Allah yasa dai yafara sona, cike da farin ciki tayi gyarar murya, yadan zabura a sannu sannan yadawo hayyacinsa, cike da jindadi tace "kwalliyar ta maka ne"
Sai a lokacin faisal yagane cewa ba rumaisa bace a gabansaba, janjayen edonsa yadago ya kalleta sai kuma ya sunkuyar dakai ya tsuke fuska, uffa bai furta mata ba,
Murmushi tayi tana kallonsa tace " nasan haryanzu cikin tsanata kake, amma dan Allah kayi hakuri, yaufa kwanana ukku kenan bangan kaba, kullum sainaso gurin aiki nayita nemanka, lafiya dai kuwa meke faruawa?"
Shiru yayi mata yamaa kasa dago edonsa ya kalleta,
Yanayin fuskarsa take nazari ga alama kuka yayi cikin salon kisisina ta furta " meke damunka ne dear?, ko anmaka laifine?"
A hankali bakin faisal yasoma rawa yasoma fadan "ZARAH plx liv my office, bana bukatar kowa a yanzu inaso na huta"
murmushi naga wadda yakira da zarah tayi kafin tace "aini dama a kullum baka bukatar zuwana gurin ka, nikuwa gashi nadake sai zowa nake, kuma ni bana ganin laifin kaina domin nasan wannan ba komai bane face sonda zuciyata take maka... tadan marairaice fuska kamar zatayi kuka "dan Allah faisal ka aminta da...."
Da sauri yadaga mata hannu yana huci, kalamanta haushi suke bashi, ya nuna mata kofar fita yace "ki fita nace"
Zarah tayi murmushi takara gyara zama, tana kokarin yin magana,
Faisal ya mike tsaye yadaka mata tsawa, I said liv my office"
Da sauri zarah ta miki a lokacin harta soma hawaye muryata narawa kuka yasoma zomata, hannusa yana nunin kofar office din , tana kuka take furta " zan fita, amma wlh zandawo, kai wane irin marar tasaurayine wadda baisan darajar wadda yake sonsa ba, a kullum burinka bai wuce kaga kawulankatani a gaban kowa, amma ni zuciyata a kullum burinta shine na kyautata maka, kai ne muradina amma kakasa fahimtar haka... ina sonka faisal, takarasa maganar tana kuka tana fadan I love you faisal,
yaji tausayinta sosai, domin a yanzu duk ciwonsa daya, amma yakasa nuna mata haka, kara tsuke fuska yayi "kifita nace " yafada yana hawaye,
Zarah ta firgi kofar office din dasauri ta fita tana kuka, jin karar rufe kofar kakeji da karfi gaff,
A hankayi yake sulalewa akan kujera yana kuka yadafe kansa, wannan wane irin sone yake a zazzalar zuciyarsa, son rumaisa yana kokarin haukatar dashi
A haka dai yawuni a office din ba wani aikin kirki da yayi har yamma tayi baici komaiba,
Karfe 6:00 na yamma time din tashinsa yayi, yatashi yabar office din yakoma gida, koda yaje gida yasami daddy zaune a falo yana kallon news, anan yake tambayarsa anga rumaisa kuwa ?" Daddy yace a a ba a gantaba,
Bai kara furtawa daddy komaiba yatashi yabar falon yanufi dakinsa,
Yana karasa ya cire tufafinsa yafada toilet yayi wanka, sannan yafito ya chanza kaya, yazaune yana jirar a kira sallar magriba,
Baijima kuwa a zaune ba aka fara kira nan yatashi yaje yayi alwala, yafita yaje masallaci, bayan sungama sallar magriba yayi zamansa a masallaci saida aka kira isha sukayi sallah sannan yadawo gida, jikinsa duk ba kwari, yana kokarin saka jallabiya yana shirin bacci momy tashigo dakin"kafito kaci abinci"
Faisal ya mutse fuska " banajin yunwa momy naci abinci a waje"
Momy ta girgiza kai kawai tafita tabar dakin...
