x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - BAKAR GUGUWA

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 36828 words

Category: Adventure Stories

Views 105

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ya raunana, ki sani cewa tsafi da sihiri
shirka ne wadda ba ta tasiri akan gaskiya, wato addinin
musulunci kuma Allah yana tare da duk wanda ya dogara da
shi zai kuma kareshi daga sharri ma’abota tsafi da sihiri komai
tasirin tsafi sa gareshi na dogara garesa kasancewar shi mai
rinjaye ne akan duk wani aikin sihiri na samu labarin abinda
yake faruwa gareki game da wannan shu’umin matsafin
wannan shi ne dalilin da ya kawoni gareki har na ambata ina
qaunarki cikin yarda Allah sai na rabaki da wannan matsafin
na kuvutar da ke daga halin da kike ciki”.
Gimbiya Hasima ta sake cewa da shi “Ka yi haquri ya
kai wannan bawan Allah, ba na so ka halaka a kaina kamar
yadda wasu da dama suka hallaka saboda ni” Zuhairu yace da
ita “Idan ya samu nasara hallaka wasu mazajen saboda ke a
baya Allah ne ya qaddara faruwar hakan a kansu kuma wannan
ba yana nufin cewa ya fi qarfin hukuncin ubangiji ba, cikin
yarda Allah ni zan zama sanadiyyar halakarsa matuqar bai rabu
da ke ba. Daga kaina ba zai sake halaka wani ba”.
Gimbiya Hasima ta yi shiru ba ta sake yin musu akan
maganarsa ba, bayan wani lokaci ta xago kanta tace da shi

24

BAKAR GUGUWA
“Yaya sunanka kuma ina labarin garinku da abinda yake
kawoka wannan wajen?”
Zuhairu yace “Sunana Zuhairu bin Safwan kuma na kan
zo wannan wajen ne daga birnin samaras dake qarqashin
masarautar mahaifinki” Nan ya sanar da ita dukkanin labarinsa
sannan suka yi sallama, ta kama dokinta ta hau sauran
kuyanginta suma suka kama nasu dawakan suka hau suka yi
masa sallama suka kama hanyar komawa birnin Bahazum sai
da suka yi nisa sannan shima ya kama dokinsa ya hau ya nufi
hanyar komawa gida.
**
Da isar Gimbiya Hasima gida ta sauka daga kan dokinta
ba ta tsaya a ko ina ba sai cikin xakin mahaifinta ta shiga cikin
matuqar murna da farin ciki ta sameshi a zaune cikin halin
damuwa, saboda baqin cikin da ‘yarsa take ciki. Da shigowarta
sarki shaiban ya ganta cikin murna da farin ciki abinda ya daxe
rabon da ya ga ‘yarsa Gimbiya Hasima a cikin irin wannan
yanayi tun daga sanda matsafi Bahalu ya ambata yana qaunarta
ya miqe cikin sauri yana mai matuqar mamakin tare da
tambayarta abinda ya sanyata wannan farin ciki.
Gimbiya Hasima tace da shi “Ya kyautu gareni na yi
godiya ga ubangiji Allah buwayi a bisa taimakon da rahamarsa
da ya saukar gareni” Ta kwashe labarin abinda ya faru gareta
tsakanin matsafi Bahalu da jarumi zuhairu a bakin lambun da
take zuwa ta sanar da mahaifinta.
Ta ci gaba da cewa “Ya samu nasara akansa har sai da
matsafi Bahalu ya gudu da kansa dan neman tsira,ya kuma
xauki alqawarin taimakona da raba tsakanina da wannan
shu’umin matsafin cikin yarda Allah” Sarki shaiban ya yi

