biyu saran ya wuce, ta
jikinsa ko kuma ya vace ya zama iska.
Haka suka yi ta fafatawa da arangama a tsakaninsu har
sai da kaifin takobin zuhairu ya dakushe haskenta ya dusashe,
saboda yawan kai sara da haxuwar da take yi da sandar sihiri
da take hannun matsafi Bahalu. Da Bahalu ya ga lamarin ya
ta’azzara a gareshi zuhairu ya tsananta masa da kai sara yana
shirin halakashi,sai ya yi wani irin qaraji da kururuwa mai ban
firgici dake tattare da aikin sihiri wata baqar guguwa ta turniqe
a tsakaninsu sannan ya nunashi da sandar sihiri dake hannunsa
46
BAKAR GUGUWA
yana ambaton wasu xalasimai na aikin sihiri, wata irin iska mai
tsananin qarfi ta yi sama da zuhairu ta makashi da qasa,
zuhairu ya yunqura ya tashi matsafi Bahalu ya sake nunashi da
sandar sihirin iska ta sake yin sama da shi ta makashi da jikin
bishiyar dake tsakiyar lambun ya bugu da buguwa mai tsanani
har takobin da take hannunsa ta suvuce ta faxi qasa.
Haka matsafi Bahalu ya ci gaba da nuna zuhairu da
sandar sihirinsa iska mai qarfi tana wujijjigashi tana maka shi
da itatuwan da ke cikin lambun har sai da zuhairu ya yi
matuqar jigata, ya faxi qasa jini na zuba ta hanci da bakinsa,
matsafi Bahalu ya dubeshi ya bushe da dariya sannan yace
“Ahir xinka da yin jayayya da hamshaqin matsafi da ya
buwayi cikin lamarinsa kamanta Bahalu nake bin kauwas
cikamakin ma’abota sani na ilimin bokanci da sihiri da ke raye
a doron qasa ka sani cewa na yi yanka ga ababen bautata don
neman nasara a kanka kuma ina da tabbacin samun nasara akan
naka,babu shakka ka cika namiji ma’abocin jarumta da
sadaukantaka don duk a cikin masoyan Gimbiya Hasima da na
halaka babu wanda ya kai ka jarumta da qarfin zuciya sai dai
wannan rana ita ce sa’arka ta qarshe a rayuwar duniya da zan
halakaka kamar yadda na xauki alqawarin halaka duk wanda
ya ambata yana qaunar Gimbiya Hasima.
Ya xaga sandar sihirin dakehannunsa zai daki zuhairu
da ita a tsakiyar kansa ya halakashi Gimbiya Hasima da ke
tsaye tana gani abinda yake faruwa ta yi qaraji da kururuwar
irin na firgita da ganin matsafi Bahalu zai halaka zuhairu a
sannan Buniyatu ta farfaxo daga suman da ta yi ta hangi abin
da yake shirin faruwa yayanta matsafi Bahalu ya xaga sandar
sihirinsa zai daki zuhairu da ita,ya halaka nan take ta miqe
47
BAKAR GUGUWA
cikin sauri ta shiga tsakaninsu ta kare zuhairu kafin ya dakeshi
da sandar tana mai faxin cewa.
“Kar ka halaka abin begena dan kuwa ba zan iya
rayuwa a duniya ba tare da shi ba, idan kuma ka ce sai ka
halakashi to kuwa sai dai ka halakamu gaba xaya ni da shi”
Matsafi Bahalu ya fasa dukan zuhairu da sandar sihirin ya dubi
‘yar uwarsa Buniyatu yace da ita.
