Dasauri Majnoon yadago kansa yana kallonta yace " abba baya sonane"
Rumaisa ta girgiza masa kai tana murmushi tace " yana sonka mana, kaida zaka aure 'yarsa mezai hana yasoka, tana kallonsa tace " kodai ka fasa aure nane"
Da sauri majnoon ya Girgiza kai yana dariya yace "a a, ina sonki sosai" yana gama fada ya sunkuyar da kansa kasa yana wasa da yatsunsa, shi ala dole yaji kunya,
Yanayinsa yabawa rumaisa dariya,
Baba driver yana a mota sai mamaki yake me rumaisa takeyi a gurin mahaukaci gashi yaganta sai Murmushi take, ta mirror motar ya hangi wata mota a bayansa wadda tayi sanadiyar sakashi firgita fiye da kima, bakinsa na rawa ya iya furta "alhaji"
Da sauri yafito daga cikin motar, yana kiran rumaisa, domin tayi sauri tazo sutafi, tana juyowa yayi daidai da lokacin da abbanta yafito daga cikin motarsa, sukayi edo hudu ko kashe motar bai tsaya yiba, yanufi gurinsu,
Rumaisa kuwa tuni tayi mutuwar tsaye,
Fuskarsa ba annuri kwata kwata, yakarasa gurinsu, kafin yayi magana saida yadauke Majnoon da wani irin wawan mari, rumaisa ta kanne edonta domin bazata iya ganin ana duka Majnoon ba, a dai dai lokacin Hawaye suka sauko kan kuma tunta,
Kafin ta bude idonta itama taji saukari mari tas tas, saida ta ja da baya kamar zata fadi,
Yana dafe da kumatunsa Ganin an mari rumaisa yasa yayi ihu cikin sigarsa ta marasa hankali yayi kan abban rumaisa ya kamo kwalar rigarsa, ya ware hannu zai mazga masa mari rumaisa tayi saurin rike hannunsa tana kuka tace " karka maresa abba nane "
A hankali Majnoon yasaki wuyan abba yana huci,
Abba kuwa gabaki daya ya tsorata, ganin yadda majnoon ya damkesa, indai baibar gurinsaba to komai zai faruwa,
Majnoon ya rike hannun rumaisa, wannan shine karo na farko dataji majnoon yataba jikinta, wani zar taji, ta lumshe ido, tayi mamakin jin hannunsa da laushi,
Abban rumaisa yagyara rigarsa yana huci yace "sakarmun 'ya"
Uffan Majnoon baice dashiba, rumaisa kuwa kuka kawai take, tana fana dan Allah abba kayi hkr wallahi bazan sakeba,
Da karfi da yaji abban rumaisa yashiga Firgar rumaisa daga hannun Majnoon shikuwa Majnoon yariketa gam saikace abarsa,
Nan take mutane suka taru a gurin, da kyar aka iya b'amb'are rumaisa daga hannun Majnoon, mutane suka rirrikesa..
Abba rumaisa ya fincikota tana kuka, yanunawa majnoon yatsa yace "kaiiii dani kakee sa insa" sannan yayi kalci yaja hannun Rumaisa dakarfi yanufi mota da ita,
Janta yake amma tana juyowa tana kallon Majnoon, wanda mutum sama da biyar duk sun rirrikesa,
Rumaisa kuka take sosai,
Abba na karasa bakin mota ya bude kofar motar ya jefata a ciki, sannan ya zagaya ya shiga motar yabar unguwar.
Baba drive duk ya tsorata,
tsoro yakeji kar ya rasa aikinsa...
Bb driver kuwa Cike da fargaba abinda zai tarar a gida yashiga motar yatada yabar unguwar..
