da su zuhairu suka yi matuqar
razana da ganin wannan yanayi da kuma al’amarin da yake
faruwa mai matuqar firgitarwa shi kuwa zuhairu ko a jikinsa
don ya saba da ganin irin wannan yanayi a duk sanda matsafi
Bahalu zai bayyana, kuma ya san wanna ba komai ba ne face
aikin tsafi da sihiri irin na ma’abota shirka da tacewa wa iyazu
billahi ya ce a zuciyarsa yana duban wannan baqar guguwa da
ta tunkaro inda suke cikin jarumta da qarfin zuciya har ta
qaraso ta tsaya a gaban su ta sauka. Da tsayawar iska sai ga
matsafi Bahalu ya bayyana ta cikin baqar guguwar a wannan
karon ya sha babban da yadda suka saba ganinsa ya bayyana, a
yanzu yana sanye ne da suturu irin na alfarma da manya
sarakuna da suke ji da kansu a duniya suke sanyawa, hannunsa
na hagu yana riqe da kurtunsa na sihiri a dama kuma yana riqe
da sandarsa ta tsafi, ya dubi su zuhairu ya yi magana da murya
irin ta nuna qasqanci a garesu yace da su.
“Ban yi zato ga samun nasara cikin abinda ku ke nufin
aikatawa ba don kuwa a yanzu lamarina ya ta’azzara akan wani
abin halitta ya samu nasara a kaina komai qarfin tasirin tsafi da
sihirinsa, na san za ka fito neman Gimbiya Hasima da nufin
zuwa fadata ku karvota daga hannuna, sai dai ina mai sanar da
ku cewa abinda ba za ku tava samun nasara a kansa ba ne ku
riski inda fadata take, bare ku karvi Gimbiya Hasima daga
hannuna, kuma halaka ta tabbata ga duk wanda ya shiga lardin
Ashtar da nufin zuwa fadata saboda ma’abota tsaro da masu
bada kariya dake tare da ni, babu wata jarumta ko aikin sihiri
da zai yi tasiri a kaina, kuma babu wani masani na ilimin
69
BAKAR GUGUWA
bokanci da zai iya sanar da ku yadda za ku samu nasara zuwa
fadata.
Ya dubi ‘yar uwarsa Buniyatu yace da ita “Ke kuma kin
yi zavi ga abinda zai kai ki ga halaka, kasancewarki tare da
wannan jarumin da kike son taimaka masa idan har ba ki rabu
da shi ba, don kuwa ba za ku tava samun nasara ba, kuma
hallaka ta kusanta ta gabata gare ki matuqar kina tare da shi
cikin wannan tafiya da ku ke yi, ki zama mai neman afuwar a
gareni tare da yin rantsuwa da alqaluman sihiri masu girma
akan za ki rabu da wannan jarumi ki dawo gareni, kuma na
miki alqawari zan maida miki alqaluman sihirin da na qwace
daga gareki na tafi da ke fadar mahaifinmu da na mallaka a
yanzu, mu zauna tare da ke cikin salama da aminci kamar
yadda mahaifinu ya so mu kasance kafin ya rasu” Buniyatu ta
amsa da cewar.
