x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - MAJNOON

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 47364 words

Category: Romance Story +18

Views 122

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
yarona, taya akayi hakan tafaru, kina ina kikabarsu suka aika wannan mummunan kudurinsu akansu.." yakarasa maganar yana kuka sosai

Muryata na rawa tasoma magana "nasan komai Mubarak, komai akan edona akayi, KISAN GILLA sukayi musu"

Mubarak yafito daga jikin ummansa yace "umma mesukayi musu"

Umma tashare hawayenta sannan tace "babu abinda sukayi musu Mubarak, ranar dakayi tafiya zuwa abuja, a ranar suka kashesu, bayan tafiyarka, naje sashenka zanje na dauko khalid daga gurin mamansa domin nai musa wasa, ina karasa sashen, natarar da adnan menan kashe matarka, ina sauri nakarasa gurinsu, amma ina kafin nakarasa ya soka mata wuka a ciki, anan nayi saranda nakasa zuwa ko ina, akan edona bayan yagama da matar taka, ya dauko yaron shima yayakashi, tashin hankali nagani karara, ihu nasa haka yayi sanadiyar adnan ya biyoni da gudu, nima da niyar zai kasheni, da gudu nafita ina ihu, neman taimako, harna karasa shigowa sashena, ina shigowa anan kuma natarar da mutane ana kuka, koda na tambaya akancemun kaine ka mutu..." kuka ya kubuce mata ya hata karasa mganar,

Zuciyar Mubarak tayi zafi sosai, huci yasomayi duk hankalinsa yatshi mikewa tsaye yayi yana huci, yakarsa kusa da adnan ya shaki wuyansa, yana fadan "kaima saina kasheka irin kisan da kayiwa ahalina" ya shaki yuwansa, shakar dabazai iya furta komaiba,

Bodyguard sukayo kansa suna kokarin hanashi, basu karasa gurinba, mai martaba ya daga musu hannu, alamar karkowa ya hanashi, dole sukaja da baya,

A haka Mubarak yaci gaba shakar wuyan adnan cikin zafin rai, saida ya dauke nunfashi, tun yana shure har yazo yadaina, (Wannan shi ake kira da KISAN GILLA my next novel )

Saida yadaina motsi Sannan yasakesa, yana huci,

Rashin imani karara umman adnan tagani, a hankali take kai hannunta ta riko hannun adnan anan taji hannu yayi nauhi, tana sakin hannun kuma taga ya sulala kasa,

Wata irin kara tayi tana kuka tace " ya mutu, adnan karka mutu, dan Allah karka mutu kabarni, wayyyyyoo, takara saka ihu, ta dora kanta kan kirjij gawar adnan, tana kuka,

Mubarak yana gurfane agurin, duk ya fita hayyacinsa, zuciyarsa sai zogi take masa, har yanzu bai huce yakaicin rashin matar saba da yaronsa,

Kamar daga sama umma adnan tatsayar da kuka ta dago kanta ta dube Mubarak, edonta sunyi ja sosai, tayi ihu ta cafki wuyan Mubarak tana sunbatu "kaima saina kasheka kamar yadda kakesemun yarona" mugun shaka tamasa
Mubarak yakasa kwabar kansa,

Bodyguard sukayo kanta, da kyar suka iya babbare hannunta akan wuyansa,

Mubarak ya galabaita sosai, tana sakinsa ya sulale yafadi kasa somamme,

Ita kuwa ihu ta saka, tana kuka take fadan "sunkashe, wlh banyafe mukuba, mugaye azzalumai, maciya amana" tana cikin magana saikuma tasaka dariya,

Bodyguard suna rike da ita tasoma, kuce kuce tana ihu da karfi, tamkar zautanciya, sambatu kawai takeyi,

Mai martaba yana tsaye, tunda aka fara maganganun yakasa iya furta komai, tunanin yadda abin yakasance kawai yake,

Ihun umman adnan ne yadamesa, da karfi ya juyo, cike da hargowa yace " kufitarmun da ita daga cikin dakin nan, kukaita cen cikin dakin bayan gida kujefata a ciki kurufeta"

Haka kuwa akayi, suka fita da umman adnan aka kaita cen dakin bayan gida aka rufeta,

