x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - BAKAR GUGUWA

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 36828 words

Category: Adventure Stories

Views 106

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
sai na ji an wafceni an yi sama da ni cikin iska, na

79

BAKAR GUGUWA
yi qaraji da kururuwar neman taimako daga sauran kuyanfin da
suke tare da ni amma babu wanda take ganina saboda tsananin
duhu da ya rufe xakin kamar yadda bana ganin kowa, daga nan
sai na ji kaina ya juye na fita daga hayyacina ban sake sanin
abinda yake faruwa gareni ba.
Sai da na dawo hayyacina sai na ganni a cikin wannan
wajen da kuma wanda ya kawoni wato Boka Kauwas mahaifin
matsafi Bahalu da ya xaukoki, ni ce mace ta farko da aka kawo
wannan waje dukkanin sauran daga baya ne aka kawo su.
Kuma duk wadda ki ka gani a cikin wannan fada ‘yar wani
sarki ce ko kuma ‘yar attajiri aka xaukota daga hannun
mahaifinta aka kawota nan, yau shekarata uku kenan rabona da
mahaifina da sauran dangina, na yi kukan baqin ciki da takaici
mara misaltuwa, har na haqura na miqa lamarina ga Allah ina
mai roqon sa ya kuvutar da ni daga wannan hali da nake ciki,
wannan shi ne labarina da abinda ya faru a gareni”.
Da Gimbiya Hasima ta ji wannan labari nata sai ta yi
matuqar tausayawa wannan kuyanga, itama ta bata nata labarin
da abinda ya faru tsakaninta da matsafi Bahalu ya xaukota ya
kawota wannan wajen, suka taya juna jimami tare da addu’ar
Allah ya kuvutar da su daga halin da suke ciki, daga nan suka
ci gaba da hira har zuwa faxuwar rana, suka yi sallar magariba
sannan suka yi sallama Gimbiya Hasima ta tashi ta koma
xakinta.
Tun daga wannan rana Gimbiya Hasima ta kan ziyarci
wannan kuyangar su yi hira, ko kuma ita kuyangar ta je xakinta
da haka har suka yi matuqar shaquwa da juna.

80

BAKAR GUGUWA
**
Su kuwa su zuhairu bayan da suka ci gaba da tafiya a
cikin wannan daji suka shafe tsawon kwanaki shida sannan
suka iso inda wata bukka take ita kaxai a tsakiyar daji,Buniyatu
dake gaba ta dubi zuhairu tace da shi.
“Wannan shi ne bigiren da kakata tsohuwa Diyanuwa
take zaune, don haka bari mu isa gareta kaga abin al’ajabi cikin
hikima da baiwar da Allah ya hore mata. Kuma keta wanda ya
yi magana daga cikinku ku yi saurare ku ga abinda zai faru
tsakanina da ita dan ku zama shaidu da tabbatar da abinda na
ambata”.
Suka tunkari inda wannan bukka take, kafin su isa
gareta sai suka hangi wata tsohuwa ta fito daga cikin bukkar da
ta ji takun sahun tafiyar dawakansu sanye da baqaqen tufafi
hannunta riqe da sanda tana dogarawa, ta tunkaro inda take jin
motsin tafiyarsu ta tsaya har suka qaraso gabanta suka ja
linzamin dawakansu suka tsaya, gaba xaya babu wanda ya yi
magana daga cikinsu, ita kuma idanunta a rufe irin na halin
makanta tace da su.
“Su wanene waxannan jama’a da kuka zo gareni haqiqa
na ji akwai jikata Buniyatul Hajari a tare da ku” Buniyatu ba ta
yi magana ba ta karvi kwari da baka daga hannun wani jarumi
daga cikin jarumai da suke tafe tare da su, ta sanya kibiya a
cikin bakar ta ja ta sakar mata kibiyar a sairin qirjinta, kibiyar
ta tafi gareta da qarfi kafin ta kai jikinta tsohowa Diyanuwa ta
ji hucin tahowarta, ta sanya sandar dake hannunta ta kaxe
kibiyar ta tafi jikin wata bishiya ta cake a jikinta, sannan ta
sake yin magana ta ce da su.

