shiru meyake faruwane" momy taja nunfashi kamar zatayi magana saikuma tafasa, daddy ya dubeta yace "fada masa mana"
Momy tayi jim kafin tace "Faisal, rumaisa ta bata, yanzu haka nemanta ake" wani irin tashin hankali yaji ya ziyarci duk ila hirin jikinsa, tuni hawaye suka soma fita a edonsa, kasa yadda da maganar yayi, ya dube daddy yace "daddy idan bazaka amince da aurena da rumaisaba basai kasa ammin karyaba domin karya bata kama cekuba, momy kufa iyayena meyasa bakoson farin cikina"
Daddy ya sunkuwar dakai, wani irin bacin rai yakeji, koda yadagonkansa eedo sa sunyi ja sosai, ya daga hannu ya wankawa Faisal mari, yanaa huci zuciyarsa har wani zafi take cike da masifa yake fadan "so haukane, ko kuka so zai iya sakaka kafada iyayenka magana, idan mun maka karya meye ribarmu...to.to" daddy yakasa yin maganar domin wani irin bacin rai yakeji, Faisal yana dafe da kumatu, yana mamakin wai yau daddy ne yadaga hannunsa ya maresa hawaye kadai ke fita a cikin edonsa, ya dube daddy da momy, muryar na rawa yasomma magana "yaune karo na farko daka fara dukana daddy, badan komaiba sai dan akan innason rumaisa, yadanyi shiru kamar zaiyi kuka, sai kuma yafasa sannan yaci gaba da cewa "bazan hanaka dukanaba domin kai mahaifinane kuma kanada incin dukana aduk lokacin dakasoz, amma bazaka iye cire soyayyar rumaisa a cikin zuciyata ba, idan kuwa kukayi yunkurin rabani da rumaisa ts karfi da yaji to tabbas kuna kokarin rabani da rayuwata ne, kuka yasomayi sannan yamike har a lokacin dafe yake da kumatunsa, kamar zai tafi saikuma yatsaya ya juya musu baya yana fda "idan har kuka rasa wani farin ciki a cikin gidan nan ni zanyi duk yadda zanyi nadawo muku dashi,, ammani abu daya kalilan kukasa cikamun, da kunsan irin yadda nakeji akan son rumaisa da bazaku hanani auren tabs, da kunsan yadda zuciyata kemun zafi a yanzu dabazakuyi yunkurin fadamun wannan maganarba, amma bakomai bazanga laifin kuba amma dai zance kunyi sonkai" yanaa gama fada yanufi hanyar fita,
Momy tani zuciyarta tayi snyi, hawaye take cike da tausayin d'anta daya kasa fahimtar abina suka fada masa, daddy kuwa edinsa sunyi ja sosai yama rasa mezaiyiwa faisal,
Faisal kuwa tunda yatashi tsaye yakejin jiri, yana dibarsa yana kai daf da kofor fita yaji bugun zuciyarrsa yasoma karfi, dafe kirrjinsa yayi yana jan nunfashi da karfi, a hankali ya sulale ya fadi kasa...
Tana tsaye a gurin tana kuka, a hankali ta sulale kasan carfet, Tana rokon Allah daya kara tsareta daga shairin fahad,
Cike da mamaki Fahad yabar dakin, baitaba jin tausayin macce ba idan yazo kosantarba sai Rumaisa,
Dakinsa ya wuce, ya cire rigarsa, daga shi sai singlet da wandon rigar daya cire, yayi zaune bkin gado, yana maida nunfashi, telephone kawai yakira yasa a odo masa giya, bada jima waba kuwa ma'aikacin gidan yashigo dakin da kwalabe a hannnunsa,
ya zubesu a gabansa sannan yafita, fahad yabude kwalba daya yafara korawa yana lumshe edo, kamannin rumaisa kadai kemasa gizo, yarinyar kara shiga ransa take...