Suka dawo aka kwashi gawar Adnan akaje a kayi mata salla, harda mai martab, dakuma faisal, sannan aka kaishi makwancinsa, anyi masa hukunci daidai irin wanda ya aikata, kuma wanda shari'ar musulunci tatanada, wannan shine gaskiya
□□□□ □□□□ □□□□
_Bayan wasu awanni_

Mubarak yafarfado, duk ya jigata, hankalinsa, baya kansa sai sabbatu yake, yakasa natsuwa

Daman dr bukar yana gidan, yacewa mai martaba, kawai yabari amasa allurar bacci, idan yasamu bacci kona wuni daya ne to tabbas idan yatashi kwakwalwarsa zata samu relax,

Mai martaba ya amince da maganar dr bukar, aka narkawa Mubarak allurar bacci, nan yashiga sharara baccinsa,

Bawani zaman makoki da akayi, kowa ya watse yakama gabansa,

A daren ranar mai martaba yasa aka kira masa faisal yace yanason faisal yasanar dashi komai daya sani akan Mubarak, kafin suzo dashi nan..

https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:54 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

115 and 116
Via *OHW*
_A love story_💝

Faisal yayi shiru, yana nazarin mema zai fada nan, sai ce dai yafara fadowa mai martaba komai daya sani akan lamarin majnoon, tun daga mahaukansa, har zuwa cutar daya samu sannan kuma da maganar aurensa da Rumaisa, wanda ya tarwatse ana daf da daurasa,

Mai martaba ya girgiza akan lamari, kuma yaji dadin taimakon da abban rumaisa yayi akan Mubarak,

Tausayawa 'yar tasa yayi kamar yadda yaji faisal yafada, tana matukar sob Mubarak sosai, lokaci daya yaji son, yarinyar yashigo ransa, saboda shi yanason duk wani maison Mubarak, ajiyar zuciya
Mai martaba yayi sannan ya dube Faisal yace " kabani number mahaifin rumaisa zamuyi magana dashi"

Cike da rawar murya faisal yace "banada numbansa, amma zanbaka ta daddyna atare suke komai, duk maganar da kukayi zaije yafada masa yanzu"

Mai marta yace " bani number abban naka"

Nan Faisal yashiga karanto masa yana yasakawa,

Saida yagama sannan mai martaba yakira number, cikin sa'a kuwa wayar tashiga,

Mai marta yayi sallama, daddy ya amsa, sannna mai martaba yace "mahaifin Mubarak ke magana, daga kogi"
Muryar daddy na rawa yace "eh nagane.."

Mai martaba yace "yawwa, nasamu labarin kunason kuhada aurensa da 'yarku"

daddy ya tsora sosai,har lokacin muryarsa bata daina rawa ba "Eh hakane yallabai" sai kuma yayi shiru,

Mai martaba yayi murmushi yace "karka samu damuwa, daman nakirakane inaso nasanar dakai cewa, karku fasa daurin auren nan, inason a daura auren nan a yau bayan angama sallar isha, sannann kuma kai kaneson kawakilci yarona Mubarak, daga baya koda zuwa jibine zaizo yadauki matarsa"

Bakaramin dadi daddy yajiba , yayiwa sarki godiya soaai sannan suka katse wayar,

Faisal dake zaune jigum, yayi tagumi, azuci yake fadan "nikam dai banda sa'a, a kullum sainaga samu saikuma naga rashi, shikenan na rasa rumaisa, 😰)
□□□□ □□□□ □□□□
Cike dajindadi daddy yashiga mota yaje gidan abba yasanar dashi komai da mai martaba yace asanar masa, shima yayi na'am da wannan abin, kuma ya amince da a daura auren rumaisa da Mubarak bayan sallar isha,

Goron da suka saya kawai sukaje suka dauka, sukayi alwala suka nufi masallaci,

Sukayi salla isha bayan angama, tun ba'a fara fitaba, abba yakarasa gurin liman, yasanar dashi cewa yanason ayi daurin auren 'yarsa a yanzu, lamarin ya girguza liman dakuma mutane dake cikin masallacin, sunyi mamakin yin daurin aure cikin dare,

Haka dai aka rabawa mutane goro bayan angama daura auren yarima Mubarak da Rumaisa, ( saidai kawai muyi musu fatan Allah yabasu zaman lafiya)