81

BAKAR GUGUWA
“Babu shakka wannan harbin kibiyar na jikata ne
Buniyatu, marhabin da zuwanki gareni kuma ke da su wa ku ke
tafe har ku adadin mutum arba’in da biyu kuma ke kaxai ce
mace a cikinsu?” Su zuhairu da sauran baradan dake tare da shi
suka cika da mamaki abinda ya faru tare da maganar da
tsohuwa Diyanatu ta ambata, wadda babu kuskure a cikinta
tamkar idanunta a buxe tana ganin adadin yawansu.
Buniyatu ta amsa mata da cewa “Babu shakka ni ce
jikarki Buniyatu Hajari, na ziyarceki tare da waxansu jarumai
da muke tafe tare da su cikin wata buqata da ta kawomu gareki,
amma ya aka yi ki ka san adadin yawan mu cewa mu arba’in
da biyu ne muka zo wannan wajen kuma ni kaxaice mata a
cikinsu?”
Tsohuwa Diyanuwa ta yi murmushi sannan tace da ita
“Jikata mantawa kika yi dani shi yasa ki ka yi min wannan
tambayar amma ki sani ina da hikimar gane mace a cikin taron
maza komai tsananin yawansu kuma koda ba ta yi magana ba,
ta hanyar hucin numfashinta da bil adama suke yi wanda
kunnena yake ji kuma na gane adadin yawanku ne tun daga
takun sawun dawakanku da na ji sanda kuka tunkaro inda
nake” Ta juya ta nufi wajen bukkarta tana dogara sanda tare da
yi musu izinin su qaraso, su zuhairu da Buniyatu suka saki
linzamin dawakansu suka qarasa bakin wannan bukka suka
sauka suka xaure dawakansu, tsohuwa Diyanuwa ta gabato
musu da abinci da abin sha na daga ‘ya ‘yan itatuwa suka ci
suka sha har sai da ya ishe su gaba xaya duk da yawansu.
Bayan sun huta sun nutsu tsohuwaDiyanuwa ta
tambayesu me ke tafe da su gareta, kamar yadda Buniyatu ta
fara sanar da ita da farko. Buniyatu ta kwashe labarin duk

82

BAKAR GUGUWA
abinda ya faru tsakanin zuhairu da kuma yayanta matsafi
Bahalu ta sanar da ita, ta kuma yi mata bayanin abinda ya
kawosu gareta, don ta karanta musu wannan rubutaccen saqo
na sirri da mahaifinta ya bari kafin ya rasu, saboda su sami
damar zuwa wannan fada da matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya
Hasima su karvota daga gareshi, su kuma xebo ruwan da yake
cikin rijiyar tsakiyar fadar, don samun waraka daga aikin
sihirin da aka yiwa zuhairu su kuma kawo mata don karya
sihirin dake tare da ita, ta warke daga halin makantar da take
ciki.
Da tsohuwa Diyanatu ta ji wannan bayani sai tace da
Buniyatu “Haqiqa zan taimaka muku ko don na samu waraka
daga halin da nake ciki, idan kun cimma nasara, kuma bana
qaunar zallunci ba kuma zan tava goyan bayan azzalumi ba a
duk inda yake a faxin duniya” Ta juya ga Buniyatu tace da ita
“Ina rubutaccen saqon yake?”
Buniyatu ta xauko wannan fata ta miqa mata, tsohuwa
Buniyatu ta karva ta warware fatar ta shafi rubutun dake jikinta
da tafin hannunta, ta soma karantawa tana sanar da su ma’anar
rubutun kamar haka:Darul sabar wata shahararriyar fada ce aka ginata a
lardin Ashtar tsakanin wasu manya tsaunuka guda uku,tana da
matuqar kariya da tsaro na xalasumai na aikin sihiri da sihiri
dake zagaye da fadar, kuma kafin ku isa inda wannan fada take
da zarar kun shiga lardin Ashtar za ku fara gamuwa da fitintinu
iri daban-daban, na abubuwan cutarwa da za su taso gareku da
nufin halakaku, sai kun yi da gaske wajen samun nasara a kan
su, don shi kansa lardin Ashtar yanayinsa ya bambanta da
sauran yanayin da ku ka saba ji a cikin wannan duniya, akwai

