x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 16 - MAJNOON

  • 45001 words
  • 47364 words
  • Out of 47364 words

Category: Romance Story +18

Views 123

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*πŸ˜ƒ

127 and 128
Via *OHW*
_A love story_πŸ’

_Washe gari_

Daddy yaje yasami abban zarah suka daidaita komai, damacen ashe sunsan juna abokanan junane, nan dai suka tsayar da maganar auren nanda wata daya, haka dai suka rabu kowa yana cike da farin ciki,
β–‘β–‘β–‘β–‘ β–‘β–‘β–‘β–‘ β–‘β–‘β–‘β–‘
_Bayan wata daya_
*KOGI*

Yaune su Rumaisa zasu dawo daga honeymoon dinsu, tunda safe mai martaba ya turo motoci airport,

Suna sauka aka daukosu suka dawo gidan, Rumaisa takara kyau da haske tayi bul2,

Suna shigowa falon suka tarar da umma da mai martaba, rumaisa ta rungume umma, suna hada jiki da umma, kamshin turaren umma yadaki hancinta, nan take zuciyarta tatashi, yankuri tayi zatayi amai, dasauri tabar falon tafada toilet, ai kuwa NAN tafara kwararo amai,

Hankali kowa saida yatashi, da sauri mai martaba yakira dr bukar akan yazo yadiba,

Bada jima waba kuwa yakarsa gidan, yaje ya dubata,

Bayan ya dubata ya tabbatar da musu dacewa tanada juna biyu,
Bakaramin farin ciki sukayiba, Mubarak saida yayi hawayen farin ciki, akan dadi,

Mai martaba yayiwa dr bukar kyauta ta musanman sannan yabar gidan,
β–‘β–‘β–‘β–‘ β–‘β–‘β–‘β–‘ β–‘β–‘β–‘β–‘
*ABUJA*

bikin Faisal da zarah saura kwana biyu, har an fara hidimar biki, domin har ansaka zarah a lalle,

Yauma walimar mata ake, sun kira malamai mata dayawa sunzo sunyi nasiha sosai akan abinda yashafi zaman aure,

Soyayyar faisal da zarah kuwa kullum kara yaduwa take acikin zukatansu,

_Bayan kwana biyu_

A yaune aka daura auren faisal da zarah, bayan shafe fatiha, kowa fatan zaman lafiya yake musu,

Babu yadda faisal baiba da Mubarak yabari rumaisa tazo aurensa amma yaki, acewarsa bayason ta wahala, saboda juna biyun dake jikinta, yace shidai zaizo ya wakilceta,

Haka dindai akayi shiyazo bayan an gama daurin aure yakoma kogi,

Da dare aka kai amarya zarah dakin angonta faisal, burinta yacika ta mallaki faisal, farin cikinta, muradinta, sannan kuma burinta,

Abokanan ango suka kawo ango, sannan kuma kowa ya watse abarsu subiyu, daga ango sai amarya,

Faisal ya umurceta data tashi suyi sallah, sukayi alwala atare suka dawo suka yi sallah,

Sunkwararo adu'a sosai akan Allah yabasu zaman lafiya,

Bayan sun gama suka tashi, zarah kam bawata kunya a gurin Faisal, duk abinda ya buka tabashi, kuma sun raya auren su cikin farin ciki da kaunar juna,
β–‘β–‘β–‘β–‘ β–‘β–‘β–‘β–‘ β–‘β–‘β–‘β–‘
_*BAYAN SHEKARA HUDU*_

*KOGI*
Rumaisa ce a tsaye tana gyarawa Mubarak saka hularsa, saida ta tabbatar da hular ta zauna A kansa daram, sannan ta janye hannunta tana murmushi, shima murmushin yakemata, sannan tace "amma fa kayi kyau"

Ya lakuci hancinta yace "ai duk wannan kyau sanadinkine, domin badan keba da yanzu ina nan a matsayina na MAJNOON" suka kwashe dadariya suduka, rumaisa tace "uhh wayaga MAJNOON da Rumaisa" suka kara kwashewa dadariya,

Rumaisa tadan tsayar da dariyarta sannan tace "tunjiya fa nake magana akan inaso naje naga su umma amma kayimun shiru, kusanfa shekara kenan banjeba, dan Allah kabarni naje sati daya zanyi indawo"