**** *** ****
*FAISAL* yana kwance saman gado ya tayar da edonsa sama yana kallon ginin dakin, edonsa sunyi ja sosai, da duk kan alamu kuka yayi sosai, kaman nunta yafara zayyanowa mai kyauce da fasali, bayajin zai iya rabuwa da ita,
Kofar dakinsa yaji anturo da sauri yashare hawayensa, yana kallon kofar,
Abbansa yashigo cikin shigar kamala, da jikar aiki makkale a kafadarsa,
Basai an fada masa yasan halin da yaronsa yake ciki, domin zai iya kasan cewa shine silar matsalar,
Daddy ya nisa yace " jiyafa bakaci abinciba yau ma haka zaka wuni, kawai aka na hanaka auren rumaisa, nifa cetonka ne nake akan bakin cikin da zaka shiga bayan anyi aure domin yarinyar nan ba sonka takeba, kayi hakuri kacire yarinyar nan a ranka domin ni banzan yarda ka aureta ba" Faisal yayi saurin tashi yana hawaye "daddy dan Allah kayi hakuri, wlh nakasa cire son rumaisa acikin zuciyata, ban taba tunanin zan iya bijirewa umarninkaba amma a yanzu zuciyata takasa hakura daddy" yakarasa maganar kamar mai shirin yin kuka ,
Daddy yayi ajiyar zuciya yana kallon tilon d'ansa faya susuce akan soyayya,
Daddy ya furzar da iska yace "rumaisa bata sonka danme dazaka cewa dole saika aureta, nifa badan MAhaifinta yana amininaba da tuni na dade da tarwatsa wannan lamarin, look faisal, daddy yadafa kafadarsa sannan yaci gaba dacewa "hakuri shine jigon komai kasawa zuciyarka salama insha Allah wata rana zaka manta da ita, kaji faisal" yakarasa yana kallonsa ido cikin ido
Shiru faisal yayi nadan wani lokaci kafin yace " daddy wlh inasonta plx dan Allah kabari na aureta, nikobata sona zan iya zama da ita plx daddy" yakarasa maganar cike da magiya
Daddy ya girgiza kai yana mamakin almarin faisal shi ana gaya masa magana amma ko dauka bayayi, baice dashi komaiba, ya mike tsaye sannan yace "shikenan zanyi shawara akai tashi kaje kaci abinci, saina dawo zamuyi magana" bai jira me zai furtaba daddy yafice yabar dakin, sai a lokacin faisal yaji sanyina zuciyarsa, sannan ya mike tsaye.. soyayyar rumaisa itace a cikin kowanne bugun zuciyarsa a koda Yaushe. ..
*_Waye faisal_*
Faisal d'a daya tilo a gurin mahaifinsa Alhj nura(wato daddy)Yataso cikin gata da azriki, iyayensa suna matukar sonso domin shine kadai d'ansu daya tsaya a duniya, sun haifi wasu yaran kusan hudu amma duk sun rasu, faisal ne kad'ai yatsaya,
Hakan yasa suka dauki son duniya suka daura masa, sun bashi tarbiya akan tsarin addinin musulunci..
