fa saita fara aman jini... abba yayi shiru yana kokarin goge wasu gajerun hawaye dake kokarin saukowa kan kuma tunsa,
Daddy yayi saurin cewa "subhanallah" sai kuma yayi shiru
Abba yayi ajiyar zuciya sannan yaci gaba dacewa "to shine muka kawota asibiti, bayan mun kawota asibiti, likita yake sanar damu cewa tana daf da kuma da cutar hawan jini matukar bamu nema mata abinda take soba domin tunani da damuwa sun mata yawa, shine bayan ta farka aka tambayeta meye matsalarta anan take sanar damu cewa ita mahaukacin nan takeso, naso nadauki maganar tata a shirme amma Likita yace bai dace nakasa ceton rayuwar 'yataba akan wani banza kudiri nawa, Likitan ne yabada tabbacin cewa zai iya warkar da mahaukaci matukar ba asiri akayi masa ba, nikuwa shine nabi shawararsa mukaje aka daukosa, a garin daukosa kuma mota takara kadesa, yanzu haka likita yasanar dani cewa bayan cutar hauka dake jikinsa, kwakwalwarsa tayi losing wasu abubuwa wadanda koda yasamo lafiya bazai iya tunawaba, abba yadan shiru yana share hawayen dake zubo masa, jikin daddy duk yayi sanyi tausayin majnoon yaji sosai aransa, bayan abba yashare hawayensa yaci gaba dacewa "alhj kayi hakuri, kuma kabawa yaronka hakuri akan maganar aurensa da rumaisa, domin bazan zamo mai sonkaiba akan abinda 'yata kesoba, ni a yanzu farin cikinta kawai nake nema"
Daddy yayi yasauke nunfashi edonsa sunyi ja sosai, shima shirin yin hawayen yake, sai dai yadanne aransa, domin tunba yauba yaso faisal yadaina zancen auren rumaisa amma yaki, to yanzu dai komai yazo karshe, daddy yace "alhj bazan taba kamaka da laifi ko cin amanaba domin wannan hukuncin daka yanke ko nine hakan zanyi, fiyema da hakan zan iyayi domin kawai in nemawa yarona farin ciki, amma wannan shawarar daka yanke itace mafita mai kyau, mukanmu munsan dacewa rumaisa batason faisal, saidai munyi amfani da ikon mune na zama iyayenta zamu aura mata shi a dole, gaskiya bazanga laifin kaba, kuma najidadi sosai daka taimakawa yaron nan Allah yasaka maka da khairan"
Murya a sanyaye abba yace "ameen"
Sai kuma sukanyi shiru, kamar kurame saicen daddy yace "saidai wani hanzari ba guduba, abba yayi saurin dago kansa yana kallonsa "menene "
Daddy yace "sai dai akwai matsala daya, matsalar kuwa itace manta komai dayayi, domin zai iya tunawa da komai aduk lokacin dayaga abinda yataba faruwa dashi abaya, to idan yatuna ya kake ganin kenan zakayi idan yakasa amincewa da auren rumaisa, kokuwa yagudu yabarku"
Abba yadanyi shiru kamar bazaiyi magana, sai cen kuma yace "idan ma hakan zata faru tosaidai a bayan auren su, domin ana sallamarmu a asitibin nan zan fara shirye 2 aurensu, kaga kenan idan daga baya yatuna zuwa lokacin zai iya kasancewa sun samu haihuwa ita dashi, kaga kuwa bazai iya guduwaba yabar iyalansaba"
Daddy ya girgiza kai yace " kumafa hakane, Allah dai yasa shiyafi zama alkhairi"
Abba ya amsa da ameen , sannna yace "mukoma ciki koh"
Nan dai suka dan daidai kansu kafin sukoma cikin asibitin amma dakaga yananin daddy zaka gane cewa baya cikin farin ciki, domin edon nan nasa sunyi jajir....
