x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - MAJNOON

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 47364 words

Category: Romance Story +18

Views 116

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
kasa,

Tunda tafadi kalmar majnoon abba yashiga tashin hankali, yafara tunano abinda yafaru kwanakin baya,

Hajja luba kuwa mamaki yacika kasa hakura tayi saida tayi magana "majnoon fa kikace, mahaukaci kenan"

Abban yayi saurin cewa "eh hajiya wani mahaukacine takeso, nayi kokarin rabata dashi amma taki rabuwa dashi"

hajja luba tamike tsaye cike da masifa tace " wannan ai haukane, niko a tarihi bantabajin mai hankali yaso mahaukaci ba, nima ban goyi bayan a aura miki mahaukaci ba domin wata rana zai iya illataki, meye abinso a cikin mahaukaci mtsw, ni wlh nayi tunanin kinada hankali ashe ke baki hankali ko kadan" takarasa maganar tare dajan tsaki,

Abba ya girgiza kai yana kallon hajja luba yace "kemadai kya fada, meye abinso a gurin mahaukaci, amma babu yadda zanyi tunda kince abata wadda takeso, dan haka shi a aura mata kawai"

Hajja luba tace "ai ko bayan raina bazata auresaba, ni wlh dama nasan akan mahaukaci kike wannna kurciyar da wlh bakisa nabaro sokoto nazo nanba"

Tunda suka fara maganar rumaisa tasoma kuka, hajja luba taci gaba da zabga mata fada, kamar ta daketa, taga rashin hankalin na rumaisa yayi yawa, daga karshe tace "wannan duk kurciyace, dan haka idanma kinada wanda kikeso kifito dashi amma ba mahaukaci ba, idan kuwa bakida kijira zuwansa amma bazamu aurar dake ga mahaukaci ba" tana gama maganar ta dube abba tace "tashi muje kamaidani sokoto, domin ni bazan zauna ina sauraron wannan tatsuniyarba, sanna tasake duban rumaisa tace "ke kuwa idan kika tanace akan cewa sai mahaukaci, to bani bake, karki kara daukata a matsayin kakarki" takarasa maganar tana huci tanufi kofar fita, rumaisa tayi saurin mikewa cike da tashin hankali tashiga gabanta ta durkusa a gabanta tana kuka ta rike mata hijjab " inna dan Allah kiyi hakuri akan abinda nafada, wlh na hakura dashi, zan iya barinsa amma ke bazan iya jurar ganin fushinkiba, saidai inna dan Allah kitayani da adu'a Allah yasa kar ciwon zuciya ya illatani"

Tausayi tabawa hajja luba sosai, duk yadda taso tayi fushi da rumaisa bazata iyaba, idanhar tatuna irin hallacci da mahaifiyarta tamata, hajja luba tasa hannu ta dagota suna facing din juna sannan tace "na hakura rumaisa, kuma insha Allah ciwon zuciya bazai illatakiba, zaki dawo sumul kamar kowa zaki manta dashi a rawuyawaki" rumaisa tana kuka ta rungume hajja luba, hajja luba tarika suka wuce daki, akabar daga umma sai abba a falo,

Abban yadube ya tsuke fuska yace "kitashi kigirka mana abinci"

Umma ta girgiza kai kawai ta wuce kicin...

***** ***** ***

Abban fahad kuwa tun a mota yaci fadansa mai isarsa, har suka karasa gida a faloma yakara dora wani fadan yana cewa "bazan barka a kasar nan ba, akan macce dukkabi ka susutaminkai, yau zamubar kasar nan tare dakai, yadube umman fahad yace " tashi maza ki had'o masa kayasan muwuce dashi"

Umma tace " hakan ma yafi muje dashi cen yana gabanmu" haka kuwa akayi umma taje tahada masa kayansa, suka fita suka nufi airport,

Fahad banda kuka babu abinda yake, duk yarasama mezai musu, duk da dai shima yanason tafiyar, domin yanason yamanta da rumaisa a yanzu, matukar yana ganinta bazai taba daina sontaba,

Hakadai suka shiga jirgi sukabar 9ja, suka lula zuwa American...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:46 PM] β€ͺ+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*πŸ˜ƒ

71 and 72
Via *OHW*
_A love story_πŸ’