25

BAKAR GUGUWA
matuqar mamaki da al’ajabi na jin wannan labari tare da yabon
jarumta da bajinta jarumi zuhairu tare da farin cikin jin cewar
ya xauki alqawarin zai taimakawa ‘yarsa Gimbiya Hasima ya
rabata da wannan shu’umin matsafi ya xaga hannunsa ya yiwa
Allah godiya sannan ya dubi Gimbiya Hasima yace da ita.
“Idan kin koma bakin wannan lambun da kike zuwa ki
ka haxu da wannan jarumin ki ce masa ya zo birnin Bahazum
ni sarki shaiban ina son ganinsa” Gimbiya Hasima ta amsa
masa da cewa za ta sanar da zuhairu abinda ua umarceta
sannan ta tashi ta koma cikin gida wajen mahaifiyarta.
**
Shi kuwa zuhairu da ya koma gida bai sanar da kowa
abinda ya faru tsakaninsa da Gimbiya Hasima ba ya ci gaba da
harkokinsa kamar yadda ya saba.
Washe gari da yamma ya sake yin shiri ya tafi bakin
wannan lambu kamar yadda ya saba, yana zuwa ya sauka daga
kan dokinsa ya xaureshi sannan ya koma inda ya saba zama ya
zauna. Bai daxe da zama ba sai ya hangi Gimbiya Hasima tafe
ta nufo inda yake ya cika da mamaki ganinta ita kaxai ba tare
da kuyanginta ba kamar yadda ta saba wani abu da ya qara
bashi mamaki shi ne bai ganta akan doki ba, kuma ya san ba
zai yiwu ta taho daga birninsu zuwa bakin wannan lambun da
qafarta ba.
Zuhairu ya ci gaba da dubanta har ta qaraso inda yake
tana mai yi masa murmushi sai dai ya sake yin mamaki da ya
ga bata yi masa sallama ba, kamar yadda yake a shari’ar
musulunci ga duk wanda ya zo ga xan uwansa musulmi sai ya
ji ta ci gaba da yi masa magana da cewa “Zuciyata na cike da
farin ciki sake ganinka masoyina, marhabin da zuwanka abin

26

BAKAR GUGUWA
begena cewa dai ni na kasance mai ni’imtuwa da qaunarka a
raina tamkar buguwar numfashi ga dukkan mai rai” Duk da
zuhairu ya ji murya tare da ganin surar mai yi masa magana
tamkar ta Gimbiya Hasima amma sai ya ji yana kokonton
tabbatar da cewar ita ce ya ci gaba da dubanta bai yi magana ba,
zuciyarsa tana shakka ace Gimbiya Hasima ce ya ji a jikinsa
cewa akwai yaudara a cikin lamarin don haka ya yi
takatsantsan.
Ta sake matsowa gareshi tana mai yi masa magana
cikin tattausar murya da cewa “Ya ya na ga ka yi shiru ba ka yi
magana ba, kuma ka qi sakin jikinka da ni kamar kana cikin
wani hali na damuwa”.Ta kai hannu zata tava jikinsa a sannnan
ne ya ji zoben da yake hannunsa ya yi motsi. Alamar wani
ma’abocin sihiri ne ya kusanceshi cikin sauri ya miqe daga
inda yake zaune ya zare takobinsa da take xaure a xamararsa
ya dubeta yace da ita. Duk da jin murya da ganin sura irin ta
Gimbiya Hasima ban yi imani da cewar ke ce Gimbiya Hasima
ta gaskiya ba, don haka ki sanar da ni wace ce ke kuma daga
wane jinsi ki ka kasance, idan ba haka ba kuma na halakaki dan
na ga akwai aikin sihiri irin na ma’abota shirka da vata a cikin
lamarinki”.
Matar nan dake tsaye a gabansa cikin surar Gimbiya
Hasima ta dubeshi ta bushe da dariya sannan lokaci guda sai ta
rikixa daga wannan surar ta koma surarta ta asali wato
Buniyatu Hajir qanwar matsafi Bahalu dake hallaka duk wanda
yace yana qaunar Gimbiya Hasima ta sake dubansa tace da shi
“Lallai ka yi zurfi cikin begen Gimbiya Hasima yadda har ka
ke iya gane cewa ba ita bace koda an suffantu da irin surarta da
ni kake bege kamar yadda kake begenta a zuciyarka babu

