tadau zafi, wani irin haushin abban rumaisa takeji, tace " bana mason kifadamun sunansa ko sunan iyayensa, wlh babu makawa shizaki aura kuma nayi miki alkawarin indai ba mutuwa nayiba saikin auresa" sai kuma ta koma fada " maganar banza maganar wofi yanzu ai zamani ya chanza andaina yiwa mata auren dole, 'yar jikan tawa kwaya daya tak, za'a nemi amata auren dole salon idan aka kaita gidan mijin bakin ciki yanemi kasheta, toh bai isaba wollah"
Rumaisa tayi shiru sauraronta kawai take, tasoma ganin nasara acikin lamarinta da majnoon, amma saidai tana fargabar ya Hajja luba zata dauki abin idan har taji labarin cewa mahaukaci takeso"
Dafa kafadunta Hajja luba tayi hakan yayi sanadiyar fitowarta daga duniyar tunanin data shiga Hajja luba ta dubeta tace "kitashi kije kiyi wanka, kizo kici abinci, insha Allah gobe zamu koma abuja, kuma ina mai tabbatar miki dacewa zaki aure wadda kikso"
Rumaisa ta rungumeta tana kuka " nagode inna" kukan farin take,
Sannan A hankalin tafito daga jikin Hajja luba tana share hawayenta sannan ta mike tafita tabar dakin tanufi ban daki,
Wanka tayi tafito koda tafito Hajja luba ta ajiye mata abinci, zaunawa tayi taci ta koshi, sai alokacin tasamu natsuwa,
Daki takoma takwanta saman gado, tunina barkatai suka rika zomata, yanzu ya fahad yake oho itama bata saniba, sai dai har yanzu akwai sauran tausayinsa a zuciyarta, wannan me yake nufi *so'ne ko tausayi*,
Majnoon dintafa yanzu wane hali yake ciki, tabbas tayi kiwarsa sosai, kalaman Hajja luba suka rika dawo mata a kwakwalwa nacewa dole saita aure wadda takeso,
murmushi tayi cike dajindadi, a zuci tace "Allah yasa hakan nee" nan dai taci gaba da tunani kala kala, har bacci yazo mata...
*Washe gari*
Tunda sassafe hajja luba tazo tatashi rumaisa, tun agurin ta sanar da ita cewa, idan tagama salla tayi wanka tazo tasameta, domin motar safe zasubi suwuce abuja,
Haka kuwa akayi bayan rumaisa tayi salla sannan tayi wanka ta shiya, tazo tasami hajja luba zaune a harabar gidan itama ta shirya, karin kumallo kawai sukayi, suka wuce tasha, basu dad'e sosai ba a tashar suka sami mota nan suka hau hanyar zuwa abuja,
***** ***** ******
A *Abuja*
Fahad yana kwance kan gadon asibiti edonsa suka fara motsawa, sunana kokarin budewa, a hankali har edon suka yashe, kallon dakin yakeyi gefe da gefe, firgir ya mike zaune, yana mamakin wannan dakin inane, juyowar dazaiyi suka hada edo da ummansa, cike da farin ciki take kallonsa,
Shikuwa mamaki yacikashi, abubuwan da suka faru jiya yarika tunawa, muryarsa na rawa yace " ina rumaisa"
Abba yana tsaye ya kura masa edo cike da rashin fahimta, maganarsa, wace rumaisa kuma? Abba ke tambayar kansa,
umma takaraso gurinsa ta rike hannunsa tace "wacece kuma rumaisa"
