ya bugi
fuskarta nan take idanunta suka daina ganin komai barci mai
nauyi ya xauketa, ta fita hayyacinta daga nan ba ta sake sanin
abinda yake faruwa a gareta ba.
Matsafi Bahalu ya ci gaba da tafiya da ita cikin
alqaluman sihirin rage nisan tafiya, sai da ya shafe tsawon
kwanaki goma yana tafiya tare da yada zango ya huta sannan
57
BAKAR GUGUWA
ya isa lardin Ashtar inda wannan fada ta Darul sabar take, ya
wuce cikin fadar dake tsakanin wasu manya tsaunuka guda
biyu a tsakiyar dajin.
Fadace da aka ginata da qananan duwatsu abin yiwa ado
da jauhari an zagayeta da manyan katangu masu matuqar girma
da tsayi tare da kariya ta alqaluman sihiri da babu wani
mahaluki da ya isa shiga cikinta matuqar ba da izinin wanda ya
mallaketa ba, akwai itatuwa da furani masu matuqar kyau da
suka qayata wajen tamkar lambu, ga rafuka da qoramu masu
gudanawa a tsakiyar wajen kana zuwa inda fadar take za ka
tabbatar da cewa ka zo wata qasaitacciyar fada, irin ta manyan
sarakuna da suka shahara a fagen tarin dukiya da qarfin iko.
A ciin fadar akwai hadimai mata kyawawa wanda
dukkaninsu an xaukosu ne daga hannun iyayensu aka kawo su
wannan fada aka ajiyesu don yin hidima ga wanda ya
mallaketa, kuma da ywansu ‘ya ‘yan sarakuna ne da manyan
attajirai, sai dai daga cikinsu babu wadda matsafi Bahalu yake
ganin ta dace ya zauna da ita a matsayin matarsa sai Gimbiya
Hasima, don haka dukkanin matan da ya tara a fadar suka zama
kuyangi don yin hidima a gareta.
Matsafi Bahalu yana shiga cikin fadar ya wuce da
Gimbiya Hasima wani xaki mafi kyawun ado daga cikin
xakunan dake fadar, an qawatashi da kayan alatu na zinare da
azurfa masu kyan gaske, ya sauketa akan wani faffaxan gado
irin na alfarma da aka yi shi da zinare. Sannan ya nuna ta da
sandar sihirin da take hannunsa, haske ya fito daga cikin sandar
ya shiga jikinta, nan take ta farka daga nannauyan barcin da
take yi cikin aikin sihiri har na tsawon kwanaki goma.
58
BAKAR GUGUWA
Da farkawarta ta ganta kwance akan wannan gado cikin
xakin da ba ta tava shigarsa ba, sannan ta ga matsafi Bahalu
tsaye a kusa da ita yana dubanta, nan take ta tashi cikin tsoro
da razani ta dubi matsafi Bahalu tace da shi.
“Wacce qaddara ce ta sa na ganni cikin wannan hali da
nake ganin kaina a yanzu…?” Matsafi Bahalu yace da ita
“qarfin iko da isata ne cikin alqaluman sihiri ya sa na xaukoki
na kawki wannan fada tawa, kamar yadda na sha sanar da ke
cewa hakan za ta kasance a gareki wata rana daga ranakun
rayuwarki”.