Giyar yasha yayi mankas har kusan karfe 2 na dare baiyi bacciba, tunain rumaisa yahanashi bacci, tashi naga yayi yana tangadi kamar zai fadi, yana sambatu yafita, yana tafiya kamar zai fadi yanufi dakin rumaisa, yana zuwa ya tura kofar dakin yashiga..
A inda yabarta a tsaye anan ta sulala kasa, tayi bacci, tayi sharkar kasan carfet, yakarasa gurinta yayi tsaye a kanta, yana kallonta yana tangadi kamar zai fado mata,
kakin amai yasoma yi hakan yayi sanadiyar tashin rumaisa daga bacci taganshi a kanta, da karfi ta zabura ta miki tana fadan innalillahi wa innalillahi raju un,
Amai yafara kwararowa tana tsaye tana kallonsa, wani irin tashin zuciya takeji kamar itama zatayi aman wani irin kyankyami, tayi mamakin ganin fahad yanashan giya, a take cewa lallai kuwa wannan yana cikin bala'I ga nema mata kuma ga shan giya,
Saida yagama kwara amansa sanna ya kalleta yana murmushi cikin salon murya irin ta mashaya yake fadan "rumaisa nakasa bacci saboda ke, com to me plx" yana kokarin fado mata da sauri takauce masa tana kokarin gudu, ya riko hannunta gam, kuka tasaka tana dukan hannun amma yaki sakinta, cizo takai masa, da sauri yasaki hannun yana wash,
Tasamu tabar gurin, yakara daga kasan ya hengeta acen gefe tana kuka tayi wani kakkame jiki,
Yanufi gurinta yana tangadi, yana fadan rumaisa com plx, com an hug me, I need u , rumaisa,
Kokarin kai ga jikinta yake da karfi tasa hannu taturesa, rakafff kakeji yafadi kasa kansa ya daki gefen gado, jini kadan yafito, shiko ajikinsa bai damuba, kokarin tashi yake sai kuma yakasa,
Rumaisa tayi tsaye tana kallonsa, lallai giya bala'ice, ace mutum yajiciwo amma shi baimasan anyiba,
Kasa tashi yayi a gurin ya sulale ya kwanta a hankali bakinsa ke furta rumaisa, I need u rumaisa, " har bacci yadaukesa,
Rumaisa tayi tsaye akansa tana kallon jinin dake fita akansa, tausayi yabata sosai, a hankali ta durkusa gurinsa cike da tsoro jikinta na rawa, ta kira sunansa cikin siririyar murya, taga ko motswa baiba, hannunta na rawa takai a jikinsa tadan dakesa kadan taga bai motsaba,
gabanta yafadi, kardai ace ta kashe dan mutane,
Sai kuma ta lura da kirjinsa na harbawa, hakan ya tabbatar mata da cewa yana raye,
Mikewa tsaye tayi tarasa yadda zatayi, gajini yana fita a kansa,
Jitayi tanason tataimaka masa , a hankali tashiga neman tissue, tsumma a dakin, tazagaye kaf dakin bataga komaiba,
Rigarta ta bacci datazo da ita daga gida ita tatuna, dasauri tadaukota ta yaga sannan tadawo gurinsa har a lokacin jikinta rawa yake, ta daga kansa kadan tasa tsumman ta dauremasa kansa, sannan ta mayar dashi a kwance...