Mahaifiyar faisal haj cima yar asalin mali ce, alhj nura kuwa dan 9ia ne, aikine yakaisa mali acen kuma yagano haj cima yanemo aureta kuma aka bashi, bayan andaura aurene yadawo da ita 9ja,
Faisal farine amma ba iri farin nan sosaiba yanada tsayi daidai misali, yanada gwarjini sosai a gurin wadda baisaba dashiba, sannan kuma yanada fara 'a,
Wata rana yaje karbar sako a gurin mahaifin rumaisa a lokacin yaganta kuma yaji yana sonta kuma yanaso takasance matarsa, bayan yakarbi sakon yadawo gidane yasanar da daddy cewa shifa yaga matar aure gidan amininsa, bakaramin jindadi daddy yayiba, domin ya kosa faisal yayi aure,
Washe garin ranar tunda safe daddy yaje yasanar da mahaifin rumaisa cewa d'ansa yaga 'yarsa ynaso, abban rumaisa yajidadi sosai tun a gurin yace yabayar da ita ga Faisal kuma tana kare karatu za a daura musu aure,
A daren Ranar da faisal yafara zuwa gurin rumaisa babu abinda yaganewaa domin taki sake masa fuska, kuma taki yi masa magana,
Shine daya dawo gida yasanar da iyayensa yadda sukayi da rumaisa, daddy ya tsorota sosai dominshi bayason dansa ya aure wacca bata sonsa, domin yasan illar auren dole
Washe gari daddy yaje gidan abban rumaisa domin yaji gaskiyar lamari shin rumaisa nasaon yaronsa ko bata sonsa,
Bayan yakarasa gidan a bakin kofar falon yajiyo hargowar abba yana yiwa rumaisa fada akan acewa dole saitaso faisal kuda kuwa ranta zaifitane,
Hankalin daddy yatashi makura, baijira abba yazo yasamesaba yayi saurin dawowa gida yasanar da faisal komai dayaji tare da bashi shawarar cewa yadaina tunanin rumaisa a ransa domin shi bazai barshi ya aure wacca bata sonsa ba, Momyn faisal ma tabiyewa daddy akan itama bata yarda ya aure wacce bata sonsa ba..
**** ***** ***
A harabar wani dankararen gida yaja parking ma'aiktan gidan sukawo kansa da gudu suka bude masa kofar motarsa, yafito cike da kasaita wani farin dattijone fuskarsa amurtuke, alamun tsufa sun bayya a fuskarsa makura,
Farar shadda ce a jikin dakuma babban riga ga hula fara hakama takalmi farare, sai wata yar gajeruwar sanda dake rike a hannunsa,
A hankali ya kalli ma aikatan yace "where is my son" daya daga ma'aikatan ya sunkuyar dakai domin sunsan halinsa ba a maganani dashi ana kallonsa "alhj wlh tun jiya daya shiga cikin dakinsa bai sake fitowaba kuma yahanawa kowa shiga cikin dakinsa, yanzu haka abincinsa na nan a kichin, sai kira yakeyi yace a akawo masa kayan maye"
Farin dattijon yace "what!! Yakara kalon ma'aikatan ya rafka musu tsawa"kuna aikinme, meye amfaninku a gidan, dabazaku kirani kusanar daniba, wlh duk wani abu yasami d'ana saina kasheku baki daya, yana ina yanzu"
Muryar ma'aikacin tasoma rawa domin ganin yadda ya tambayesa a hnakli yake cewa "yana ciki "
Baijira yakara maganaba ya yanufi cikin gidann....
Rumaisa ta kwanta saman gadon duk jikinta ciwo, fatarta harta kunbura , idonta sun fito bulla2,
Tunanin ummanta kawai take, tasan da ace yau ummata nan da bazata bari ayi mata wannan dukanba, sai a lokacin tasamu tayi kuka,
Sosai takeyin kuka, bata ankarabba bacci yadauketa, zuciyartaa cike da bakin cikin halin datake ciki,
Abba kuwa daki yakoma yayi wanka yagyara jikinsa domi duk yayi gumi a kan dukan dayaiwa rumaisa,
Sannan yafita police station yanufa yafadawa yan sanda cewa yanaso akama majnoon, sukam sukace bazasu kama mahaukaciba, haka yayita musu magiya amma sukace sufa bazasu iyaba,
Dolensa ya hakura yabar station din amma zuciyarsa takasa hakura akan abinda majnoon yamasa, kawai yayanke shawara aransa zaisa 'yan daba su narkawa majnoon dukan tsiya cikin dare... haka kuwa ya ajiye a ransa..