83

BAKAR GUGUWA
masifu da wahalhalu masu tsanani wanda zai wahala wani
bil’adama ya shiga cikinsa ya fito ba tare da ya halaka ba”.
Idan kun shiga lardin Ashtar kafin ku isa inda wannan
fadar take za ku fara tarar da wasu manya-manya sansanin
barada kuma jarumai ma’abota aikin sihiri har guda uku,
mahaifinki boka kauwas ne ya samar da wannan sansanin
baradan, kuma sai da ya shage shekaru uku cur yana tattaro
manya sadaukai da suka shahara a fagen jarumta, sannan ya
kafa waxannan sansanonin qarqarshin alqaluman sihirinsa, don
su zama masu bada kariya da tsaro ga dukkan wanda zai kawo
farmaki akan fadarsa, ya sanyawa kowane sansani shugaba
daga cikinsu da kuma sunan da yake kiran sansanin da shi,
sansani na farko sunansa DARUL UQUB sai na biyu DARUL
MUSIBA na qarshe shi ne DARUL MAUTU babu abinda
waxannan baradan suke aikatawa a kowane sansani illa bauta
ga wasu manya gumaka dake kusa da tsaunukan nan guda uku
da suka zagaye fadar,tun daga farkon hudowar rana har
faxuwarta, kuma sukan ci su sha ne daga abinci da abin sha da
yake zubowa daga saman wannan tsaunukan da zarar sun fara
bauta ga gumakan da suke kusa da su, wannan wata hikima ce
ta zubowar abincin daga saman tsaunukan daga mahaifinku da
ya tara waxannan jaruman cikin alqaluman sihirinsa don su
qara qarfafa imaninsu ga gumakan da suke bautawa.
Babu wata halitta mai rai da zata gifta ta wannan waje
baradan basu farmaketa sun halakata ba, koda kuwa tsuntsune
dake shawagi a sararin samaniya, don haka babu wani mutum
da zai wuce ta wajen ba su farmakeshi da nufin halakashi ba,
don haka ya zama dole kuma sai kin bi ta wannan sansanin kun
halaka su sannan ku qarasa wannan fadar.

84

BAKAR GUGUWA
Idan kun samu nasarar halaka waxannan baradan ku ka
isa inda fadar take za ku tadda tana kewaye da manya qofofi
guda uku, ban san yadda za ku iya buxe qofofin ku shiga cikin
fadar ba, saboda ba a rubuta a jikin wannan saqon na sirri zuwa
fadar ba, sai dai na yi sani da cewa qofofin suna tare da tsaro
na xalasumai na aikin sihiri, wanda ba za ku iya tunkarar qofar
kai tsaye ku buxe ku shiga cikinta ba, ku yi qoqarin neman
hanyar da za ku buxe qofar da kanku, idan kun samu nasara
shiga cikin fadar shi kenan babu wani aikin sihiri da zai iya
tasiri a kanku, daga nan kuma ya rage tsakaninku da shi wanda
yake zaune a fadar ku yaqeshi don samun nasara a kansa”.
Da ta gama karanta wannan rubutaccen saqo da suka
kawo mata tare da yi musu bayanin abinda saqon ya qunsa, ta
qara da cewa “Kada abinda na sanar daku na daga wahalhalu
da masibar dake tare da wannan tafiya da zaku yi ta sa ku
karaya ko ku zama masu rauni da fargaba, ku yi imani da cewa
za ku iya samun nasara akan abinda ku ka sa gaba a zuwanku,
za ku ga nasara akan abinda ku ka sa gaba a zukatanku, za ku
ga nasarar tana tare daku ku kai ga cimma qudirinku akan duk
abinda kuka sa gaba”.
Su zuhairu suka yi mata godiya a bisa wannan shawara
da ta basu, da kuma karanta musu rubutaccen saqon da ta yi ta
sanar da su yadda za su iya zuwa Darul sabar fadar da matsafi
Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima, da yake yamma ta yi sai
suka yada zango a wannan wajen suka kwana da gari ya waye
suka yi shiri suka yi bankwana da tsohuwa Diyanuwa suka
kama hanya suka ci gaba da tafiya, suka tunakari dajin da zai
kai su lardin Ashtar inda wannan fada ta matsafi Bahalu take.
**

