gida kafin ya isa garinsu
yarinqa ganin gawarwakin baradan nan da suka arce suka gudu
12
BAKAR GUGUWA
sanda yake fafatawa da su, baqar guguwar nan ta biyosu ta
halakasu baki xaya daga su har dawakansu sun qone qurmus
zuhairu ya sake cika da matuqar mamaki tare da neman tsari da
irin wannan aikin sihiri. Ya wuce ya ci gaba da tafiya yana
tunani da saqe-saqe a ransa, babu shakka duk abinda ya faru na
wannan aikin sihiri yana da nasaba da Gimbiya Hasima sai dai
bai yi sani da dalilin faruwar hakan ba. Gashi dai duk baradan
da suka kama su Gimbiya Hasima da kuyanginta da nufin cutar
da su sun hallaka hatta gawarwakin wanda ya halaka duk sun
qone qurmus. Shi kaxai ne da ya yi nufin taimakonta bai
halaka ba.
Yasan sarki shanban bin Yasar musulmi ne kuma mai
ilimin addini ba zai yuwu ace daga shi ne yake aikata irin
wannan shirka da sihiri ba. Yana cikin tafiya yana wannan
tunanin a ransa, kafin ya isa garinsu sai ya hangi wani mahayi
tafe akan doki ya fito daga garinsu zai kama hanyar tafiya
birnin Bahazum ya iso inda yake sai zuhairu yaga ashe
abokinsa ne Muzaffar dake tafiya birnin Bahazum dan yin
fatauci suka haxu suka gaisa zuhairu ya yi nufin sanar da shi
abinda ya faru garehi, ko zai samu wani labari game da
Gimbiya Hasima ‘yar sarki shaiban bin Yasir da ya ke zuwa
birnin Bahazum da mahaifinta yake sarauta yawan fatauci.
Zuhairu yace da shi “Ya kautu gara na sanar da kai
abinda yake faruwa gareni game da begen gimbiya Hasima
‘yar sarki shaiban bin Yasir da kake zuwa birnin Bahazum da
mahaifinta yake sarauta dan yin fatauci wata qila za ka yi sani
da abinda zaka labarta mun game da ita”.
Ya kwashe labarin dukkanin abinda ya faru gareshi ya
sanar da shi yana mai faxin “Abinda ya bani mamaki shi ne
13
BAKAR GUGUWA
duk irin taimakon da na yi mata bata ko yimin godiya ba
kasancewarta mafi girman daraja daga ‘ya ‘yan manya
sarakunan duniya ni kuma gani ba xan sarki ba kuma ba xan
attajiri ba dan haka zuciyata ta karaya ga ambaton qaunarta
gareta.
A bayan tafiyarta kuma nga wani abin mamki da ban
al’ajabi wata baqar guguwa irinta aikin sihiri dake ci da wuta
duk ta halaka dukkanin baradan nan da suka tare Gimbiya
Hasima da nufin cutar da ita. Babu shakka duk abinda ya faru
yana da nasaba da ita, ina labarin wannan lamarin.
Muzaffar ya dubi zuhairu da duba irin mamki da
al’ajabi sannan ya ce da shi “Kaicon rashin sani dake sanya
zuciya afkawa a begen wandda ajali yakan kusanta ga duk
wanda ya ambata yana qaunarta, na san baka da masaniyar
abinda yake faruwa game da Gimbiya Hasima shi yasa har ka
ambata kana qaunarta amman labari ya ishe duk wanda yake
da masaniya maganar cewar wani hamshaqin matsafi ne daga
cikin manya matsafa ma’abota aikin sihiri dake yamma cin
birnin Sinar yake qaunarta. Kuma ya sha alwashin auranta kota
wane irin hali dan haka yake halaka duk wanda yace yana
qaunart, duk da ita tace bazata auri mushiriki ma’bocn tsafi da
sihiri ba ‘ya ‘yan sarakuna da dama tre da manya attajirai masu
yawa sun hallaka kn neman aurenta kuma wannan mtsafin shi
ne ya halakar da su”.
