x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - BAKAR GUGUWA

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 36828 words

Category: Adventure Stories

Views 104

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

BAKAR GUGUWA

BAKAR GUGUWA

SHEHU USMAN MUHAMMAD
1


2

BAKAR GUGUWA

BAQAR GUGUWA
uhairu yana tafe akan ingarman
dokinsa cikin sassarfa da hanzari ya nufi
bakin wani makeken lambu ma’abocin
ni’ima da ‘ya ‘yan itatuwa furanni da
qoramu masu gudanarwa a cikinsa.
Zuhairu jarumi ne na gasken gaske
wanda jarumta da bajintarsa ta shahara a
dukka nin faxin alqaryun dake kusa da
birnin su yana da qarfin zuciya da rashin
tsoro na ban mamaki. Shi kaxai yakan fasa
rundunar mahara da masu tare hanya su yi wa fatake masu
tafiya a daji fashi.
Al’addar zuhairu ce yakan ziyarci bakin wannan lambu
ako wanne yammaci don yaga wata ‘yar sarki dake zuwa
lambun tare da kuyanginta ako wacce rana. Tun daga ranar da
ya fara ganinta a cikin wasu ranaku da yake yawo a wannan
wajen ya ji zuciyarsa takamu da tsananin begenta irin wanda ba
zai musaltu ba, sai dai baisan makomar rayuwarsa ba bisa ga
qaunar da yake yiwa wannan ‘yar sarki, kasancewar, mafi
girma da daraja daga cikin manyan ‘ya ‘yan sarakunan duniya.

Z

3

BAKAR GUGUWA
Ya yi sani da cewar ‘ya ‘yan sarakuna a wannan lokacin
basa auran wanda ba xan sarki kamarsu ba, ko kuma attajiri
wanda dukiyarsa ta shahara shi kuma gashi ba xan sarki ba,
dan haka ya kauda kai gabarin tunkararta ya bayyana mata
abinda yake zuciyarsa na daga begenta saboda girman
matsayinta da ya wuce nasa, sai dai yakan ziyarci bakin
wannan lambu da take zuwa akowane yammaci dan ya ganta.
Da isarsa bakin wannan lambu ya sauka daga kan
dokinsa ya kaishi gefe ya xaure sannan ya koma gindin wata
itaciya dake fuskantar qofar lambun ya zauna ya xauko wata
sarewa ta azurfa da ya gaa a wajen mahaifinsa ya soma busawa
cikin nishaxi yana mai sauraron isowar wannan ‘yar sarki dan
ya ganta. Yana zaune a wannan wajen har rana ta kusa faxuwa
wannan ‘yar sarkin bata zo ba, ransa ya vaci saboda kewar
rashin ganinta ya yi shiru yana tunani da saqe-saqe a ransa.
Yana cikin wannan halin kamar daga sama sai ya ji anyi
masa magana da wata irin zazzaqar murya mafi sanyi daga
ababan sauraro muryar tace masa “Da kazama mai yiwa
zuciyarka adalci da babu shakka da ka rabu da begen wadda
bata san kana begenta ba. Da ka rabu da tunanin wadda bata
san kana tunaninta da ka sauya lamarinka daga quncin qaunar
wadda ba za ta so ka ba, saboda girman matsayinta da ya wuce
naka”.
Zuhairu ya xago kansa cikin sauri ya dubi inda ya ji
muryar da ta yi masa magana amma baiga kowa ba ya duba
kowane vangare na daga inda yake baiga mai maganar ba.
Muryar ta sake cewa da shi “Kada ka damu ko kaji tsoro mai
qaunarka ce take yin magana da kai, ko kana inkarin abinda na
ambata na bayyana gare ka dan tabbatarwa”. zuhairu ya dubi