“Ai babu juya baya ga abinda na tabbata a kansa, na
taimakawa abin begena da kasancewa tare da shi har abada
kuma yadda mahaifinmu ya bar duniya abadan ba zai sake
dawowa cikinta ba, haka na rigaya na rabu da kai har abada ba
zan sake komawa gareka ba, kuma ka sani a yanzu na karvi
addinin musulunci tare da yin imani da Allah mahaliccin kowa
da komai, don haka ba zan sake komawa ga alqaluman sihiri
da bautar gumaka da tsafi ba, wanda a yanzu na yi sani da
cewa aikata hakan shirka ce da vata mabayyani,Allah ya
kiyashemu da sake afkawa a cikinsa” Matsafi Bahalu yace da
ita“Ke dai kina cikin fagamniya da vata saboda kasancewar
zuciyarki akan begen wannan jarumi, kin zavi kasancewa da
shi cikin halin wahala da qunci wanda qarshensa halaka. Fiye
da kasancewa dani xan uwanki cikin salama da tasirin aikatawa
70
BAKAR GUGUWA
abinda ki ke so na alqaluman sihiri, to kuwa za ki kasance abar
yiwa kaico da danasani mara misaltuwa cikin wannan hali
kuma ba za ku tava samun nasara akaina ba, cikin qudirinku
idan ma kina da wani sirri da ki ke son xauka a cikin wannan
kogon dutsen kamar yadda bayanai suka tabbatar mini to kuwa
ba za ki samu nasarar shiga cikinsa ba, bare ki xauka don na
xaure kogon dutsen da xalasimai na aikin sihiri da ba za ki iya
shiga ba, tunda ba kya tare da alqaluman sihiri a yanzu”.
Zuhairu ya zare takobinsa cikin fushi yana mai maida
masa raddi da cewa “Mu mun yi sani da cewa samun nasara ko
rashinta daga Allah ne, kuma a gareshi muke neman taimako
don haka muka yi imani da cewa zai bamu nasara a kanka, ko
don ya tabbatar da qarfin iko da buwayarsa akan duk wani
aikin sihiri da ya sa ke inkarin samun nasara a kanka, kuma
bari na fara tabbatar maka da cewa kai ba komai bane a cikin
rayuwar duniya, na hallaka ruhina da salwantar da rayuwarka,
wata qila san da zamu isa fadarka mu xauko Gimbiya Hasima
kai ka daxe da tafiya barzahu.
Ya saki linzamin dokinsa a sukwane ya iso gare shi, ya
kai masa sara a fusace da dukkanin qarfinsa, matsafi Bahalu ya
vace saran ya wuce shi kuma ya bayyana a baya, zuhairu ya
sake juyowa gareshi ya kai masa wani saran, Bahalu ya sake
vacewa bai sake bayyana ba sai da ya yi nisa da inda zuhairu
yake sannan suka hangeshi ya bayyana akan wani qaramin
dutse dake gabansa yadu bi zuhairu yace da shi.
“Ai yanzu girman matsayina ya fi gaban na yi arangama
da kai dan fafatawa,ka sani a yanzu ni ne shugaba na duk wani
ma’abocin aikin bokanci da sihiri da ke wannan yanki a duniya
don haka yin mubazara da kai nuna qasqancine a gareni, kuma
71
BAKAR GUGUWA
idan na halaka ka da kaina zai zama nuna gajiyawa cikin aikin
sihirina don haka zan bar ka ka halaka ne cikin wannan tafiya
da ku ke yi daga kai har sauran jarumai da ku ke tare da su”
Yana gama maganar sai baqar guguwar nan ta sake turnuqewa
ta gauraye wajen, iska mai qarfi ta taso ta yi sama da guguwar
ta nufi vangaren yamma inda baqar guguwa ta vullo tunda
farko, suka riqa duban wannan baqar guguwar har ta vacewa
ganinsu sannan sai suka ga wajen ya washe duhun da ya
lulluve sararin samaniya ya yaye ya washe duhun da ya lulluve
sararin samaniya ya yaye, komai ya koma yadda yake alamar
matsafi Bahalu ya tafi kenan.
Bayan tafiyar matsafi Bahalu sai Buniyatu ta sauka daga
kan dokinta, ta nufi qofar shiga kogon dutsen da zuwa qofar
sai suka ga wata irin iska mai tsananin qarfi ta fizgeta ta yi
sama da ita ta makata da jikin wani qaramin dutse dake kusa da
wajen, Buniyatu ta yi qara a firgice sannan ta zube a qasa
sumammiya sulken jikinta ya kama da wuta za ta qone ta
halaka.