Cike da firgita taja hannun da karfi ta mike tsaye jikinta sai rawa yake,
Hannun fahad kuwa ya sulalel kasa yafadi, har a lokacin bakin sa yana furta I need you rumaisa,
Tajima a tsaye tana kallonsa, kafin taje tadauko sauran tsumman rigar data daure masa kansa, ta share aman dayayi, takara kallonsa ta girgiza duk tausayinsa takeji, sannan tajanye daga gurin, takoma gefe daya acikin dakin ta takure, jikinta sai kyarma yake, a hankali hawaye kefita a cikin idonta, tana tsoron kartayi bacci fahad ya farka ya farmata, soboda haka ta hana idonta bacci sai shanshekar kuka take,
gangad'I tafarayi sai kuma ta farka da sauri, a haka dai bacci yagarara zomata tana zaune tafara jin kiran sallah, nan tamike tashiga toilet tayi alwala sannan tafito,
Ba sallaya a dakin, ta karkade kasan carfet tafara sallah,
Bayan tagama, tayi adu a sosai sannan tafara karanto alqur'ani mai girma a daidai inda ta hadda ce, reroshi takeji cikin murya mai dadi gaske,
Sautin yakeji yana shiga masa kunne yarasa ko meye, jinsa yakeyi kamar ana rairai masa waka, amma dai ba waka bace, a hankali yasoma bude idonsa, a lokacin har gari yasoma wayewa,
Kadan ya iya furta wash, a lokacin yadafe kansa, domin ciwon dayaji yanai masa, a hankali yake kokarin tashi yasa hannu yadafe kansa gefen da yakejin zafin,
mamaki yake meya jimasa ciwo, kuma waya daura masa tsumma a kai, juya yayi gefen daya kejin sautin na fita, idonsa suka sauka kan rumaisa, baki ya saki yana kallonta ita kuwa cike da mamaki ita kuwa wannan metakeyi haka yafada a zuci,
Kamar mai kowon tafiya yafara taka kafarsa yana kokarin karasa gurin Rumaisa, .
Jin motsin mutum a bayanta baisa ta tsayar da karatun da takeba, idonta sunyi ja sosai sakamakon rashin bacci dabata samuba,
Gabanta yazo yayi tsaye yana kallonta, kamar zaiyi magana saikuma yakasa, zaunawa yayi ya kura mata ido yana kallonta, sai yaji ta kara shiga ransa,
Gaban rumaisa duka yake tara2 kanta a sunkuye ta kanne idonta, sai karatunta take billahakki,
Ganin takai karsher sura yasa tadakatar da karatun, a hankali take bude idonta, tadago kanta sukayi ido hudu, tagumi taga yayi yana mata murmushi, cike da tsoro ta iya furta "ina kwana" sai kuma ta sunkuwar da kanta, tana jiran taji mezaice,
murmushi yayi "lafiya lau, sai kuma ya tambayeta meya kawoni dakin nan"
Duk da batason hada ido dashi amma a hakan tadaure ta daga kanta ta kallesa, tayi mamakin tambayar da yayi mata, sai kuma tatuna da cewa kodafa yazo dakin cikin maye yake, ajiyar zuciya tayi sannan tace "cikin maye kazo dakin nan"
"Oh god, Allah yasa ban dakekiba" fahad yafada yana kallon rumaisa,
Sai a lokacin tayi masa murmushi "bakamun komaiba, hasalima nicee..." saita kasa karasa maganar tana kallonsa , fahad yace ihum karasa maganar mana,
Rumaisa tace " a a kabarshi kawai katashi kaje kayi sallah"
Fahad ya zare ido da mamaki "sallah kuma, lokaci yayi ne"
Cike da mamaki rumaisa tace "au bakamasan lokacin salla ba"
Fahad yafada a kasale "nibanma iya sallarba, domin rabona da salla tun ina dan shekara 15. Amma tunda nagirma na daina" yana gama fada yamike yana kokarin fita daga dakin, rumaisa ta bishi da kallo harya fita, sannan tayi ajiyar zuciya tana mamakin rayuwar fahad ace mutum dan musulmi amma bai iya sallah ba, sai taji tanason zama dashi domin takowa masa sallah dakuma addini koda Allah zai saka mata da tukuicin abinda takeso wato majnoon, ( nace kekuwa rumaisa meya ganoki, nacewa saikin kowar dashi addini ko kin manta satoki yayi ) nidai nayi shiru naci gaba da rubutuna
Yunwa tasoma addabarta a hankali ta mike tsaye, tanufi kofar fita tana leken falon, batasan gidanba, ai kuwa tana leka kanta sukayi ido hudu da wani bodyguard fuskarsa a murtuke ba imani, dasauri ta koma cikin dakin ta jingina jikinta a ginin dakin tana jan nunfashi...