4

BAKAR GUGUWA
inda ya kejin muryar yace “Idan kin kasance tare da alhairi ki
bayyana gare ni don nasan wacece ke da kuma dalilin zuwanki
gareni har ki kayi sani da halin da nake ciki da faxar magana
mafi munin ambato idan kuma bakya tare da alhairi to kuwa
ina mai neman tsari da ke da roqon ki nisanta da ni ko wacece
ke”.
Zuhairu ya ji anyi dariya cikin tattausar murya sannan
murya tace da shi “Zan kasance alhairi gareka tunda ina tare da
xunbin qaunarka a zuciyata, dan haka zan bayyana gareka
nasanar da kai koni wacece da kuma abinda ya kawoni gareka
kamar yadda ka ce” Tana gama faxar maganar sai yaga wani
farin haske ya bayyana a gabansa daga cikin farin hasken sai ga
wata mace ta bayyana kyakkyawar budurwa tana sanye da
fararen tufafi hannunta riqe da wani qaramin gora abin
zagayewa da guraye da kambuna irin na aikin sihiri.ta dubeshi
tayi murmushi tare da juya fararen idanunta dan jan hankali.
Zuhairu ya qare mata kallo sannan yace da ita “Wacece
ke kuma meya kawoki gareni cikin wannan yanayi na aikin
sihiri, ki sani cewar babu aminci tsakanin musulmi da duk
wasu mushirikai ma’abota tsafi da sihiri, matuqar basu tuba
sun bi Allah ba” Kyakkyawar budurwa nan tayi dariya sannan
tace da shi “Da dai kayi sani da irin martaba da daraja da take
tattare da alqaluman sihiri da kuwa ka yi biyayya ga ma’abota
mallakarsu dan kazamo daga cikinsu shi ne abin tunqaho da
alfaharin mu dan a yanzu duniyar ma’abota sani na alqaluman
sihiri ne keda tasiri akan komai”.
Ta sake yi masa murmushi irin na jan hankali sannan ta
ci gaba da cewa “Suna na BUNIYATUL HAJARI BIN
KAUWAS mahaifina shi ne shugaban bokaye da ma’abota

5

BAKAR GUGUWA
aikin sihiri dake yammacin birnin SINAR ya rasu cikin wannan
shekarar yana tsakiyar tafiya ba tare da wata rashin lafiya ko
cuta ba, bayan rasuwar sane muka gaji sihiri tsafi da sihirinsa
ni da yayana da ya rasu ya barmu a duniya, na gaji kashi xaya
cikin xari na alqaluman sihiri mahaifina yayana kuma ya gaji
kashi casa’in da tara daga ciki.
Dalilin zuwa na gareka kuma shi ne na kasance mai
bibiyar rayuwarka tun daga lokacin da na fara ganinka zaune a
wannan wajen kana busa sarewa, tun daga wannan ranar na kan
ziyarci wannan wajen dan na saurari busar sarewar da kake yi
mai sanyaya zuciya har zuciyata ta kamu da tsananin begenka.
Sai dai bantava bayyana gareka ka ganniba sai a yau, kuma na
lura cewar zuciyarka ta kamu da qaunar wata ‘yar sarki da take
zuwa wannan lambu, dan haka na baiyyana gareka dan na raba
tunaninka da begen wacce bata san kana begenta ba”. zuhairu
ya fusata dajin wannan maganar yace da ita.
“Da kinsa yadda nake tsananin gaba da qiyayyar
mushiriki ma’abocin tsafi da sihiri da ko kusa baki tunakri inda
nake da buqatar na qaunace ki ba, kiyi alqawari zaki
musulunta dan samun rabo da kaucewa vata na aikin sihiri da
kike aikatawa, ko kuma ki nisanta da inda nake. Idan kuma ba
haka ba na rantse da wanda raina yake hannunsa sai na
halakaki da kisa mafi muni da azabar kaifin takobina”.
Buniyatu tayi dariya sannan tace da shi “Babu qiyayya
ko gaba a tsakanina da kai masoyina idan da ina gaba da kai zai
zama mafi sauqi gareni na halakaka ta hanyar qarfin tsafi da
sihirina” Ta xaga kurtun sihirin da yake hannunta ta girgiza shi
ta soma wasu irin surutai da sambatu irina aikin sihiri nan take
wuta takama daga kowace kusurwa huxu dake zagaye da

