x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - BAKAR GUGUWA

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 36828 words

Category: Adventure Stories

Views 107

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
tunda kin yi zavi da
kasancewa cikin wannan hali tare da jama’ar da ki ke tare da su,
to ku yi sauraren da zuwan musibar sa za ku riskeku ta kai ku
ga halaka, ita ce za ta zama hanyar salwantar rayuwarku ba za

90

BAKAR GUGUWA
ku tava kuvuta daga gareta ku qetare wannan kogi da ku ke
ciki ba”.
Yana gama ambato wannan maganar ya sake bushewa
da dariya irin ta mugunta da zallunci sannan ya vace cikin
baqar guguwar da ya bayyana a cikinta ya bar wajen, daga nan
sai suka sake jin wata tsawa da rugugi mai ban firgici ya
gauraye wajen can daga gabansu sai suka hangi ruwan kogin
nan ya dare gida biyu ya yi tsiri sama,tsayinsa zai iya shan kan
jirgin ruwan da suke ciki ya nutse da su su halaka, sannan sai
wata iska mai qarfi ta soma tura jirgin ruwan yana tunkarar
inda ruwan kogin nan ya dare gida biyu za ta dulmiyar dasu su
halaka, su zuhairu suka ci gaba da addu’a don neman
kiyayewar ubangiji ya kuvutar da su daga wannan musiba da
suke ciki. Jirgin ruwan ya ci gaba da tafiya yana qara tunkarar
inda ruwan kogin ya dare gida biyu zai dulmiyar da su su
halaka.
Shin me zai faru?

BAQAR GUGUWA 3
irgin ruwan yaci gaba da
tafiya da su zuhairu har ya isa da su
inda ruwan kogin ya dare gida biyu
ya yi tsiri sama, suka ji an kece da
dariya irin ta mugunta da zalunci cikin muryar matsafi Bahalu.

J

91

BAKAR GUGUWA
Kuma sun tabbatar dacewa shi ne yake yin dariyar duk da cewa
basa ganinsa,suka ci gaba da addu’a dan neman kiyayewar
ubangiji ya kuvutar da su daga wannan masufa da suke ciki,
suna zuwa tsakiyar inda ruwan kogin ya dare gida biyu, sai
suka sake jin wani rugugi mai matuqar ban firgici da hauhawa,
iska mai qarfi ta sake juya ruwan kogin igiyar ruwa ta murxa,
ruwan ya sake yin tsiri sama tare da ambaliya ya dawo akan
jirgin ruwan da su zuhairu suke ciki, nan take jirgin ruwan ya
yi wata irin qara mai tsananin qarfi ya ragargaje ya fashe qarar
fashewarsa tamkar fashewar dutsen da aka jefa da majaujawar
wuta.
Su zuhairu Baniyatu da sauran jaruman da suke tare da
su, suka gantsama cikin ruwan kogin suka nutse a cikinsa
sakamakon fashewar da jirgin ruwan ya y, igiyar ruwa ta ci
gaba da juyawa da su tana dulmiyar da su qasa tamkar sun
halaka baki xaya, matsafi Bahalu ya sake bushewa da dariya
daga inda yake tsaye, yana ganin abinda ya faru ga su zuhairu,
sannan ya juya ya kama hanyar komawa fadarsa cikin farin
cikin ya halaka su zuhairu saboda abinda ya aikata akan su na
aikin sihiri.
Su kuwa su zuhairu da suka faxa cikin kogin iskar nan
mai qarfi ta ci gaba da juyawa da su a cikin ruwan tana
dulmiyar da su qasa, sannan ta xaga sy sama har sai da suka yi
matuqar jigata, suka fita daga haiyancinsu. Da yake Allah bai
qaddara za su hallaka gaba xaya ba, sai igiyar ruwa ta tura su
bakin gavar kogin ta watsar da su a gefe bisa rairayi. Suka tashi
da qyar suka qarasa fita, daga inda ruwan kogin yake qarasowa
idan ya yi ambaliya.