Ummanta nazaune a falon taga ta fad'I cike da firgita ta karaso gurinta, tana jinjigata, tana kiran sunanta amma taji shiru, daman umma likitace, da sauri ta dube feena, wacca tuni tafara tana fadan wayoo anty zarah tamutu, umma tadaka mata tsawa tace "jeki daukomin ruwa a firij"

Dasauri feena ta mike jikinta na rawa, taje tadauko ruwa tadawo, umma ta karba ta kwara mata,

Firgit tafarka tana kuka, ta kakkame umma, umma tace "lafiya kuwa meyake faruwa ne"

Zarah kuka take sosai da kyar da iya fadan "ammi dan Allah achanzamun gurin aiki, wlh matukar ina gurin aikin nan bazan taba samun kwanciyar hankaliba, zuciyata zata iya fashewa"

Ammi ta sauke nunfashi tace "toh shikenan daman tun shekarar jiya da damukayi magana dake nakira abbanki na sanar dashi komai, kuma yace insha Allah za'a nema miki wani gun, ki kwantar da hankalinki, tashi muje nakaiki dakin ki kwanta"

Nan zarah tamike ammi tarika sukabar falon suka nufi dakin zarah, a dakinta ammi takaita saman gado ta ajiyeta sannan tafice tabar dakin,

Bayan fitar ammi kuka sosai zarah tayi, tare da yiwa zuciyarta alkawari cewa koda son faisal zai kasheta to dole zataja baya2 da lamarinsa domin yanzu yasamu wadda yakeso, bazataso shi ya shiga irin halin da ita take ciki ba'ayanzu,

Haka dai taci kukanta mai isarta, hadisin annabi Muhammad S A W ta tuna inda yake cewa "kugusar da damuwarku dayin sadaka, Allah subhanahu wata'ala zai yaye muku damuwarku kuma ya doraku akan makiyanku" wannan ta ajiye aranta, takira feena tazo tabata kudi tace taje masallacin bakin layi takai musu tace sadakace, haka kuwa akayi feena taje takai kudin ta dawo.....

A hankali tasoma samun natsuwar zuci, harda bacci yayi awon gaba da ita,

*Bayan kwana biyu*

Rumaisa tadan warware amma haryanzu takasa sakin jiki, akoda yaushe tunanin majnoon take, tama daina fitowa falo, kulum tana cikin daki saikace wata amaryar kulle,

Batada aiki sai tunina sai kuma kuka idan taga babu kowa a kusa da ita,

Yauma kamar kullum tana cikin daki zaune, abbanta yashigo, yana murmushi yazauna kusa da ita ya dube yace "rumaisa!!" Ya kira sunanta tadago kanta "naam abba"

"Kirage yawan tunaninnan domin baya haifar da alkhairi kinji" rumaisa ta noke kai tace "toh abba zandaina"

Abba yayi ajiyar zuciya yasake dubanta yace "daman abinda yakawoni shine, maganace akan faisal munyi magana nida iyayen sa yau zaizo gurinki, domin kufara fuskantar juna kafin ranar aurenku, dan Allah Rumaisa kibashi kulawa, karki sharesa, idan kikayimun haka zanyi matukar farin ciki"

Hawaye suka cicciko a edon Rumaisa murya a sanyaye tace "shikenan Abba insha Allah zanyi kokarin yin haka"

Abba yajidadi sosai yace "Allah yayi miki albarka" rumaisa tace "ameen" muryarta na rawa kamar zatayi kuka,

Abba ya mike tsaye "kifito kici abinci, kafin yazo" yana gama fada yabar dakin

rumaisa ta gagara yin magana domin a lokacin har kukan yasoma zomata,

Ai kuwa abba na fita ta fashe da kuka, kuka mai sauti take amma a hanakali sautin kefita dan kar wani yaji,

Kuka sosai tayi saida taji zuciyarta tafara zafi sannan tadaina, tashare hawayenta, tatashi tashiga toilet, wnka tayi sannna tafito,

Bawani mekupp tayiba, porder ce kawai tashafa, sannan ta janyo wata doguwar gown tasaka tayi kyau abinta, amma dai fuskar a daure,