6

BAKAR GUGUWA
zuhairu sannan wutar ta taso kansa gadan-gadan zata qonashi
ya halaka zuhairu ya yi niyyar kaucewa amma yaji ya kasa
koda motsi daga inda yake kamar wanda qasa tariqeshi wutar
ta taso masa haiqam zata qoneshi ya halaka sai da ta kusa zuwa
inda yake ya soma jin zafi da hucinta sannan sai yaga wutar ta
mutu ta kuma vace ya dena ganinta.
Buniyatu ta sake bushewa da dariya sannan tace da shi
“Wannan kaxan kenan deaga tasirin tsafi da sihirin dana gada a
wajen mahaifina wanda zan iya halakaka da shi idan na so. Sai
dai bani da nufin cutar da kai bare aje ga batun halakaka,
saboda qaunar da nake yi maka kai dai ka yi azama ga zurfafa
tunani dan amincewa da qaunar mai qaunarka, zai zama mafi
kyautuwa gareka ka amince da buqatata muyi aure. Wannan
shi ne qudirina akanka ka yi tunani akan maganar na barka
lafiya”.
Tana gama faxar maganar sai yaga ta vace daga wajen
da yake ya daina ganinta sannan ya ji shuru bata sake yin
magana ba bare motsinta. Dan haka ya tabbatar da cewar ta tafi
tabar wajen don haka ya tashi ya kama dokinsa ya hau ya nufi
hanyar komawa gida. Da isar zuhairu gida ya xaure dokinsa ya
tafi wajen kakansa MARWAN BIN HADIS wanda shi kaxaine
ya rage masa a duniya iyayensa sun rasu tun yana qarami, a
hannun kakan nasa ya taso ya zauna kusa da shi ya gaishe shi
sannan ya kwashe labarin abinda ya faru gareshi tsakaninsa da
wannan shu’umar mace da suka haxu da ita a fitarsa ta wannan
yammaci ya sanar da shi.
Dattijo marwan ya cika da mamakin wannan labarin
sannan yace da zuhairu “Babu shakka duniya ta qara qazanta

7

BAKAR GUGUWA
da shu’uman mutane mushirikai ma’abota tsafi da sihiri a
doron qasa”.
Ya tashi daga inda yake zaune ya nufi wata akwatin
baqin qarfe ya xauko wani zobe na azurfa ya dawo ya bawa
zuhairu sannan yace da shi “Ka sanya wannan zoben a xan
yatsanka cikin yarda Allah zai zama kariya gareka daga sharrin
ma’abota tsafi da sihiri babu wani aikin sihiri da zai yi tasiri
akan ka kuma komai rintsi kada ka sake ka cireshi daga
hannunka a duk sanda wani matsafi ya tunkareka ko mai aikin
sihiri za ka ji zoben ya yi motsi a hannunka koda kuwa baka
ganinsa, haka kuma idan kaji dokinka ya yi haniniya ko ka lura
akwai wani abin cutarwa kusa da kai dan shi yana ganin abinda
kai baka gani kuma kar ka sake ka shiga wajen da dokinka ya
yi gardama shiga,haka kuma kar ka sake kaji tsoron duk abinda
dokinka bai ji tsoronsa ba. Kar ka manta yawan addu’a duk
inda kake dan neman tsari da kariya daga wajen Ubangiji ka
kiyaye da abinda na sanar da kai”.
Zubairu ya karvi zoben ya saka a hannunsa sannan ya
yiwa kakansa dattijo godiya ya tashi ya tafi.
**
Washe gari da yamma Zuhairu ya sake yin shiri ya
kama dokinsa ya hau ya nufi hanyar wannan lambu da
Gimbiya Hasima take zuwa akowane yammaci dan ya ganta.
Ya ci gaba da tafiya cikin sassarfa da hanzari har ya
soma hango bakin lambun da Gimbiya Hasima take zuwa kafin
ya qarasa bakin lambun sai ya hangi wasu barade su kimanin
arba’in sanye da kayan faxa da makamai sun zagaye wasu ‘yan
mata sun kamasu sun xora akan dakansu za su tafi da su, ‘yan