Sai 4 na yamma rumaisa tafarka, jikinta duk yayi tsami da kyar ta iya tashi taje tayi wanka d ruwan dumi, koda zataji saukin ciwon dake damunta, bayan tagama wanka tayi alwala sannan tafito, tadan shafa mai,, sannan takarasa bikin drower tadauko hijab, komai datakeji ba kama jiki, a hakan tayi salloli biyu azahar da la'assar, bayan taggama taci abinci, sannan taka dawowa saman gado ta kwanta,
A hakadai ta yuni bawani kuzari a jikinta.
Misalin karfe 9 nadare rumaisa kwance a tsakiyar gadonta, sanye take da rigar bacci,tunani kawai take tana hawaye, dukta fita hayyacinta, a yuni daya dukta soma ramewa,
Majnoon dinta take gani a duk lokacin data rufe idonta, hawaye fal a idonta, ummata ta tuna sai kuka, kuka tasomayi sosai cikin kukan take fadan "haba umma meyasa zaki tafi kibarni, meyasa nakasa binki, umma na nisan nan kusa zanzo gareki cikin yan kwanakinnan domin nagaji da duniyarna... ummana zan mutu...." takarasa maganr tana kuka abin tausayi Allah sarki rumaisa, tayi rashin mahaifiyarta tun tana tanada shekara 12, tun daga lokacin da mahifiyarta ta rasu bata kara samun farin cikiba sai lokacin da ta hadu da majnoon, to gashi shima ana kokarin rabasu,
Haka dai taci kukanta mai isarta har dare yafara nisa sannan tayi adu'ar bacci tabi lafiyar gado, har bayan bacci yafada daukarta tatuna bata rufe kofar dakintaba, Taso ta tashi amma saita kasa, hakura kawai tayi tashiga sharar baccinta...
Karfe 2:00am nadare mutun biyu cikin baka ken kaya suka dirko ta ginan gidan su rumaisa a hankali suka karasa cikin falon bakowa hakan yabasu damar shigewa dakin rumaisa kai tsaye, kwance suka sameta saman gado tana bacci,
Dayan yakarasa inda take yafitar da wata porda ya zuba mata a hanci, kadan tayi kara saikuma takomaba bacci haka suka daukotaa suka fice da ita daga gidan babu wadda yasani,
_Washe gari_
Misalin karfe 8:30 nasafe abba yayi shirinsa zai fita aiki, amma yaji shiru yayi dubin rumaisa tafito zuwa skull amma sai yaji shiru,
tashi yayi yanufi dakinta, yaduba bata ciki, sunanta yashiga kira a tunaninsa kotana cikin toilet hakan ma yaji shiru, tiolet din yanufa ya bude yaduba bata ciki fitowa waje yayi zuciyarsa cike da sake2 kala2, yadaisan rumaisa bazata guduba, yafi zargi saceta akayi, da karfi ya kalawa umma kira, dasauri ta kara gurinsa "gani alhj lafiya kuwa "
Ina rumaisa " itace kalamar daya fara fada fuskarsa a murtuke
Umma ta kallesa da mamaki tace " ni ina zansan inda rumaisa take rabona da ita tun jiya dadare "
Cikin fushi abba yace " bazaki fito da itaba kenan, inafa sane daduk wata kisisina da kike shiryawa, jiyama najiki kina waya wato kinsa aje akasheta koh" abba yakarasa maganar yana kallon umma wacce tuni tafita hayyacinta tana mamakin kazafi, cikin tsawa abba yace "zaki fito da ita ko sai kin sha bakar wahala"
Nan Umma tashiga yi masa rantsuwa akan wallahi bata san inda take ba, amma cewa yayi wlh bai yarda ba ita tasa ta aka dauke masa rumaisa, dan haka tajirashi yana zuwa
Fita yayi yabar gidan yana huci, sai bayan yafita sannan umma ta tuntsure da dariya, tana fadan ruwa su iza harda matuka jirgi, ace akarata ... rumaisa anshiga duniya, tafada tana dariya..