Sannan kowa ya watse, abba yakoma gida cike da farin ciki, yagawa umma da haj luba, komai dake faruwa suma sunyi farinciki soaai, abba yanemi alfarma a gurinsu cewa karsu fadawa rumaisa komai dake faruwa, subarta kawai ayi mata AUREN BAZATA,,

Rumaisa na dakinsa sai faman kuka take, jitakeyi kamarma yau dinnance ranar mutuwarta, saboda ita yanzu jitayi kamar batada sauran wani amfani a duniya yanzu tunda aka rabata da Majnoon dinta.. ( amarya rumaisa ansha kuka )

Wazai iya zuwa yafadawa rumaisa cewa, tafa zama amarya yakamata yadaina kuka😜😜

https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:54 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

117 and 118
Via *OHW*
_A love story_💝

_Bayan kwana biyu_
*KOGI*

Umman Mubarak tasamu lfy sosai, domin yanzu dakowama zata iyi yin fira, ta warke sumul tadawo kan karagarta ta sarauniyar kogi,

Mubarak mahaka shima yasamu sauki, amma haryanzu zuciyarsa tana cike da zogi da radadin rashin matarsa da kuma yaronsa,

Yan kwana biyun nan duk ya kauracewa mutane, bayason zama cikin mutane yafison zama shikadai,

Yauma kamar kullum yana zaune ciki dakinsa yayi jugum yana tunani ya game hannayensa akan kirkijinsa yana kallon saman dakin, shima bashida labarin aurensa da rumaisa,

Mai martaba da ummansa suka turo kofar dakin suka shigo, suna murmushi, Mubarak yabisu da kallo har suka karaso kusa dashi suka zauna,

Mai martaba yadafashi yana kallonsa yace "Mubarak komai daya faru dakai mukaddarine daga Allah, mutum bai isa ya gujewa kaddarar saba, yakamata ace kayi imani da kaddara, anason kowanne musulmi yayi imani da kaddara ta alkhairi ce kota shairi, karfa kakasacin jarabawar da Allah yake maka"

Hawaye suka soma sauka kan kumatun Mubarak, zaiyi magana kuka yakubuce masa yasoke kansa cikin kirjin mai martaba yana kuka yace "kashe sufa akayi, kuma KISAN GILLA, kisan rashin imani, mesukayi masa, meyarona yamasa, yaro karami dan shekara daya, haba wannan rashin imanin yayi yawa ..." yakarasa maganar yana kuka,

Mai martaba yarika shafar Bayansa a hankali, sannan yasauke nunfashi yace "kayi hakuri komai mai wucewa ne, kadaina kuka"

Umma tayi ajiyar zuciya sannan tace "kadaina kukan nan mana Mubarak, mamaci adu'a yakeso ba kukaba"

Sai lokacin aka samu yadan sassauta kukansa yafitar dakansa daga cikin kirjin mai martaba yashare hawayesa sannan yace " insha Allah umma daga yau nadaina kukan nan zanci gaba da rayuwa kamar yadda kowa yakeyi"

Murmushi mai martaba yayi "haba kokaifa, ai hakan yafi"

Suduka sukayi murmushi, sannan mai martaba yayi gyaran murya kafin yace " amm daman munzone musanar dakai, cewa yakamata kaje Abuja kazo da matarka, domun azo nan asha Biki"

Gaban Mubarak yafadi cike da mamaki yake cewa "mata kuma abba yaushe akayi auren banace afasaba, nifa bana sonta"

Umma tayi saurin cewa "to mudai ko baka sonta mun riga mun daura muku aure saidai kayi hkr, domin mu bazamu zamo butuluba, a yadda naji labari, yarinyar nan tayi maka taimako sosai a rayuwarka"

Mubarak yafara gunguni, mai martaba yace "katashi kaje kayi wanka, kafin kafito zansa ashirya maka motoci, kaje kazo da matarka"

Amma abba, nifa bana sont..." mai martaba yadaga masa hannu yadakatar dashi dacewa "indai kanason farin cikinmu, to katashi katafi, ta wannan hanyarne kadai zamu sakawa yarinyar nan aka abinda tamana akanka" yana gama maganar yamike yanufi hanyar fita, umma ta mara masa baya, atare suka fita, sukabar Mubarak zaune akan gado zuciyarsa cike da sake2,