***** ***** ****
Rumaisa kuwa kaf yunin ranar bacci tasha abinta, mai isarta, bawani kuka tayiba, amma aduk lokacin da ta tuna da majnoon saita zubar da kwalla,
Tunda fahad yabar gidan bai kara dawowaba yana cen gurin sharholiyarsa, tayi jira yadawo amma taji shiru hakan yasa tabi lafiyar gado sai bacci,
Misalin karfe 12 dare fahad yashigo gidan, yana tangadi da kwalbar giya a hannunsa, duk kofar daya karasa ma aikata ke bude masa, harya karasa cikin falo, dakinsa ya nufa haryakai bakin kofar shiga sai kuma ya fasa shiga dakin, yajuya yanufo dakin rumaisa,
A hankali yatura kofar dakin, tana kwance a kan gado tana bacci ya kura mata ido, tayi bala'in burgesa, takara shiga zuciyarsa, sha'awarta ta kara yaduwa a jikinsa, cikin tangadi yakarasa bakin gadon, tunga kafarta yasoma kallo har zuwa kirjinta anan yatsalar da edonsa yana kallonta yana hadeye yawu,
A hankali yakai hannunsa yafara taba kafarta, yana shafawa hankali.....
A cikin baccinta takeji kamar ana mata sosa a kafa, dadin abin taji hakan yasa takara lafewa,
Fahad kuwa sai karayin gaba yake, harya hauro ta saman jikinta, hannunsa na rawa yasoma kai ga kirjinta, yana kai hannunsa ta zabura da karfi suka hada edo, ganinshi tayi akanta, ihu tasaka tana kokarin turesa amma ta gagara, kuka tasomayi shikuwa a lokacin yake kokarin kai bakinsa acikin nata saboda yanin budewar bakinta tana kuka shiya bashi shaawar, bashiri taji saukarsa shi a jikinta lamkwaf, yana kokarin fara shafar jikinta, ihu take a daidai lokacin taji saukar bakinsa a cikin nata, uhim uhimm kawai kakeji, alamar tana ihu amma sakamakin bakinsa yana cikin nata ihun ya garara fita,
hawaye kawai kemara sintiri akan kumatu, yaukam tashiga ukku,
Fahad kuwa tuni yafita hayyacinsa, daddan ne mata hannaye yayi yana kissing dinta da karfi da yaji, wani irin nishadi yakeji, sabanin itakuwa rumaisa wani irin zafi takeji,
Da karfi takai masa cizo a lips dinsa, saida yayi kara sannan yasaki hannayeta tayi saurin turesa gefe ta mike tsaye tana huci tana kuka,
har a lokacin kwalbar giyar tana rike a hannunsa, ya soma saukimowa aka gadon yakasa tsayi guri daya sai tangadi yake, ya nunawa rumaisa dan yatsa " kifa tsayafa, domin naga kin rabemin gida ukku"
Rumaisa sai bin ginin dakin take tana kuka, shikuwa sai binta yake yana kokarin kamota,
Cikin muryar 'yan maye f yake fadan 'kifa tsayafa, Allah zan illataki"
Kuka sosai rumaisa keyi tarasa yadda zatayi dashi a lokacin tafara karanta adu o inta, a cikin zuciya,
Sai zagayar dakin suke ita dashi, harta soma gajiya,
A angle daya na ginin dakin tasamu ta rakube tana kuka,
Fahad yakai dubansa a gurin yaga ta rabe masa gida ukku, kallonta yakeyi kamar baisan taba, harya karasa gurin,
Hannunsa daya rike da kwalbar giya, dayan hannun kuwa yadaga ya nuna rumaisa data rabe masa gida ukku,
Cikin murya irin ta masu maye yace "yaushe kika zamo mutum ukku, wacece ta kwarai a cikinku"
Rumaisa tayi shiru sai karanto adu oninta take, tasa hannu ta toshe bakinta domin kar saurtin kukanta yafito,
Fahad yazo daf d ita yace "bari na fitar data kwaran a yanzu"
Yad'aga hannusa dake rike da kwalbar yakai duka a gurin,
Saukar kwalbar kawai taji akanta rakwasss , tunganan bata kara ihuba, ta sulale a gurin tafadi,
Fahad ya kuramata da ido yana kallon ta,
ya yarfa hannunsa "au bacci kikayi, toh shikenan bari nima na tayaki"
A kusa da ita ya kwanta, hannunsa yadora akan cikinta....