Abba shima yakaraso gurin yana cewa "wacece kuma Rumaisa son" duk mamaki yacika su,
Fahad ya dafe kansa dake masa zafi yana kokarin tashi tsaye abba ya zaunar dashi, tuni hawaye suka cinciko masa edo, nan yasoma kuka yana fadan "kubarni natafi gurinta abba, wlh banzan samu salamar zuci ba matukar banga Rumaisa ba, itace farin cikina, dan Allah kubarni natafi"
Umma ta dube abba, abba ya dube umma sudukansa mamaki yacikasu, wace irin rumaisa ce wannan data rikita musu yaronsu,
Ganin basuce dashi komaiba yasa Fahad yakara fashe da kuka yana cewa " nacuce kaina, na cuce zuciyata, ya dube abba sannan yaci gaba dacewa "abba daga yau nadaina shan giya, wlh duk abinda rumaisa bataso zan daina, zan dawo mutumen kirki sabida ita, dan Allah abba kanemamin aurenta, idan bansamu auren rumaisa ba wlh bazan iya rayuwaba, dan Allah abba kanemamun auren rumaisa..." yakarasa maganar yana kuka sosai duk ya fita hayyacinsa,
Umma duk ta rikice, tunda take bata taba ganin kukan fahad ba akan macce sai yau,
Abba kuwa tuni edonsa sunyi ja sosai, yana tunanin wannan wacece ita kuma 'yar gida waye, tabbas zai nemota kuma zai nemawa yaronsa neman aurenta koda kuwa dukiyarsa zata kare kaf akan wannan matsalar,
Abban fahad ya sunkuwo yadafa gadon da Fahad yake zaune yana kallon fahad edo cikin edo yace "waye mahaifinta kuma a ina take"
Fahad ya yashare hawayesa yana cewa "A nan garin take, bansan sunan mahaifinta ba amma nasan unguwarsu da kuma gidansu"
Nan suka shiga hada kayansu, bayansun gama hada kayan, sukaje karbar takardar sallama a tare suduka ukku,
Bayan sun karba suka fita motar suka shiga suka, abban fahad ne yaja motar har sun fara tafiya abba yace "mezai hana mutsaya mukarya kafin mukarasa, domin kunsan ni bana iya zama yunwa yanzun nan ulcer ta zata iya tashi"
Nan aka ordo musu abinci kala2 suka fara ci... (ganin zasu batamin lokaci gurin kallon cin abincinsy yasa, nabar gurin, nace idan sun gama cin abinci nasu na 'yan gayu, ma hadu a gidan su rumaisa, nan na fece nakarasa tashar mota)
***** ****** ******
*TASHAR MOTA* _A Abuja_
A tasha mai motar ya jibgesu, bayan sun fito suka tare mai napep suka shiga, yakaisu har unguwar, suka biyasa sannan suka shiga cikin gidan,
Abban rumaisa yana zaune a falo, lamarin duniya duk ya ishesa, duk ya kara ramewa,
Sallama yajiyo a waje ana kokarin shigowa falon, ya kura kofar falon edo yana jiran yaga wazai shigo,
Ummansa yagani saida gabansa yafadi, ya mike tsaye cike da mamaki, a zuci yace "kardai ace tasamu labarin cewa rumaisa tabata"
Ganin yanayin fuskarta a murtuke, yaji tsoro sosai domin yana matukar tsoron ummansa,
Abinda yakara firgitashi saida yaja da baya jiyake kamar mafarki yake, ganin rumaisa da yayi a bayan hajiyarsa,
Hannusa yadaga yana nuna rumaisa cike da mamaki bakinsa ke furta "RUMAISA!!"