Zuhairu da sauran jaruman da suke tare da shi suka diro
daga kan dawakansu cikin sauri suka tafi gareta don kai mata
xauki kada ta halaka, suka yi qoqarin kashe wutar da ta kama
jikinta har ta mutu, kafin ta fara qonata, daga nan zuhairu ya ci
gaba da shafa mata ruwa a goshinta yana yi mata addu’a har ta
farfaxo daga suman da ta yi, bayan ta dawo hayyacinta ta tashi
ta dubi zuhairu tace da shi.
“Haqiqa ba zan iya samun nasarar shiga wannan kogon
dutsen ba, saboda aikin sihiri da yayana matsafi Bahalu ya
aikata, don haka sai dai wani daga cikinku ya shiga saboda ni
bani da damar shiga cikinsa” Da jin haka sai ragowar baradan
72
BAKAR GUGUWA
dake tare da su suka yi shiru, babu wanda ya yi magana bare a
samu wanda zai ce zai shiga, saboda ganin abinda ya faru
gareta, shi kuwa zuhairu cikin qarfin zuciya da jarumta sai ya
amsa da cewa “Ni zan shiga kogon dutsen na xauko wannan
saqo, sanar da ni inda saqon yake na je na xauko”.
Buniyatu tace da shi “Saqon yana rubuce ne a jikin wata
fatar vauna dake cikin akwatin baqin qarfe da ke ajiye a
qarshen wannan kogon dutsen, idan ka shiga cikin kogon
dutsen kada ka sake ka tava komai sai wanan aikwati, kada ka
sake ka ji tsoro ko ka razana akan duk abinda za ka ga ya
tunkaroka idan ka shiga kogon dutsen haka kuma kada ka yi
magana ko ka yi waiwaye ka juyo baya har ka isa inda akwatin
take, idan ka isa gareta sai ka xauko akwatin ka fito da ita, ni
kuma zan buxe mu xauki wannan rubutaccen saqon dake
cikinta”.
Da zuhairu ya gama jin wannan bayani na Buniyatu sai
ya tashi ya nufi qofar wannan kogon dutsen ba tare da wani
tsoro ko fargaba ba, yana zuwa ya shiga cikinsa da shigarsa
wuta ce ta fara tasowa kansa tana wani irin huci da ruri na
azaba, zuhairu ya xaga hannun zai kare fuskarsa don kada
wutar ta qonashi amma sai ya tuna da maganar Buniyatu cewa
duk abinda ya gani kada ya ji tsoro ko ya razana don haka ya ci
gaba da tafiya har wutar ta qaraso gareshi ya ji ta wuce ta
jikinsa ba tare da ya ji zafinta ko kuma ta qonashi ba.
Ya sake ganin wani qaton dutse ya taho daga sama zai
faxo kansa ya halakashi, zuhairu bai razana ba, har dutsen ya
kusa kansa amma sai ya ga ya vace babu shi ya sake jin kamar
muryar kakansa marwan ya kira sunansa ta baya, zuhairu bai
juya ba ya ci gaba da tafiya.
73
BAKAR GUGUWA
Haka ya yi ta ganin abubuwa na ban tsoro da razanarwa
iri daban-daban, amma zuhairu bai razana ba har ya isa inda
wannan akwatin baqin qarfen take ya ganta da matuqar girma
yadda idan mutum ba sadauki bane ba zai iya xaukarta daga
inda take ba, ya matsa gareta ya sa hannu ya cicciveta da qyar
ya rabata da qasa ya xora a kansa saboda tsananin nauyi,
sannan ya juyo ya kama hanyar fitowa daga kogon dutsen.