“Tunda kin zavi kare abin begenki akan zama da ni xan
uwanki to kuwa zan barki tare da shi ba zan halakashi ba, duk
da nayi rantsuwa da ababen bautata akan aikata hakan, sai dai
ki sani daga yau babu ke babu sake aikata wani aikin sihiri
tunda na qwace kurtun sihirin dake hannunki, kuma ba zan
sake maida shi gareki ba har abada.za ki ci gaba da zama da a
wannan birnin tare da wanda kika zava fiye da ni xan uwanki
na jini, ni kuma zan xauki Gimbiya Hasima na tafi da ita Darul
sabar fadar da mahaifinmu ya gina kafin tare a cikinta ya rasu,
mu zauna a can tare da ita. Kuma abadan ba za ki iya riskar
inda wannan fadar take ba, bare ki dawo gareni har qarshen
rayuwarki, saboda ba kya tare da duk wasu xalasimai na aikin
sihiri da za ki iya amfani da su don zuwa wannan fadar”.
Yana gama faxar maganar ya juya ga zuhairu ya
nunashi da sandar sihirin da take hannunsa ya soma karanta
waxansu xalasimai na aikin sihiri wani farin haske ya fita daga
jikin sandar ya shiga jikinsa,nan take zuhairu ya soma tsuma da
maqyarqyata irin ta rawar sanyi har sai da ya durqushe a qasa,
sannan sai kamaninsa suka soma sauyawa daga siffarsa ta
saurayi maji qarfi zuwa siffar dattijo mai tarin shekaru
ma’abocin rauni, gaba xaya gashin jikinsa ya koma fari fat irin
48
BAKAR GUGUWA
na furfura tamkar dattijo da ya haura shekaru tamanin a duniya
daga nan ya faxi qasa a sume.
Buniyatu da Gimbiya Hasima suka qwala wata
razananniyar qara saboda ganin abinda ya faru akan
zuhairu,matsafi Bahalu ya bushe da dariya irin ta mugunta da
zalunci sannan ya dubi Buniyatu yace da ita “Wannan shi ne
yadda abin begen naki zai kasance har qarshen rayuwarsa
kuma haka za ki kasance da shi cikin wannan siffa ta
dattijantaka abadan ba zai dawo siffarsa ta asali ba ko matuqar
bani ne na karya wannan aikin sihirin ba ko kuma aka bashi
ruwan dake cikin rijiyar BASRA dake tsakiyar fadar Darul
sabar da zan tafi da Gimbiya Hasima, kuma babu wani
mahaluki da ya isa shiga cikinta komai qarfin tsafi da sihirinsa
idan bani da na mallaketa ba ko kuma wanda na yiwa izinin ya
shigeta”.
Ya sake qyaqyacewa da dariya sannan ya daki qasa da
sandar sihirinsa iska mai qarfi ta keto daga bayansa tare da
baqar guguwa suka haxu suka turnuqe wajen suka yi tsiri sama,
matsafi Bahalu ya bi ta cikin baqar guguwar ya vace,sannan ya
biyo ta inda Gimbiya Hasima take a tsaye cikin kuyanginta ya
sureta ya yi sama da ita.
Gimbiya Hasima ta yi qaraji da kururuwa mai tsananin
qarfi sanda matsafi Bahalu ya sureta ta cikin baqar guguwar
nan ya tashi sama da ita,Buniyatu da sauran kuyanginta suna
ganin sanda guguwar ta yi sama da Gimbiya Hasima tana
qaraji da kururuwar neman taimako, tun suna ganinta da
hangenta da jin qarajinta har ta vace cikin baqar guguwar nan
matsafi Bahalu ya tafi da ita.
49
BAKAR GUGUWA
Bayan tafiyar matsafi Bahalu sai wajen ya washe duhun
da ya lulluve sararin samaniyar ya yaye suka daina jin qaraji da
rugugin da suke ji tun farko. Buniyatu ta dubi zuhairu ta ganshi
cikin halin suma ta tafi gareshi cikin sauri ta xago kansa tana
girgizashi taga babu alama motsi a tare da shi, hankalinta ya
qara tashi ta tashi cikin sauri ta tafi bakin kogin dake gudana a
tsakiyar lambun ta xebo ruwa ta dawo ta zauna ta riqa shafa
masa ruwan tana girgizashi cikin kuka, sai da ta xauki lokaci
mai tsawo zuhairu yana cikin wannan hali sannan ya farfaxo
daga suman da ya yi.