Hajja luba tayi saurin karbe maganar, cike da masifa take fadan "eh rumaisa ce wadda kukayi yunkurin kashewa, to ta Allah bata kuba, ina muguwar matar nan taka take, toga rumaisa tadawo gidan ubanta saiki mutu, kina inane " hajja luba tashiga kiran sunan umma,
Abban rumaisa wadda tuni murmushi ya mamaye fuskarsa, cike da farin ciki da jindadi yaga 'yarsa,
Hajja luba taji shiru, bataji motsin ummaba , ta dube abba tace "ina matarka take"
Abba ya sauke hannunsa ya dube hajja luba yace "barka da zuwa Hajiya, ya hanya " yafada cike dajin kunya,
Hajja luba ta dalla masa harara "ni ba wannan na tambayeka ina matarka domin ni danta nazo garin nan"
Abba yace "hajiya kiraso kuzauna mana sai muyi magana, ya dube rumaisa yana murmushi yace "rumaisa ta zoki zauna kinji"
Rumaisa ta tsuke fuska, hajja luba taja hannunta suka karasa bakin kujara suka zauna
Bayan sun zauna abba yayi dariya yace "bari nakawo muku ruwa" da sauri ya mike yaje yadauko ruwa a firij yakawo musu, rumaisa sai kallon abbanta take taga duk ya rame, saida yabata tausayi, kallon gidan take duk taga ya canza mata komai na gidan a hisgitse,
Abban rumaisa shima ita yake kallo duk ta koma masa bakuwa,
Hajja luba ta katse musu tunina da cewa " wai ba magana nake maka ba nace ina matarka, ko kafita yawon iskancin nata ne"
Yanayin fuskar abba ya chanza zuwa bacin rai sannan yace "tana police station" saida rumaisa ta furzar da ruwan dake bakinta saboda razana akan maganar da abbanta yafada,
Cike da mamaki hajja luba tace "meta keyi a police station"
Abba yace "tun lokacin da rumaisa ta bata nasa aka kamata domin ni nayi zaton cewa akwai hannunta acikin wannan matsalar"
Rumaisa tuni hawaye suka sauko kan kumatunta cike take da tausayin umma duk da ba itace ta haifetaba amma tanajin sonta har cikin zuciyarta, rumaisa ta marairaice fuska ta dube abba tace "Dan Allah abba kaje kazo da ita, wlh babu hannunta a ciki" sai a lokacin tayi magana,
Abba yadube yaga yata hawaye tausayi ta bashi, yace "toh shikenan" da sauri ya mike, yanufi hanyar fita,
Hajja luba tace "ina kuma zakaje"
Abba yajuyo yace " zanje station din ne nazo da ita tunda rumaisa ta bukaci ganinta"
Bai jira hajja luba tasake maganaba yafita yabar gidan,
*Bayan minti 30*
Falo ya cika umma da Abba Hajja luba da kuma rumaisa, duk suna zazzaune, sunyu jugum2, umma dukta galabaita tayi baki, ta wahala sosai,
Abba yana zaune yana kallon hajja luba,
Umma tatashi tazo gurin rumaisa kwalla duk sun cika mata edo tace " Dan Allahki rumaisa kiyafemin, Alhakinkine ke fita akaina, nasan dacewa na cuceki, na hanaki jindadi a gidan nan, amma wlh yanzu nayi nadama sosai, dan Allah kiyafemin"
Kuka rumaisa takeyi ta d'ago umma ta rungumeta tana fadan " nayafe miki ummata, wlh nayafe mike har cikin zuciyata"
Umma tana kuka tace " nagode rumaisa" suka kara kakkame juna, suna kuka,
Duk haushi umma take bawa hajja luba,
Hajja luba taja tsaki sannan tayi gyaran murya, domin ita har yanzu bata sauka daga dokin zuciyar data hauba, tace " ni ba ruwan da kukanki, kukan munafinci, mtsw,
Hajja luba ta juya gurin abban rumaisa tace " kai kuma bara kaji, maganar auren dole dazakayiwa rumaisa na janye wannan maganar, kabawa rumaisa wadda takeso, idan kuwa ba haka wlh nida kaine"
Cike da mamaki abban rumaisa yake kallon Hajja luba, wai kodai batasan wadda rumaisa takeso bane, mahaukacine fa, taya zai aurar da diyarsa ga mahaukaci,