Bayan zuhairu ya fito ya nufi inda su Buniyatu da
sauran jarumai da suke tare suke tsaye suna jiran fitowarsa ya
sauke akwatin a gabansu, Buniyatu ta yi matuqar farin ciki da
samun nasara xauko akwatin da ya yi, sannan ta sa hannun ta
buxe murfin akwatin, wani haske mai tsananin qarfi tamkar
walqiya ya tashi sama bayan da ta buxe, baradan dake tare da
su suka ji tsoro suka ja da baya,yayin fitar wannan hasken
bayan lafawar hasken Buniyatu ta sanya hannu a cikin akwatin
ta xauko wata baqar fatar vauna dake nannaxe da baqin zare
wadda ita kaxaice a cikin akwatin,sannan ta dubi zuhairu tace
da shi.
“Tunda har mun samu wannan rubutaccen saqon na
sirri,to kuwa mun samu damar samun nasara akan matsafi
Bahalu yanzu zamu tafi ga tsohuwa DIYANNUWA don ta
karanta mana wannan rubutaccen saqon, ta kuma sanar da mu
yadda zamu iya zuwa wannan fada ta Darul sabar da matsafi
Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima, don babu wanda zai iya
karanta wannan rubutaccen saqon a faxin duniyar nan sai ita”
Zuhairu ya dubeta cikin mamaki yace da ita “Wacece
kuma tsohuwa Diyanuwa da zamu tafi gareta don ta karanta
mana wannan saqo kuma menene alaqarta da wannan rubutu
da ke jikin wannan fata da babu wanda zai iya karantawa sai
74
BAKAR GUGUWA
ita?” Buniyatu ta ce da shi “Ita wannan tshowar Diyanuwa
kakata ce ta wajen uwa, kuma a hannunta na girma tun
tasowata, bayan mahaifiyata ta rasu, tana matuqar qaunata fiye
da yadda take son komai a duniya don babu abinda zan nema a
gareta ta gaza mallaka min matuqar tana da ikon bani shi, sai
dai kuma ba ta qaunar xan uwana Bahalu tare da mahaifinmu
kauwas a rayuwarta ta duniya, ta tsanesu da mafi munin tsana
saboda kasancewar halinsu iri xaya na tsananin mugunta da
zalunci, wannan ne dalilin da ya sa mahaifina ya karveni daga
hannunta ya dawo dani gareshi, a halin yanzu ta makance ba ta
gani kuma mahaifinmu ne sanadin makancewarta, sakamakon
jifanta da alqaluman sihirin sa da ya yi.
Babu wanda zai iya karanta wannan rubutaccen saqon
sai ita duk da cewa makaniya ce ba ta gani, kuma idanunta ba
za su warke daga wannan makantar ta aikin sihiri ba har sai an
xebo ruwan dake cikin rijiyar dake tsakiyar fadar Darul sabar
ta wanke idanunta da shi, idan muka isa gareta muka sanar da
ita buqatarmu babu shakka za ta taimaka mana ta kuma sanar
damu bayanan da bamu sani ba, game da ita wannan fada, ko
don mu xebo mata ruwan dake cikin wannan rijiya ta tsakiyar
fadar ta warke daga halin makantar ta aikin sihiri da ke tare da
ita” Zuhairu ya sake cika da mamaki ya dubeta ya ce da ita.
“To ita da take cikin halin makanta ta yaya za ta iya
karanta wannan rubutaccen saqon dake jikin wannan fatar?”
Buniyatu ta yi murmushi sannan ta ce da shi “Idan muka isa
gareta za ka gani har ma da wasu abubuwan ban mamaki da
al’ajabi daga gareta, don Allah ya yi mata baiwa gane duk
abinda ya kusanceta koda kuwa tsutsune ya wuce a sama ba
75
BAKAR GUGUWA
tare da ya yi kuka ba, idan ta ji hucin iskarsa za ta faxa maka
sunansa kuma babu kuskure ka ga shi ne ya wuce”
Zuhairu bai sake cewa komai ba ya ci gaba da mamakin
wannan al’amari da ta faxa masa, daga nan suka tashi suka
kama dawakansu suka hau suka ci gaba da tafiya, inda za su yi
tafiyar kwanaki goma sha biyu akan hanyarsu ta zuwa lardin
Ashtar kafin su isa inda tsohuwa Diyanuwa take zaune.