92

BAKAR GUGUWA
Bayan sun gama fita daga cikin ruwan suka duba suka
ga mutum bakwai ne daga cikinsu suka halaka a cikin wannan
ruwa da suka faxa. Adadin yawansu ya zama saura mutum
talatin da biyu suka rage daga cikin mutum arba’in da biyu da
suka taho tun da farko. Suka yi godiya ga Allah da ya kuvutar
da su ba su halaka gaba xaya ba. Tare da addu’a ta neman
gafara da rahamar Ubangiji ga waxanda suka halaka.
Da yake sunyi matuqar jigata gaba xaya basu bar bakin
kogin ba sai da suka huta sosai suka samu nutsuwa.
Bayan sun nutsu Baniyatu ta dubi zuhairu tace da shi
“Ya inganta mu qara godiya ga Allah da ya bamu nasarar
qetare wannan kogin muka iso wannan waje kuma daga nan
zuwa lardin Ashtar tafiyar kwanaki biyu ce zamu fara tarar da
sansani na farko daga cikin sansanonin baradan dake tsaron
wannan fada sai dai kafin mu isa inda wannan sansani yake ya
kyautu mu fara neman hanyar da zamu buxe qofofin da ke
kulle da fadar idan mun isa inda take, kamar yadda tsohuwa
Diyanuna ta umarcemu. Saboda idan bamusan yadda za mu
buxe qofofin shiga fadar ba, koda mun yi nasarar yaqar
waxannan sansanonin barada mun halakasu mun isa inda fadar
take ba zamu samu damar shiga cikinta ba shi ke nan duk
wahalar da muka yi ta tashi a banza kenan”.
Zuhairu ya yi shuru yana sauraronta da ta gama
bayaninta ya yi tambaya a gareta da cewa “To yanzu menene
shawararki cikin wannan lamari?” Buniyatu ta sake cewa da
shi “Shawarata shi ne na yi sani da labarin wani boka mai suna
Afrahu dake zaune a tsaunin wannan kogin da sansanin barada
ma’abota tsaro na farko a cikin wannan kogin dutse, idan mun
isa gare shi zai sanar da mu yadda za mu buxe qofofin dake

93

BAKAR GUGUWA
kulle a fadar sabat idanmun isa gaeta” Zuhairu ya sake duban
Baniyatu cikin mamaki yace da ita.
“Wane ne kuma Boka Afrahu da za mu tafi gare shi don
ya sanar damu yadda za mu shiga fadar, kuma mene ne
alaqarsa da fadar da yake da masaniyar yadda za mu shiga
cikinta bayan kin ce bayanai sun tabbatar da cewa babu wani
mahaluki da yake da masaniyar sirrin fadar, bare yasan yadda
za’a shiga shiga cikinta, sannan ki sani cewa yarda da maganar
Boka kuskure matuqar abinda ya faxa ya zama bincike ne na
cikin alqaluman sihiri da tsafi”.
Buniyatu tace da shi “Ai ba za mu je gareshi bane don
ya yi mana bincike alqaluman tsafi da sihirinsa ba, sai don
kasancewar shi wanda yake da masaniya cikin dukkanin
hanyar ta shiga fada, saboda asali ita wannan fadar ba
mahaifina bane kaxai ya ginata, sun ginata ne tare da wasu
mashahuran bokaye da alqaluman sihiri su biyar, kuma sun
ginata da nufin su shiga ciki gaba xaya su zama manya
bokayen duniya da za su riqa bada umarni ga qananun bokaye
dake cikin wannan lardin kamar yadda suka ga manya
sarakunan musulmai suna yi, idan sun kafa daular musulunci
ga sauran sarakuna mabiyansu.
Bayan sun gama gina fadar ne mahaifinmu ya hillace su
ya halaka bokayen guda huxu daga cikinsu, ta hanyar qarfin
tsafi da sihirinsa dan ya mallaki fadar shi kaxai. Sauran boka
xaya ne yarage daga cikin bokayen mahaifina bai halakashi ba,
wato wannan boka Afaraha da zamu tafi gareshi a yanzu,
shima ya gane cewa mahaifinmu yana shirin halaka shi ne
kamar yadda ya halaka sauran bokayen dan haka ya yi gudun
hijira daga wannan da’ira tasu ya koma cikin wani kogon dutse