Da farfaxowar zuhairu ya tashi zaune a firgice ya duba
bai ga matsafi Bahalu da suka fafatawa a kusa da shi ba, ya
dubi jikinsa ya ga yadda kamanninsa suka koma irin na tsoho
tamkar dattijon da ya shafe shekaru casa’in a duniya, ya sake
duban inda kuyangin Gimbiya Hasima suke tsaye bai ganta a
cikinsu ba, hankalinsa ya yi matuqar tashi, duk da irin halin da
yake ciki na komawar kamaninsa irin na tsufa, babu abinda ya
fara tambaya sai ina Gimbiya Hasima.
Xaya daga cikin kuyangin nan ta amsa masa da cewa
wannan shu’umin matsafin ya xauketa, ya tafi da ita.
Zuhairu ya miqe tsaye cikin qaraji duk da siffa irin ta
tsufa da kamanninsa suka koma yana jin qarfin jikinsa kamar
yadda ya ke ji tun da farko. Kafin matsafi Bahalu ya yi masa
wannan aikin sihiri a jikinsa, ya xauki takobinsa ya tasarwa
Buniyatu cikin fushi da hatzuqa yana mai faxin cewa “Sanar
da ni inda yayanki matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima,
idan kuma ki ka bijerewa ambatona na rantse da sarkin da raina
yake hannunsa sai na halakaki da kisa mafi muni da qasqanci,
kafin na kai ga gano inda yayan naki yake na tafi gareshi shima
50
BAKAR GUGUWA
na halakashi akan xaukar Gimbiya Hasima da ya yi” Buniyatu
ta amsa masa da cewa “Ya abin begena zuhairu ka yarda dani
da abinda zan ambata gareka, xan uwana Bahalu ya tafi da
Gimbiya Hasima Darul sabar dake lardin Ashtar fadace da
mahaifinmu ya gina kafin ya kai ga tarewa a cikinta wa’adinsa
ya gabata ya halaka. Ni kaina ban tava zuwa inda lardin Ashtar
take ba, bare na gano inda fadar take”.
Zuhairu ya sake fusatuwa da jin maganar ta ya fizgota
ya cirata sama ya makata da qasa, ya xora kaifin takobinsa
akan wuyanta ya ce da ita “Ki sanar dani gaskiyar lamarin inda
yayanki ya tafi da Gimbiya Hasima idan kuwa ba haka ba na
shayar da ruhinki xacin mutuwa da azabar kaifin takobina”
Buniyatu ta sake cewa da shi.
“Ai abinda na saranr da kai shi ne gaskiya cikin wannan
lamarin, idan kuma ba ka gasgata ni ba, kana inkarin abinda na
ambata to9 ka halakani kamar yadda ka ambata, kuma ba zan
yi kaico ba, ko kuma nadama akan haka saboda wanda nake
begene ya halakani, wanda na sadaukar da rayuwata dan na
taimaka masa, wanda na guji xan uwana na jini na dawo
gareshi na zavi kasancewa da shi, wanda na rasa duk wani
gatana da tasirin tsafi da sihiri da na gada a wajen mahaifina
saboda shi, wanda nake burin taimaka masa cikin kowane irin
hali matuqar ina da damar aikata hakan”.
Jikin zuhairu ya yi sanyi zuciyarsa ta karaya da jin
kalaman da ta ambata ya cire kaifin takobinsa daga kan
wuyanta ya saketa, Buniyatu ta miqe tsaye ta dubeshi suka
fusanci juna sannan tace da shi “Ya wanda nake bege da
dukkanin ruhina baki xaya na rantse da duk abinda nake yin
rantsuwa da shi cewar zai taimaka maka ka kuvutar da
51
BAKAR GUGUWA
Gimbiya Hasima daga hannun xan uwana da ya xauketa dan na
tabbatar maka da irin begen da nake yi maka ya zarce yadda
nake son komai a duniya” Zuhairu yace da ita.
“Ba zan amince da maganarki ba, har sai kin yarda za ki
yi imani da Allah ki karvi addinin musulunci, ki daina bautar
gumaka da tsafi ki rabu da duk wata shirka da sihiri da kike
aikatawa”.