**
Ita kuwa Gimbiya Hasima daga ranar da matsafi Bahalu
ya kawota wannan fadar ta Darul sabar ta kasance cikin halin
tsananin damuwa da baqin ciki mara misaltuwa, babu abinda ta
rasa na daga suturu, abinci ko abin sha, a wannan fada har ma
da hadimai masu yi mata hidima, sai dai ba ta iya cin abinci
sosai kullum tana cikin tunani da damuwa da baqin cikin
rabota da mahaifinta da matsafi Bahalu ya yi, cikin kwanaki
kaxan ta rame ta yi baqi tamkar wadda ta shekara a halin
rashin lafiya, ba ta da aiki sai yawaita ibada don ta riqa samun
nutsuwa, tun da Gimbiya Hasima take a cikin wannan fada ba
ta tava fita daga cikin xakin da matsafi Bahalu ya ajiyeta ba,
duk da ya bata damar ta fita ta zagaya cikin wannan fada duk
inda take so, wata rana da yamma ta yi tunani ta fita waje don
ta xan zaga a harabar fadar ko ta ga wani abin nishaxi da zai
xebe mata kewa.
Ta tashi ta fita daga xakin ya zuwa waje ta ga an zagaye
harabar fada da shuke-shuke masu matuqar qayatarwa ga
furani da ‘ya ‘yan itatuwa na ababen marmari iri daban-daban
ta ci gaba da tafiya a cikin harabar fadar tana zagayawa har ta
iso wani xan qaramin lungu da duhun itatuwa da furanni suka
76
BAKAR GUGUWA
lulluveshi tana shiga sai ta riski wata kuyanga daga cikin
kuyangin dake hidima a wannan fada tana sallah, Gimbiya
Hasima ta cika da matuqar mamaki don ba ta yi zaton akwai
ma’abocin addinin musulunci a cikin wannan fada ba, ta tsaya
daga bayanta har sai da ta idar da sallah ta zauna ta yi addu’a ta
shafa, sannan Gimbiya Hasima ta matsa gareta ta yi mata
sallama.
Kuyangar nan ta xago kai da sauri ta dubi me yi mata
sallama da ta ga Gimbiya Hasima ce ta amsa mata cikin
mamaki don ba ta yi zaton cewa itama ma’abociyar addinin
musulunci bace ba. Gimbiya Hasima ta zo kusa da ita ta zauna
sannan ta ce da ita “Ya ke wannan baiwar Allah ina labarinki
kuma me ya kawoki wannan waje na ganki a halin yin hidima
qarqashin wannan shu’umin matsafi, ma’abocin shirka da
sihiri bayan ke kin kasance musulma mai bauta ga
Allah(SWT).” Kuyangar nan ta sunkuyar da kai hawaye ya
zubo daga idanunta sannan ta xago ta dubi Gimbiya Hasina
tace da ita.
“Sunana SANAWIYATUL ASSAD BIN ABDULNAS
mahaifina sarki ne dake sarautar birnin KUBAIRU gabas da
kogin Haisa, kuma jarumi ne da ya shahara a fagen yaqi da
runduna mayaqa, wanda hakan ta sa sauran sarakunan
qasashen kafirai ma’abota bautar gumaka da tsafi suke matuqar
shakka da tsoron kai hari akan birinsa, ya yi yaqe-yaqe da
dama na jahadi dan xaukaka addinin musulunci har sai da ya
kafa daular musulunci a wannan yanki, na taso cikin gata da
kulawa tare da tarbiyya irin ta addinin muslunci har na kai
girmana.