Har suka fita Mubarak kallon kofar yake, bayan sun fita yaja tsaki, sannan yatashi akasale "wannan wane irin AUREN BAZATA ne, aure babu ko soyayya" yafada yana kokarin shiga toilet yayi wanka,

Bayan yafito yazo bakin mirrio yashafa mai, sannan yaje yadauko wasu hadandin kayan sarauta yasaka, bakaramin kyau yayiba, yafito yarimansa sak, yazo bakin mirror yana kallon kansan, sai kuma yayi murmushi,

Wani irin farin ciki yakeje a yanzu bayan fitowarsa daga toilet wanda shikansa baisan da zuwansa ba,

Tun a lokacin daya samu labarin matarsa da yaronsa sun mutu, baikara tsintar kansa cikin farin cikiba kamarna yanzu ba,

Saida yafeshe jikinsa kaf da turare sannan yafita, koda yakarasa harabar gidan,

Mai martaba yasa anjera masa motoci a kalla zasukai guda biyar,

Yana zuwa yashiga mota ta tsakiya nan suka fita daga hatabar gidan suka hau hanya, mai martaba yayi musu fatan Allah yakai lafiya yadawo dasu lfy,

Suna barin gidan, mai martaba yakira abban Rumaisa yasanar dashi cewa gasu Mubarak nan kanhanya,

Abba rumaisa yayi farin ciki sosai, bayan sun katse wayar Sannan yaje yasanar da umma da haj luba, nan fa suka shiga gyaran gidan, rumaisa tana dakinta, cikin bakin ciki batasan irin wainar da ake toyawaba,

Sai bayan sungama shirya gidan tsaf sannan umma taje dakin rumaisa, a kudundune tasameta gefen gado, kamar shege a gurin rabon gado,

Umma tazauna kusa da ita, tafara yimata 'yan nasihohi akan tadauki kaddara akan abinda yafaru da ita,
Nasihohin sun ratsa jikinta sosai, daga kashe dai umma tace "yanzu dai kitashi kije kiyi wanka domin zamuyi baki a gidan nan, kuma dan Allah karki nuna masu alamar kina cikin damuwa, kisaka fuskarki a murmushi kinji"

Murmushi karfin hali Rumaisa tayi " tohm umma insha Allah zanyi kokarin yin hakan"

Umma ta mike tana murmushi "tohm shikenan idan kin gama wanka kikirani nazo zabama miki irin kalar tufafin da zaki saka"

Rumaisa tace " tohm" tana gama fada, umma tajuya tana kokarin barin dakin, Rumaisa ta kwalla mata kira , ta juyo , Rumaisa tace "umma halam bakin waye zasuzo" takarasa maganar tana Murmushi, itama dai fada mata din nan da akayi baki na nan zuwa, harta soma jin farin ciki, wanda batasan meye dalilin yinsaba,

Umma tayi murmushi tace "bakin abban kine " tana gama fada ta fice tabar dakina,

Rumaisa tatabe baki "bakin abba, daga ina kuma? " itaka kadai take magana,

Murmushi kawai tayi sannan tafada toilet,

Wanka tayi sosai domin tana wankan tanajin nishadi, kamar bata cikin wata damuwa, karasa wannan tafito,

Bayan tafito harta zauna tana shirin fara mekup tatuna da umma tace takirata idan tafito,

Tashi tayi ta janyo hijab tasaka, tana kokarin bude kofar, a daidai lokacin umma taturo kofar tashigo, tayi turus tana kallonta tana sosa kanta " amm daman yanzu nake batun zuwa kiranki saikuma gashi kinzu"

Umma tayi murnushi tace "gani nayi baki fitoba shine nace bari ninazo, kin fitone?"