Tazo gaban mirror tayi tsaye tana kallon kanta, sai lokacin ta lura da irin ramar datayi, har kansanta na wuya sunfito.... Allah sarki rumaisa😭
***** ******* ******
Tunda yafito daga wanka yake cikin farin ciki, dasauri sauri yashafa mai, sannan yakarasa bakin akwatinsa ya janyo wani light blue yadi, yasaka yayi kyau abinsa, yazo bakin mirror yayi tsaye yana kallon kansa, yayi murmushi a lokacin yana kokarin daidaita hula akansa, bayan yazaunar da hular daidai, yakarayin murmushi, sannan ya janyo turare yafeshe jikinsa kaf nan take ya kwashi kamshi,

Sannan yakarasa wurin ajiye takalminsa, yajanyo wasu takalmi masu ratsin blue a cikinsu, yasaka, sannan yafita falo,

Momy naganinsa ta washe baki tana fadan " a a lallai wannan shirin saidai zuwa gurin rumaisa"

Faisal yayi murmushi sannan yakaraso gurinta, har zai zauna sai kuma yafasa, momy tace "zauna mana" faisal yayi murmushi yace "a a momy bazan zaunaba domin banason nayi leti zuwa, kidai jirani idan nadawo zaki sha labari" yana karasa maganar ya nufi kofar fita, cikin zumuri da jindadi momy tace a dawo lafiya" nan dai yafita yaje yashiga motarsa, yayiwa mai gadi hoh yabude masa kofar, yana fita daga gidan yasaka wakar Soyayyace tafito dani, ta ko ina ansan dani kizo muje muza gaya, Alkawarin so murike,) wakar umar m sharif, cike da nishadi sautin wakar ke fita ta speakers na motar, wakar tana ratsashi sosai domin harya haddace wakar wani baiti naji yana rairowa kamar haka "tarkon so yakama zuciya, gidan sarauta da sarauniya, natabbata banishan wuya dan adalcinta da gaskiya na tabbata nafad'a a hannnu nagari bata cutar dani, dan lele nazamo a guntane, bazatasoni insa wuya" haka dai yaci gaba da suburbuda wakarsa yana tafiya,

Misalin karfe 7:30 na yamma abba yadawo daga masallaci yana zaune a falo, umma kuwa tana kicin tana hada musu girki, hajja luba tana dakin rumaisa saman sallaya tana lazumi,

Yaro yashigo gidan, yayi sallama abba ya amsa, yaron yace "wai ana sallama da rumaisa a waje" cike da farin ciki abba yace "kace tana zuwa "

Yaron yace "toh" yafita

Yana fita abba yatashi dasauri yaje yasanar da rumaisa,

Bata tsaya bata lokaciba gurin yin mekup, tadan kimtsa jikinta sannan tafito hajja luba tayi mata magana akan tadan saki fuska mana, hakan yasa tadan waye fuskarta kadan sannna tafita,

A jikin motarsa ta samesa a tsaye, tun daga nesa yake kallonta yana mata murmushi, rumaisa takaraso gurinsa ta gaidashi ya amsa cike da farin ciki, suna gama gaisuwar tayi shiru, shima yayi shiru ganan fuskarta a murtuke yasa yayi murmushi yace "rumaisa kibani dama nanumiki irin sonda nake miki, a koda yaushe muradina shine naga kin kasance tawa"

Murmushi kadan rumaisa tayi kafin tace "ai banice zan baka damaba, zuciyatace, domin ni ai nagama baka dama tunda har nazo gurinka"

murmushi faisal yayi yace "toh shikenan nikuwa zan nunawa zuciyarki cewa duk duniya babu wadda yake sonta kamar yadda nakesonta"

Hmm kawai rumaisa tace masa, haka dai sukaci gaba da firarsu, duk yayi magana saita bashi amsa, amma dai ta gagara sakin fuskar,

Shikam dai ko a haka suka tsaya yaji dadi sosai, koda ace duk yazo zaginsa take to shikam babu abinda zai damesa,

Sun kusan awa daya suna magana, rumaisa dukta tsargu, wani irin zafi takejin zuciyarta nayi, nan take kanta yadau ciwo, jiri tasoma gani,

Ta mike tsaye kamar zata fadi, tace "banajindadi jiri nake gani,kaje saida safe" bata jira yayi maganaba, tabar gurin dasauri,

Faisal ya mike cike da farin ciki, yadan tabe baki, yace "any way! Gobema zan dawo"