27

BAKAR GUGUWA
shakka da na yi farin cikin da babu wata halitta da ta tava yin
kamarsa a duniya. Zai kyautu gareka ka cire qaunarta daga
zuciyarka dan ita ‘yar sarki ce mafi girman daraja daga ‘ya
‘yan sarakunan duniya ba za ta auri wanda ba xan sarki
kamarta ba.
Zuhairu yace da ita “Ba zan so ki ba ba zan aminta da
maganarki ba, kuma babu shiriya tsakanina da duk wani
mutum ma’abocin tsafi da sihiri a duk inda yake ina mai sake
jaddada nasiha gareki ki gaggauta tuba daga halin da ki ke ciki
dan samun rahama idan ba haka ba kuma ki nisanta da inda
nake ko kuma na salwantar da kaifin takobina”.
Buniyatu ta sake yin dariya sannan ta ce da shi “Mai ya
haddasa irin wannan gaba da qiyayya tsakanina da kai
masoyina? Me Gimbiya Hasima tafi ni da kake matuqar
qaunarta har ka kasa amincewa ka so ni kamar yadda ka ke
sonta” Zuhairu ya ce da ita “Shirka tsafi da sihiri sune suka
haddasa gaba da qiyayya tsakanina da ke. Kuma ba zan tava
aminta da ke ba cikin wannan hali da ki ke ciki har abada, ita
kuma Gimbiya Hasima ta fi ki daraja ta addini da hasken
musulunci. Ta fi ki nasaba ta xaukaka da daraja, sannan ke
najasace a bar qi kasancewar kina halin vata da tavewa kuma
za ki zama mafi munin halin vata da tavewa kuma za ki zama
mafi munin makoma idan ki ka mutu cikin halin da ki ke ciki a
yanzu”
Buniya ta fusata da jin maganar da ya faxa ta ce da shi
“Haqiqa ka zama mai muzanci da tozarci matsayina akan
wadda ka ke bege na rantse da girman daraja abin da na gada
na sihirin tsafi da sihirin mahaifina ba don na yi alqawarin
aurenka ba, kuma ba na so ka shiga halin damuwa har ka

28

BAKAR GUGUWA
halaka da sai na xauke Gimbiya Hasima na hallakar da ita
yadda ba za ka sake ganinta ba har abada. To amma ka sani na
yi alqawarin aurenka ta kowane irin hali, kuma ko ba ka
amince ba sai ka zamo miji a gareni har qarshen rayuwarka, ba
za ka auri Gimbiya Hasima ba, ka yi saurare da zuwan abin da
zai faru gareka nan gaba a duk sanda na sake dawowa muka
haxu”.
Tana gama faxar maganar ta vace a fusace cikin
alqaluman sihirinta ba tare da ta saurari abinda zuhairu zai sake
cewa ba da zuhairu ya ga Buniyatu ta tafi sai ya maida
takobinsa sannan ya koma wajen da yake zaune ya zauna yana
tunanin abinda ta ce cikin kalamanta. Bayan tafiyar Buniyatu
ba da daxewa ba, sai ga Gimbiya Hasima tare da kuyanginta
sun iso bakin wannan lambu da zuwansu ba su shiga ciki
lambun ba kamar yadda suka saba sai zuhairu ya ga sun
tunkaro inda yake zaune, suna zuwa Gimbiya Hasima da kanta
ta yi masa sallama zuhairu ya amsa mata sannan tace da shi.
“Na zo gareka ne domin na sanar da kai saqon
mahaifina sarki shaiban ya ce na shaida maka ka zo yana son
ganinka a bisa ga taimakon da ka yi min” Zuhairu ya xan yi
shiru kamar yana tunani sannan ya ce da Gimbiya Hasima
“To” Ya tashi ya je ya kama dokinsa ya hau suka juya baki
xaya suka kama hanyar komawa birnin Bahazu suna tafe suna
hira har suka isa qofar shiga birnin.
Tun daga bakin qofa masu tsaron qofar suka fara duban
zuhairu cikin mamaki da al’ajabin ganinsa tare da Gimbiya
Hasima ba tare da ya hallaka ba kamar yadda suke da
masaniyar cewa duk wani namiji da ya kusanci inda take sai
wannan matsafin ya halaka shi matuqar ba mahaifinta ba. Da