85

BAKAR GUGUWA
Bayan su zuhairu sun bar inda tsohuwa Diyanuwa take
zaune ita kaxai a cikin daji suka ci gaba da tafiya har suka
shafe tsawon kwanaki takwas, sannan suka iso bakin wani
qaton kogo ma’abocin girma da faxi, ruwan cikinsa na kaxawa
daga gabas zuwa yamma, iska na turashi da qarfi yana
ambaliya da toroqo ya yi tsiri sama, daga gefen kogin suka ga
wani qaton jirgin a tsaye tamkar ana jiran isowarsu su shiga
dan qetare ruwan, suka ja linzamin dawakansu suka tsaya a
bakin wannan kogin Buniyatu ta dubi zuhairu tace da shi.
“Wannan shi ne ruwan da zamu qetare mu shiga lardin
Ashtar da mun wuce wannan kogi tafiyar kwana biyu za mu yi
mu shiga cikin lardin, kuma mun yi sa’a ga jirgin ruwa a bakin
kogin da zamu iya shiga cikinsa mu qetare, anan zamu bar
dawakanmu har zuwa sanda zamu dawo, don dukkanin tafiyar
da zamu yi a cikin lardin Ashtar zamu yi ta ne da qafafunmu”
Da Buniyatu ta yi musu wannan bayani sai zuhairu da
sauran baradan suka sauka daga kan dawakansu suka xaure su
a bakin wani kogi,suka tunkari jirgin ruwan za su hau, sai
zuhairu ya dakatar da su, ya zare takobinsa ya nufi wajen da
jirgin ruwan yake don ya tabbatar da cewa babu wani abin
cutarwa a cikinsa kafin su shiga yana zuwa ya shiga cikinsa tun
daga farko ya fara ganin jini face-face a jikin jirgin ruwa ko ina,
ya riqa tafiya a hankali yana qara shiga ciki, sai ya soma ganin
qasusuwa da gawarwakin bil Adam birjik a cikin jirgin, ya ci
gaba da tafiya yana dube-dube ko zai ga abin da ya halaka
wannan jama’a sai ya soma jiyo wani gunji da huci tamkar na
wata halitta da ke da rai a cikin qarshen jirgin ruwan.
Zuhairu ya gyara riqon takobinsa ya ci gaba da tunkarar
inda yake jin wannan gunji da huci don ya ga abinda yake yin