Abba yana zaune a falo umma ta kawo masa abinci yana shirin fara ci,
Rumaisa ta shigo falon, ta dafe kanta da kuma zuciyarta, abba yace "lafiya kuwa "

Kala bata ce masaba takarasa dakinta, da sauri yabiyo bayanta, tana shiga dakin jiri ya kwasheta ta sulala a kasa tana tari da karfi ta dafe gefen kirjinta daidai gurin zuciyarta, tana kuka, hajja luba dake zaune akan sallaya tayi saurin karasawa gurinta tana fadan rumaisa lfy kuwa, koda taduba taganta tana aman jini tsorata sosai hajja luba tayi dasauri ta kwalawa abba kira, a daidai lokacin ya turo kofar dakin yashigo...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:46 PM] β€ͺ+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*πŸ˜ƒ

73 and 74
Via *OHW*
_A love story_πŸ’

yana shigowa dakin yaga halin da rumaisa take ciki dasauri yasa aka daukota suka nufi asibita,

Sa isarsu asibitin Aka kaita emergency room, aka bata taimakon gaggawa,

Umma, abba , hajja luba duk sun tsorota da ciwon rumaisa, ace yarinya harda aman jini,

Bayan wasu yan mituna likita yafito daga cikin da rumaisa take ciki a hargitse, dasauri su hajja luba suka karasa gurinsa, tun basuyi maganaba likitan yace "tana bukatar karin jini da gaggawa domin jini yafita a jikinta sosai"

Abba duk ya firgice da sauri yace "toh yanzu likita yaza ayi kennan"

Cikin gaggawa likatan yace "kuzo muje a gwada jininku mugani ko za a samu wadda yadace danata" haka kuwa akayi suka bi bayan likitan akaje aka gwada jininsu, na umma ne yayi daidai danata, aka kuwa d'ibi roba daya akaje aka sakawa rumaisa

*BAYAN MINTI 50*
likitan yakara fitowa daga cikin da rumaisa take ciki a karo nabiyu, sun abba sukayi saurin karasawa gurinsa,

Hajja luba hawaye take tana cewa "likita meya faru da itane"

Likita ya dube abba sannan yaja nunfashi yace "'yarku tana daf dakamuwa da cutar hawan jini, domin tunani da damuwa sun mata yawa, meyake damunta?"yakarasa maganar da tambaya

Abba ya dubi umma, umma ta dube hajja luba, sukansu basusan meye damuwarba, abbane yayi saurin cewa "muma bamu saniba likiti, saidai idan zata iya magana mezai hana a atambayeta"

Likita yace "ba yanzu, domin yanxu munsamu munyi mata karin jini kuma yanzu haka bacci take bazata samu farkawaba sai nan dazuwa awa daya"

Abba yace " to shikenan zamu jirata, yadanyi shiru har likitan zaibar gurin sai kuma yayi saurin cewa "likita yanzu ya jikin nata"

Likitan yajuyo yayi ajiyar zuciya sannan yace "tasamu sauki, sosai" yana gama fada yabar gurin, abba yadube umma duk jikinta ya mutu yace "mungode da bayar da jini" murmushi kawai tamasa shima yamata sannan suka samu guri suka zauna suna jirana farkawar rumaisa,

BAYAN AWA DAYA DA RABI

Umma tana zaune kusa da rumaisa, rumaisa ta tafarka tana kallon dakin a hankali,

Umma ta dubeta tace "sannu rumaisa ya jikin" bata iya cewa komaiba saikawai bin dakin take da kallo,

A daidai lokacin abba da likita suka shigo dakin, abba yace "alhmdulillah ta farka" da sauri yakarasa gurinta ya fadan "ya jikin" suna hada edo da Abba rumaisa ta fashe da kuka mai sauti saida hankalin kowa a dakin yatashi, hajja luba takaraso ta rike mata hannuwa tana cewa "rumaisa kigaya mana menene damuwarki, meye matsalarki"

Cikin kuka rumaisa tace "inna bazan iya sakaku kumin abinda baku soba, haka nima bazan iya hana zuciyata tunaniba, bazan taba samun salamar zuciba matukar bana tare da majnoon, ta dube abba sannan taci gaba dacewa "abba majnoon shine farin cikina shine kadai wadda nakeso Dan Allah abba kabarni naganshi koda saudayane...." takarasa maganar tana kuka sosai,