Gimbiya Hasima ta fashe da kuka sannan tace da shi
“Kaicon rayuwata da ganin wannan halin baqin ciki da ka
sanyani a ciki, me ya sa za ka rabani da ‘yan uwana ka kawoni
wannan wajen me ya sa kake son cutar da rayuwata don biyan
buqatar zuciyarka? Me ya sa zaka nisantani da duniyar
musulunci ka kawoni gareka cikin halin da kake ciki shirka da
bautar gumaka da tsafi, ka sani cewa la’anar Allah ta tabbata a
gareka bisa ga abinda kake aikatawa na shirka da sihiri”
Bahalu ya bushe da dariya irin ta manyan azzalumai sannan
yace da ita “Ai ban xauko ki na kawki wannan gurin ba sai dan
ina begenki da muradin kasancewa tare da ke a matsayin
matata kuma uwar ‘ya ‘yana da nake fatan su gajeni a fagen
tsafi da sihiri, za ki kasance a qarqashin ikona kuma mai yin
biyayya a gareni har qarshen rayuwarki” Gimbiya Hasima ta ce
da shi “Allah ya yi mini tsari da dukkanin sharri da mugun
nufinka a kaina, ya kuma kuvutar da ni deaga wannan hali don
shi mai qarfin iko da isa ne cikin buwayarsa akan kowane
tasirin tsafi da sihiri da kake taqama da shi, kuma qiyayyata na
59
BAKAR GUGUWA
tare da kai har qarshen rayuwarta ba zan tava qaunarka ba,
bare na yi biyayya a gareka”.
Bahalu ya sake bushewa da dariya sannan yace da ita
“Ai lamarina ya yi nisa a gareki daga fita daga wannan fada,
kuma bakin alqalami ya riga ya bushe tunda har na riga na
kawoki cikinta, ki sani cewa babu wani mahaluki da ya isa
shigowa wannan lardi komai jarumta da sadaukantakarsa bare
ya kuvutar da ke daga hannuna” Ya tafi jikin wata qaramar
qofa dake saman xakin ya buxeta sararin samaniya ya bayyana,
a lokacin da dare ne kuma babu hasken farin wata sai tsananin
duhu sanna akwai wasu taurari masu matuqar haske guda biyu
daga daidai qofar da ya buxe, ya dubi Gimbiya Hasima ya ci
gaba da cewa.
“Ki yi duba ya zuwa waxannan taurarin guda biyu dake
sararin samaniya, sune taurarin da na daxe ina jiran bayyanarsu,
don samun nasarar xaukoki daga birninku na kawoki wannan
fada, kuma da suka bayyana na samu nasara aikata hakan,
saboda haka ki ci gaba da duba ya zuwa wannan taurari tsawon
kowane dare, a duk sanda kika ga wanna taurarin sun taho sun
haxe da juna to wannan rana ce da take bayyana kasancewarki
matata da tabbatar aure a tsakaninmu,kamar yadda bayyanar
taurarin ta tabbatar da samun nasarar xaukoki daga birni ku.
Ya sake bushewa da dariya irin ta mugunta da zallunci
kamar yadda ya saba sannan ya juya ya fice daga xakin ya
barta. Gimbiya Hasima ta sake fashewa da kuka saboda baqin
ciki da takaicin halin da matsafi Bahalu ya sanya rayuwarta a
ciki, ta daxe tana wannan kuka don tausayawa kanta har kusan
asubahi, sannan ta haqura ta ga zoben nan na zuhairu yana tare
da ita ba ta jefar da shi ba, ta xaukeshi ta saka a xan yatsanta ta
60
BAKAR GUGUWA
sumbaci zoben sannan ta xaga hannunta sama ta yi addu’a don
neman Allah ya kuvutar da ita daga hannun wannan shu’umin
matsafin da ya xaukota daga birninsu ya rabota da ‘yan uwanta
ya kawota wanann wajen.
**
Shi kuwa zuhairu cikin kwanaki biyar ya gama shirinsa
na tafiya lardin Ashtar don ‘yanto Gimbiya Hasima daga
hannun matsafi Bahalu tare da neman makarin aikin sihirin da
Bahalu ya yi masa ya maida siffarsa irin ta tsoho mai tarin
shekaru. A ranar da zuhairu zai tafi ya fito cikin shiri na sulken
yaqi ya yiwa dokinsa xamara da shiri na sosai, haka itama
Buniyatu an bata doki tare da sauran kayan yaqi daga fadar
sarki shaiban, ta gama nata shirin cikin sulken yaqi ta fito idan
ka ganta za ka yi zaton wani hamshaqin jarumi ne sadauki da
ya shahara a fagen fama ba mace ba ce, kafin su tafi suka yi
bankwana da dattijo marwan kakan zuhairu ya yi musu addu’a
ta fatan samun nasara sannan suka yi sallama suka kama
hanyar birnin Bahazum.
