labari yasamnin akan cewa kanine ya kashemun iyali matata da yarona KISAN GILLA, wannan shine dalili dayasa mai martaba yasa aka daura aurena dake batare da saninaba, acewarsa ta wannan hanyarce kadai zamu saka miki akan taimakon dakikayi akaina, lokacin da mai martaba yasanar dani cewa andaura min aure dake, banjidadiba, amma kafin nazo nan sainaji kamar kece silar dawowa da farin cikina, kuma danazo sainaji kwata-kwata bana kunyarki, jinakeyi a jikina kamar munyi shekara goma atare, lallai wannan ba komai bane illa alakar zukata biyu, ma'ana zuciyata da taki, rumaisa yanzu nadawo gareki.."
Hawaye suka sauko kan kumatunta wanda itama batasan dalilin zuwan suba, shin na tausayin labarin Mubarak ne kona farin ciki ne, hawayenta tashare sannan tace "Allah yajikansu da rahama"
Kunya rumaisa taji ta rufe fuskarta tana murmushi, tasowa yayi daga inda yazo kusa da ita, ya kura mata edo wani irin sonta nakara shiga zuciyarsa, yarasa dalili dayasa sonta yashiga zuciyarsa lokaci daya, kafin yazo abuja babu sonta ko kadan a cikin zuciyarsa amma yanzu sonta gabaki daya ya mamaye zuciyarsa, nan take ta meye masa gurbin margayiya matarsa,
Cike da fargaba yariko hannunta, saida taji jikinta yadau wata irin sock, da karfi tasauke nunfashi tare da lumshe edo,
A hankali yake murza hannu, yana murmushi cikin wata sanyanyiyar murya yace "I LOVE YOU RUMAISA" yakarasa maganar yana kallonta,
Wani irin farin ciki takeji har cikin zuciyarta, da karfi ta kanne edonta, saboda wata irin kunyarsa dataji, da sauri ta mike ta janye hannunta daga nashi, tana murmushi ta kauda edonta daga kallonsa cikin b'arin murya tasoma furta "mee..t.." takasa karasa maganar saboda wata irin kunya takeji, da gudu tafita tabar dakin,
Prince Mubarak yayi dariya yana kara jin sonta a cikin zuciyarsa,
Tana fita ta zarce dakin umma, da gudu tashigo dakin, umma tana zaune akan sallaya taga sallar laa'sar, tafado jikinta cike da farinciki, umma tace "lalala rumaisa karyani zakiyi, wannan irin fadowar haka"
Rumaisa tadago kai ta harari umma cikin wasa sannan tace "wato umma shine kukayimun AUREN BAZATA koh, yaushene akayi auren daba a sanar daniba"
Umma tayi murmushi tace "karkiga laifina, laifin abban kine shiyace kar'a sanar dake, jiya bayan sallar isha aka daura muku aure a masallaci"
Farin ciki kam a gurin rumaisa adaina magana, domin bazai iya misaltuwaba, yau dinnan jinta takeyi kamar ba itaba,
Umma tadago daga jikinta tace "kitashi kije kishirya masa ruwan wanka, idan yafito kikaisa dinner yaci abinci koh"
Rumaisa ta zare edo "umma nikuma, nifa kunyarsa nake, shibazai iya hadawa kansa ruwan bane"
Umma tabe baki "au sai yanzu kika fara kunyasa bayan yazama mijinki, adacen ai bakya kunyarsa, nidan Allah tashi kije banason maganar banza" Rumaisa ta mike tana dariya tafice tabar dakin,
Dakin baki takoma, tana shiga tasame zaune kan kujera ya tayar da kansa sama yana tunani,
sallamar taace ta katse masa tunani, ya juyo yana kallonta, murmushi ya mata, kanta a sunkuye takaraso gurin, cike dajin kunya tace "zakayi wankane nashirya maka ruwan wanka"
Murmushi yayi sannan yace "eh zanyi mana, amma tare dake zamuyi koh?"