A yanzu Gimbiya Hasima ta zama tamkar hanyar
kuantar ajali ga duk wanda yce yana qaunarta hasalima babu
wani namiji da ya isa ya tunkareta bare ya yi mata magana
matuqar ba mahaifinta ba idan ba haka ba wannan matsafin sa
ya halakashi, shi yasa zaka ga a duk inda za ta je babu wani
14
BAKAR GUGUWA
namiji mai yi mata rakiya daga cikin baradan mahaifinta daga
ita sai kuyangunta mata take tafiya kuma duk abinda ya faru
akan wannan baradan na aikin sihiri suka halaka wannan
matsafine ya halakasu kaima saboda niyar taimaka mata ka yi
shi yasa baka halaka ba.
Wannan shi ne dalilin da yasa gimbiya Hasima bata yi
maka magana ba bare godiya a sandaka taimaketa babu shakka
data buxe baki ta yi maka godiya da kuwa wannan shu’umin
matsafin ya halakar da kai don haka kayi hattara. Zuhairu ya
cika da matuqar mamaki nain labarn abinda yake faruwa da
Gimbiya Hasima tare da gasgata mganar muzaffa ya sana da
shi. Saboda abinda ya gani da idanunsa sai dai lamarin baisa
zuciyarsa ta karaya ga barin qaunar ta ba sai ma ya ji ya qara
begenta a ransa ya kuma xauki alqawarin taimaka mata ya
rabata da wannan shu’umin matsafin iyacin iyawarsa.
Ya dubi muzaffar yace da shi “Idan har abinda ka
ambata ya tabbata gaskiya babu shakka na xauki alqawarin
kasancewa wanda zai raba tsakanin Gimbiya Hasima da
wannan shu’umin matsafin ko wanene shi, za sadaukar da
rayuwata dan na taimaka mata takuvuta daga makircin wannan
matsafin matuqar ina raye”. Muzaffar ya sake dubansa cikin
mamaki yace da shi “Kaicon zuciyar da ta makance akan
soyayya har take naman kai ruhi da gangar jikinta ga halaka.
Ka sani cewa rayukan mazaje da dama sun salwanta akan
qanarta kamar yadda kai ma za ka halaka matuqar baka nisanta
zuciyarka da begenta ba, menene dogaronka na tunkarar
hamshaqin matafi da ya halaka manya jarumai ‘ya ‘yan
sarakuna da attajirai masu ji da kansu akan Gimbiya Hasima”.
15
BAKAR GUGUWA
Zuhairu yace da shi “Kai dai bari ga ambaton irin
wannan zance kada imaninka y raunana cewa ni na dogara da
Allah ubangijin musulunci, gareshi nake neman taimko kuma
na yi imani da cewa shi mairinjayene akan akan kowane irin
qarfin tsafi da sihir dan haka bazan tava zama mai rauni ba
akan shakkar wani mutum ma’abocin tsafi da sihiri kuma da
sannu zan zama mai cimma nasara akan abinda na xauki
alqawari akansa cikin yarda Allah” Yana gama faxar maganar
ya yiwa muzaffar sallama ya kaxa linzamin dokinsa ya wuce.
Muzaffar ya bishi da kallo har ya vace sannan shima ya
saki linzamin dokinsa ya ci gaba da tafiya ya zuwa inda ya
nufa.
Da zuhairu ya isa gida bai sanar da kakansa marwan
abinda ya faru gareshi a wannan ranar ba, dan gudun kada yace
yarabu da Gimbiya Hasima saboda wannan shu’umin matsafin
ya bar maganr a ransa tare da xaukar alqawarin cewa idan har
ya koma bakin wannan lambun da Gimbiya Hasima tak zuwa
idan ya ganta zai tunkareta ya sanar da ita yana qaunarta ko
dan yaga wannan shu’umin matsafin da aka basa labarinsa.
**
Bayan wasu kwanaki da faruwa wannan lamarin zuhairu
ya sake yin shiri ya nufi bakin wannn lambu da Gimbiya
Husaima take zuwa da isarsa wajen ya tadda Gimbiya Hasima
bata qaraso ba, ya sauka daga kan dokinsa ya xaure shi, sannan
ya koma inda ya saba zama ya zauna yana jiran zuwanta.