Buniyatu tace da shi “Na amince zan karvi addinin
musulunci idan har za ka yarda dani na zama abar gasgatawa a
gareka, maganar aikin sihiri kuwa a yanzu bani da ikon
aikatawa tun da xan uwana ya qwace kurtun sihirin da yake
hannuna wanda a cikinsa ne alqaluman sihirin da zan iya
amfani da su don yin wani aikin sihiri suke ciki, kuma a yanzu
ya yi fushi dani saboda ina qoqarin baka kariya daga abinda
yake son aikatawa a gareka, ya kuma yi alqawarin ba zai sake
maidashi a gareni ba har abada”. Da ta gama masa bayani
zuhairu ya sata ta yi kalmar shahada ta shiga addinin
musulunci tare da sanar da ita abinda ya wajjaba akan kowane
musulmi, daga nan ya tambaye ta cewa “Yanzu ta wace hanya
zamu iya riskar inda matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima
dan na kuvutar da ita daga hannunsa”.
Buniyatu ta amsa masa da cewa “Ban san inda fadar
take ba, a faxin duniya amma na yi sani da wani rubutaccen
saqo na sirri da mahaifinmu ya bari, wanda ke qunshe da
tarihin yadda aka gina fadar da dukkanin sirrinta sai dai a
yanzu rubutaccen saqon baya tare da ni yana cikin kogon
dutsen da muke zaune tare da xan uwana da mahaifinmu kafin
ya rasu” Zuhiaru ya sake tambayarta “A ina wannan kogon
dutsen yake?”
52
BAKAR GUGUWA
Buniyatu tace da shi “Yana can kusa da birnin kisira
tsakanin wasu manyan tsaunuka a gavar kogin bahar sugaira,
tafiyar kwanaki biyu muke yi a cikin alqaluman sihiri na rage
nisan tafiya, kafin mu isa wannan kogon dutsen amman a
yanzu sai mun yi tafiyar kwanaki arba’in saboda bada
alqaluman sihiri zamu yi tafiyar ba”.
Zuhairu yace “Na xauki alqawarin sai na kuvutar da
Gimbiya Hasima daga hannun matsafi Bahalu da ya tafi da ita
ta kowane irin hali matuqar zan yi sani da inda wannan fada
take a faxin duniya, don haka mu tafi ya zuwa birnin Bahazum
fadar sarki shaiban mahaifin Gimbiya Hasima na sanar da shi
abinda ya faru gareta, sannan mu wuce alqaryarmu na sanar da
kakana abinda ya faru gareni daga nan na yi shiri don tafiya
wannan fada”. daga nan ya juya ga kuyangin Gimbiya Hasima
ya umarcesu da su kama dawakansu su hau don komawa
gidansu sanar da sarki abinda ya faru, kuyangin suka kama
dawakansu suka hau ita kuma Buniyatu ta hau dokin Gimbiya
Hasima zuhairu ya hau nasa dokin suka kama hanyar komawa
birnin Bahazum.
**
Da isar su Birnin Bahazum suka wuce fadar sarki
shaiban don su sanar da shi abinda ya faru ga ‘yarsa Gimbiya
Hasima, suna zuwa qofar fadar kuyangin suka shiga ciki
zuhairu da Buniyatu suka dakata daga waje don neman iso
kafin a basu damar su shiga ciki. Da shigar kuyangin cikin
fadar suka tarar da sarki shaiban a zaune cikin fadawa ana
fadanci sarki shaiban ya yi duba ya zuwa kuyangin bai ga
‘yarsa Gimbiya Hasima ba, kuma yanayin kuyangin suna cikin
wani hali na firgici da ruxani, nan take hankalinsa ya tashi ya ji
53
BAKAR GUGUWA
jikinsa cewa wani abu ne ya tokare shi ya miqe cikin sauri
daga kan kujerar sarauta da yake zaune yana mai tambayarsu
cewa ina Gimbiya Hasima take.