Dasauri tace "nikuma" tare da nuna kanta,
Kai ya kida mata " eh mana kedin, keba matata bace"
Cikin rawar murya Tace "to..to..to.." yana murmushi ya katseta dacewa "kwantar da hankali, kije kawai nizanyi wanka dakaina, kije ki huta saina fito"
Kai kawai ta girgiza masa sannan tafice tabar dakin,
Yana kallonta harta fita sannan yayi murmushi, ya mike yafada toilet, wanka yayi sosai sannan yafito, yasake saka wasu sabanbin kaya, sannan yafita,
A falo sukasha fira sosai shida su umma da haj luba, har aka kira sallar magriba, sannan ya mike yaje yayi alwala yatafi masallaci, bai dawoba saida aka gama isha,
Koda yashigo gidan, anjera masa abinci kala2 akan diner table, rumaisa ce tamasa jagora har suka karasa bakin diner, suka zaune , bayan sunzauna tayi serve dinsa,
Yana cin abincin suna fira duk da ba wata mata sosai take masaba, tarasa dalilin dayasa yanzu yake mata kwarjini,
Hakadai yaci abinci yayi nak, Sannan sukayi saida safe, yatashi ya wuce sashen baki, ita kuwa ta wuce dakin umma..
Tana shiga tazauna gefen gadon da umma take kwance, ta sauke nunfashi tana kallon umma,
Umma ta harareta cikin wasa "to shine bazaki tayashi bacci ba, kefa nalura dake Allah yanzu kinaso kizamo wata huhulahu, idan kikayi wasa da mijiki wata zata kwace mikishi kina zaune kinyi sakaci, shifa namiji kulawa yakeso da tarairaiya tamkar kwai, kikula da mijinki fiye da yadda zaki kula da kanki, kibashi farin ciki fiye da yadda zaki bawa kanki, ki rike abinki hannu bibbiyu, karkiyi wasa dashi"
Jikin rumaisa yayi sanyi, tare dajin wani irin kishi, akan umma tace wata zata iya kwace mata shi, murya a sanyaye tace "yanzu umma yazanyi"
Murmushi umma tayi sannan ta dafata tace "kije kitayashi bacci, karkisa komai a ranki, kinji Rumaisa"
Girgiza kai tayi jiki a sanyaye "toh umma" sannan ta mike tafita,
Kafin taje dakin saida ta wuce dakinta ta sanya katon hijab, sannan takarasa dakinsa,
Yana kwance akan gado yana wasa da wayarsa, taturo kofar dakin tashigo, suna hada edo yasaka mata murmushi, dukar da kanta tayi harta karaso kusa da gadon tazauna a bakin gadon,
Uffan baice da itaba, yaci gaba da dannar wayarsa, shima miskilin karshene,
Ta jima a zaune batayimai maganaba shima baimataba,
Dadai taga bayada imanin yimata magana, sannan ta sauke nunfashi cike da kunya tace "zowa nayi natayaka bacci"
Murmushi yayi sannan yace "uhim ga gurinan ki kwanta nibanajin bacci yanzu"
Bata kara furta uffanba, ta juya tagefe daya ta kwanta, batare data cire hijab dintaba, a hakan ta kudunne cen karshen gado ta juya masa baya,
Yanayin kwanciyarta yabashi dariya, yayi murmushi tare da girgiza kai,
Yajima yana game din kafin ya ajiye wayarsa sannan yatashi yacire rigarsa, yakoma dagashi sai singlet da dogon wando rigar daya cire,
Sannan yadawo kan gadon yakwanta, tanajin kwanciwarsa ta kanne edonta, duk jikinta yayi sanyi,
Bayan ya kwanta yakurawa bayanta edo, sannan ya ja jikinsa yakarasa kusa da ita, hannunsa yasa ya sarkafota ta baya,
Yajuyo da fuskarta daidai gurinsa, yasa hannu yana shafa fuskar,
Nan take jikinta yadau kyarma, ya lura da irin yadda jikinta yake rawa, hakan ya tabbatar masa dacewa batayi bacci ba, murmushi yasaka sannan yasauke muryarsa yace "kunyata kikeji ne, dabazaki bude edonba"
Ta girgiza masa kai,
Yayi murmushi yace "toh shikenan, kisha kwanciyarki lafiya saida safe" yana gama fada ya manna mata kiss a goshi, sannan ya juya ya janyo blanket ya rufe jikinsa,
Tajima a yadda yabarta, bata motsaba domin takasa yin komai duk jikinta yayi sanyi,
Saida ta dainajin motsinsa sannan ta bude edonta, koda tajuya taganshi har yayi bacci,
A sannu tatashi ta kura masa edo tana kallonsa, sai kara shige masa rai yake, taja jikinta takarasa kusa dashi, jikinta narawa ta kwanta akan kirjinsa, saida tayi wani sauke nunfashi,
Ashe shima ba bacci yakeba, a hankali yake sauke hannayensa akan bayanta, yakara manneta kam a jikinsa,
A hakadai har sukayi bacci, ko wannensu zuciyarsa cike da kaunar juna....