Bai daxe da zama ba sai ga Gimbiya Hasima tare da
kuyanginta sun nufo bakin wannan lambu da take zuwa,
zuhairu ya yi farin ciki da sake ganinta yana dubansu har suka
iso bakin wannan lambun suka sauka daga kan dawakansu
16
BAKAR GUGUWA
sannan sai ya tashi ya tunkari inda suke dan ya sanr da ita
abinda yake ransa na daga begenta ko dan yaga wannan
matsafi da aka bashi labari kamar yadda ya yi alqawari a ransa.
Tunda ya tunkari inda suke sai yaga sunja sun tsaya
suna dubansa a tsorace kamar wanda suka ga wani abin
cutarwa ya tunkaro inda suke, zuhairu bai karaya ba saboda
sanin lamarin da aka bashi labari, ya isa garesu ya yi musu
sallama kuyangin Gimbiy Hasima suka amsa masa ita bata yi
masa magana ba, ta ma kauda kai ga barin dubansa kamar
yadda ta yi a waccan lokacin da ya taimake su. Ya ci gaba da
magaa yana mai faxin cewa “Idan har na yi dace da zuwana
gareki bai zama laifi ga Gimbiya ba, ina miqa gaisuwata gareki
cikin girmamawa da martaba ‘yar sarki jikan sarki abin bibiya
da koyi a fagen adalci ga sauran sarakunan duniya, na zo
gareki ne dan neman yarda bisa ga begenki da yake zuciyata
idan kin amince dani cikin lamarinki”
Yana faxar wannan magana sai yaga Gimbiya Hasima
ta xago kanta da sauri ta dubeshi cikin yanayin tsoro da razana,
kamar wadda ya faxa mata mummunan kalami mafi munin
ambato amm bata yi masa magana ba.
Kafin zuhairu ya sake yi mata magana sai suka ji wata
irin tsawa mai tsananin qarfi tare da wani rugugi mai hauhuwa
tamkar faxowar aradu ya guraye wajen, qasa ta soma girgiza
tana raurawa tamkar zata tsage su nutse a cikinta su halaka,
iska mai tsananin qarfi tare da baqar guguwar nan mai fesar da
wuta daga cikinta, irin wadda zuhairu ya gani a waccan karan
ta keto daga vangaren yamma ta nufo inda suke.
Zuhairu ya ji zoben dake hannunsa ya yi motsi alamar
wani matsafine ya tunkaro inda yake.
17
BAKAR GUGUWA
Baqar guguwar nan ta taso kan zuhairu kamar zata
rufeshi ya halaka da ganin haka sai Gimbiya Hasima da sauran
kuyangun da suke tare da ita hankalinsu ya tashi, suka shiga
halin kixima, shi kuma zuhairu sai yaci gaba da kallon baqar
guguwar dake tafe tana feshin wuta cikin jarumta da qarfin
zuciya, kuma yasan duk wannan abun ba komai bane face aikin
sihiri da tsafi irin na ma’abota shirka, wa’iyazubillah yace a
ransa yana duban guguwar har ta qaraso inda yake.
Da guguwar ta qaraso bata rufe shi ba kamar yadda ya
yi zato sai yaga ta tsaya a gabansa tayi tsiri sama tana juyawa,
sannan ta sake yo qasa har sai da talafa wajen ya washe sai
wani farin hayaqi da ya tsaya a gabn zuhairu, suka sake jin
wani qaraji mai ban firgici daga cikin hayaqin sannan suka ji
anyi zagi da kalma mafi munin ambato akan zuhairu, aka ci
gaba da yi masa magana cikin kakkausar murya mai hauhuawa
da faxin cewa.
