam ya iso gidan ya Sami wannan chapter ya dubi hakim Yana Fadin

"Kai Kar ka sake wallahi ka tsaya ka duba Yar mutunci don ni Yar gidan mutuncin ce Amma Babu mutuncin kawai mummy a fadawa Daddy Yana da wacce Yake so Amma ai naji Dadi shine garin ba na saba ba....


Nina mike a fusace tana Fadin
"Yanzy in Hakim ya wulakanta Ni Anam Kai zaka yarda Kai ma ka wulakanta Ni? ....

"A a mummy wallahi ba wulakanci bane yayi Miki ita yarinyar ta Rasa Mai so ne ko kuwa wahayi akayi sai Hakim ne zata aura? Don Allah mummy ki Rika duba abunda zai je ya dawo yanzu yadda na Rasa mutunci a idon Nimra ai ba Zan so Hakim ya kasance irin yadda na kasance ba don Haka ki Bawa yarinyar hakuri kawai ta nemi wani gaba shikenan....


Mummy ta fice daga falon yayin da tayi hikimar janye Mayra zuwa uwar dakin ta tunda ta fahimci boren da Hakim zai Mata ...


"Kai wallahi Kar ka yarda a cuce ka Hakim Ni wannan kyalkyalin Kar ya dauke ka cuta ce wallahi ka auri matar ace baka Isa ka saka ko ka Hana ba? Ni fa yanzu tana gidan su na mayar da ita na jingine ciki ne fa da ita Amma Wai mummy ce ke goyawa Nimra baya Wai a zubar kaji fa? To wallahi Kai idan ka sake suka jona maka wanna yarinyar Mai Kama da kilaki sai ka fini Shan wahala tunda ana takamar Yar wani ce Uban ta tsohon gwamnan kaduna ne kofar rago zasuyi maka ....

"Ni yaya ai na Kama wacce nake so ma Kuma Yar mutunci ba irin wannan da take yawo tsirara ba....


Mayra ta dubi Nina tana Fadin
"Na kula gayen Nan Jan wuya ne anty zai bani ciwon Kai...

"Wallahi yaci Uwar karya ya kwana da yunwa Mayra bari ki gani ai yayi sake da ya Bari na Riga shi zuwa duniya na Kuma fi shi makirci....

Ta jawo wayar ta tana Kiran Daddyn Nasu
Kara biyu uku ya dauka Yana Fadin

"Dearest Yaya ne?
"Distinguish nayi maka over talking fa na yanke hukuncin auren Hakim ban sanar maka ba sai da magana tayi nisa don Haka ina so manya su Shiga cikin maganar don ban yarda da yaron ba ya soma leke leke Ni Kuma abinda nake tsoro kenan idan ya waye da Hakan to likkafar neman matan shi zata wuce Haka don Allah manya su Shiga cikin maganar....


"An Gama my dearest a Ina ne ya Samo yarinyar?...

"Shi fa Babu maganar aure a gaban shi nice dai na sama mishi wacce kowa zai yaba Yar gidan a fakallahu na kaduna ai ka San shi ....

"Sosai kuwa to Bari ma na Kira shi mu yi magana kome kenan sai na tura su iliyasu suje mishi tambayar...

"Yauwa gara ayi a Gama da zafi zafi akan Daki karfe Nagode distinguish sai na shigo Abuja Zan maka surprised zuwan ba zata ...

"To Ina saurare..


Ta aje wayar yayin da Mayra ta jinjina Mata Hannu tana Fadin

"Kai anty wallahi kin iya Allon ki har anyi an Gama?
"Uhum ai yaron Nan sai na na fito mishi ta Bayan gida wallahi Yana bani ciwon Kai da yawa bashi da tsoro ko shakka tunda ya Gane wani Abu ya ke min Jan Ido Amma ki bar shege ya Shiga koma shima......




Ziyada ta daga waya ta tana kallo cike da mamaki kafin ta dube ni tana zaro idanu tana Fadin


"Kika ce farin mutumin Nan ya Baki ita Halimatu? Haba no wonder wallahi irin kallon da Naga Yana Miki na San an gamu Amma fa kun matukar dacewa wannan Zan so Naga Ya'yan ku Halimatu kyau cikin kyau kai Masha Allah Amma kin kuwa San tsadar wayar Nan? Wallahi in Kika ji kudin ta Zaki Sha mamaki don duk garin Nan masu ita zasu lissafu cikin sauri don ba Duka Kai ba sunan wata hula....