94

BAKAR GUGUWA
a cikin wannan daji ya zauna a cikinsa dan ya tsira daga
hallaka.
Mahaifinmu ya yi ta neman inda ya shiga a cikin faxin
duniya dan ya bishi ya halaka shi kafin ya tare a wannan fada,
saboda gudun kada a samu sauran wanda yasan sirrin fadar a
haxa baki da shi dan kawo hari a gareshi, da kuma sanin
shu’umancin wannan boka kada wata rana ya dawo gareshi dan
yi ramuwa, amma yarasa inda ya shiga cikin alqalaman
sihirinsa saboda kasancewarsa qwarare kuma masani cikin
alqaluman sihiri na bada kariya ga wani voyayyen al’amari,
dan Boka Afrahu shi ne ya samar da wannan qofofi guda uku
dake kulle da fadar da kuma duk wannan tsaro dake cikinta, sai
dai a yanzu ya zama nakasashe wani sashe daga jikinsa ya dena
amfani sakamakon jifansa da alqaluman sihiri da mahaifinmu
ya yi a sanda yake qoqarin halakashi kafin ya yi hijira ya dawo
wannan waje,kuma mahaifinmu bai samu nasara gano inda
yake ba cikin bincikensa sai bayan shekara biyu bayanai suka
bayyana a gareshi, kuma a ranar da ya gama shiri da nufin
tafiya wannan kogon dutse halaka Boka Afrahu sai ajali ya
gabata gareshi ya halaka.
Dan haka zamu tafi ga wannan Boka dan ya sanar da
kai yadda za ka samu nasarar shiga fadar, idan mun isa inda
kogon dutsen yake kai kaxai za ka shiga cikinsa, kuma zan
sanar da kai yadda za ka shiga da abinda zaka sanar da Boka
Afrahu dan ya amince ya sanar da kai sirrin buxe qofofin shiga
fadar, bisa ga sharaxi kanaso ka halaka mahaifinmu ne saboda
ba shi da labarin rasuwarsa”.
Data gama yi masa wannan bayyani sai zuhairu ya
amince da shawararta. Daga nan suka tashi tare da sauran

95

BAKAR GUGUWA
jaruman da suke tare da su suka ci gaba da tafiya, da yake
tafiyar qafa ce ba akan dawakai ba, kuma ga ramuka da
kwazazzabai da suke ratsawa ta tsakaninsu basu isa inda
wannan kogon dutsen da Boka Afrahu yake cikinsa ba sai da
suka yi tafiya kwana uku.
**
Shi kuwa matsafi Bahalu bayan da ya koma fadarsa
cikin murna da farin ciki na zato cewa su zuhairu da jaruman
da suke tare da shi sun halaka a cikin wannan kogin da ya baro
su, ya koma aikansa na saurara bayyanar haxewar taurarin nan
na aikin sihiri su zama xaya, dan samun damar mallaka
Gimbiya Hasima ta zama matarsa kamar yadda ya yi imani da
tabbatar hakan, yakan ziyarci xakin da take ciki a kowace rana
dan yaganta ya ji sanyi a ransa, kuma a kullum qaunarta da
muradinta na qara qaruwa a cikin zuciyarsa, sai dai bashi da
ikon kusantarta da nufin biyan buqatarsa da ita, saboda
alqaluman sihiri da ya yi imani da su basu bashi damar tabatar
da hakan ba.
Bayan kwanaki biyu sai ya ji zuciyarsa tana mai
muradin sanin yadda su zuhairu suka halaka dan fanin qarshen
su da yadda suka kasance a bayan halakarsu kamar yadda yake
zato, ya tafi ga kaskon nan na lu’u-lu’u dake xauke da farin
rairayi a cikinsa ya yi ane akan farin rairayin ya share sannan
ya rufe idanunsa ya soma karanta waxansu xalasumai na cikin
sihiri bayan ya gama ya buxe idanunsa bayanai suka bayyana a
gare shi cikin wani mummunan lamari mai matuqar ban
mamaki da tu’ajjabi a gareshi da ya sashi fargaba da razani
ganin cewa zuhairu da sauran jarumai da suke tare da shi basu