Kuyangin nan suka fashe da kuka sannan xaya daga
cikinsu ta amsa da cewar wannan shu’umin matsafin ya
xauketa ya tafi da ita…
Tun kafin ta qarasa maganar sarki shaiban ya faxi qasa
sumamme saboda jin mummunar labarin abinda ya faru akan
‘yarsa jama’a da ke fadar suka taso kan sarki shaiban don kai
masa xauki, aka riqa shafa masa ruwa da yi masa addu’a sai da
aka xauki lokaci mai tsawo sannan ya farfaxo daga suman da
ya yi. Bayan sarki shaiban ya dawo hayyacinsa ya nemi yadda
al’amarin ya faru, kuyangar nan ta kwashe labarin yadda
matsafi Bahalu ya xauke Gimbiya Hasima ya tafi da ita da
abinda ya faru tsakaninsa da zuhairu ya maida shi shi siffa irin
ta tsoho cikin alqaluman sihirinsa ta sanar da sarki.
Sarki shaiban ya tambaya “Yanzu ina zuhairun yake?”
Kuyangar nan ta amsa da cewa “Yana qofar fada don neman
iso a gareka kafin ya shigo” Nan take sarki ya umarci wani
bafade da cewa aje a kira zuhairu ace masa ya shigo. Bafade ya
tashi cikin sauri ya fita don cika umarnin sarki, ya je ya sanar
da zuhairu cewa sarki yace ya shigo. Zuhairu ya biyo bayan
bafade suka shigo tare da Buniyatu.
Da shigowar zuhairu cikin fadar, sarki shaiban ya dube
shi cikin matuqar mamaki da tu’ajibin ganin yadda kamaninsa
suka jirkita daga siffar matashin jarumi, sadauki ya zuwa siffar
dattijo mai tarin shekaru, kamar yadda kuyangar nan ta sanar
da shi, gaba xaya duk wani gashi dake jikinsa ya zama fari fat
irin na furfura ta tsufa. Zuhairu ya faxi gaban sarki ya kai
54
BAKAR GUGUWA
gaisuwa cikin murya mai rauni irin ta dattijontaka, sarki
shaiban ya amsa masa sannan ya sake tambayarsa abinda ya
faru, zuhairu ya sake sanar da shi kamar yadda kuyangar nan ta
sanar da shi da farko daga nan ya qara da cewa.
“Ya kai wannan sarki mai tarin daraja da martaba ta
hasken addinin musulunci da adalci ga jama’ar ka, ka sani
cewa na xauki alqawarin sai na kuvutar da Gimbiya Hasima
daga hannun wannan matsafin cikin yarda Allah, zan bi shi duk
inda ya shiga a faxin duniya na karvota daga gare shi” Ya juya
ga Buniyatu ya gabatar da ita ga sarki shaiban yace da shi
“Wannan ita ce Buniyatul Hajari bin kauwas ‘yar uwace a
wajen matsafi Bahalu sai dai a yanzu ta karvi addinin
musulunci, kuma ta yi sani da yadda za mu samu nasarar riska
inda wannan shu’umin matsafin yake da yadda zamu samu
nasara a kansa, ta kuma yi alqawarin za ta taimaka min na cika
alqawarin da na xauka cikin yardar Allah” Sarki shaiban ya yi
shiru hawaye na zuba daga idanunsa sannan ya xago kansa ya
dubi zuhairu yace da shi “To zuhairu na amince da wannan
shawara da ka yanke, sannan zan haxaka da jarumai da za yi
maka rakiya, zan kuma ba ka duk abinda kake buqata daga
gareni na guzuri yayin wannan tafiyar. Ni kuma zan sanya
malamai su ci gaba da yi muku addu’a tare da fatan Allah ya
baka nasara ka kuvutar da ita daga hannun wannan shu’umin
matsafin da ya xauketa” Zuhairu ya yi godiya ga sarki bisa ga
amincewar da ya yi akan shawarar sa, sannan suka yi sallama
ya tafi ya fice daga fadar da Buniyatu suka kama hanyar tafiya
alqaryarsu.