Tu da sassafe aka shiga hada musu kayansu, komai anshirya musu na zuwa kogi,
Karyawa kawai sukayi, sannan suka shiga motaci, rumaisa da Mubarak, a mota daya, abban rumaisa da umma a mota daya, haj luba kuwa motarta ita kadai, sai sauran bodyguard din suka shiga sauran motocin
Haka dai suka kwashe gidan gabaki daya suka wuce kogi,
Daga baya daddy yakira abba yasanar dashi cewa shima zaizo amma sai zuwa gobe a motarsa zaizo, yau dinma yanada aiki daya tsayar dashine, abba yamasa fatan Allah yakawosa lafiya,
β β β β β β β β β β β β
*KOGI*
Kusan azahar suka karasa kogi, sunga karamci iya karamci,
Umma Mubarak kuwa tunda akazo take neman surukarta, tana ganinta kuwa ta rungumeta cike da farin ciki,
Faisal yana dakinsa cikin bakin ciki, tun jiya dadare yaci kukansa mai isarsa, tare da bawa zuciayrsa hakuri, domin a yanzu yasan dacewa rumaisa tasha gabansa, saboda a yanzu ita matar wanice, kumako wani D'in yarima dan sarki, ya karbi gaddara kuma yayarda dacewa daman dai tunchan Allah yayi rumaisa ba matar sa bace, zaiyi kokarin cire sonta a zuciyarsa,
Hakadai yazaune cikin daki sai saka-sake yake, daya gaji da zaman yatashi yashiga toilet, bayan yayi wanka yafito,
Yayi kokarin boye damuwarsa sannan yafito yatayasu farin ciki,
Umma da abba aka kaisu masaukinsu,
Haka kuma haj luba itama aka kaita nata masauki,
Umman Mubarak kuwa cewa tayi itakam bata tashi kai 'yarta daki mijintaba, sai bayan angama shagalin baki, sannan za'a kai rumaisa dakinta,
Haka kuwa akayi, saida aka kara gyara sashen Mubarak aka cire masa duk wani abu dazai sashi yatuna da margayiya matar aka saka sama sabo,
Da dadare suka taru a falo sukasha firarasu harda mai martaba, ko wannensu cike da farinciki, anan suka tsara yadda bikin zai kasance, kwana ukku za'ayi anashan biki kafin akai amarya dakinta,
Mai martaba yasa angayyato manya2 mawaka, harda 'yan fim, and, ( nima saida nayi tawa gayyatar, na gayyato, rankatakaf OHW, da kuma my members yan hausa book) kowa yazo,
Gida yacika da mutane, hatta yan aikin dake gidan suna farin cikin da wannan auren,
*Day 1*
Aka shirya wani katon hell awani babban hotel dake cikin garin kogi, acen akaje akasha biki, manyan mutane, da manyan sarakuna duk sun hallara, an watsa naira iya naira,
Amarya da ango sunyi kyau abinsu, daka gansu zaka tabbatar da cewa suna cikin farin ciki,
Tuni su daddy suka karaso shida momy, komai a gaban edonsa akayi, faisal yayi farin ciki sosai da zuwansu, ansha biki iya biki, har zuwa yamma sannan kowa ya watse,
*Day2*
Wani gurin hutawa babba, aka kama, amma wannan ba wata gayyata akayiba, wannan bakin family, shimadai anci kuma ansha, an baje an chase,
*Day3*
A rana ta uku kam malamai aka kira aka gabatar da walima, mai martaba ya gayyaci manyan malamai, dakuma alaranmominsu, ansha wa'azi sosai, abinsa sai wanda yagani,