“Kaicon rayuwa da kusantar ajali sababin abinda ka
ambata na begen Gimbiya Hasima, zai zama mafi munin
abinda ka ambata ka sani cewar Gimbiya Hasima mallakina ce
kuma na yi alqawarin hallaka duk wani namiji da ya kusanci
inda take matuqar ba mahaifinta ba bare ya ambata mata qauna
kamar yadda ka ambta na rantse da qarfin tsafi da sihiri na sai
na halakashi kamar yadda na halaka wasu mazaje da dama
saboda begenta”. zuhairu ya maida raddi ga inda yake jin
maganar cikin qarfin zuciya da cewar.
“Da zan ga wanda yake ambato wannan kalamin har ya
voye kana cikin aikin sihiri da kuwa na yi jihadin kawar da
mushiriki ma’abocin aikin tsafi daga doron qasa, wane ne kai
18
BAKAR GUGUWA
kuma ka bayyana gare ni ko kazama daga wanda suka isa
sufaxa aji ba masu voyuwa cikin aikin shiri ba”.
Yana faxar maganar sai ya sake jin wata tsawar mai
matuqar razanarwa ta sake cika wajen sannan iskar da take
kaxawa mai matuar qarfi ta tsaya cak daga cikin farin hayaqin
nan dake tsaye a gabansa sai yaga wani mutum ya bayyana ta
cikinsa qotone qarqarfa babu alamar tausayi ko imani a tare da
shi. Yana sanye da suturu irin na mashahuran matsafa
hannunsa na dama yana riqe da ‘yar qaramar sanda wadda aka
yiwa ado da zinare na hagu kuma yana riqe da wani gora irin
wanda ya gani a hannun matsafiya Buniyatu an zagaye bakin
gorar da wasu guraye da kambuna irina aikin sihiri ya dubi
zuhairu yace da shi.
“Ahir xinka da ambaton waxannan kalaman akan
wadda ya buwaya cikin aikin sihiri, nine matsafi BAHALUL
HAJARI BIN KAUWAS, mahaifina shi ne sarkin bokaye da
matsafa ma’abota bautar gumaka da ke yammacin birnin sinar,
bayan rasuwarsa na gaji kashi casa’in da tara na sirrin tsafinsa
‘yar uwata ta gaji kashi xaya dan haka yau duniya babu wani
masani cikin alqaluman sihiri da yasan kashi goma cikin xari n
abinda na gada wajen mahaifina.
Sannan ina qaunar Gimbiya Hasima ne da nufin ta zama
matata saboda na yi bincike a cikin alqaluman sihirina sun
tabbatar babu wata mace da ta kai ta kyau da cikar halitta a
wannan zamanin don haka na yi alqawarin aurenta ta ko wanne
hali, duk da ita tace ba zata auri mushiriki ba, ni kuma na xauki
alqawarin halaka duk wanda ya kusanci inda ta ke bare ya
ambata mata kalmar qauna, na halaka mutane da yawa akanta
wasu ma bata san da su ba, wucewa ta zo yi suka yaba
19
BAKAR GUGUWA
kyawunta surarta na halakasu kuma na yi rantsuwa da abin
bautata tare da qarfin tsafi da sihirina sai na hallaka duk wanda
yace yana qaunarta ko waye shi har zuwa ranar bayyanar wasu
bayanai cikin alqaluman sihirina da za su tabbatar da mallakar
Gimbiya Hasima gareni ta zama matata”.
Da jin wannan bayanin na matsafa Bahalu sai zuhairu
ya gane cewa shi ne yayan Buhaiyatu Hajari da ta tava zuwa
gareshi cikin halin aikin sihiri tace dashi tana qaunarsa da
muradin ya aureta.
Zuhairu ya sake maida masa raddi da cewar “Kaiconka
masu munin ambato zan yi ishara gareka da zuwan qarshen
wannan ta’asa da zalunci da kake aikatawa idan har ba ka rabu
da Gimbiya Hasima ba babu shakka ajali zai gabata gareka
sababin haxuwar ka da ni” Bahalu ya fusata da jin maganar
zuhairu yace da shi.