Nayi murmushi Ina Fadin
"Kai Ziyada kin San Abu Mai tsada amma Ni kin San ba tsdar wayar ne a gaba na ba irin tsadar Wanda ya bani wayar a zuciya ta? Wallahi Ziyada in dai Haka so Yake sai nace Babu abu Mai Dadi a duniya irin so musamman son Wanda Yake son ka wallahi Ziyada ina son Hakim irin son da in na Rasa shi Zan mutu....

Ziyada ta kame Baki cike da mamaki tana Fadin
"Tabdijan Nan Kam tun ba a tafssa ba za a kone ....
"Wallahi da gaske nake Miki Ziyada kwanaki fa Yan iskan matsiya tan mutanen can masu bakaken Kaya suka Kama mini shi suka kulle saboda lambar mota kawai ai ban tab'a tsanar Yan sanda ba sai da suka Kama Hakim wallahi....

"Ai fa Abu yazo ga masu iya shi to shi kuma Dan bawan Allah balange Kuma a Ina a ka Dora shi tunda na kula Hakim ya mamaye zuciyar....

Nayi tsaki ina Fadin

"Don Allah Ziyada bar tuna min wani balange da ko sunan sa ma yake Tayar min da zuciya ke in banda Rashin adalci nayi Miki Kama da irin matar balange? Ai matar balange tana kauyen su kamar yadda Nima nawa mijin yake Dan garin mu...

Wayar da take hannun Ziyada ta dauki tsuwwa ta duba inda taga hoton Hakim Wanda ya mamaye screen din wayar yayi kyau matuka Gaya har ita da kanta Ziyada taji wani Abu Akan kwarjinin Hakim da sauri ta Miko min wayar na dauka ina shigewa uwar dakin Dada muka balle da fira wacce yake fada min kalaman da suka sa naji duk duniyar ma Babu mace sai Ni . Muna kwashe fiye da awa muna waya har nayi ta Mamakin kudin d yake zubawa
Tun Ban goge da iya fira da Hakim ba har na Saba da mayar da martani abinda ya karawa soyayyar mu wani irin armashi Mai yawa muka Kara kullewa muna Jin tamkar zamu hadiye juna saboda kauna da soyayya...


Tun Ziyada na jiran na Gama wayar Nan har ta gaji Tayi tafiyar ta gida tana Fadin
"Wannan Kam in aka barsu kwana zasuyi suna magana Kai sabon shigar soyayya sai ka Rufe idon ka in kuwa ba Haka ba yanzu ne zaka Sha kunya............


























To ko hakan ne Halimatu? Ko kuwa SHARRIN Ziyada ne? Amma dai Bari muga yadda za a kare wanna kitimirmira tsakanin Mayra da Hakim ga can dai za a Kai kudin neman auren Amma ango Bai Sani ba......


















✍🏻 Alkalamin GIDAN IKO💖
[8/20, 10:53 AM] Gidan Iko: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻








🧆 *_LINZAMI DA WUTA_*🧆







Pages
2️⃣3️⃣/2️⃣4️⃣









GIDAN IKO💖










_Hakkin mallakar ma na gidan iko ne kuma abin kiyayewa ne kowane Abu Yana da mamallakin sa Babu Kuma Mai son a daukar mishi kayan sa ba tare da izinin sa ba mu kiyaye hakkin juna sai mu Zauna lafiya_






_Gaisuwa ga dukkan marubutan mu masu kokarin kawo gyara ba masu son tarwatse tarbiyar yaran Al umma ba Allan ka Taya musu kayi Ruko da hannayen mu Baki Daya_






_Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da Aminci mara yankewa zuwa ga shugaban mu fiyayyen halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam da ahalin gidan sa madaukaka da masu bin su da kyautatawa har izuwa Ranar Alkiyama_










_DANGIN SHAIDAN_
💖



...................Nimra ta iso gidan anty Nina a fusace tamkar mai shirin kamaww da wuta inda kuma aka hadu Mayra da nimra suka hadu haduwar bazata. aka yi kallon kallo cike da izza kowa najin zafin kowa nimra taja tsaki kafin kowace ta kawar da kanta cike da takaici da Jin tamkar ta shake Yar uwar ta.