86

BAKAR GUGUWA
sa, har ya isa qarshen jirgin ruwan da zuwansa sai ya tarar da
wata qatuwar macijiya a nannaxe ta fasa kai tana huci,
girmanta kamar wani qaramin dutse za ta iya haxiye mutum ya
halaka lokaci guda a gabanta ga gawarwakin mutane nan da ta
halaka take haxiya a matsayin abinci, nan take zuhairu ya
fahimci macijiyar nan ce ta halaka jama’ar dake cikin jirgin
ruwan gabaki xaya.
Da ganin zuhairu sai macijiyar nan ta yi wani huci mai
qarfi ta taso ta kawo masa sara, zuhairu ya kauce ta samu jikin
itacen jirgin ruwan ya xaga takobinsa ya kai mata sara ya samu
jikinta amma sai ya ji kamar ya sari dutse takobinsa ta tashi
sama ba tare da ta yanki jikinta ba.
Macijiyar ta sake kawo masa sara zuhairu ya goce, ta
sake kai masa sara za ta haxiye shi, ya kai mata sara ya samu
bakinta, macijiyar ta yi gunji da girgiza saboda azabar saran da
ya yi mata, jirgin ruwan ya yi tangal-tangal kamar zai kife,
sauran baradan da ke bakin kogin suka ja baya saboda jin
wannan gunji shi kuwa zuhairu ya sake jan daga don tunkarar
ta, da ya lura sosai sai ya ga ya ji mata rauni a inda ya sareta a
baki, don haka ya qara azama da kai sara a wannan wajen don
ya halakata.
Macijiya ta sake taso masa a fusace tana kai masa sara
da wafta za ta haxiyeshi shi kuma zuhairu ya riqa gocewa da
kai mata sara cikin tsananin jarumta da qarfin zuciya, duk inda
macijiya ta sara a jirgin ruwan sai ka ga itacen wajen ya fashe
ko ya ragargaje.
Da ragowar jaruman da suke tare da zuhairu suka hangi
abinda yake faruwa sai nan da nan suka zare makamansu,
gwanayen harbi kibiya suka riqa sakarwa macijiya ruwan

87

BAKAR GUGUWA
kibbau daga inda sue, masu jifa da majaujawa suka riqa jifanta
da wasu dunqulallun qarafa masu tsini dake huda jikinta,
sauran jaruman masu faxa da takubba ko mashi suka tafi ga
jirgin ruwan don kai xauki gareshi, da zuwansu suka far mata
da sara da suka babu qaqqautawa, macijiya nan ta kawo wafta
cikinsu ta suri xaya ta haxiye shi daga shi har takobi da sulken
yaqin dake jikinsa,ta sake kawo sara ta samu mutum uku lokaci
guda, iska ta kwashesu ta yi sama da su saboda qarfin saran
suka zube a gefe matattu ba su ko shura ba, jikinsu ya riqa
zagwanyewa yana narkewa kamar jini, saboda masifar dafin da
ke jikin macijiyar.
Da ragowar jaruman suka ga haka sai suka ja da baya a
razane, shi kuwa zuhairu ya sake tasar mata a fusace ya kai
mata wani gawurtaccen sara irin na zaratan sadaukai da
dukkanin qarfinsa, ya yi sa’ar ya sameta a lokacin da take
qoqarin kai masa sara, macijiyar ta yi wani irin gunji mai
tsananin qarfi saboda azabar saran da ya kai mata, jini ya yi
tsartuwa sama daga inda ya sari jikinta, macijiyar ta yi tsalle ta
faxi cikin ruwan kogin, masu jifa da majaujawa da harbi da
kibiya suka ci gaba da harbin ta har ta nutse a cikin ruwan
kogin, jini ya taso sama ya gauraye ruwan kogin daga inda ta
nutse.
Zuhairu ya tsaya yana sauraron ko zai ga macijiyar ta
sake tasowa saman ruwa daga inda ta nutse amma har aka
shafe lokaci mai tsawo ba su sake ganinta ba don haka ya yi
zaton ta halaka sun gama da ita, daga nan suka kwashe
gawarwakin ‘yan uwansu da sauran jama’ar da macijiyar ta
halaka a cikin jirgin ruwan suka fita da su suka binnesu, sannan
suka share jirgin ruwan suka gyara duk abinda ya lalace a