A daren ranar umman Mubarak tasa aka tsarawa rumaisa wata irin kwalliya tagani da fada, ga hannayenta sunsha lalle, dawasu irin turararuka masu kamshi,
Aka shirya rumaisa cikin wani sari (Indian dress) mai ruwan orange mai haske, hade yake da wani siket maii ratsin baki, aka barbazo mata gashinta agabanta, gashin shima yasha gyara, sannnan aka yafa mata gyale akai, hakadai tafito 'yar india sak, tayi kyau sosai,
A bagaren Mubarak kuwa shima yashirya sosai, sakamakon yau walima aka yasa yanada rawani, shima yayi kyau abinsa, yafito kamar sarki,
Misalin karfe 10:30 na dare, aka gama walimar, sannan kuma aka kai amarya Rumaisa dakinta, saida umma tamata nasihohi sosai, haka ita haj luba takara tofa albarkacin bakinta,
Saida rumaisa tayi hawaye, saboda sunyi mata nashisa mai ratsa jiki,
Dakin yasha kamshi iya kamshi, komai nadaki white ne dakin yayi haske sosai, umma da haj luba sukakai rumaisa dakinta sannan suka fito sukabarta ita kadai,
Mubarak kuwa saida yasake sabon shiri, sannan yasa Faisal yarakashi dakin amarya, ba karamar rigima sukayiba akanshi bazai jeba dakyardai Mubarak yasamu faisal yaje, koshi yana zuwa ba wani surutu yatsaya yiba, ya bar dakin, saboda zafin da zuciyarsa ke masa,
Yana komawa daki, yasauke nunfashi yana Hawaye, lokaci daya yaji son aure yashigo masa rai, tambayar kansa yake "toshi wama zai aura bayan shidai rumaisa yakeso"
Zarah ta fado masa a rai, tunani yayi irin wulakanci daya rika mata,
Harara ta dalla masa tare dajan wani irin wawan tsaki, ta kwashi jakarta tabar gurin, dasauri yabita a baya yana kirar sunanta, amma ko juyowmsa bata yiba,
Dayaga bata imanin tsayawa yayi saurin riko mayafinta tare da shiga gabanta, ai kuwa nanta daga hannu ta wankesa da wani irin wawan mari, saida yaga wata wuta,
Saukar hannunta akan kuncensa yasa ta kanne edonta, saboda wani irin zafi dataji acikin zuciyarta, kafin ta bud'e edon tuni hawaye sun sauko mata, takasa maida hannu a jikinta,
Faisal yana dafe da kumatunsa edonsa sunyi ja sosai kamar zaiyi kuka yace "lokacin kine, kiyimun duk abinda yadace, domin yanzu a shirye nake dana dauke duk wani wulakancin dazaki mun, idan mari daya bai mikiba kiramun daya, ya nuna mata gefen kumatun sa daya, sannan yace " amma kisani sabon sonkine a cikin zuciyata kuma a yanzu zan fara rainonsa"
Tana tsaye sai hawaye take, itama marin data masa har cikin zuciyarta taji, duk sai taji ta tsani hannu jitake kamar tasa wuka ta gutsure sa, yau wai ace itace tadaga hannu ta mari faisal dinta farin cikin, muradin ta, tabbas tayi babban kuskure da bazata taba mantawa dashiba,
Dakarfi kuka ya kube mata da gudu ta kauce masa ta nufi cikin motarta, tana shiga motar tafashe da wani irin masifaffen kuka, cike da tsanar kanta meyasa tayi hakan, meyasa sai bayan yadawo gareta zata wulakantashi, tana kuka bakinta ke furta " ina sonka faisal, wlh ina sonka..."