Ajiyar zuciya Mubarak yayi yana kallonta tabashi tausayi yace "toh shikenan kishirya zuwa jibi saiki wuce, amma fa karki wuce sati dayan nan fa domin ayanzu ke wani bamgarece na jikina idan bakya a kusa dani, bana samun farin ciki" yakarasa maganar tare da kifta mata edo,

Murmushi tayi masa tana kallonsa tace "toh MAJNOON dina" ta saka dariya, tana ja da baya,

Mubarak ya nunata da dantsa cikin wasa yace "bazaki daina bako"
Tana dariya tatoshe bakinta tace "to nadaina shikenan, bazan karaba rabin raina"

Tana cikin dariya aka banko kofar dakin da karfi, aka shigo wani dan kyankywana yarone, kamannin sak dana MAJNOON wai Mubarak nakeson nace shiya yadauko,

Da gudu yakarasa gurin rumaisa ya rungumeta yana dariya yana fadan "ammi kice karka grandma ta dakeni"

Rumaisa tafitar dashi daga jikinta tana murmushi ta kallesa tace "AREEF meka mata ne, ai nasan bazata dakeka abanza ba"

Yajuya yana kallon kofar kafin yace "nifa ba abinda namata da wasa nake mata, cije mata kunneta kawai nayi shine wai saita dakeni"

Mubarak yayi murmushi yace "zonan areef" da gudu yakarasa gurin Mubarak, mubarak ya tallabesa sama yana masa wasa yace "karka kara cizarmun umma, idannkuwa kakara nima zan cije amminka" suduka suka kwashi dariya, areef yace "papa! Zaka kaini insha Ice cream yau"

Mubarak yace "zan kaika yanzuma kuwa, je ammin ka tamaka wanka ta shiryaka kazo muje"
yana kokarin saukesa kasa,

Rumaisa tace "nima wlh bazaku barniba tare zamuje"

Haka kuwa akayi suka shirya suduka suka fita sayen ice cream, haka rayuwar gidan yarima Mubarak take kasancewa cike da farin ciki da kaunar juna,

Sai kusan azahar suka dawo
Bayan sundawo suka tarar da mai martaba ba lafiya,

Dasauri suka isa sashensa, suna shiga suka gansa kwance kan gado, umman Mubarak tana zaune a kusa dashi, areef yaje ya fada jikinta,
Tayi murmushi tace "bamunyi fadaba"
Areef yace "toh kiyi hakuri bazan sakeba" murmushi kawai tamasa, sannan Mubarak yace "umma wai meke damu abba ne"
Umma tace "ai kasani ciwon sane yatashi, kuna fita, wannan ciwon yaki sakinsa, kusan shekara biyu kenan, kullum saiya kwata, sai.kuma ya kara tashi" takarasa maganar cike da nuna damuwa,

A daidai lokacin mai martaba yadago hannusa ya kira Mubarak, yaje zauna kusa dashi, mai marta ya rike hannusa yace "Mubarak nifa tsufa yazomin, babu yadda zanyi dole saina sauka kan mulkinnan, bazan iya jira saina mutuba, domin inason insamu farin ciki kafin hakan, dan haka zanyi murabus kai kahau kujerar"

Gaban Mubarak ya fadi, harga Allah shidai bayason mulkin nan, domin bayason abinda zai tauyesa ya hanashi farin ciki da iyalinsa, amma babu yadda zaiyi, domin shine magajinsa,
Cikin rawar murya yace "nikuma"
Mai martaba yace "eh kaidin, kuma banason nadin sarautarnan ya wuce nan da sati biyu, dan haka kaje kishirya duk abinda zaka shirya kafin zuwan wannan lokaci"

Ba'a son ransaba ya amsa tayin mai martaba, akan sai karbi sarautar kogi, sannan yabar dakin,
Rumaisa kam dadi taji har cikin zuciyata, zata zamo matar sarki, arika kiranta da princess rumaisa
β–‘β–‘β–‘β–‘ β–‘β–‘β–‘β–‘ β–‘β–‘β–‘β–‘
Jibi aka hadawa Rumaisa kayanta ita da areef suka wuce abuja,

Bayan sunkarasa abuja, umma tayi matukar farin cikin ganinsu, haj luba ma tana gidan, domin abba yahanata komawa sokoto, ba a son rantaba tazauna abuja,