29

BAKAR GUGUWA
suka shiga cikin birni duk inda suka wuce sai jama’ar gari su bi
zuhairu da kallo saboda ganin sa tare da Gimbiya Hasima suna
masu mamaki da ganin wannan al’amarin shi kuma zuhairu bai
damu da abinda yake faruwa ba, suka ci gaba da tafiya har suka
isa fadar sarki shaiban. Bayan sun isa fada Gimbiya da sauran
kuyanginta suka shiga ciki ta je ta sanar da mahaifinta sarki
shaiban zuwan zuhairu ta yi masa iso. Sarki ya bada umarnin
zuhairu ya shiga aka je aka shigo da shi har cikin fadarsa. Tun
da aka shigo da zuhairu cikin fadar sarki shaiban ya dubeshi sai
ya sake cika da matuqar mamaki saboda ganin shi ne jarumin
da ya yi mafarki da shi mahayin doki da ya yaqi matsafi
Bahalu ya halakashi a cikin mafarkinsa, gashi yanzu ya ganshi
a zahiri kuma shi ne wanda ya xauki alqawarin taimaka wa
‘yarsa. Zuhairu ya kai gaisuwa gaban sarki shaiban, sarki ya
amsa masa aka yi masa ishara da wajen zama, ya zauna suka
kaxaita daga shi sai sarki a fadar sannan sarki shaiban yace da
shi.
“Labari ya isheni game da taimakon da ka yiwa ‘yarta
Gimbiya Hasima, tare da alqawarin da ka yi na kuvutar da ita
daga halin da ta ke ciki shi ya sa na umarceta cewa idan ta
koma inda ku ka haxu da ita ta sanar da kai cewar ina son
ganinka. Ya kamata na sake yin godiya ga ubangijina bisa
baiwa da ni’imar da yake saukarwa akan bayin sa, don kafin
faruwar wannan lamari na yi mafarki da zuwan wani jarumi
mahayi doki da ya zo ya halaka wannan shu’umin matsafi ya
kuvutar da ‘yata daga halin da take ciki, sannan a yanzu da aka
shigo da kai fadata sai na ga cewa babu shakka kaine jarumin
da na yi mafarki da shi ya halaka wannan matsafi, don haka

30

BAKAR GUGUWA
nake mai kyakkyawan zato na samun nasara mafarkina ya
zama gaskiya.
Ba za mu zama masu yawaitar mamaki akan abinda ya
faru ba don buwaya ubangiji da ikonsa ta wuce haka, sai dai
mu yawaita godiya gareshi da addu’ar neman nasara, kuma na
yi maka alqawarin cewa matuqar ka rava Gimbiya Hasima da
wannan shu’umin matsafin da ya sanya rayuwarta cikin qunci,
to kuwa zan baka aurenta tunda itama tana qaunarka, wannan
shi ne dalilin da ya sa na ce ta sanar da kai ina son ganinka
Allah ya yi maka albarka”. Zuhairu ya yi matuqar farin ciki da
jin wannan bayani na sarki shaiban saboda qaunar da yake
yiwa Gimbiya Hasima ya yi masa godiya cikin girmamawa tare
da tabbatar masa da alqawarin da ya xauka na taimakawa
Gimbiya Hasima akan sha’anin matsafi Bahalu.
Daga nan suka yi sallama da sarki shaiban zuhairu ya
tashi ya fita daga fada ya koma wajen su Gimbiya Hasima ya
sanar da ita abinda ya faru tsakaninsa da mahaifinta Gimbiya
Hasima ta yi matuqar murna da farin ciki, sannan ta sa aka kai
zuhairu wani xaki na hutawa, abin qawatawa da kayan ado
nau’i daban-daban, suka zauna suka yi hira irin ta masoya aka
kawo masa abin sha na ‘ya ‘yan itatuwa na marmari dangin su
tufa,inibi da kayan ciye-ciye na karama masoyi zuhairu ya ci
ya sha daga abinda aka kawo masa sannan suka yi sallama a
bayan gama hirarsu ya tashi ya kama dokinsa ya hau ya kama
hanyar komawa gida.
Tun daga wannan lokacin zuhairu ya ci gaba da ziyartar
Gimbiya Hasima cikin wannan lambu da take zuwa a kowane
yammaci suna hira, wani lokacin kuma ya kan tafi har birnin
Bahazum fadar mahaifinta ya ziyarceta a can su yi hirarsu irin