5:30Am na safe,
A hankali naga fatar idonsa tasoma motsi sai kuma naga yana kokarin bude idon a hankali har idon suka yashe,
Nisji yake kamar wadda yayi wani aikin wahala, har a lokacin rabin kwalbar giyar na hannunsa, dayan kuwa yana kan cikin rumaisa,
A hankali yakai dubansa ga hannunsa dake rike da kwalbar giya, yaga kwalbar a fashe, da sauri ya zabura yatashi domin yasan yayi aika aiki baisaniba,
Caraf edonsa suka sauka kan rumaisa dake kwance sharkar tamkar gawa, goshinta ya fashe kadan,
Cike da firgita yakai hannusa yana jinjigata, yana kiran sunanta cike da hargowa, yaga ko motsi batayi, muryarsa na rawa ya furta "OMG , nakashe 'yar mutane, rumaisa!!!!" Yakara kiran sunanta cikin hargowa a daidai lokacin kuka yazo masa,
Yadafe kansa ya gurfana a gabanta yana kuka sosai, ya riko hannunta ya murzawa a hankali " plx rumaisa karki tafi kibarni, dake na tsara rayuwata, ceke silar farin cikina, plx rumaisa com back 2 meeeee,( cry)...."
Dubasa yakai gurin rabin Kwalbar giyar dake gefensa yakara dauka cike da jin zafi yakara tarwatsata a kasa duk tafashe a dakin, karar fashewar kwalbar yasa rumaisa taja nunfashi da karfi, tana tari, saikuma tayi shiru,
Fahad dake kuka yakara kiran sunanta cikedajin dadin bata mutuba, da sauri ya ciro wayarsa yakira Doctor. .
Yana rike da hannunta yana shanshekar kuka, akayi knocking din kofar dakin, da hanzari ya mike yakarsa bakin kofar ya bude, bodyguard dinshi yagani a tsaye, " likitane yazo, yana falo " bodyguard din yafada,
Fahad bai furta masa koh uffanba, yajuya da sauri ya koma wurin rumaisa, hannunsa yakai yana kokarin daukoto, sai kuma ya tuna da magabar data masa jiya, (HARAMUN NE NAMIJI YATABA MATAR DABA TASHIBA)
Yayi jim yana nazarin maganar ya kalleta, hawaye suna fita a edonsa, a koda yaushe kara jinson rumaisa yakeyi a zuciyarsa
A hankali bakinsa ya iya furta "kai bazai yuyuba, noo" hannunsa yakai ya tallabo rumaisa,
wani irin nishadi yaji ya ziyarcesa, da sauri ya lumshe edo, sai kuma ya bude, edon sunyi ja sosai, ya nufi waje da ita akan kujera ya saukar da ita, likita yafra dubata ....