Fahad nakarasa dakinsa yasa hannu ya warware daurin da rumaisa taimasa akai, sannan yaje yayi wanka, bayan yafito ya dauko wasu sabanbin kaya yasaka dominshi baya yiwa tufafi sawa biyu,
Yadan zauna a bakin gado yana nazarin kalaman rumaisa, sonta yakeji yana kara shiga masa zuciya, bayajin zai iya rabuwa da ita,
Ajiyar zuciya yayi
Sannan Tashi yanufi dakinta yana shiga dakin yasameta manne a jikin ginin dakin ta sunkuwayar da kai,
kallonta kawai yayi yana murmushi sannan yajuya zai fita, murya kasa2 rumaisa ta furta "yunwa nakeji" fahad ya juyo ya kalleta "to basai kije ki girkaba abinciba, aina gaya miki bazan kara siyo miki abinciba, domin ke matata ce"
rumaisa ta tsuke fuska "to ai bansan inane kichin dinba"
Yadda tayi maganar yabashi dariya, yace "muje nanuna miki "
Rumaisa tazo gurinsa
Tayi tsaye, riko hannunta yayi yana murmushi da sauri ta firgi hannunta cike da tsoro, fahad yace miye haka,
"haramun me namiji yataba jikin macce idan har ba matarsa bace" rumaisa ta fada saikuma taja da baya,
Mumrshi fahad yayi yakara kai hannusa "oya lez go" yana kokarin koma rikota, ta janye daga gurin, tasoma hawaye kuka na kokaron kubce mata, ganin zatayi kuka yasa fahad yadaga mata hannu "ya isa haka muje" fita yayi tabi bayansa tana share hawayenta,
Nan yaje yanununa mata ko ina a gidan duk inda ta daga ido bodyguard take gani, a zuci tace wannan gidan ba wurin fita saidai taimakon Allah ko ina da mai tsaronsa,
haka dai ya gama nuna mata ko ina sannan, yace shizai fita, sai ya yadawo,
Kai kawai takada masa,
Yana fita takoma kichin tafara dafa abinci...
**** ***** **
Tun wayewar ake tursasawa umma akan tafadi inda takai rumaisa amma umma tace ita wallahi batasan inda rumaisa tajeba" tasha duka iya duka, duk jikinta ya kumbura,
Abban rumaisa yana zaune a cikin police station din, domin anan yakwana tare dashi ake ganawa umma wahala, dominshi a yanzu yama daina jin sonta a zuciyarsa, baya mason ganinta, shidai kawai Rumaisa yakeson gani ko a raye ko a mace,
Edonsa sunyi ja sosai domin bai samu bacci ba jiya, daya daga cikin police din ne yaoi gurinsa yana fadan "alhj wlh matar taki fada, nifa ina ganin kamar ba Hannunta a cikin batan wannan yarinyar"
Abba yadago janjayen Idonsa ya kalli police din yace " taya akayi kasan babu hannunta aciki, kaine mijinta, ko kuma kaike tare da ita, ninasan matata kuma nina baku izinin kamata, dan haka idan zaku iya bincikenta ku binciketa idan kuwa bazakuniyaba tokubarta anan har sai zuwa lokacin da akacemun anga 'yata sannan kusaketa" police din zaiyi magana Abba yadaga masa hannu yana huci "karka kara mun magana, bana bukatar jin kowa a yanzu"
Police din ya girgiza masa kai kawai ya fice yabar gurin, abba yajima a gurin yana tunani kala2 sannan yatashi yaje yaja motarsa yabar station din..
**** **** ****
Nikaina bazan iya misilta muku iya kukan da faisal yayiba, a yunin jiya domin yunin jiya yakasance masa kamar ranar mutuwarsa, yakasa cin komai a haka yuni har dare, a daren ma bai samu isanshen bacciba, domin daya kwanta zai fara tunanin rumaisa, dolensa ya mike..