Sunyi farin ciki sosai da ganin jinikansu ya girma yayi wayo, yaro mai kyau da shiga rai,

Yau kwanan su biyu a abuja, areef ya aza masifa akan shi ala dole sai ankaisa yasai ice cream,

Rumaisa ta shiryashi sannan suka fita tare, bayan sun karasa gurin mai ice cream, suka siyo sannan suka juya suka nufi gurin mota,

Tana kokarin bude kofar motar, tajiyo sautin wata murya a kusa da ita ana fadan "Aina gaya miki zan dawo, bazaki taba gujemunba"... dam, dam gabanta yafadi, domin tasoma gane mai muryar, a hankali take dago kanta, caraf sukayi edo hudu da FAHAD....

https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:55 PM] β€ͺ+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*πŸ˜ƒ

*Last episode*

Via *OHW*
_A love story_πŸ’

Firgita karara ta bayyana a fuskar Rumaisa saida taja da baya saboda tsoro, ya kura mata edo, kamar ya cinyeta,

Da kyardai tasamu tayi controling kanta ta dago kanta ta dube cike da bacin rai ta tsuke fuska tace "karka kara mun magana, ni matar aure ce.... " bata karasa maganarba taga wata yar karamar yarinya ta nufi inda suke da gudu tana fadan "daddyyy" rumaisa ta tsureta da kallo,

Yarinyar ta zuwa ta fada jikin fahad cikin shagwaba tace "daddy shine kazonan koh, nida momy munacen muna jiranka"

Fahad yayi murmushi ya tallabo yarinyar sannan yace "sorry my little RUMY, ina nan gurin mamanki"

Rumy tace " wacece mamana,? Momy fa tana cikin mota"
Fahad ya nuna rumaisa yace "gatanan"

Rumy ta juyo ta dube rumaisa tace "daddy wacece kuma wannan"

Fahad yayi murmushi yace "sunanku daya keda ita, ta sanadiyarta kika samu wannan"

Rumaisa duk mamaki yacikata, a hankali tana murmushi ta dube fahad tace " kayi aurene?"

Fahad ya ajiye rumy kasa, yana jiyeta tazura da gudu tana fadan "bari naje nakira momy"

Sannan Fahad yace "ga alama nan kingani, bayan rabuwarmu nasamu shiryuwa sosai, nazamo cikakken mutum, sannan kuma nayi tunanin bakomai mutum ke nema a rayuwarsa yasamuba, daman tun cen Allah yayi keba mamata bace, nayi nadama sosai akan abinda namiki, najima ina nemanki akan nabaki hakuri, sai yau Allah yahadamu, dan Allah rumaisa kiyafemun"

Rumaisa tayi murmushi, yabata tausayi sosai "nayafe maka fahad, nidaman ban rikeka a rainaba, ina matar taka take"

Yajuya yana nuna mata mota, a daidai lokacin wata farar mata tass tafito daga cikin motar tana rike hannu rumy, suka nufo inda su Fahad,

Rumaisa tace wow!! Beauty ce, Allah yabarku tare" murmushi kawai yamata tare da cewa "ameen"

Suna kara sowa suka gaisa ita da rumaisa,
Matar tace "rumaisa koh?" Takarasa maganar tana kallon rumaisa

Rumaisa tayi yake tace "eh nice kefa ya sunanki"

Matar tace "sunana Sadeeya, amma anfi kirana da ummi"

Rumaisa tace " to fa, sannu ummi, ya gida"

Ummi tace " lafiya lau, amm my husband yajima yana bani labarinki, yacemun kece silar gyara masa rayuwasa, gaskiya ngode miki sosai, domin ni kika taimakawa, yanzu jinake kamar nafi kowacce macce sa'ar miji aduniya, kinga yana bani kulawa, tufafi..."