Da isar su Birni suka wuce fadar sarki shaiban, suka
tarar da an shirya wasu manya jarumai cikin shirin yaqi, su
kimanin mutum arba’in da za su yi musu rakiya cikin tafiyar da
za su yi, zuhairu ya sauka daga kan dokinsa ya tafi gaban sarki
ya kai gaisuwa sarki ya amsa masa sannan ya ce da shi “Allah
ya baka nasara na gama shiri dan yin tafiya bisa ga alqawarin
da na xauka, na neman Gimbiya Hasima duk inda take a faxin
duniya”.
Sarki shiaban ya ce da shi “Na shirya wasu jarumai da
za su yi maka rakiya adadin mutum arba’in daga cikinsu akwai
mutum goma qwararu a fagen iya harbi da kibiya sannan akwai
61
BAKAR GUGUWA
wasu mutum goma da suka qware wajen faxa da mashi, sai
kuma mutum goma masu iya jifa da majaujawa, sai mutum
goma na qarshe sune qwararu a fagen iya faxa da takobi
waxannan sune adadin mutum arba’in Allah ya baku nasara
cikin tafiyar da za ku yi”.
Zuhairu ya yi godiya sanann sarki shaiban ya sa aka yi
musu addu’a ta fatan samun nasara ya kuma umarci baradan da
za su yiwa zuhairu rakiya su kasance ma su yi masa biyayya a
matsayin shugabansu har su je su dawo, daga nan suka yi
sallama da sarki aka yi musu rakiya zuwa bayan gari suka
kama hanya suka ci gaba da tafiya. Buniyatu tana gaba don yi
musu jagora zuwa bigiren da suke zaune tare da yayanta
matsafi Bahalu, don xauko rubutaccen saqon wanda zai shiryar
da su hanyar da za ta kaisu lardin Ashtar inda fadar da matsafi
Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima take.
Kwanci tashi suna tafiya cikin wannan daji tun daga
ranar da suka baro gida, har suka shafe kwanaki ashirin daga
cikin kwanaki arba’in da za su yi kafin su isa bigiren da
Buniyatu suke zaune a cikinsa, sukan yi tafiya daga bayan
ketowar alfijir har zuwa faxuwar rana sallah da cin abinci ne
kawai yake tsayar da su sai dare ya yi su yada zango don su
kwana kafin gari ya waye su ci gaba da tafiya. A rana ta ashirin
da xaya daga cikin ranakun tafiyarsu da la’asar sakaliya suna
tsakiyar tafiya sai suka hangi wasu rundunar mahaya cikin
shirin yaqi suna xauke da tutoci irin na mabiya addinin bautar
rana, su zuhairu suka yi nufin su ratse musu su ci gaba da
tafiya, don kada baradan su tsayar da su su vata musu lokaci
cikin tafiyar da suke yi, amma sai waxannan ayarin baradan
suka hangesu suka kan su suka tsayar da su, xaya daga cikin
62
BAKAR GUGUWA
baradan wanda kuma shi ne babbansu ya dubi zuhairu yace da
su.
“Kai waxannan matafiya daga ina kuke kuma ku
jama’ar wane birnine da inda kuka nufa? Sannan nina labarin
dukiya da guzuri da kuke tare da shi. Ku yi gaggawar miqoshi
garemu don a yanzu kun zama ribatattu a garemu ababen tafiya
da ku ya zuwa birninmu don kaiwa sarkinmu ku zama bayi,
kamar yadda mukan yi ga duk jama’ar da muka haxu da su
wannan daji cikin tafiyar da muke yi” Zuhairu yace da shi.