8

BAKAR GUGUWA
matan suna kuka da kururuwar neman taimako amma babu
wani wanda zai iya taimaka musu a wajen.
Zuhairu ya saki linzamin dokinsa ya qara azama dan ya
isa garesu yaga abinda yake faruwa da isarsa wajen sai yaga
Gimbiya Hasima ce tare da kuyanginta baradan nan suka kama
za su tafi da su. Zubairu ya fusata da ganin wannan aikin
zallunci ya dakawa baradan tsawa yace da su “Kai fajirai
qasqantattu ma’abota zallunci da rashin imani, mai kuke nufin
aikatawa ga waxannan bayin Allah da kuka kama?”
Baradan nan suka juyo suka dubi zubairu da suka ga shi
kaxaine tsaye akan dokinsa sai suka bushe da dariya irin ta
mugunta da zallunci sannan xaya daga cikinsu ya bashi amsa
da cewar “Babu shakka ajalinka ya kusanto da kai wannan
wajen, har kake tambayar abinda muke nufin aikatawa ga
waxannan ‘yan mata bari mu sanar da kai dan ya zama
guzurinka na tafiya barzahu, zamu tafi da su ya zuwa ga
shugabanmu domin su zama bayin mu masu yi mana hidima da
biya mana buqata duk sanda muka ga dama idan mun gaji da
su ko kuma an samu xaya daga cikinsu ta samu ciki, sai mu
sare kanta dan shayar da jininta ga ababan bautarmu, wannan
shi ne makomarsu da abinda zamu aikata garesu idan mun tafi
da su”.
Zuhairu ya fusata da jin wannan maganar yace da su
“Kaicon rayuwarku da abinda kuke aikatawa mafi munin
makoma na zallunci da rashin imani kuma idan wannan shi ne
qudirinku a rayuwa to kuwa zan halakaku da shafe ruhinku
daga doron qasa dan kawar da wannan zallunci”.
Baradan nan suka sake bushewa da dariya sannan xaya
daga cikinsu ya fita gaban zuhairu ya tsaya yana sanye da sulke

9

BAKAR GUGUWA
da kayan faxa hannunsa riqe da baqar takobi ya yi huci ya
xaga takobin sama cikin qaraji ya taso kan zuhairu.
Zuhairu ya zare takobinsa ya tare shi suka haxu ta
kubbansu suka yi karciya tartsatsin wuta ya tashi sama zuhairu
ya sake kai masa sara bardan ya goce kaifin takobinsa ya tafi
ya zuwa wuyan dokinsa nan take ya sare wuyan dokin suka tafi
suka faxi qasa gaba xaya. Barden nan ya miqe a fusace kafin
ya yi wani yunquri zuhairu ya cimmasa ya sanya takobinsa ya
yi masa saran karan tsaye nan take ya tsarga shi gida biyu duk
da sulken qarfen da yake jikinsa ya zube qasa matacce bai ko
shura ba.
Wani daga cikin radan mai qarfin zuciya ya sake
zaburowa cikin qaraji fusata zuhairu ya tareshi da zamiya ta
salon iya faxa irin na zaratan sadaukai ya kai masa wani
gawurtaccen sara da qarfin qarar da ruhi, bardan nan ya sanya
garkuwarsa ya kare, garkuwa ta kece gida biyu saboda tsananin
qafin saran, qafafun dokin barden na gaba suka durqushe dokin
ya yi haniniya wadda ta haxu da hucin saran da zuhairu ya sake
kaiwa bardan ya sameshi a tirken wuya nan take ya sare masa
kai ya faxi qasa matacce.
Da ganin haka sai ragowar baradan suka fusata suka
sauke su Gimbiya Hasima da kuyanginta daga kan dakansu
suka zare makamai suka tasar ma zuhairu baki xaya cikin
qaraji da gunjin fusata. Shima ya karkata garesu ya taho suka
haxu yana mai kai sara a tsakaninsu irin na qara da abokan
gaba, baradan nan suka zagaye shi ta ko ina suka yi masa
qawanya amma duk inda zuhairu ya keta sai dai kaga yana
saransu suna zuba qasa matattu, haske takobinsa ya koma jajawur saboda jinin azzaluman baradan nan. Gaba xaya wajan