Dakin yayi shiru nadan wani lokaci,

Abba yashiga tunanin maganar rumaisa, tabbas 'yarsa ta susuce akan soyayya da majnoon

Likita ya katse mata tunani dacewa " waye shi wannan majnoon din, daman tanada wadda takesone"

abba yasauke a jiyar zuciya yace "eh tanada amma kuma ai mahaukacine, ni banga ribar auren mahaukaci ga mai hankaliba "

Likita yace " idan har yana raye yakamata azo mata dashi, idan har kunason tasamu lafiya, yakamata ace kacece rayuwar 'yarka, ka ajiye maganar hauka gefe, domin hauka zata iya warkewa matukar ba mugun asiri akayi masaba, wasu iyayen suna bani mamaki, duk da sunsan matsalar yayansu kuma sunada maganinta amma saisu kafe da nuna iko da isa, wannan kwata2 bai daceba, nidai shawarata anan itace kanemawa 'yarka lafiya ka ajiye maganar hauka a gefe, ai ko mahaukaci mutumne"

Abba yayi jim yana nazarin maganar sai cen yadube likita yace " yanzu kana ganin zai iya warkewa kuwa "

likita yace " insha Allah zai warke, indai har ba asiri akayi masaba, kagama idan har kayi haka kasamu riba biyu kenan ga ribar taimako, kuma sannan kanemawa 'yarka wadda takeso"

Abba yayi ajiyar xuciya yace "to shikenan zanje yanzu nazo dashi" yana gama fada yanufi hanyar fita
Likita yiyi saurin cewa "yasan fuskar kane, domin kasan yadda suke, basa yadda da sabuwar fuska"

Abba yadan tsaya kafin ya juyo ya dube likita sannan yace "eh yasan fuskana, domin nataba zuwa mukayi hatsaniya dashi sau daya"

Likita yace "tare zamuje domin banason yaganka yafirgita "

abba yace to shikenan muje,

Tare suka fita

Nan suka fita sukabar asibitin sukanufi unguwra da majnoon yake,

Suna zuwa kuwa suka ganshi kwance yana bacci duk ya kara hargisewa, jikinsa har wani tsamin datti yake,

likitan yatoshe hancinsa, sannan suka suka karasa gurinsa,

Abban rumaisa yadan dakeshi kadan, ai kuwa da karfi yafarka,

Cike da firgita suka hada edo da abban rumaisa, da karfi yatashi yana ja dabaya,

Abban rumaisa yace "tsaya kaji munzone mutafi dakai asibiti"

Majnoon yanajin zancen munzone mutafi dakai, ya zura da gudu, abban rumaisa da likita suka mara masa baya suna kiransa amma ko juyosu baiba,

Kan titi yahaura babu ko duban motocin dake zuwa , ai kuwa yana kai tsakiyar titi, naji abba na fadan katsaya mota ga banka, kafin majnoon ya ankara kaji wani karrrrrrrrrrrr......

Note" Aslm, ina mai baku hkr akn gaskiya bazaku jini kwana biyu ba domin banada lfy kuma gobe zamu fara exam, nagode da nuna kaunarku akan novel dinnan"

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:46 PM] β€ͺ+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*πŸ˜ƒ

79 and 80
Via *OHW*
_A love story_πŸ’

Abba yadan zabura kadan dominshi harya shiga duniyar tunani, gyaran murya yayi sannna yafara dacewa "bansan yadda zakaji maganarba, amma yazama dole ingayamaka ita, soboda koda ban sanar dakai ita yauba to tabbas gobe ko jibi zan sanar dakai komai, wannan daka tambayeni waye shi, nikaina bansan waye shiba, kaddarace ta had'ashi da rumaisa, kuma shi mahaukaci ne, tayi mugun kamuwa da sonsa, nayi kokarin naraba dashi amma nakarasa yin haka, sanadin hakan yasa kaga komai yana faruwa ba daidaiba, kamar yadda nasanar dakai a waya cewa muna asibiti, jiyane bayan faisal yabar gidana, rumaisa tashigo gidan a hasgitse, ina zaune a falo naga shigowarta, nake tambayarsa meya faru amma tagagara mun magana, abin ya tsoratani, shine nabi bayansta tana karasa dakinta tafadi kasa a cikin dakin nan
End Ads