“Ba ma tare da wata dukiya ko guzuri da zamu baku
bisa ga buqatarku, cewa dai mu mun kasance matafiya ne cikin
wata buqata da take tare da mu,kuma bamu fito dan yin faxa da
kowa ba sai don tunkarar abinda muka sa a gaba saboda haka
muna neman afuwa a gareku, ku bamu hanya mu wuce ya
zuwa inda muka nufa” Wanda ya fara magana ya dubi zuhairu
yace da shi “Kai dattijo ma’abocin rauni da gazawa ka sani
cewa ba za ku kuvuta daga hannunmu ba har sai kun zama
ribatattu a garemu, don na ga alama kun kasance daga cikin
mabiya addinin musulunci ba masu bauta ga rana ba, za mu tafi
da ku ya zuwa birninmu don mu bautar da ku kamar yadda
muke bautar da duk wanda bai zamo daga jinsinmu ba kuma
baya bauta ga rana abar bautawa ta gaskiya, to kuwa sunansa
bawa a garemu kuma ya halatta mu bautar da shi ko mu
halakashi mu shayar da jininsa ga rana abar bautawarmu bisa
ga tsarin addininmu”
Zuhairu ya fusata da jin maganar wannan mutum ya ce
da shi, “Kaicon rayuwarka da abinda kake ambatawa cikin
zantukanka masu munin ambato, Allah wadai da miyagun
kalamanka na zalunci da ke bayyana tsantsar shirka da vata
63
BAKAR GUGUWA
mabayyani na bauta ga rana abar halitta, kuna shayar da jini
gareta ka sani cewar halaka ta tabbata gareka da rundunar
baradan da kake jagoranta sababin abinda kake aikatawa na
zalunci a doron qasa, don shafe ruhinka daga bayan qasa shi ne
mafi alkairi ga sauran jama’ar musulmi”.
Barden nan ya bushe da dariya saboda jin abinda
zuhairu yace sannan ya dubeshi yace da shi “Kai dattijo
ma’abocin rauni da gazawa saurara ga ambaton waxannan
kalamai naka da kake ambatawa, ka bari matasa masu ragowar
jini a jiki da jarumta su yi magana, ba kai dattijo ma’abocin
rauni dan haka ko ku miqa wuya garemu ko mu tursasaku ga
aikata abinda muka umarceku ta hanyar qarfi da tsananin
yawanmu”.
Zuhairu ya zare takobinsa ya fita gaban rundunar
baradan yace da su “Ba zamu zama masu tsoro ko karaya da
ganin yawan rundunarku da ku ke alfahari da ita ba, don Allah
da muka yi imani da shi muke bauta masa zai iya bamu nasara
akan ku koda kun fi yawan adadin qasa, don haka idan da mai
qarar kwana ya fara fitowa gareni ya ga yadda zan aika da
ruhinsa barzahu, idan kuma kun qi fitowa ni na gabata cikinku
na hau ku da sara da kisa irin na qare dangi, har sai na tarwatsa
rundunarku na sanyaku nadamar halittarku a bayan qasa da
abinda kuke aikatawa”.
Jarumi nan ya sake bushewa da dariya lokaci guda
kuma sai ya turvune fuska, irin na mugunta da zalunci ya dubi
zuhairu yace da shi “Ban zamo daga cikin mutane masu imani
da zan ji tausayin tsufanka ba na qyaleka ba, tunda har kana jin
ka isa jarumi bari ni na halakaka da kaina, don ya zama izina
ga sauran jama’ar da ke tare da kai” Ya zare takobinsa ya taho
64
BAKAR GUGUWA
ga zuhairu sai kuma ya sake shawara ya maida takobinsa yana
mai faxin cewa “Ai halaka ka da takobi ma nuna rashin
jarumta ne, da gazawa don kuwa iskar gudun dokina kaxai ta
isa waftoka daga kan dokinka ka faxo qasa ka halaka”.