31

BAKAR GUGUWA
ta ma’abota begen juna. Sannan zuhairu ya sanar da kakansa
marwan dukkanin abinda yake faruwa game da soyayyarsa da
Gimbiya Hasima da yadda mahaifinta ya karveshi da martaba
hakan yasa dattajo marwan ya yi mamaki da wannan lamari
sannan ya gargaxeshi cewa ya guji shiga abinda bai shafeshi ba,
matuqar ba taimako zai yi akan xan uwansa musulmi ba,
sannan kada ya sake ya cire zoben da ke yatsansa ko kuma ya
taka sahun wani matsafi da ya taso masa da nufin halakashi a
duk inda yake, idan ya kiyaye wannan sharaxi babu shakka zai
samu nasara akan kowane irin shu’umin matsafi komai tasirin
tsafi da sihirinsa.
**
Al’amarin matsafi Bahalu kuwa bayan da ya koma
bagirensa da suke zaune tare da ‘yar uwarsa Buniyatu a cikin
wasu manya tsaunika da suke nesa da Birnin Bahazum sai da I
sukan yi tafiya cikin alqaluman sihirin rage nisan tafiya su je
birnin cikin qanqanin lokaci, kuma idan suka je yankin da
birnin yake sukan shafe kwanaki masu yawa wani lokacin ma
har watanni kafin su sake komawa bigirensu. A sanda matsafi
Bahalu ya fara qaunar Gimbiya Hasima ya kan zauna kusa da
birnin Bahazum cikin halin vata na alqaluma sihiri yana lura da
duk wanda zai ce yana qaunarta ya halakashi, kamar yadda ya
halaka ‘ya ‘yan sarakuna da dama.
Bayan matsafi Bahalu ya yi jinyar raunin da zuhairu ya
ji masa a hannu tsawon kwanaki masu yawa har ya warke,
sannan sai ya sake yin shiri dan komawa birnin Bahazum da
nufin halaka zuhairu yana mai fusatuwa da abinda ya aikata
gareshi. Ya tafi ga taskarsa ta ajiyar kayan sihiri da tsafi da ya
gada a wajen mahaifinsa ya buxe ya xauko wani kurtun sihirin

32

BAKAR GUGUWA
daga cikin taskar ya maida taskar ya rufe ya koma gaban wani
farin dutse mai haske dake tsakiyar xakin ya faxi ya yi sujjada,
sannan ya xaga kurtun sihirin ya girgiza shi yana mai surutai
da sambatu irin na aikin sihiri wani farin hayaqi ya soma fita
daga cikin kurtun zuwa jikin dutsen, nan take sai ga zanen
siffar zuhairu ya bayyana a jikin farin dutsen tamkar madubi.
Matsafi Bahalu ya nuna wannan surar ta zuhairu da ta
bayyana a jikin dutsen da tafin hannunsa yana mai ci gaba da
ambaton wasu kalamai irin na aikin sihiri da nufin neman sa’a
a kansa ya halakashi idan ya sake komawa gareshi. Yana cikin
wannan hali na aikin sihiri sai ga ‘yar uwarsa Buniya ta shigo
cikin kogon dutsen, ta dubi jikin farin dutsen nan dake gaban
matsafi Bahalu, sai ta ga zanen surar masoyinta zuhairu tamkar
a jikin madubi nan take farin ciki ya lulluveta ta gabata gareshi
tana mai yin yabo da begen wannan surar.
Da jin abinda take cewa sai Bahalu ya dakata da abinda
yake yi ya juyo ya yi mata magana da cewar “Shin ko kin yi
sani da wannan jarumi da kike yabo da ambaton kyawun
surarsa” Bunayatu ta amsawa yayanta matsafi Bahalu da cewar
“Babu shakka na yi sani da wannan jarumin sunansa zuhairu
bin safwan yana zaune a birnin samaras dake qarqashin
masarautar birnin Bahazum, na kasance mai bibiyar rayuwarsa
cikin bege tun daga ranar da na fara ganinsa, cikin wasu ranaku
da na ziyarci yankin birnin Bahazum, shi ne wanda zuciyata
take bege da mafi kyawun ambato dan kasancewa tare dani, shi
ne wanda na kyautata rantsuwa ta akan alqawarin aurensa duk
da ya nuna rashin amincewarsa akan muradina”.
Matsafi Bahalu yace da ita “Ni kuma na kasance mai
nuna tsananin gaba da qiyayyata gareshi sababin abinda ya