10

BAKAR GUGUWA
ya yamutse aka shiga artabu da baqin gumurzu wanda ya kawo
salwantar rayuka barada masu dama.
Da baradan suka ga haka sai wasu daga cikinsu suka
razana suka koma arcewa suna gudu dan su tsira da rayukansu
saboda azaba masu qarar kwana suka ja daga aka ci gaba da
kafsawa har sai da zuhairu ya qara da su baki xaya. Bayan
zuhairu ya gama da waxannan azzaluman baradan ya tsaya
akansu yaga babu sauran wani mai numfashi a cikinsu, sannan
ya juya ga su Gimbiya Hasima ya hangeta tsaye a gefe daga ita
sai doguwar riga a jikinta babu mayafi ya yi sauri ya sauko
daga kan dokinsa ya xauki mayafinta dake yashe a qasa ya tafi
inda take ya miqa mata.
Gimbiya Hasima tasa hannu ta karvi mayafinta ta rufe
jikinta da shi, bata ko yiwa zuhairu magana ba bare godiya
abisa taimakon da ya yi masu, sai ma ta kauda kai gabarin
duban inda yake ta tafi ta kama dokinta ta hau sauran
kuyangunta suma suka kama na su dawakan suka hau, ta kaxa
linzamin dokinta suka kama hanyar komawa birnin Bahazum
ba tare da ta sake duban inda yake ba bare tayi masa godiya.
Wannan lamari ya qara karya zuciyar zuhairu game da
begen da yake yiwa Gimbiya Hasima ya duba duk irin
taimakon da ya yi mata bata ko yi masa magana ba bare godiya.
A tunaninsa saboda girman matsayinta da ganin shi ba
xan sarki bane yasa bata ko yi masa magana ba. Ya bisu da
kallo har suka vace sannan ya kaxa kansa ya juya ya kama
dokinsa ya hau, ya saki linzamin dokin ya fara tafiya. Kafin ya
yi nisa da wajen sai ya ji wata irin tsawa mai tsananin qarfi da
ban firgici tamkar faxuwar aradu ta gauraye wajen, sararin
samaniya ya yi duhu mafi tsanani daga yankin kudu take qasa

11

BAKAR GUGUWA
ta soma girgiza tana raurawa kamar zata tsage. Zuhairu da
dokinsa su afka ciki, can daga nesa wata baqar guguwa tare da
iska mai tsananin qarfi suka keto daga vangaren yamma,
guguwar tana tafe feshin wuta yana zuba daga cikinta, ta tafi
wajan da ya halaka azzaluman baradan nan ta wuce ta kansu
gaba xaya gawarwakin baradan suka kama da wuta suka qone
qurmus hadda sauran dawakansu da suke da rai duk suka
hallaka.
Zuhairu yaja linzamin dokinsa ya tsaya yana duban
wannan abin al’ajabin da yake faruwa, ya ji zoben dake
yatsansa ya yi motsi alamar wani ma’abocin aikin sihiri ne ya
kusanceshi, ya duba kusa da shi baiga kowa ba, kuma baiji
dokinsa ya yi haniniya ba. Ya dubi cikin baqar guguwar nan na
irin abinda yake faruwa, nan take ya tabbatar cewa wannan ba
komai bane face aikin tsafi da sihiri irin na ma’abota shirka.
Wa’iyazubillah yace a ransa yana mai neman tsari da wannan
lamari. Sannan sai yaga wannan baqar guguwar ta taso ta nufo
inda yake tsaye tana ci gaba da feshin wuta duk abinda ta wuce
takansa tun daga itatuwa har ciyayi sai kaga ya kama da wuta
ya qone qurmus.
Da farko zuhairu ya ji tsoro ya razana amma sai qarfin
zuciya da jarumta suka dawo masa saboda ganin dokinsa bai
razana ba. Ya ci gaba da addu’a yana mai neman tsari da
wannan aikin sihiri, guguwar tana zuwa kusa da shi sai yaga ta
ratse tabi gefe bata bi ta inda yake ba ta nuasa tayi gabas.
Zuhairu ya bita da kallo har ta vace daga ganinsa sannan ya
saki linzamin dokinsa ya ci gaba da tafiya.
Akan hanyarsa ta komawa
End Ads