Nimra ta wuce zuwa Dakin anty Nina yayin da Mayra tabi ta da kallon cikin jikin ta Wanda ya turo Riga taja wani tsaki Mai karfi tamkar zata tsunke harshen ta abunda ya fusata Nimra wacce taji tsakin Mayra Amma bata dawo ba ta shige Uwar dakin Nina


Nimra da Mayra ba a ga maciji tamkar masu ganin hanjin juna . Nimra dai tana yakar Mayra ne da kyawun da tafi ta baza capacity a ko ina ne kuwa kyawun nimra ya zarce na Mayra . yayin da Mayra kuma take yakar nimra uba da kudi da girman gida har da mahaifi Wanda Yake tsohon gwamna. Al Amarin Nasu dai dadadde ne Wanda ya Samo asali Kuma har yau din Bai Kare ba ba Kuma zai Kare ba _kun San dalilin wannan tsama kuwa? Ku biyo ni na fallasa muku sirrin_


Anty Nina ta fito daga wanka taga Nimra wacce duk ta fita a hayyacin ta yayin da laulayin ciki ya tasa ta a Gaba duk ta fita hayyacin ta tausayin ta ya Kama Nina duk da ta kula kamar a fusace Nimra take don har ta iso inda take tana Fadin


"Nimra me Yake damun ki ne duk Kika sauya Haka?
Nimra ta dago cike da fushi tana saukewa Nina wani shegen kallo tamkar zata kama da wuta tana Fadin

"Har ma za a dube Ni ace tambaya ta abinda ke damu na za ayi? Nifa nace ba Zan haifi cikin Nan ba Kuma Haka nake nufi amma saboda Rashin adalci kin San ya mayar da ni gidan mu ya Kuma zayyane musu komai har da gindaya sharuda Amma anty kuka banzatar Dani Babu ke Babu shi? A Haka ake Shirin Bari na shikenan anci moriyar ganga?....


Nina ta zauna tana fadin
"Nimra rigima to yi hakuri ko wani ya fada Miki hakan ai zaki karya ta bare kuma ke da kanki me kike so ne yanzu ?....


Nimra ta Kara tsuke fuska tana Fadin
"A dawo Dani gida na don in har Ina gaban su mama ne Babu Ranar da zanyi nasarar zubar da cikin Nan . Kuma dubi Duka Duka ciki wata uku na Zama wata Allah saraki Haka Ina ga Nan gaba Kuma? Haka Zan Zauna a wahale har Nan da six months? Wallahi impossible yadda nake ganin Mata da Uban ciki a gaban su tamkar an kifa musu kwarya Zama da kyar tashi da kyar Haka Nima Yake nifin nayi mishi ? ....


"Ke kin San nafi kowa tsanar cikin Nan Nimra kin Sani Amma shammatar da yaron Nan yayi Mana itace da ya sanar da su baffa Halin da kike ciki. Da na San hakan yaushe Zan yarda ma ya San zancen wani ciki? Yanzu tashi zakiyi mu wuce asibiti a fidda Miki shi....


"Ba dai yanzu ba don mama Bata yarda tabarni Ni kadai na fito ba sai da ta hado Ni da nabil ta kuma ce duk inda muka je ya fada Mata a maido ni can kawai don ba zan samu zubar da cikin nan ina gaban su mama ba. yaje ya taho Dani na koma gida Ina ganin hakan kawai Zan samu na aiwatar da kudiri na sai kuma ina bukatar kudi ko don matsalolin cikin nan da suka ishe Ni...


"An Gama Bari na dauko Miki in ma basu isheki ba ki sake sanar dani Kuma a yau din Nan zai zo ya taho da ke nayi miki akkawarin hakan ki saki ranki kinji?
Ta mike ta koma Uwar dakin sai gata da kudi har Rafa uku ta fararen bugun Abuja wato Dubu Dubu ta bude Jakarta nimra ta zuba Mata kudin ....

Ta harari kudin tana Jan tsaki
"ki cewa shegiyar matar can ta fita harka ta Ni ba sa ar ta bace sai dai uwar ta na shigo Nan tana min tsaki to ko waye Uban ta Bai Zama min Aiki ba na yaga ta ....