88

BAKAR GUGUWA
cikinsa, suka zuba kayansu suka hau suka xauki fila-filai da
ake amfani da su wajen tuqa jirgin ruwan suka soma tuqawa
suka kama hanyar da za su qetare kogin.
Bayan sun yi tafiya mai nisa a cikin kogin har rana ta
kusa faxuwa ba su kai qarshensa ba, can daga bayansu sai suka
riqa jin wani qugi da gunji yana tunkaro inda suke, iska mai
qarfi ta soma tasowa daga gabas tana kaxa ruwan, kogin ya
soma tanbatsa yana ambaliya da tsiri sama, igiyar ruwa ta soma
kaxawa tana girgiza jirgin da suke ciki sannan sai suka ji wata
irin tsawa mai tsananin qarfi da ban firgici ta sake gauraye
wajen, ruwan ya sake hautsinewa yana kaxawa da qarfi tare da
yin tsiri sama kamar zai sha kan jirgin ruwan ya nutsar da su su
halaka, jirgin ruwan ya soma tangaxi da tangal-tangal kamar
zai dulmiyar da su su halaka.
Can daga bayansu sai suka hango wannan baqar
guguwar ta keto ta saman ruwan kogin tare da iska mai
tsananin qarfi sun tunkaro inda suke, gaba xaya wajen ya yi
baqiqqirin sararin samaniya ya yi duhu mafi tsananin gani
daga yankin duhun dare, suka sake jin wata tsawa mai tsananin
amo da rugugi mai matuqar hauhawa da ban firgici, jirgin
ruwan ya sake yin girgiza da tangal-tangal tamkar zai kife da
su daga cikin baqar guguwar nan ta qaraso inda suke sai ga
matsafi Bahalu ya bayyana akan iska hannunsa riqe da gorarsa
na aikin sihiri tare da sandarsa ta tsafi ya dubi su zuhairu ya
bushe da dariya irin wadda ya saba yi a duk sanda zai aikata
wani abu na mugunta da zallunci ya ci gaba da qyalqyala
dariya har zuwa wani tsawon lokaci sannan yace da su.
“Halaka ta tabbata a gareku cikin wannan rana babu
shakka ba za ku kuvuta daga wannan musiba da ku ke ciki ba

89

BAKAR GUGUWA
har sai kun halaka, kamar yadda na sanar da ku cewa ajali zai
gabata gareku cikin wannan tafiya, saboda babu wani mahaluki
a faxin duniya da ya isa ratsa lardin Ashtar bare ya je inda
fadata take, saboda ma’abota tsaro da bada kariya dake tare da
ita”, ya dubi ‘yar uwarsa Buniyatu yace da ita.
“Ke kuwa Buniyatu zan sake bada dama a gareki kafin
ku riski inda za ku halaka, ki zama mai neman afuwa a gareni
tare da yin rantsuwa da alqaluman sihiri masu girma akan cewa
za ki rabu da begen wannan jarumin da ku ke tare da shi, tare
da barin addininsu da ki ka yi imani da shi a yanzu, ni kuma na
yi miki alqawarin zan kuvutar da ke daga wannan halaka da ku
ke ciki na maida miki alqaluman tsafi da sihirinki da na rabaki
da su, na tafi da ke fadata mu zauna tare cikin salama da tasirin
aikata abinda ki ke son na daga alqaluman sihiri”.
Buniyatu ta maida masa raddi da cewa “Bana buqatar
taimako daga gareka ka kuvutar dani, ga Allah nake neman
taimako kuma ba zan tava juya baya ga abinda na tabbata a
kansa yanzu ba, na fita daga addinin musulunci ba, kuma na
neman ka dawo da alqaluman sihirin da ka qwace daga gareni
don a yanzu ina neman tsari da su, kuma ba ka isa ka tabbatar
da hallaka akan mu ba, komai qarfin tasirin tsafi da sihirinka
har ranar da ubangiji ya so tabbatar da hakan a kanmu”.
Matsafi Bahalu ya fusata da jin kalamanta masu tsauri a
gareshi ya dubeta yace da ita.
“Ke dai kina cikin ximuwa da tavewa wadda ba za ta
dawo dake kan turbar gaskiya ba, kuma
End Ads