77
BAKAR GUGUWA
“Wata rana daga cikin ranakun rayuwata wani xan sarki
daga cikin ‘ya ‘yan sarakunan yamma ma’abocin bautar
gumaka ya ganni ya ce yana sona ya tafi ya sanar da
mahaifinsa buqatarsa ta san a nema masa aurena, da yake yana
da gata a wajen mahaifinsa saboda shi kaxai ya haifa a duniya,
tun a wannan rana sai mahaifinsa ya taso ‘yan aike daga
fadarsa zuw fadar mahaifina akan neman aurena ga xansa ‘yan
aike suka iso fadar mahaifina suka nemi iso aka basu damar su
shiga bayan sun shiga suka kai gaisuwa sannan suka sanar da
mahaifina saqon sarkinsu na neman aurena ga xansa.
Da mahaifina ya ji bayani dake tafe da su sai ya basu
amsa da cewa, su koma su sanar da sarkin su cewa babu
auratayya tsakanin xansa ma’abocin bautar gumaka da ‘yarsa
musulma, sai dai idan ya amince zai karvi addinin musulunci
daga shi har jama’ar birninsa su daina bautar gumaka da tsafi,
to kuwa zai bada aurena ga xansa.
‘Yan aike suka tashi suka kama hanya suka koma
birninsu, da suka isa birnin suka sanar da sarkinsu abinda
mahaifina ya ce sai ran sarki ya vaci, ya yi fushi da harzuqa
mai tsanani ya xauki alqawarin sai ya yaqi mahaifina ya rushe
birninmu ya xaukeni ya tafi dani fadarsa ya aurar dani ga xansa,
tun daga sanan suka shiga shirin yaqi, sun kawo hari har sau
uku birninmu amma ba su tava samun nasarar shiga birnin ba,
bare su samu nasara abinda suke nufin aikatawa kuma a duk
sanda zo sukan koma ne cikin tsananin rauni da
tagayyara,yawan rundunar baradansu ya kan qaranta jarumai
daga cikinsu su zama raunana, maxaukaka daga cikinsu su
zama maqasqanta.
78
BAKAR GUGUWA
Bayan da suka dawo daga yaqi na uku ne da suka je kai
hari birninmu, wannan xan sarki ya fusata da ganin baradan
mahaifinsa sun kasa samun nasara akan jama’ar birninmu ya
tafi ya xauki guba ya sha ya halaka da mafi munin mutuwa
saboda ni, sarkin nan ya yi matuqar baqin ciki mara misaltuwa,
saboda hallakar xansa saboda ni wanda shi kaxai ya mallaka a
duniya. Tun daga wannan lokaci ya sake xaukar alwashin akan
sai ya halakani ya halaka mahaifina don xaukar fansar
salwantar xan sa, ko ta wane irin hali don haka ya koma neman
taimako daga manyan matsafa da hamshaqan bokaye don a
samu wanda zai je fadar mahaifina ya halakashi ni kuma ya
xaukoni ya kai masa fadarsa, amma cikin hukunci ubangiji
babu wanda ya samu nasara a kaina ko kan mahaifina daga
cikin jama’ar da yake turowa har zuwa sanda ya haxu da boka
Kauwas, wanda shi ne mahaifin matsafi Bahalu wanda ya
xaukoki ya kawki wannan wajen, shi ne ya xaukoni daga fadar
mahaifina ya kawoni wannan wajen duk da bai samu nasara
halaka mahaifina ba, kuma bai kaini fadar wancan sarki da ya
yi alqawarin zai xaukoni ya kawo ni ba, sai ya taho dani
wannna wajen ya ajiye ni.
“Yadda al’amarin ya faru kuwa shi ne wata rana da
yammaci muna zaune a xakina tare da sauran kuyangina muna
hira, sai muka ji wata irin tsawa mai tsananin qarfi daban
firgici ta gauraye xakin,qarfin tsawar kamar faxuwar aradu
muka razana matuqa daga ni har kuyangin da suke tare da ni
muka tashi za mu fice daga xakin a firgice sai muka ga wata
guguwa ta turnuqe ta rufe qofar fita daga xakin, nan take kuma
ta gauraye ko ina, xakin ya yi duhu mafi tsanani daga yankin
dare, sannan