Cikin sanyin jiki abba yace "hajiya waddafa takeso dinnan mahau..." bai karasa maganarba sukaji an turo kofar falon aka shigo tare dayin sallama,
Falon gabaki daya kallon kowa su yake kallo, abban rumaisa, da umma, hajja luba da basu san suba su na mamakin suwaye su,
Rumaisa kuwa tuni jikinta yadau rawa, muryarta na rawa ta dube fahad cike da masifa tace "mekazo yi a gidanmu, meya kawoka"
Abban rumaisa ya cika da mamaki ya dubi rumaisa yace "suwaye wadan nan kuma"
Rumaisa ta fashe da kuka tanajin yadda zata gayawa abbanta cewa shine wadda yasaceta, sai tayi shiru kawai tana kallonsu taji dame sukazo,
Tun shigowarsu fahad yake kallon Rumaisa sannan suka karaso cikin falon, suka gaisa da juna,
Abban fahad yace "ni sunana Alhaji sani babba" abban rumaisa yayi saurin katsesa da cewa "ok nagane, Allah sarki, ban taba ganin ganinkaba amma inajin labarin sosai a garin nan"
abban fahad yana murshi yace "eh hakane kasan ni bamai yawan zama kasar nan bane"
abban rumaisa yace "eh hakane, lafiya kuwa " yafada yana kallon abban fahad,
Abban fahad yanisa sannan yace "nine mahaifin fahad, wato wannan yaron" yajuya yana kokarin nunawa abban rumaisa fahad, sai yaga wayam babu fahad a gurin,
Koda suka juya, a lokacin har Fahad yakarasa gurin rumaisa edonsa sunyi ja sosai, ya durkusa a gabanta,
Falon gabaki daya saida kowa yayi mamaki,
Ya dago kansa ya kalleta a lokacin har hawaye sun fara fita a cikin edonsa, murya a sanyaye yace "kada zuciyarsa tayi zargin cewa nazone domin na cuta miki a a, hakika rumaisa bazan taba mantawa dakeba a tarahin rayuwata saboda irin gudun muwar da kika bani wacca ita narasa tun a baya da rayuwata bata kasance a yadda kika tsinceniba, banada alkhairin dazan iya saka miki dashi sai dai ina rokonki Alfarmar abu guda daya agurinki" fahad yadanyi shiru yana kokarin share hawayensa, folon gabaki daya shi ake sauraro, sannan yace "Dan Allah rumaisa ki yarda ki aureni, ta wannan hanyarce kadai zan iya saka miki akan alkhairin da kikaimun"
Gaban rumaisa yayi mummunar faduwa tabbas fahad yabata tausayi amma saidai idan tayi na am da kudurinsa to tabbas ta cuci kanta, domin bashine a cikin zuciyarta ba, hawaye ke fita a edonta tasa hannu ta share, cikin sanyin murya take Takira sunansa, yadago kansa ya kalleta, sannan taja nunfashi taci gaba dacewa "tarayyata dakai banayita tabe danna aureka saboda ni ban taba kaunar kaba, na kusancekanee kawai dan na fidda kai halin dakake ciki amma ni bantaba jin sonka a zuciyataba, kayi hakuri"
Tunda tafara maganar zuciyar fahad tasoma duka tara2 , hankalinsa yayi mutukar tashi dajin kalaman rumaisa, hawaye suka kara sauko masa, yakara marairaice fuska yana cewa "amma rumaisa idan kikamun haka bakimun adalciba, dakinsan haka zakimun dakin barni naci gaba abubawan danake daya fimin, amma danme zaki dandanmun zuma a baki kihanani lasa, dan Allah rumaisa ki amincedani"
Rumaisa tayi ajiyar zuciya tana kallonsa tace "fahad nifa bazan aure kaba, domin ni inada wadda nakeso" tana karasa maganar sai kuma tayi shiru, ganin hankalin kowa a falon yadawo kansu, duk taji ta tsargu, a hankalin sautin kuka fahad yasoma fita, jiki a sanyaye ya mike tsaye yana kallon rumaisa sannan yace "amma meyasa zakimun haka, kinkuwa san yadda zuciyata take bugawa ayanzu, wlh jinake kamar zata fasa jirkina tafito, karki illatamun rayuwa rumaisa, kece kadai wacca nakeso dan Allah rumaisa kiyarda ki ...." rumaisa ta daga mishi hannu tasauya yanayin fuskarta zuwa bacin rai cike da hargo tace "me kakeson nayi maka ne, nidakai munyi alkawarin aurene, ko kuma nace zan aurekane, nagaya maka bana sonka, kafita rayuwata mana aaaa"