96

BAKAR GUGUWA
hallaka a cikin wannan ruwan kogin gaba xaya ba wasu daga
cikin sune suka halaka.
Nan take kammaninsa suka sauya daga yanayin farin
ciki ya zuwa baqin ciki, zuciyarsa ta yi masa qunci ya sake
share rairayin yayi wani rubutun akansa dan neman sanin halin
da suke ciki a yanzu, bayanai suka sake bayyana a gareshi dake
sanar da shi cewa, su zuhairu da sauran jaruman da suka rage
basu halaka ba, suna cikin dajin dake tsakanin lardin Ashtar da
ruwan da suka nutse a cikinsa yake zaton sun halaka kuma
suna kan hanyar sune ta zuwa cikin wani kogon dutse inda
wani boka masanin sirrin buxe qofofin shigowa fadarsa ta
Darul sabar da ke kulle yake zaune, dan neman sani daga
gareshi ya sanar da su yadda za su shiga fadar. Matsafi Bahalu
ya sake yin matuqar mamaki da ganin cewa akwai wani biladama masanin sirrin wannan fada a duniya ba tare da ya san
da shi ba. Don haka ya quduri aniyar zuwa ya halaka wannan
boka kafin su zuhairu sukai gare shi ya sanar da su sirrin shiga
fadarsa. Duk da yana ji a ransa cewa su ba masu samun nasara
bane akan sa koda ya sanar da su sirrin shigowa fadar. Saboda
sansanonin ma;abota tsaro da bada kariya da yake tare da su
kafin su kai ga isowa inda fadar take.
Nan da nan ya tashi ya yi shirinsa na kayan aikin
Bokanci da sihiri ya fita daga fadar ya kama hanyar tafiya
kogon dutsen da Boka Afrahu yake zaune a cikinsa. Dan ya
halaka shi kafin ya kai ga sanar da zuhairu sirrin shiga fadarsa.
**
Su kuwa su zuhairu da sauran jaruman da suke tare da
shi, bayan da suka isa bakin wannan kogon dutsen da boka
Afrahu yake zaune a cikinsa. Suka ja linzamin dawakansu suka