33

BAKAR GUGUWA
aikata a kaina, ya kasance mai qaunar wata ‘yar sarki da nake
so da muradin aurenta, na kuma yi alqawarin halaka duk
wanda yace yana qaunarta don ta zama mallakina duk da ta ce
ba za auri ma’abocin tsafi da sihiri irina ba. Shi ne mutum na
farko da ya tava xaga makami a kaina da nufin yin gogayya
dani har ya fidda jini daga jikina. Shi ne wanda ya fasa xaya
daga cikin kurtun sihirin da na gada a wajen mahaifina har
qarfin tsafi da sihirina ya raunana.
Wannan shi ne dalilin da ya sa na xauki alqawarin
halakashi dan yin ramuwa akansa bisa ga abinda ya aikata a
kaina a duk sanda na sake komawa birnin Bahazum”. Buniyatu
ta ce da shi.
“Ina mai neman afuwa gareka kada ka halaka masoyina
bisa ga abinda ya faru, cewa ni na kasance mai yawan bege da
qaunarsa gwargwadon bugawa zuciya da fitar numfashi,kuma
zai zama abin kaico gareni da wanzuwa cikin qunci da baqin
ciki idan na rasa wannan jarumi ban ma san yadda makomar
rayuwata za ta kasance ba” Bahalu yace da ita “A rayuwata
bana afuwa kuma bana fasa xaukar fansa, ba zan saurara ga
duk wanda ya xaga makami gareni ba da nufin halakashi har
sai da naga bayansa, kuma bani da kaico akan kowane irin hali
da rayuwarki za ta kasance idan na halaka wannan jarumin.
Bakin alqalami ya riga ya bushe gareki don na yi rantsuwa da
ababen bautata tare da yin yanka garesu akan hakan ba zan fasa
abinda na yi niyya ba, sai ki yi haquri”.
Buniyatu ta fusata da jin maganarsa tace da shi “Idan
kuwa har ka halaka masoyina kamar yadda ka ambata na rantse
da duk abinda nake yin rantsuwa da shi, sai na je na halaka

34

BAKAR GUGUWA
Gimbiya Hasima ‘yar sarki shaiban bin Yasar da kake son ka
halaka masoyina saboda ita”.
Tana gama faxar maganar ta tashi cikin fushi ta fice
daga kogon dutse ta barshi, Bahalu bai damu da maganarta
ba,ya ci gaba da abinda yake yi na aikin sihiri dan neman
nasara akan zuhairu ya halakashi duk da cewar yasan Buniyatu
zata iya aikata abinda ta ambata akan Gimbiya Hasima.
**
Bayan fitar Buniyatu daga kogon dutsen ta fita ta zauna
ta rasa abinda yake yi mata daxi a duniya ta shiga tunanin
maganganun da yayanta ya amabata na cewa sai ya halaka
masoyinta zuhairu, damuwa ta yi mata yawa har ta rasa abinda
yake mata
End Ads