Tare dashi ake aikin domin tsaye yayi yana kallon duk abinda likitan keyi, duk ya fita hayyacinsa, zuciyarsa cike da takaicin giya data sakashi yayi wannan aika2, gashi yanzu yayi yunkurin kashe a bar sonsa a banza da wofi,
Dafe kansa yayi kafarsa sai rawa take yakasa tsayuwa guri daya,
Bayan Likita ya kammal mata dressing, sannan ya juyo ya kallo fahad yace "ogaa komai ya kammala insha Allah nan bada jima waba zata sami sauki"
Fahad ya girgiza masa kai, yana hawaye, nan likitan yayi sallama dashi yatafi,
Da kyar ya iya karasa bakin kujera wadda take duban tata shima ya kwanta yana kallonta... jira yake ta farka,
7:52am
Har safiya tafara bayyana, rumaisa ta bude idonta, zafi taji a kanta hakan yasa tasa hannu ta dafe kanta tana wasshh, jin bandeji a goshinta yasa tafara tuna abina yafaru jiya, da sauri ta mike tana kokarin tashi, nan kuma jiri yakara d'ibanta, tangal-tangal tayi zata fadi a lokacin fahad yakaraso gurin da sauri ya rikota tafada kirjinsa tana mayar da nunfashi, shikuwa ya kura mata edo, yana kallonta,
Ita kuwa edonta a rufe yake domin ida ta bude edon gani take dakin na juya mata,
Tajima a kirjinsa, kafin ta fara bude edon a hankali, caraf edonta suka sauka akan nashi, da karfi ta mike tana kallonsa, ranta a bace, wani irin haushinsa takeji,
Harara ta auka masa sannan tanufi hanyar dakin datake,
biyota yayi yana kiran sunanta amma ko juyosa bata yiba, tana karasawa bakin kofar dakin tashiga sannan ta turo kofar da karfi kamar zata game da hannunsa da sauri yaja baya, tasaka key ta rufe kofar, ta jingina jikinta a jikin kofar, kuka ta somayi mai sauti a hankali take sulalewa kasa tana kuka hartakai zaune,
Fahad kuwa sai knocking kofar yake yana kiran sunanta amma taki budewa, jin sautin kukanta dayake yakara tayar masa da hankali,
A hankali ya ke furta "plx rumaisa kiyi hakuri, wallahi bada sanina komai yafaruba, dan Allan kibude kofar"
rumaisa tayi bnza dashi kuka kawai take,
Fahad yaja nunfashi yace " nayi miki alkawarin daga yau nadaina shan giya, dan Allah kibud'e kofar"
Duk da kukan datake amma saida tayi murmushin karfin hali, jin kalaminsa nacewa zai daina shan giya,
Amma kuma saita gagara tashi ta bude masa kofar,
Sautin karar budan kofar yatsayar dashi, yatsa cak guri daya, yana kallon kofar,
Tana bude kofar takoma bakin gado tazauna ta dafe kanta tana hawaye,
A hnkali ya turo kofar dakin yashigo, yakarasa bakin gadon, kusa da ita yazauna, yashare hawayensa, ya kalleta yace " wai garin yayi wannan abin yafaru, ni bnsan lokacin dana aika hakan agarekiba"
Rumaisa tayi bnza dashi ko uffan tagagara ce masa, a lokacin ta tuna da batayi salla ba,
Tana yunkurin tashi Fahad yace " talk mana" harara ta dalla masa tamike tanufi toilet,
dasauri yatashi yabita baya,
Takai bakin kofar toilet din taga yana kokarin binta hannu ta daga masa " karka kuskura kabiyoni"
Tana gama fada bata jira yayi maganaba, tafada toilet din tamayar da kofar ta rufe,....
Shiru yayi yana kallon kofar ban dakin kafin yajuya yadaki ginin dakin, yana yajan nunfashi sannan ya koma bakin gado yazauna, yana tunanin rayuwarsa wai yau shine kebiyar macce, shida bai mayar da mace komaiba, amma yau gashi macci na wahalar dashi,
A lokacine yaji kamar kafarsa na masa ciwo, kallon kafar yayi yaga jini, kwalbar giyar daya fasace yataka kuma harta fasa kafar, yadago kafar yana kallon, zafi yakeji sosai,
A daidai lokacin rumaisa tafito daga ban dakin, yana jin fitowarta yayi saurin sauke kafarsa yana murmushin sai kaice wadda babu abin kedamunsa,
Bata kulashiba, yana kallonta ta karkade kasan cafet din tafara sallah, yana zaune yana kallonta tana salla,
Jiyayi yana sha'awar yayi sallah,
Amma ya gagara tashi, yana zaune har rumaisa ta kammala sallar, sannan tazauna tayi adu oi, tana gamawa ta soke kanta kasa tana hawaye,
"Harkin gamane " fahad yafada cike da fargaba,
Rumaisa ta dago kanta amma bata juyo gurinsaba tace "meya dameka da sallana, aikai bakayi" tana gama fada saikuma tayi shiru, .