97

BAKAR GUGUWA
tsaya. Buniyatu ta dubi zuhairu tace da shi “Wannan shi ne
kogon dutsen da boka Afrahu yake zaune a ciki, kuma kai
kaxai za ka shiga cikinsa, don neman ya sanar da kai sirrin
shiga fadar ta Absar da muka zo nema a gare shi. Saboda idan
muka shiga tare da ni zai ganeni ya shaida cewa ni ‘yar gidan
Boka Kauwas ce, wanda ya aikata wannan aikin sihiri na
naqasar da jikinsa ya yi akansa, kuma ya nemi halaka shi kafin
ya yi gudun hijira daga da’irar da suke zaune gaba xaya. Ba zai
tava yadda da ni ba, kuma ba zai tava yadda da abinda zan
ambata a gare shi ba. Don haka sai dai ka shiga kai kaxai,
kuma zan sanar da kai yadda za ka shiga wannan kogon
dutsen”.
Ta ciro wani zobe na azurfa daga hannunta ta miqa
masa sannan tace da shi “Ka sanya wannan zobe a xan
yatsanka dan ba za ka iya shiga cikin kogon dutsen ba, sai kana
tare da wannan zoben idan ka shiga cikin kogon dutsen za ka
riski Boka Afrahu zaune akan wata karaga ta zinare ya harxe
qafaffunsa. Gaba xaya jikinsa ya naqasa tun daga kafaxarsa
har ya zuwa qafarsa, babu abinda yake iya motsawa bare ya yi
amfani da shi. Hannnayansa sun shanye, kan sa ne kawai yake
iya waiwaiyawa baya, ko kuma ya buxe baki ya yi magana,
haka kuma yana iya hangen duk abinda zai shigo cikin kogon
dutsen koda kuwa aljani ne”.
Idan ka tunkari inda yake za ka ji ya daka maka tsawa,
ko kuma ya yi maka magana. Kada ka sake ka amsa masa har
sai ka isa inda yake zaune. Ka durqusa a gabansa ka shafi
dogon farin gemunsa, sannan ka cire wannan zobe da na baka
ka sanya a xan yatsansa ka kama hannunsa na dama ka saka
masa zoben ana sa xan yatsan, za ka ga ya dubi zoben sannan

98

BAKAR GUGUWA
ya sake dubanka kada dai ka sake ka yi magana sai ka ci gaba
da saurare dan jin abinda zai ambata a gareka”.
“Idan ya nemi sanin sunanka ka sanar da shi sunanka na
gaskiya, amma ka shaida masa mai wannan zobe shi ne
mahaifinka, kuma ya turoka garesa ne dan ka taimaka masa ya
samu waraka daga halin naqasa da yake ciki kuma kai ma ka
samu waraka daga aikin sihirin da yake tare dea kai. Ka faxi
buqatar ka ta son ya sanar da kai sirrin buxe qofofin da ke
zagaye da fadar Darul sabar dan ka samu nasara shiga cikinta
ka halaka wanda ya mallaketa, ka kuma xebo ruwan da ke
cikin rijiyar tsakiyar fadar dan ka kawo masa, wanda shi ne za
a yi amfani da shi dan karya aikin sihirin da yake tare da shi da
kuma wanda yake tare da kai”.
“Idan ya ji wannan bayani da za ka yi masa na tabbatar
zai yi matuqar farin ciki sosai. Zai kuma sanar da kai sirrin
yadda za ka shiga wannan fada. Sai dai duk abinda ya uwarce
ka ko ya sharxanta ma kafin ya sanar da kai yadda za ka shiga
fadar, kada ka yi masa musu ko jayayya ka ce ka amince dan
ya sanar da kai” Da ta gama masa wannan bayani, sai zuhairu
ya karvi zoben ya sanya a xan yatsansa. Sannan ya kama hanya
ya tunkari qofar shiga wannan kogon dutsen. Ya shiga cikinsa
da shigarsa ya ga kogon dutsen yana da girma da faxi, ya ci
gaba da tafiya har ya isa wani waje mai kama da fada an
qwawata shi da abubuwan qawa da ado mai tsari. Can daga
gefe ya hangi Boka Afrahu zaune akan karagar zinare kamar
yadda Buniyatu ta sanar da shi, sai ya ji an daka masa tsawa da
maxaukakiyar murya mai matuqar razanarwa da ban firgici aka
ce da shi.