Abban fahad duk jikinsa yayi sanyi a hankali yakarsa gurin ya janyo hannun fahad, kuka fahad yake sosai,
umman fahad ma haka kuka take tasa gyale ta toshe bakinta kar sautin kukanta yafita, tana mamakin rashin tausayi irin na rumaisa,
Abban fahad yace "muje koh " ya riko hannun fahad, fahad ya firgi hannunsa daga rikon abbansa yamasa, ya juyo ya kalli rumaisa yace "baki taba yimun ba amma kin nunamin alama, bantaba tunanin imaninki da tausayinki a iya baki kadai suka tsayaba idan aka bukata bazaki iya yiwa mutumba, to Amma wlh inason kisani" fahad yanuna mata dan yatsaya kafin yaci gaba cewa "duk ranar da muka sake gamo dakee..." sai kuma yayi shiru yakasa karasa maganar ya yarfar da hannunsa yana kuka, cike da tausayi,
Abban fahad ya kara janyo hannunsa suka nufi kofar fita fahad sai kuka yake yana fadan "karku rabani da rumaisa wlh itace muradin raina, dan Allah abba kubata hkuri ta amince ta aureni, dan Allah umma kubata hkr" haka yarika jiro kalaman magiya duk ya fita hayyacinsa,
Hakadai suka jasa suka fita dashi, a mota suka sakashi umma ta zauna gidan baya a tare dashi tana lallashinsa, ran abba a bace ya firgi motar da karfi tsiya suka fice sukabar gidan...
Suna fita abban rumaisa yace "waye kuma wannan a ina kika sansa"
Rumaisa tadan bata fuska kamar batason fada ganin falon kowa ya sakar mata edo, yasa tace " Sunansa fahad, shine wadda yasaceni, akan yana sona" tana karasa fadan maganar ta sunkuye kai,
Falomln gabaki daya kowa yacika da mamaki, hajja luba ranta a bace tace " wannan ai haukane mugun mutum kamar wannan yashigo gidan nan shine bazaki fadaba, meyasa baki gaya mana tun farko shi bane da basai asaka police sukamshiba"
Abban rumaisa yayi saurin cewa "hajiya amma dai bakisan kowauye alhj sani babba bako, ai wannan dakike gani duk kasar nan babu wadda ya isa yakamashi, saidai kawai muyi hakuri tunda Allah yasa rumaisa tadawo lafiya lau, mugodewa Allah"
hajja luba tayi ajiyar zuciya sannan tace "toh shikenan, sai kuma ta dube umma tadan tabe baki kafin tace " ke kuma wlh nasake jin wani tashin hankali yashiga tsakaninki da rumaisa to ina mai tabbatar miki dacewa zamanki a gidan nan yazo karshe" umma tadan share hawaye, domin yanzu nadamce karara a kan fuskarta tace "insha allah babu abinda zai sake faruwa" tana gama maganar tayi shiru,
Hajja luba ta dube abba tace "kai ma ina kara fad'a maka cewa karka kara dukanta kuma karika mata abinda takeso, yarinya karama saiku nemi kusa mata hawan jini"
Abba yayi yake yace "insha Allah hajiya babu wata takura dazata sake shiga tsakanina da rumaisa, yanzu haka sonake tafadamum wata keso, duk wadda takeso to shi zan aura mata, abba yadube rumaisa kafin yace " rumaisa wa kikeso?" Yana tambayar rumaisa,
Gaban rumaisa ya fad'i, ta dago edon tana kallonsu, tanajin yadda zata fadamusu cewa majnoon takeso, jin tayi shiru yasa hajja luba tace " kifada mana wakikeso"
Rumaisa tayi rau rau da edo kamar zatayi kuka, muryarta na rawa ta soma furta " majnoon, abba majnoon nakeso" tana karasa maganar tasoke kanta