“Da ka yi sanin makoma da qarshen wanda ya ambaci
irin wannan kalamin gareta da ba ka yi sha’awar ambata shi da
bakinka ba na yi rantsuwa da ni kaina sai na halaka ka da kisa
mafi muni ta hanyar qarfin tsafi da sihirina”. Ya yi qaraji da
kururuwa mai qarfi da ke tattare da aikin sihiri, dajin ya yi
amsa kuwwa da amo mai hauhawa qasa ta yi girgiza ya juya
sandar sihirin dake hannunsa nan take ta rikixa ta zama
shafceciyar takobi tana sheqi kaifinta kamar zai zuba a qasa, ya
taso kan zuhairu a fusace baqar guguwar nan ta biyo bayansa.
Zuhairu ya zare tasa takobin ya tare shi suka yi karon
battar qarfe.takubbansu suna haxuwa wata qarqarfa iska tayi
jifa da zuhairu har sai daya tafi ya faxi a qasa, Bahalu ya kai
masa sara zuhairu ya goce, sannan ya miqe cikin sauri da
azama shima ya kai masa nasa saran, babu abinda ya tare kaifin
20
BAKAR GUGUWA
takobin zuhairu amma tana zuwa jikin Bahalu sai ya kece gida
biyu saran takobin ya wuce. Suka ci gaba da fafatawa cikin
mugun nufi na san halaka abokin karawa. Da matsafi Bahalu
yaga ba zai iya halaka zuhairu ta hanyar jarumta ba sai ya
koma aikin sihiri.
Ya yi qaraji ya nuna zuhairu da tafin hannunsa yana
surutai irin na aikin sihiri, nan take wuta ta kama ta taso kan
zuhairu za ta qonashi zuhairu ya yi tsalle da majaujawa ya goce
wutar ta wuce ba ta samu jikinsa ba, ya watso masa wasu
kibiyoyi irin na aikin sihiri zuhairu ya sanya takobi ya kaxe
kibiyoyin suka tafi suka zube a qasa wajen yama da wuta.
Matsafi Bahalu ya sake yin wani siddabaru cikin
alqaluman sihirinsa, nan take sai ga wani qaton dutse daga
sama yana ci da wuta ya mirgino ya nufo kan zuhairu zai
danneshi ya halaka, Gimbiya Hasima ta qwala qara mai tsanani
qarfi saboda razana, saboda tasha ganin da irin wannan sihirin
ya hallaka wasu daga cikin masoyanta, zuhairu ya ji hucin
tahowar dutsen daga samansa ya yi tsalle ya kauce dutsen ya
faxi a wajen ya kama da wuta qasar wajen ta qone qurmus ta
yi baqi.
Bahalu ya fusata da ganin zuhairu bai halaka ba, ya sake
yin wani siddabaru cikin alqaluman tsafinsa, ya sari qasa da
takobin dake hannunsa nan take qasar ta riqa darewa tana
ruftawa da duk abinda yake kanta ta nufo zuhairu yake za ta
rufta da shi ya halaka zuhairu ya sake gocewa qasar bata rufta
da shi ba. Matsafi Bahalu ya sake yin wani qaraji dake tare da
aikin sihiri, iska mai tsananin qarfi tare da baqar guguwar nan
suka sake turnuqe wajen, Bahalu ya biyo ta cikin baqar
guguwar ya taso kan zuhairu zai halakashi, idan ya yi qaraji sai
21
BAKAR GUGUWA
ka ga feshin wuta yana zuba daga cikin guguwar saboda aikin
sihiri.
Gimbiya Hasima ta sake qara wata razananniyar qara
saboda firgici don ta sha ganin a gabanta ya halaka wasu daga
cikin wanda suka ce suna qaunarta da irin wannan aikin sihirin.
Kafin baqar guguwar ta isa kan zuhairu sai ya yi kabbara da
maxaukakiyar murya mai qarfi, tare da ambaton sunayen
ubangiji yana mai tasbihi gareshi dan yin tawassali da neman
kariya daga gareshi akan wannan aikin sihiri. Guguwar tana
qarasowa gareshi ya kai sara cikinta da dukkanin qarfinsa cikin
sa’a ya samu matsafi Bahalu a hannun kurtun sihirin dake
hannunsa ya faxi qasa ya fashe. Bahalu ya yi wata
razananniyar qara mai qarfi saboda azaba, guguwar da ta
tunkaro zuhairu ta koma baya ta vace, sannan wajen ya washe
zuhairu ya duba bai ga matsafi Bahalu ba ya shiga nemansa
cikin taka tsantsan amma bai sake ganin ya bayyana gareshi ba.