Da karfi takara bude kofar motar tafito da gudu ( kusa mata slow a gurin gudun nan nataπ)
Takarasa gurinsa,bayansa ya juya yana hawaye bai masan da zuwan taba, jiyayi kawai tatabashi ta baya,
Yanajuyo sukayi edo hudu, murmushi yasakar mata, itama cikin kuka tayi karfin hali yin murmushi tare da mika masa hankicif, yakarba ya share hawayensa, sannan shima ya mika mata hankacif din yasauke murya yace "kema kishare hawayenki, domin ni banason ganin HAWAYEN MASOYA"
Karbar hankacif din tayi tana murmushi tashare Hawaye, tasaukar dakai tace "kayi hakuri da abinda namaka, idanma zaka ramane toka rama" murmushi yayi sannan yace "aiko a mafarki bana fatan Allah yanunamin namareki, kefa wani sashece ta jikina"
Dariya tayi tace "nagode"
Hannusa yasa cikin aljihu sannan yace "muje muci abinci koh"
Ba musu tace "toh shikenan" tana Murmushi
Tana gaba yana bayanta har suka karasa bakin kujerun suka zazzauna, cike da farin ciki suke fira har suka gama cin abinci,
Kafin surabu saida zarah tabawa faisal adress dinta, shikuma yayi mata alkawarin cewa yana komawa gida, insha Allah zai sanar da mahaifinsa domin suzo akan maganar aurensu,
Hakai suka rabu cike da kewar juna, sannan kowa ya wuce gida,
Bayan faisal ya isa gida, yana karasawa cikin falon yatarar da momy da daddy zaune suna kallo, yayi sallama yashigo cike da farin ciki, yakarasa bakin kujera yazauna, momy ta dubesa, taga sai washe baki yake, tace "son yau wannan washe bakin haka, ayya kuwa lafiya" noke kai yayi yana murmushi yace "amm lafiy lau momy, abinda kuke jirane nasamo muku"
Farinciki sosai sukaji, momy tace " lallai wannan itace zarah, domin ta zare mana zuciyar yaronmu" duka falon suka kwashi dariya, daddy harda su dafe ciki saboda farin ciki, babu abinda yafiso a duniya irin yaga faisal cikin farin ciki, da kyar yasamu ya tsayar da dariyarsa yace "insha Allah gobe zanje nasamu iyayenta"
Faisal yayi farin ciki da maganar daddy, nan dai suka yi 'yar fira zuwa ana fara kiran magriba, sannan suka tashi shida daddy sukayi alwala sukayi masallaci....
β‘β‘β‘β‘ β‘β‘β‘β‘ β‘β‘β‘β‘
Zarah ma haka tana komawa gida tasanar da ummanta cewa gobe za'ayi baki,
Umma tayi murna sosai, abbanta nadawo aka sanar dashi shima yayi murna sosai,
Da dare Tana zaune a dakinta tana waya da faisal firar soyayya suke, feena tashigo tazo tazauna kusa da ita, zarah ta sarkafata sannan taci gaba da wayarta,
Feena tabita da kallo taganta sai washe baki take, takasa hakura saida tace "anty zarah meya sakaki farin ciki" zarah tadan kauda wayar daga kunnenta tace "faisal ne"
Feena ta zare edo "faisal kuma anty zarah, halam yadaina sakaki kuka ne"
Zarah tayi murmushi takara kauda wayar daga kunnenta tace "eh barima nabakishi kugaisa" tana gama maganar ta mayar da wayar a kunneta sannan tace "ga wata kanwata mai masifar surutu, sunanta feena, zaku gaisa"
Faisal yace "toh shikenan" cike da farin ciki,
Ta mikawa feena wayar, feena ta karbi wayar suka gaisa cikeda girmamawa, daga karshe dai take tambayarsa meyasa yake saka antynta kuka a kwanan baya,
Zarah tayi saurin karbe wayar tana dariya tace " manta da ita kawai"
Haka dai sukci ga da wayarsu cike da farin ciki, kusan kare daren sukayi suna waya, sai kusan 3 snnan suka katse wayar suka samu suka kwanta...