Dakin jinyar rumaisa suka karasa, momy tana zaune akan kujerar roba, suka shigo, daddy yadanyi murmushi karfin hali ya dube umma sannan yace "toh mu zamu wuce, Allah yakara bata lafiya" sai kuma ya juya ya dube momy yace "tashi muje koh" momy ta mike itama tana kallon yanayin fuskarsa kamar marar gaskiya, saidai ta basar ta juya gurin su umma da hajja luba "Allah yakara bata lafiya yasa kaffarace" su umma suka amsa da ameen,
Sannan daddy yasanar dasu cewa gobe zasu dawo, yana gama sanar dasu, sukafice daga dakin,
Suna fita abba yasamu guri yazaune, anan yafara bayyana musu komai da yafaru tundaga zuwa dauko majnoon dakuma mantawa da abubuwan da yayi dama komaima saida yasanar dasu,
daga karshe dai yace musu yanzu an cire haukar dake kansa,
Bakaramin dadi rumaisa tajiba, umma ma haka, hajja luba kuwa tsoro lamarin yabata itamadai tana tsoron kar yaje yatuna daga baya ya gujesu,
Tayiwa abba magana akan wannan dalilin kawai saiya nuna mata cewa bakomai. Shidai kawai 'yarsa tasamu lafiya, edonsa ya rufe baya ganin komai sai lafiya 'yarsa ,,,
******** ******** ******
Tunda suka shiga mota daddy bai furta uffaba haka zalika momy, har suka karasa gida, itadai ta lura da yanayinsa yana cikin damuwa,
Suna karasa gida a falo suka dire, daddy ya zaune akan kujera ya furzar da iska,
Momy tadan dubesa kadan, bayan tazauna ta kasa hakura tanason tasan matsalar mijinta "abban faisal wai meke damum kane naga tunda muka baro asibitin nan baka cikin hankalinka, yana yinka gaba daya ya chanza, wai meke faruwane"
Daddy ya dago edonsa ya kalleta, yajima yana kallonta kafin yace "zan iya bawa faisal kowane gata da d'a ke samu agurin mahaifinsa, amma bazan iya saka soyayyarsa a Cikin zuciyar dabata sonsa ba, ni mahaifinsane zan kara umartarsa akaro na biyu daya fita harkar rumaisa, idan kuwa yaki magana to wlh zamu samu sabani dashi, domin ni bazanyi sonkai irin nasaba na kashe 'yar aminina"
Tunda yafara maganar momy ta tsorata sosai domin tana fargatar ayya kuwa faisal zai iya rabuwa da rumaisa, cike da mamaki da fargaba take tambayar daddy" meya farune ko wata matsala takoma taso wane"
Nan daddy ya fede mata biri har wutsiyarsa kamar yadda abba yamasa bayani, itama ta gamsu sosai kuma ta tausayawa rumaisa bakaramar girgiza tayiba dataji labari saida tayi hawaye,
Jikinta duk yayi sanyi, murya kasa2 tace "nima na goyi bayan maganarka domin nina bazanso araba wannan soyayyarba ta rumaisa da majnoon ta hanyar faisal ba, kawai fatana Allah yasa shiyafi zama alkhairi" daddy ya amsa da ameen, sannna yace tatashi taje tahada masa ruwanka zai fita yanzu"
Momy ta mike taje tahada masa ruwan wanka, sannna tazo tasanar da shi yatashi yaje yayi wanka ya shirya sannna yafita,
****** ******* ****
Daga dawowar abban zarah daga dubai yasa akayi mata transfer aka maida wani company,