Kafin ya gama magana zuhairu ya fusata ya xaga
takobinsa ya kai masa sara, jarumin ya yi sauri ya sanya wata
garkuwa ta baqin qarfe ya kare saran, kaifin takobin zuhairu ya
keta garkuwa gida biyu ta tarwatse, jarumin ya yi baya tagataga kamar za su faxi daga shi da dokinsa da qyar dokin ya
tirje ya tsaya saboda qarfin saran da zuhairu ya kai masa irin na
sadaukantaka, jarumin nan ya dubi zuhairu cikin tsananin
mamaki kafin ya qare mamakinsa zuhairu ya sake kai masa
wani saran cikin qarfin zuciya da zafin nama jarumin ya yi
sauri ya zare takobinsa ya kare saran, a wannan karon ma sai
da ya sake yin baya kamar zai faxo daga kan dokinsa saboda
qarfin saran.
Zuhairu bai saurara masa ba ya ci gaba da kai masa sara
a fusace, barden nan ya yi qoqarin ya kare amma tuni ya
makara kaifin takobin zuhairu ya sari tirken dokin wuyansa,
kansa ya fita daga gangar jikinsa, ya yi tsalle sama ya tafi ya
faxi a gaban sauran baradan da ke tare da wannan jarumin.
Da ganin haka sai ragowar baradan dake tare da wannan
jarumin suka harzuqa suka taso kan zuhairu cikin qaraji da
gunjin fusatuwa, suka far masa da sara da suka kamar za su
halakashi, zuhairu ya shiga karewa da maida martani yana
saransu da halakasu, suma ragowar jarumai da suke tare da shi
tare da Buniyatu suka zare makamansu suka farwa baradan nan
da sara, nan take waje ya yamutse qura ta turnuqe ta tokare
65
BAKAR GUGUWA
sararin samaniya, qarar haxuwar takubba ta cika wajen
kururuwar mazaje da haniniyar dawakai ta yawaita.
Kafin wani lokaci su zuhairu sun ragargaza rundunar
baradan nan da suka taso kansu suka tarwatsa su,maxaukaka
daga cikinsu suka zama maqasqanta, manyan jarumai da ke ji
da kansu suka zama raunana, da yawansu suka halaka sai ‘yan
qalilan daga cikinsu ne suka arce don su tsira daga halaka, a
sanda ake tsakiyar gabza yaqi. Bayan zuhairu sun tarwatsa
rundunar baradan nan suka yi godiuya ga Allah a bisa nasarar
da suka samu cikin iko da kiyayyewarsa kuma babu wanda ya
halaka daga cikinsu, daga nan suka kaxa linzamin dawakansu
suka ci gaba da tafiya ya zuwa inda suka nufa.
**
Al’amarin matsafi Bahalu kuwa bayan da ya fice daga
xakin da ya ajiye Gimbiya Hasima ya tafi izuwa nasa xakin
cikin murna da farin cikin samun nasarar xauko Gimbiya
Hasima tare da mallakar wannan fada ta mahaifinsa da ya gada,
hankalinsa ya kwanta don a yanzu babu abinda ya ke jira illa
bayyanar haxewar wannan taurari na alqaluman sihiri da za su
tabbatar da kasancewar Gimbiya Hasima matarsa ya samu
damar kusantar ta, ya yi sani da cewa mahaifin Gimbiya
Hasima zai tura wanda za su shiga duniya nemanta, saboda irin
qaunar da yake yiwa ‘yar tasa, amma ya san babu wanda zai
iya shigowa lardin Ashtar bare ya samu nasara shiga fadarsa,
ko ya karvi Gimbiya Hasima daga hannunsa, saboda ma’abota
tsaro da kariya dake tare da fadar.
A kowace rana yakan ziyarci xakin Gimbiya Hasima
don ya ganta ya ji sanyi a ransa saboda qaunar da yake yi mata,
sai dai ba shi da ikon kusantarta ko ya tavata, saboda
66
BAKAR GUGUWA
alqaluman sihiri da ya yi imani da su basu bashi damar aikata
haka ba, har sai ranar da wannan taurarin na aikin sihiri suka
haxe da juna suka zama xaya, saboda haka a kowane dare ya
kan zauna a daidai qofar da taurarin suke ya zira ido yana
dubansu da sauraron ya ga sun haxe da juna har zuwa wayewar
gari, sai rana ta fito ya tashi ya koma xakinsa, haka yake yi a
cikin kowanne dare tun daga ranar da ya kawo Gimbiya
Hasima wannan fadar.