Bayan wani lokaci sai ya ji maganar matsafi Bahalu
yana cewa da shi cikin kakkausar murya “Azaba ta tabbata
gare ka ya kai wannan jarumin dake nufin tozarci ga girman
matsayina. Na yi rantsuwa da taurari tare da qarfin sihiri da
tsafi sai na halakaka da kisa mafi qasqanci da azaba mai
tsanani sabida abinda ka aikata gareni” zuhairu yace da shi.
“Banu razanarwa ko ban tsoro ga wanda ya zama
gajiyayye ma’abocin rauni da rashin tasiri, kaicon wanda yake
gudun ceton rai cikin tsoro da firgici akan abin da ya sha
alwashin ganin bayansa, alhalin abinda ka dogara da shi ya
kasa baka nasara, idan kana inkarin abinda na ambata ka sake
bayyana a gareni na rantse da wanda raina ke hannunsa sai na
22
BAKAR GUGUWA
halakaka da shafe ruhinka daga doron qasa, kamar yadda ka
halaka waxanda ka samu nasara akansu kake alfahari da hakan.
Matsafi Bahalu ya bayyana cikin fushi amma nesa da
inda zuhairu yake jini yana zuba a inda kaifin takobin sa ya
sareshi sannan kurtun sihirin da yake hannunsa ya fashe ya
dubi zuhairu yace da shi.
“Zai zama abin kaico gareni idan na bar wannan waje
ba tare dana hallaka ba, sai dai ya zama dole gareni na koma ga
bagirena don sake yin shiri a kanka, sababin fashewar kurtun
sihiri da yake hannuna amma ina mai sake yin rantsuwa da duk
abinda nake yin rantsuwa da shi, halaka za ta tabbata gare ka a
duk sanda na sake bayyana gareka, sababin abinda ka aikata a
kaina” Yana gama faxar wannan maganar sai suka ga ya vace,
sannan baqar guguwar nan da ya bayyana ta cikinta ta sake
turnuqewa ta yi tsiri sama, ta nausa ta nufi inda ta fito har ta
vace, duhun daya rufe wajen ya washe komai ya koma yadda
yake.
Da zuhairu yaga matsafi Bahalu ya tafi sai ya yi ajiyar
zuciya irin na jarumta sannan ya maida takobinsa ya juya
wajen Gimbiya Hasima da sauran kuyanginta suke tsaye suna
kallon abinda ya faru tsakaninsu da matsafi Bahalu, suna haxa
ido da ita sai ta fashe da kuka sannan ta soma yi masa magana
cikin wata tattausar murya mai ban tausayi tace masa “Wannan
shi ne abin da yake damuna a rayuwata ta duniya, tun daga
ranar da wannan matsafin yace yana qaunata na rasa sukuni da
farin ciki har ya zuwa yau, babu shakka duk abinda ya faxa
haka yake wannan matsafin ya halaka jama’a da dama saboda
ni tun daga ‘ya ‘yan sarakuna da manyan attajirai da suka
gabata suna neman aurena har ta kai a yanzu babu wani namiji
23
BAKAR GUGUWA
da ya isa kusantar inda nake bare ya yi min magana matuqar ba
mahaifina ba, har sai wannan shu’umin matsafin ya halakashi,
wannan ne yasa ban yi maka magana ba bare godiya a sanda ka
tava taimakona a farkon haxuwata da kai don jaka ina roqonka
ka nisanta kanka da kusantar inda nake matuqar ba kana so
wannan matsafin ya halakaka ba kamar yadda ya halaka wasu
mutane a baya”.
Zuhairu yace da ita “Ka da ki zama mai raunin zuciya
da zai saka imaninki