Fahad yayi saurin katseta dacewa "toh bbc yanzu zata fara ruba miki surutu, idan kika biye ta wannan saimu kwana anan Allah" sukayi dariya su duka,

Fahad yasha kan areef yace " wannan yaronkine, ya sunansa"

Rumaisa tace "sunansa Areef"

Fahad ya dube areef yace " sannunka malam areef mugaisa koh"

Areef ya mika masa hannu suka gaisa, rumy ma ta mikawa areef hannu "mugaisa areef" saboda yarinyar akwai kaudi, da surutu saikace mamanta, areef shima yabata hannu suka gaisa,

Nan dai suka kulla zumunci, sannan fahad yaja iyalinsa suka wuce, ta glass din motar rumy take yiwa areef hannu har suka bar gurin,

Rumaisa tayi tsaye tana kallon titi, tafada duniyar tunani, tunani take ashe haryanzu fahad bai manta da itaba,

Areef ya tabota tadan zabura Sannan tadawo hayyacinta sannan suka shiga mota suma suka koma gidan,
β–‘β–‘β–‘β–‘ β–‘β–‘β–‘β–‘ β–‘β–‘β–‘β– 
_Bayan sati biyu_
*KOGI*

Mai martaba yayi murabus aka dora Mubarak aka karagar mulki,

A ranar da aka nad'a Mubarak akan karagar mulki, a ranar haj zainab rai yayi halinsa, ta mutu, sakamakon bakin ciki daya saka zuciyarta har bawa lokaci daya ta gaggara zuea lahira,

Mai martaba yasa aka kaita gidanta, na har abada wato(kushewa)

_BAYA WANI LOKACI_

Hakadai rayuwarsu tayita tafiya cikin Farin ciki da kumwa kwanciyar hankali,

Mubarak yana kwance saman gado, yayi shiru kamar bacci yake, rumaisa taturo kofar dakin tashigo, karasawa tayi bakin gado, tana kallon mijinta, tayi murmushi sannan tajuya masa baya itama ta kwanta,

Sai yadaina jin motsinta sannan ya bude edonsa ya juyo ya kalleta yaga tajuya baya tana bacci,

A hakali ya yaye blanket dinda ke jikinsa yakarasa kusa da ita yasa hannu ya juyo da ita daidai kirjinsa, yahauro ta kanta, yadora goshinsa akan nata,

Suna shakar nunfashin juna, a hankali take bude edonta sukayi edo hudu, murmushi yasakar mata itama tayi masa a hankali yake furta "yau fa MAJNOON yanason yanema areef kane" kanne edonta tayi tana murmushi,

Shima yayi dariya sannan yafara gudanar da aikinsa,.......😜

_BAYAN SHEKARU DARI UKKU DA HAMSHIN_

Kowa ya mutu, tun daga kan makaranta har zuwa marubucinπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
KURUNKUS,
ALLAH YASA MUCIKA DA IMANI

ALHAMDULILLA

Anan nakawo karshen wannan d'an takai tancen labari nawa wanda nayiwa take da suna MAJNOON( the mad man, become a prince), abinda nayi kuskure a cikinsa Allah yayafemun, domin duk dan Adam ajizine,

Ina miki sakon gaisuwata ga dukkanin ilahirin masoyana wadanda suka nuna kaunarsu akan wannan novel nawa, dafatar ya nishadartar daku kuma ya ilmantar daku, Allah yasa sakon dana keson isarwa agareku yasamu karbuwa, ina kara gode muku sosai Allah yabar zumunci.. Ameen

Jinjina gareku yan uwana marubuta na Group din ONLINE HAUSA WRITER'S dakuma duk sauran marubuta na duniya baki daya, nagode sosai da goyon bayan da kuka bani, Allah yacika mana burinmu na Alkhairi,

Kunfi kowa son novel dinna Hausa books group, especially ummun ikram, jitakeyi kamar tabini jega tayiwon typing, dole na muki godiya nagode sosai,

KUJIRANI a sabon novel dina mai suna AUREN BAZATA (marriage without love)
Sannan kuma akwai wasu novels dazanyi nida wasu kamar su, HAR A ZUCIYA, BAYA DA KURA, sannan kuma da HAWAYEN MASOYA, duk kujira zuwansu, suma suna dauke da darussa kala-kala, a cikinsu,

Ina kara gode muku masoyana kuna raina aduk inda kuke, Allah yabarmu tare NAKU ABDUL-MR, SMILESπŸ˜ƒ

Mr, smiles 07068890036 domin gaisawa dakuma gyara, nagode😘
AYI SALLAH BABBAR SALLAH, LAFIYA 😊

Bissalam saimun sake haduwa, love you oll😊
End Ads