Sanda suka isa garinsu babu wanda ya gane zuhairu
daga cikin jama’ar da suka san shi, saboda sauyawar da
55
BAKAR GUGUWA
kamaninsa suka yi ya zuwa siffar tsoho suka wuce har suka isa
gidansu suka shiga shi da Buniyatu suka tadda kakansa dattijo
marwan zaune a tsakiyar gidan kan buzu yana jan tasbaha.
Shi kansa kakansa marwan bai gane zuhairu ba, saboda
sauyawar kamaninsa da suka yi zuwa siffar tsoho, ya riqa
dubansa cikin mamaki ganin wani dattijo sa’an shekarunsa
akan dokin jikansa zuhairu tare da Buniyatu wadda suka shigo
gidan tare da ita, har ya sauka daga kan dokinsa ya qaraso
gareshi. Da zuhairu ya ga yana yi masa duban rashin sani bai
gane shi ba sai ya yi masa magana ya ce da shi “Ya kakana
marwan ni ne jikanka zuhairu na kasance cikin wannan hali da
kake ganina, kuma hakan ta faru ne sakamakon aikin sihiri da
matsafi Bahalu ya aikata a kaina” ya kwashe labarin abinda ya
faru tsakaninsu ya sanar da shi, har ya zuwa yadda ya samu
nasara akan sa ya maidashi irin wannan siffa ta dattijo da yake
a yanzu.
Dattijo marwan ya cika da matuqar mamaki da al’ajabi
wannan al’amari da ya faru gareshi, sannan ya dubi zuhairu ya
ce da shi “Haqiqa ka aikata babban kuskure na mantawa da
abinda na umarceka, ka sani cewa na haneka da cire zoben da
na baka daga xan yatsanka, kuma na sanar da kai cewa ka riqa
lura komai rintsi kada ka sake ka taka sawun duk wani
ma’abocin tsafi da sihiri da kuke artabu da shi yayin kafsawa.
Idan da ka kiyaye wannan sharaxi da na sanar da kai na yi
imanin da cewa ba zai tava samun nasara akan ka ba, cikin
yarda Allah sai dai a yanzu bakin alqalami ya bushe a gareka
tunda har wannan lamarin ya faru, kuma ita Gimbiya Hasima
da wannan zobe yake hannunta na yi imani da cewa ba zai
nasarar kusantar ta ba matuqar zoben yana tare da ita” Zuhairu
56
BAKAR GUGUWA
ya yi shiru yana mai nadamar abinda ya faru na yin mantuwa
ga abinda kakansa ya sanad ra shi sai dai ya yi matuqar farin
ciki da ya ji cewa matsafi Bahalu ba zai samu nasarar kusantar
Gimbiya Hasima ba, matuqar zoben yana tare da ita.
Kakansa marwan ya ce da shi “Yanzu mene ne
qudirinka game da abinda ya faru?” Zuhairu ya amsa da cewa
“Qudurina shi ne zan bi wannan shu’umin matsafi duk inda ya
shiga a faxin duniya, don na kuvutar da Gimbiya Hasima daga
hannunsa” Ya nuna Buniyatu ya ci gaba da cewa “Wannan
qanwace a wajen matsafi Bahalu kuma ta yi sani da yadda
zamu samu nasarar zuwa inda ya tafi da Gimbiya Hasima don
kuvutar da ita, da kuma yadda za a karya wannan sihiri dake
tare da ni, ta kuma yi alqawarin za ta taimaka mini akan haka”.
Dattijo marwan ya amince da shawarar da zuhairu ya
yanke, sannan aka bawa Buniyatu masauki inda za ta zauna
kafin zuhairu ya gama shirinsa na tafiya.
**
Al’amarin Gimbiya Hasima kuwa bayan da matsafi
Bahalu ya xauketa cikin baqar guguwar nan ya yi sama da ita,
tun tana hangen kuyanginta da sauran jama’ar dake cikin
lambun da ya xauketa tana qaraji da kururuwar neman taimako
har ta daina hangensu saboda nisa da suka yi da wajen sannan
matsafi Bahalu ya huro wani farin hayaqi daga bakinsa