Daya daga cikin nasa, ta samu natsuwa sosai, kuma ta daidai kanta ta rage tunanin faisal a kai kai, daman ganinsa ne kesa tana yawan tunaninsa, to yanzu kuwa tadaina ganinsa,
Tafito daga wanka tana shirin fita aiki feena tashigo dakin, zarah ta dube "yan mata lafiya kuwa"
Feena tayi saurin haurawa kan gadon ta kwanta tana dariya "lafiya lau anty zarah kawai fira nazo muyi, yau surutu nakeji"
Zarah tadanyi dariya sannna tace "nikuwa gashi yanzu fita zanyi, sai dai idan zakimun tatsuniya toh zan saurareki"
Dariya feena tayi kafin tace "toh shikenan anty zarah zan miki, badai kinason ta gizo da koki ba"
Zarah tace "eh inaso fara muji" zarah tahaura kan gadon tana kallon feena cike da farin ciki,
Feena tace "wata rana gizo...." sai kuma ta tsaya tana kallon zarah
Zarah ta daga mata gira "yane yan mata naji kinyi shiru"
Feena tace "anty zarah, sonake na tambayeki"
"Uhim ina jinki" zarah tafada tana kallon Feena
Feena tace "anty zarah wai naga yanzu kindaina kuka ko kindaina zuwa gurin faisal ne"
Zarah ta tsuke fuska tadakawa feena tsawa "tashi kifita daga dakin nan" ta nunawa feena kofa
Feena ta mike sum2 kamar wacca kwai yafashe mata a ciki, tana tafiya tana juyowa tana kallon zarah,
Zarah tace "idan kika kira sunan faisal a gidan nan Allah saina yankaki"
Feena tashe da kuka tafita da gudu tabar dakin,
Tana fita zarah ta dafe kanta ta furzar da iska "bazan iya manta dakaiba faisal kaine farin cikin zuciyata kaine muradin zuciyata" duk a zuci take wannan zancen,
A fili kuwa tsaki taja " nifa dole na cire sonsa a cikin zuciyata" tafada tana hawaye, (kujimun zarah wai dole ta cire sonsa, sai kace wani cire takalmi, hmm sone fa) ..
Da yamma faisal yadawo daga gurin aiki, tun a gurin aikin yayi kudurin daya dawo zai shiryane yaje gurin rumaisa, domin shi haryanzu bai samu labarin rumaisa batada lafiyaba,
Haka kuwa akayi yana dawowa yafada toilet yayi wanka, bayan yafito yafara shirinsa, yana cikin shirin yaji anturo kofar dakin, yad'ago kansa yana kallon kofar momy yagani, washe baki yayi yana murmushi "momy yanzu nake kudurin da nakammala shirin nan nazo nasameki, tund'a nashigo naji gidan yayi tsit, kamar bakowa"
Momy tayi murmushi tace "eh ina daki, ai naji shigowar motarka, tashi kawai banba, yanzun nanma abban kane yafito dani, yace nazo nafadama yana nemanka"
Gaban faisal yafadi, cike da mamaki ya dube momy yace "nemana kuma momy, Allah yasa dai lafiya"
Momy tace "koma dai meye zakaji, karkayi jinkiri yana dakinsa yana jiranka" tana gama fada tajuya tabar dakin,
Faisal yabi kofar da kallo harta fice, yana yin dayaga momy a ciki bai gamsu dashiba, yanaji a jikinsa kamar akwai matsala, furzar da isaka yayi a bakinsa, yaci gaba da shirinsa, tunani kala2 yarika zo masa,
Yakasa samun sukuni, ya kosa yaji me daddy zaice masa,