Wayewar gari
Daga wanka yafito yana goge kansa da tawol, jikinsa duk ba kwari, yakarasa bakin mirror yana kallon kwayar idonsa sunyi ja sosai,
Fusakar rumaisa ta soma yimasa gizo a bayansa tana masa Mumrshi ta jikin mirrorn yake ganinta, da sauri ya juya baya saikuma yaga bakomai, hawaye suka sauko masa, a hankali yasa hannu yashare sannan yakarasa gurin shirinsa, kananun kaya yasaka sunyi masa kyau sosai, sannan yasaka ta kalmi cover, ya janyo jakarsa saida ya kallmasa shirinsa na fita aiki sannan yafito waje....
Kwata2 fuskarsa ba annuri, a falo yasami momy a zaune tayi jim tana tunani, a lokacin daddy yafita suna cen gurin fafutukar neman rumaisa, faisal ya durkusa ya yagaidata, ba yabo ba fallasa momy ta amsa tana murmushi "har ka shirya fitar ne "
Yace "eh, banason nayi late ne"
Momy tace " toh amma ai baka karya ba, mutum na fita baici abinciba"
Mikewa faisal yayi yana wunkurin barin wurin yana cewa "bana jin yunwa" yana kallon momy, momy tace "to shikenan Allah yakai lfy"
Faisal ya amsa da ameen, sanna yasa kai yafita yabar gidan yanufi gurin aiki,
Katuwar office ce mai matukar kamshi turaren airfrshn yake a ciki ga takardu birjin akan table,
Faisal yana zaune akan wata lallausar kujera, tana juyi dashi, yayi kuru yana kallon kofar office din, edo sa sunyi ja sosai, tunani rumaisa yake, a ranar daya fara gininta, ba zato ba tsammani hawaye suka soma gaggarowa a fuskarsa, yarasa meyasa son rumaisa yakama zuciyarsa har ta yadda bazai iya mantawa da itaba, son rumaisa yazame masa wani irin tabo a cikin zuciyasa wadda bazai iya warke waba, amma duk da haka yana zargin kansa, ayya soyayya baso take ta horar dashiba, ayya ba alhakin soyayyane yake fita akansaba,
Hawaye suka kara saukowa kan kuma tunsa, a zuci yake fadan DAMA HAKA SO YAKE lallai kuwa akwai babbar matsala da wadda yakamu da son maso wani, hausawa nacewa son maso wani, koshin wahala, a hankali naji sautin kukansa yafara fita, da karfi ya daki table dinda ke gabansa, yana kuka yake fadan " why! Why! Why lov, meyasa kamun haka, meyasa ka ingizani gurin da baa sona, plx lov I accpt my fault, nasan nayi kuskure plx...! Yakarasa maganar yana kuka, ya saukar da kansa akan table din yana kuka,
Yajima yana kukan kafin yaji an fara knocking kofar office dinsa, da sauri yake kokarin share hawayensa tare da kokarin gyara kansa,
Saida ya tabbatar daya saita kansa sannan yace "yes com in" murya a raunane,
Tunda aka bude kofar kamshin turaren almiski yadaki hancinsa, yaji wata irin ni'ima tasaukar masa a jiki, ya lumshe edo, sannan yadago kai ya kalli kofar a lokacin da take kokarin shigowa, caraf suka hada edo tana murmushi, takaraso cikin office din ta zauna a kan kujerar dake duban tashi, kyankyawar maccice ajin farko ga kyau ga murmushi mai kyau, (to wacece wannan) nakasa bawa kaina amsa..
Shikuwa ya kura mata edo, gizon fuskar rumaisa yake gani akan fuskarta,
Tayi shuri tana kallonsa, cike dajindadi taga yau ya kura mata edo yana kallonta, ashe dama akwai ranar da faisal zai kalleta haka, a zuci take fadan