99

BAKAR GUGUWA
“Wanene kai kuma me ya kawo ka cikin wannan kogon
dutsen? Halaka za ta tabbata a gareka idan ba ka yi gaggawar
amsa tambayar da mai ambato ya yi gareka ba” Zuhairu bai yi
magana ba, kamar yadda Buniyatu ta uwarce shi, haka zalika
bai ga mai yin magana a gare shi ba. Dan ya haqiqance ba
wannan boka da ke zaune akan karaga da ke gabansa ne ya yi
magana ba, aka sake daka masa tsawa da murya wadda tafi ta
farko hauhawa, tare da maimaita abinda aka faxa da farko, a
wannan karo ma zuhairu bai yi magana ba, ya ci gaba da
tunkarar inda mutumin yake zaune har ya isa gare shi. Ya
durqusa a gabansa ya shafi dogon farin gemunsa sannan ya cire
zoben nan na azurfa da Buniuatu ta bashi ya kama hannunsa na
dama ya saka masa zoben a xan ysatansa sannan ya ci gaba da
saurare don jin abinda zai ambata a gareshi.
Boka Afrahu ya dubi zoben sannan ya dubi zuhairu
yace da shi “Wanene kai da ka mallaki zoben HINAS na
babban aminina. Kuma me ya kawo ka gareni har ka sanya
zoben a hannuna?” zuhairu ya ce da shi “Sunana zuhairu, kuma
me wannan zoben shi ne mahaifina, ya turo ni gareka ne don na
taimaka maka ka samu waraka daga halin da kake ciki na
naqasa irin ta aikin sihiri” Ya kwashe labarin abinda ya kawo
shi gare shi ya sanar da shi, kamar yadda Buniyatu ta tsara
masa. Sannan ya shaida masa buqatarsa ta san ya sanar da shi
sirrin buxe qofofin da ke fadar Darul sabar dan ya samu
nasarar shiga cikinta da xebo masa ruwan da ke cikin rijiyar
tsakiyar fadar wanda da shi ne za a karya aikin shirin da ke
jikinsa.
Da boka Afrahu ya ji wannan bayani sai ya yi murmushi
na nuna farin cikinsa har haqoransa suka bayyana sannan ya

100

BAKAR GUGUWA
dubi zuhairu yace da shi “Abota da aminci sun tabbata
tsakanina da Boka Gulaisu mahaifinka da ya turoka dan ka
taimaka a gareni na fita daga wannan halin da nake ciki, babu
shakka zan sanar da kai sirrin yadda za ka buxe qofofin da ke
fadar sabar ka shiga cikinta da zarar ka isa inda take dan kuwa
nine na samar da qofofin da tsaron da ke tare da su, dan haka
sirrin buxe qofar yana tare da ni, kuma na daxe ina neman
wanda zan sanar da shi wannan sirri ko dan xaukar fansar abin
da Boka kauwas ya aikata na cin amana da nufin halaka ni
bayan mun gama ginin wannan fada”
“Da farko kafin ka isa inda fadar take za ka fara tarar da
sansanonin ma’abota tsaro har guda uku da ke gadin fadar.
Kowanne sansani suna da tsananin yawan da ba za ka iya yaqi
da su ba, bare ka samu nasara akan su, hikimar da za ka yi shi
ne ka duba bakin tsaunin da baradan suke zaune za ka ga gunki
da suke bauta a gare shi, ka sanya takobinka ka sare kan gunki
shi kenan za ku samu nasara akan baradan duk da tsananin
yawa da qarfin tasirin tsafi da sihirinsu.
“Idan har ka samu nasarar hallaka waxannan barada ka
isa inda fadar take kada ka ce za ka tunkari qofar kai tsaye ka
ce za ka buxeta. Zan mallaka maka wani makulli da za ka buxe
qofofin da shi, gaba xaya duk qofar da ka sa makullin a jikinta
qofar za ta buxe da kanta, sai dai kada ka yi saurin shigarta har
sai ka jira kaga abinda zai fito daga cikinta. Idan na cutarwa ne
ka sanya takobinka ka halaka shi, idan kuma abin tsoratarwa ne
kada ka razana ka bi ta cikinta ka wuce”.
“Qofa ta biyu ita ce BUWAS za ka tadda ita a buxe
kada ka sake ka shiga cikinta har sai ka jawo qofar ka sanya
mukulin da zan baka ka
End Ads