Bayan wasu kwanaki matsafi Bahalu ya yi tunanin ya yi
bincike don ganin halin da ‘yar uwarsa Buniyatu take ciki, ya
tashi ya tafi ga tarkacen kayan bokancinsa na aikin sihiri, ya
zauna a gaban wani kasko na lu’u-lu’u a cikinsa akwai farin
rairayi, ya sa hannu ya yi zane akan farin rairaiyin sannan ya
rufe idanunsa yana karanta wasu xalasimai na aikin sihiri,
bayan wani lokaci bayanai suka bayyana gareshi a saman farin
rairayin sai ga siffar qanwarsa Buniyatu tare da zuhairu da
sauran baradan dake tare da su sun bayyana tafe akan
dawakansu kan hanyarsu ta zuwa bijiren da suka zauna tare da
mahaifinsu kafin ya rasu.
Matsafi Bahalu ya yi mamaki da ganin wannan al’amari
ya sake share rairayi ya yi wani zanen a kansa, bayanai suka
sake bayyana a gareshi cikin alqaluman sihirinsa ya ga cewa za
su je wannan kogon dutsen ne don xauko wani rubutaccen
saqo na sirri da za su samu damar sanin inda wanan fada
take,hankalinsa ya yi matuqar tashi nan take ya tashi cikin
sauri ya shiga shiri, dan tafiya wannan kogon dutsen ya rigasu
zuwa ya xauke wannan rubutaccen saqo da za su je xaukowa a
cikinsa.
67
BAKAR GUGUWA
Bayan ya gama shirin ya fice daga fadar ya kama hanya,
ya yi tafiya har ta tsawon kwanaki shida cikin alqaluman
sihirin rage nisan tafiya, sannan ya isa inda wannan kogon
dutsen yake da zuwansa ya shiga cikin kogon dutsen ya soma
duba da binciken inda wannan rubutaccen saqon yake, amma
ya rasa inda aka ajiyeshi babu abinda matsafi Bahalu bai duba
ba ko ya bincika cikinsa a cikin kogon dutsen amma ya rasa, ya
yi bincike cikin alqaluman sihirinsa bayanai suka tabbatar
masa da cewa babu shakka rubutaccen saqon yana cikin
wannan kogon dutsen amma ya yi duk binciken da zai yi ya
kasa gano inda rubutaccen saqon yake.
Da matsafi Bahalu ya gaji da nema sai ya haqura ya fita
daga dutsen sannan ya yi aikin sihiri akan kogon dutsen yadda
Buniyatu ba za ta iya samun damar shiga cikinsa ba, bayan ya
kammala ya yi dariyarsa daya saba yi irin ta mugunta da
zallunci sannan ya vace ya bar wajen.
**
Su zuhairu suka ci gaba da tafiya har suka shafe sauran
kwana goma sha tara da suka rage musu, kafin su iso inda
wannan kogon dutsen yake a ranar da suka iso wajen da sanyin
safiya suka tunkari inda kogon dutsen yake.
Da isarsu wajen kafin su kai ga shiga cikin kogon
dutsen sai suka ji wata irin tsawa mai tsananin qarfi da ban
firgici ta gauraye wajen tamkar faxuwar aradu, qasa ta soma
girgiza tana raurawa tamkar za ta tsage, zuhairu da sauran
jarumai da suke tare da shi su afka ciki su nutse, can daga nesa
sai suka hangi iska mai tsananin qarfi tare da tsawa da rugugi
mai matuqar ban firgici kamar sau uku gaba xaya dajin ya yi
68
BAKAR GUGUWA
baqiqirin sararin samaniya ya yi duhu mafi tsanani daga yankin
duhun dare.
Barada da suke tare