Kasa kammala shirin yayi, ya tashi ya nufi dakin daddy,
Yana karasawa ya tura kofar dakin yashiga, zaune ya sami daddy saman wata 'yar karamar kujera dake d'akin,
Momy kuwa tana zaune bakin gado, ko wannen su yayi shiru, fuska ba annunuri,
Yana shigowa dakin yaji gabansa yafadi, ya sunkuyar dakai kamar marar gaskiya, yakarasa kusa ga daddy ya durkusa sannan yace "daddy gani" cikin ladabi da biyayya
Daddy yayi ajiyar zuciya yana duban faisal "faisal kana son farin cikina kuwa"
Cike da mamaki Faisal yayi saurin dago kansa ya dube daddy yace "sosai makuwa daddy, fatana akoda yaushe naganka cikin farin ciki da kwanciyar hankali, sai kuma yayi shiru yana kallon daddy
Daddy yakara cewa "kana tausayin 'ya macce kuwa"
Faisal duk ya rikice da tambayoyin da daddy kemasa, kuma yarasa dalili yin tambayoyin, girgiza kansa yayi "eh daddy inajin tausayinsu sosaima"
Daddy yayi shiru, yana jin nauhin yadda zai fadawa faisal cewa yafita harkar rumaisa,
Jin yayi shiri yasa momy ta dube faisal ta kira sunansa,
Faisal ya juyo gefen momy duk ya tsorata, shima dai yakosa yaji mezasu fada masa,
Momy tace "tun bakiyi wayoba kakejin labarin matan da suka illata mazajensu akan auren dole, kayi tunani da nazari bisa akidarmu ta addinin musulunci, kazamo mai tausayi a zuciyarka, faisal! Takara kiran sunanshi yakara dago kansa edonsa sunyi ja sosai, sannna taci gaba dacewa "ba so bane mutum ya tilas tawa wanda baya sonsa akan dole saiya sosa, taya zakaji abin idanhar akace yau gashi za'a yiwa kanwarka aure dole, za'a aura mata wadda bataso, bata muradin gani, a lokacin tasauke nunfashi sannna tace "faisal! Takara kiran sunansa a karo na ukku, ykara dago kansa a lokacin harya soma hawaye, domin ya fahimci inda maganar momy ta dosa, momy tace "gabar auren dole bata taba gushewa a cikin zuciyar wasu matan, kalilan ne a cikinsu zasu iya manta dashi, duk wacca kuwa kaga tamanta to katabbatar koda akayi mata aure batada wadda takeso, amma muddi tanada wadda takeso akayi kokarin rabata dashi toh akoda yaushe bazata taba mantawa dashiba, duk wani dadi daza kabata, duk wata kula dazaka bata, duk wani so dazaka nuna mata, hakan bazaisa ta sauke akalartaba naganin ka cuceta, mazaje da dama sun fuskanci rashin zaman lafiya a gidajensu sakamakon auren matayen da basa sonsu, faisal kanasone kakasance daya daga cikin wad'an nan mazajen..." tana karasa maganar da tambaya tana duban faisal
Hawaye sosai faisal keyi duk ya fahimci maganganun momy, kuma jikinsa duk yayi sanyi, amma shikansa yarasa ta yadda zaiyi ya manta da maganar rumaisa, taya za'a yadaina sonta,
Hawayensa yashare yana sharbar majina yad'ago kansa ya dube momy sannan ya juya ya dube daddy sannna yace "rumaisa bata sona koh, wannan shine abinda kuka kasa fadamin ?"
Daddy yace "kafahimci maganar momynka faisal, rumaisa bata son....."