Rumaisa tace "eh nafito"

"Tohm jmuje"
Bakin mirrio suka fara zuwa umma ta taimaka mata tayi kwalliya mai kyau,

Sannan umma taje tadauko mata wasu sabanbin kaya daga cikin kayan aurenta da kabir, rumaisa ta karba tasaka bakaramin kyau tayiba, sai faman murmushi take,

Sai da umma ta tabbatar data shirya rumaisa tsaf sannan tabar dakin, tabarta a tsaye tana tubanin wai suwaye zasuzo haka, dahar za'ace sai umma ta shiryata, saikace wata small girl...

https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:54 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

119 and 120
Via *OHW*
_A love story_💝

Da yamma ana batun suka sauka garin abuja,

Basu dire ko inaba sai kofar gidan su rumaisa, mai gadi ya wangale musu kofa, suka fara jiro motocinsu a cikin gidan,

Abba yafito cike da fa'a yatar besu, yakarasa dasu dakin baki,

Rumaisa tana zaune a cikin dakinta sai kukan motaci takeji suna direwa a harabar gidansu, taso tatashi ta leka ta Window domin tagani amma sai kuma kawai tafasa,

Tana zaune umma tashigo fuskarta dauke da fara'a,
ganin umma tashigo yasa ta mike tana fadan "umma sunzo koh"

Umma tayi saurin cewa "eh sunzo, kaje dakin baki, sunacen saiku gaisa"

Tohm " kawai tacewa umma kanta soke akasa tafita tabar umma tsaye acikin dakin, tanufi dakin baki,

Cike da faduwa gaba tatura kofar dakin baki, wani irin kamshi ya doki hancinta, dasauri ta sauke nunfashi, sannan ta taka kafarta a cikin dakin, tare dayin sallama,

Yana zaune kan kujera yayi wani irin zama kasaita, yajuyo sallamarta, a hankali ya dube inda take tare da karba sallamar, a lokacin hartashigo dakin kanta a kasa tayi tsaye guri daya, takasa zuwa ko ina,

Yabita da kallo zuciyarsa sai duka takeyi da karfi, a hankali take jiyo sautin Muryar sa yana fadan "shigo mana" tunda tajiyo sautin muryar takejin gabanta na faduwa,

Taso ta dago kanta domin ta gazgata sautin da kunnuwanta kejiyo mata, amma kuma saita tsinci kanta da kasa yin hakan,

Bata dago kantaba a haka take tafiya kanta a kasa harta karasa bakin kujera tazauna,

Yanayin yadda tazauna yabashi dariya, yayi d'an murmushi kadan yana kallonta yace "amm fuskar taki tsadane da ita dahar bakyason d'agota mutane sugani"
Gaban rumaisa yakara faduwa itadai jitakeyi kamar tasan mai muryar,

kuma akace mata baki sunzo, ita da taji saukar ambaliyan motoci a harabar gidansu, ai yakamata taga mutane a dakin akalla sukai su goma amma saita rika jin muryar mutum daya,

kodai sauran bazasuyi magana bane saita dago kanta, duk a zuci take wannan zancen,

A hankali take dago kanta sukayi edo hudu da majnoon dinta, saida taja da baya saboda razana, ayya kuwa edanuwanta gaskiya suke nuna mata cewa Majnoon ne a kusa da ita,

Suka kafe juna da edo suna kallon juna cike da jindadi da nishadi,
Sun jima a haka kafin bakinta yasoma rawa tanason ta furta wani abu, Mubarak yadaga mata hannu "basai kinyi maganaba ninidai mubarak, ba mafarki kikeba, domin nasan zuciyarki zata saka miki hakan"

Murmushi rumaisa tayi jitakeyi kamar ta burma ihu, dariyar haure daya tayi tana kallonsa tace "mekazoyi gidanmu"

Nunfashi Mubarak yasauke yana kallonta yace "ummm nazone natafi da matata"

Rumaisa tadan zare edo cike da mamaki tace "wacece kuma matar taka, kuka ina take"

Sai da yayi murmushi Sannan yace "a yanzu haka ina tare da matata, wacca tadawomin da rayuwata daidai kamar a baya, natashi daga Majnoon nakoma Mubarak"

Dariya maganar tabata, tare da mamakin ta ina yasan dacewa shi Majnoon ne,

Takara kafe edonta akan nashi tana murmushi tace "wacece?"

Shima yayi murmushi yace " RUMAISAN MUBARAK"

Gabanta yasake yafaduwa tana cike da mamakin yaushe aka daura mata aure da Mubarak, bayan tasan dacewa ana daf da fara daurin musu aura komai ya yatarwatse,

Dakatar mata da tunaninta yayi daceewa "karkiyi mamaki, domin nasan dacewa yanzu haka shikikeyi akan ya akayi aka dauramun aure dashi, nima a bazata abun yazomin, bayan nakoma gida abinda yafaru shine mummunan
End Ads