Fahad yayi murmushin, yaji dadin data amsa masa maganar mike wa yayi yakarasa gurinta yazauna kafarsa namasa zafi sosai ya dubeta yace "fushe kike dani Rumaisa" yafadi maganar a marairaice ,
Sai a lokacin rumaisa tadago edota ta dubesa, ta share hawayenta sannan tace " dole nayi fushi dakai domin kasauka akan tafarkin addininka kakama addinin yahudu da nasara, Fahad takira sunansa, ths is th fst tmy data kira sunansa, sai yaji abin wani daban, the way yadda takira sunan yamasa dadi, yace "yes "
Rumaisa tace "baka sallah, sannan kuma baka tunanin lahirarka, kadauki duniyar nan kamar wani gidan jindadi, kamanta cewa a koda yaushe zaka iya mutuwa kuma kakoma ga Allah, mezaka fada masa idan kaje garesa, zaka fada masa cewa shan giya da neman mata shiya hanaka yin salla, bazaka iyaba, a ranarma bakinka bazaiyi magana domin baki zai iya shirya karya, sassan jikinka sune zasuyi magana wadanda kasan dacewa kana aikata barna dasu, fahad kaiba yaro bane, kamallaki hankalin kanka, yakamata kagyara zamanka da uban gijinka" nadai tashiga karoro masa nasihohi daban-daban...
Jikinsa yayi sanyi sosai, ajiyar zuciya yayi sannan yace "shikenan naji, zan daina komai, indai har hakan zai sakaki farin ciki, ya kara kallonta yana murshi kafin yace "amma namanta komai kikoyamun yadda zanyi"
Dadi sosai rumaisa taji,
Acen kasar zuciyarta tace yes my mission started,...
Zafin kafarsa yakai masa ko ina yayi yunkurin tashi, sai a lokacin rumaisa ta lura da jinin dake fita a kafarsa,
Tace "subhanallah, jin ciwo kayine" ya girgiza mata kai,
Oh sorry" tafada tana kokarin taba masa kafa, da sauri ya janye yana kallonta yace "babu kyau macce tataba kafar daba ta mijintaba"
Rumaisa ta kallesa tayi murmushin tajidadin maganar har cikin ranta tace "babu shamaki gaduk wadda zai tamakawa musulmi dan uwansa a duk lokacin da yake cikin neman taimako, dan haka idan har taimakonka zanyi babu laifi idan natabaka"
Fahad yayi dariya yace "ok shikenan" ya miko mata kafar ta kama ta matse jinin daya taru a ciki sannan tamike taje toilet ta dibo ruwam zafi a heater tazo tana gasa masa kafarshi, tana dan kara yimasa bayanin akan addini,
Haka dai harta kare, sannan tatashi taje tashirya musu breakfast, bayan sun gama suka dawo falo suka zaune tafara kowayar abubuwa, ranar tasaki jiki sosai dashi,
A ranar babu inda yafita yana gidan har yamma tayi, kuma ya koyi abubuwa dadama daga gurin rumaisa,
****** ***** ****
Allah sarki majnoon,
Majnoon nagani a rakube a gefen tati yana kakkarwar sanyi, duk ya rame yakara fita hayyacinsa,
Duk da babu hankali a tatare dashi amma dai yaji rashin zuwan rumaisa gurinsa, yashiga da muwa sosai amma babu wadda yadamu dashi balle yasan damuwa sa, yanzu yama soma daina yawan wasar nan