Faisal yadaga masa hannu yakatse masa magana, yadanyi shiru kamar bazaiyi maganaba, dakin yayi tsit nadan wani lokaci, kafin faisal yace "basai kakara maimaita kalmarba, dumin itace kalma mafi girma dana tsani naji anfurta akan soyayyata da rumaisa, nikaina nasan hakan kuma inajin hakan a jikina, tabbas so ya rufemun edo ta yadda bazan iya hango matsalar da zata faru dani nan gaba ba, ba karya mutane suke fad'aba da har sukace so makahone, nazubar da *HAWAYEN MASOYA* bila adadin a kan rumaisa, to amma a yanzu komai yazo karshe indai nine kadai wadda zai iya gushe farin cikin gidan nan to banyiwa kaina adalciba kuma! Kuma bansaka muku da alkhairin da kuka yimunba, nasan dacewa koda na aure rumaisa to tabbas nabar *BAYA DA KURA* domin akoda yaushe zan iya fuskartar barazana daga gareta" yad'anyi shiru, yana kokarin share hawayen sa,
Sannan yaci gaba dacewa "daddy indai nine matsalar ku to kusa aranku Matsalar ta kau, daga yau nabar rumaisa koda kuwa ita kadaice macce a duniya bazan aure taba, koda kuwa idan ban aureba sonta zai iya illatani a shirye nake dayin hakannnn...." yakarasa maganar yana kuka,
Momy itama hawaye take, kamar zata masa kuka tausayinsa takeji har cikin ranta, a hankali tafara magana bakinta na rawa "ba abinda zai faru dakai faisal, idan kasa natsuwa a zuciyarsa, komai zai wuce zai zamo kamar komai baitaba faruwaba"
Faisal ya mike tsaye da kyar duk jikinsa rawa yake, kuka yake marar sauti, har yakai bakin kofar fita sai kuma ya juyo ya dube daddy yace "inaso kamun uzuri naje naga rumaisa koda sau dayane"
Note* ina mai baku hakuri akan rashin jina daba kuyiba kwana biyu,haka yafarune sakamakon muna exam ne amma yanzu mungama, insha Allah yanzu bakuda shamaki da labarin majnoon kullum zaizo muku, nagode da kulawarku, kuma ina baran adu'a agareku Allah yabamu sakamako mai kyau, nagode Fansπ
Muje zuwa...π
Koda faisal yakarasa asibitin duk yad'an saki jikinsa, a mota yatsaya yakara daidaita kansa sannna ya nufo cikin asibitin,
Umma tana zaune a kusa da rumaisa tana mata fira cike da farin ciki, domin a yanzu rumaisa takara samun sauki,
Faisal yashigo dakin tare dayin sallama, suka amsa masa a tare,
Yakaraso gurin yagaida umma cike da ladabi da biyayya,
Umma ta amsa masa cike da fara'a,
Rumaisa kuwa tunda suka hada edo dashi sau daya taji gabanta yafadi, ta kauda kanta daga kallonsa,
Faisal yayi mata ya jiki, ta amsa masa da cewa naji sauki,
Ganin yayi tsaye yaki magana sai mazurai yake da edo yana sosar keyarsa, yasa umma ta fahimci akwai magana a bakinsa daya keson yayi da rumaisa,
Hakan yasa tamike tabar bakin tafita waje,
Faisal yakaraso kusa da rumaisa yana kallonta suka kara hada edo, da saurin rumaisa ta kauce edonta akan nasa,
Ya sauke ajiyar zuciya yace "rumaisa karkiyi tsammanin nazone akan maganar soyayyarmu! Aa, wannan karon nazone akan neman gafararki akan tilastaki danayi akan dole saikin soni, kiyafemun"
Rumaisa tayi rau rau da edo duk kwalla tacika mata edo muryarta na rawa tace "nibakamun komaiba, sannan kuma ni bana ganin laifinka domin *DAMA HAKA SO YAKE* bai cika kai kansa inda ake sonsa ba, yafison yaje inda zai sha wahala, tayadda daga baya koda yasamu mai sonsa yarikeshi da daraja, ina mai baka hakuri abisa Rashin karbar soyayyarka dabanyiba, kayi hakuri zuciyatace takasayin hakan "
Faisal yasauke nunfashi ya share wasu guntuyen hawaye dake makkale a gefen edonsa "shikenan, Allah yazabawa kowa abinda yafi zama mafi alkhairi agaresa"
Zuciyarsa duka takeyi tara2, yanzu shikenan an rabashi da abarsonsa, abar alfaharinsa, kai ina bazai yuyuba ace zai iya rabuwa da rumaisa, to idanma ya rabu da ita wazaiso, shifa ita kadai yafara so, duk a zuci yake wad'an nan maganganun,
Da karfi sukaji anturo kofar dakin, hakan yayi sanadiyar fitowarsa a cikin duniyar tunanin daya shiga,
Umma ce tashigo dakin cike da fara'a batama tsaya tunanin mesukeyiba, ta takarasa kusa da rumaisa tana murmushi tace "abbanki yace majnoon yafarka, kizo muje idan zaki iya tashi"