*** ***
A hankali take bude idonta tana kallon yanayin dakin wadda ya chanza mata kamanni kamar ba dakin taba,
Da karfi tatashi zaune, caraf idonta yasauka kan fahad dake zaune a gefe yana kallonta yana murmushi,
Firgita tayi ta tallatsa ihu mai matukar kara
Dariya taga yanayi mata saida tagaji sannan tadaina ihun sai ta saka kuka tana fadan " dan allah kayi hkr kamaidani gida "
Murtuke fuska yayi, yana kallonta yake fadan "aikuma keda fita daga gidan saikin haifemin yarana domin kinshigo kenan bake ba fita, naso ace munyi harkar azriki dake kishigo gidan nan amatsayin amarya amma sai kikaki, amma yanzu gaki kinshigo gidan nan a tsayin karuwa kuma bake ba fita, ya mike tsaye sai kuma yasaka dariya sannan yace "barka da zuwa sabowar alawa " yana gama fadan haka yafita yana dariya yamayar kofar dakin yarufe....
Rumaisa kuwa Kuka tayi
harna fitar arziki itakam tata kaddarar a haka tazo mata,
Data daiga kuka bazai kara sheta da komaiba hakan yasa tadan tsagaita kuka, tatashi tashiga neman bandaki a dakin, cen ta hangi kofa takarasa gurin kofar ta bude, taga ban dakine shiga tayi ta watso ruwa sannan tayi alwala tafito, kayan baccine kawai a jikinta tarasa yadda zatayi tayi sallah, duban dakin take gefe da gefe edonta duk sun kumbura,
Babu abinda tasamu wadda zai suturtata a dakin, fara bincike daken tayi a kasan gado taleka tana dube2,
Ware ido tayi tana mamaki a hankali bakinta ya iya furta "HIJAB" mamaki take meya kawo hijab din macce anan, gbanta yayanke ya fadi kardai ace fahad da gaske yake yana wiwa mata fyade,
Hawaye tasoma tana tunanin makomarta, a tsorace ta karkade hijab din tasaka sannan ta karkade kasan cafet din dakin tafara sallah, bata jimaba tagama sallar sannan tarafa kwararo adu'a akan Alllah ya kubutar da ita yasa fahad yakasa aikata komai akanta, adu'a tayi sosai kafin tagama saida tayi kuka,
Bayan tagama sallar tayi zamanta akan sallayar tana kallon dakin, yunwa takeji kamar yan hanjinta zs su fito,
Tashi tayi tashiga nemi abinda zataci, kaf dakin bata samuba hakan yasa ta koma kan gado ta kwanta tana kuka,
**** **** ****
Tunda Abban rumaisa yafita gidan daddy yanufa yasanar dashi komai dake faruwa, lamarin yayi matukar girgiza daddy, saidai yanajin yadda zai fadawa faisal wannan lamari,
Daddy ne zaune a falo shida momy sunyi jugum2 suna jimamin abinda yafaru da rumaisa, sake sake suke kala kala,
Faisal yafito daga cikin dakinsa cikin shirinsa na fita office, farin yadine a jikin filtexs irin mai shara2 dinnan yayi matukar yimasa kyau,
Cikin ladabi da biyayya ya durkusa yagaida momy da daddy,
Ganin yanayinsu kamar da dadamuwa a tattare dasu yasa yakasa hakura saida ya tambaya, duk da shima kuwa tun yafarka yau da safe yakejin gabansaa na faduwa,
"Daddy meya farune naga kamar kuna cikin damuwa" faisal yana kallon daddy yana jiran yabashi amsa , nunfashi daddy yaja yanajin nauhin yadda zai gaya masa maganar, daddy ya kalli momy, momyma haka daddy take kallon sai kuma sukayi shiru,
Faisal kasa fahimtar komai yayi duk ya soma tsorata domin yanaji a jikinsa akwai abinda yafaru,
Ya juya yakalli momy yace "momyna tambaya nake amma kuyi