"Kar ki biye Mata Nimra a saman ta fa kike kin Kuma Sani don fin da kikayi Mata ne yasa take so ta harzuka ki to ki dayka ma Bata numfashi a duniya ....



Nimra taja tsaki ta figi Jakarta ta fice ko cikakken bankwana batayiwa mummy nina ba ta fice tana sake bi ta kafafun Mayra . Mayra tana Mata kallon Dani kike zancen...



Dr Anam ya dawo Aiki ya biyo ta gidan su kamar yadda Al adar sa take ta duk in ya dawo daga Aiki sai ya biyo gidan Nasu ya gaishe da mummy in Kuma Daddy yana gari ya gaishe shi.


Yana zuwa kuwa ya Tara's da tijarar mahaifiyar sa anty Nina wacce ta Rufe shi da masifa akan mayar da Nimra gida . Bai ce mata komai ba har ta Gama wanke shi da masifa kafin ta Dora da umurnin a yau din take so yaje ya maido nimra dakin ta .....


"Mummy na dawo da Nimra kike cewa ? ...

"Eh Haka nace ko baka Jin hausa ne na sauya harshe?....

"Sai dai kiyi hakuri mummy Amma Ni Kam wallahi na Gama da yarinyar nan wallahi shiyasa ma na mayar da ita gidan su. Haihuwa kawai nake jiran tayi na Karbe Dana ko Diya ta Amma Banga amfanin Zama da mace irin Nimra ba mummy ai ko ke kyace na kyale ta matukar dai ban barranta da yadda nake yanzu ba gaskiya Banga amfanin Zama da nimra ba. Bani da ikon ayi min girki a gida na ? Bani da ikon na zartas da umarni sai anzo nan kin Shiga ciki kin yanke Mana hukunci na son zuciya. Duk na hakura na jure Amma a SHIMFIDA ta ma in na nemi hakki na ace nayi rapping ? To tunda duk bana daga cikin maza masu iyali a name da Zan dawo da ita tayi min me?...


"Ni kake fadawa Haka anam? Har anzo wanna gab'ar da zance kayi kace ba zakayi ba har kana cewa Ina yanke hukuncin son zuciya? Shiyasa bana ganin laifin Hakim idan yayi min wani Abun Kai Yake ganin baka dauke Ni da daraja ba to Amma ka Sani Akan auren Nimra har la antar ka zan iya wallahi sai ka zabi Daya umurni na ko kuwa na tsine maka no-no na da ka Sha !..


Ya dube ta da sauri Jin Abinda take fada ta Kuma gyada mishi Kai Alamar hakan take. ....

"Yanzu mummy saboda Allah me ake nufin Nimra tayi min da aka aura min ita? Shin an kawo ta ne kawai ta mike kafa sai yadda tayi da ni? Ki gafarce Ni mummy Amma ba zanyi biyayyar da Babu Allah a cikin ta ba yau da kin ce min zakiyiwa yarinyar Nan fada ki Kuma nuna Mata hakkokin miji akan matar sa don ta gyara da nace kina sona mummy Kuma gaskiya kike son tabbatar wa Amma na dawo da Nimra gida na mu Dora daga inda muka tsaya Babu wani sauyi ai Ni Kuma takaicin ta ne zai sa na soma tafiya Ina sambatu....

Ya mike zai fice mummy tana Fadin
"Kaji dai na fada maka wallahi Kar ka Bari Nimra ta Kai gobe baka dawo da ita ba....

"Nifa mummy Sai dai kiyi hakuri Amma gaskiya na Gama da yarinyar Nan in Kuma zata gyara Halin ta ne sai ta dawo don alfarmar ki da ta iyayen ta....

Ya fice ya bar Nina da bin shi da kallo

Kwana biyu uku shiru Babu batun dawowar nimra har nimrar ta fara Kiran wayar Nina tana neman ba asi

Dole Nina nufi gidan Nasu Nimra da son ta taho da ita Amma ta Tara's da baffan su Nimra ya Kuma ce ta Bari har mijin Nimra ya Gama abinda Yake shiryawa don hakikatan anyi mishi ba daidai cikin halal ace za a zubar ? Kuma ke Haj ki goya Mata baya ta
End Ads