x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - BAKAR GUGUWA

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 36828 words

Category: Adventure Stories

Views 111

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
daxi, ta san cewa tunda yayanta ya yi nufin
halakashi to kuwa babu shakka rayuwarsa tana cikin hatsari, ta
ji ta kamu da kewar son ganinsa nan take ta tashi ta kama
hanyar tafiya birnin samaras dan ta ga zuhairu duk da tayi
alqawarin cewa ba za ta sake zuwa gare shi ba har sai ranar da
za ta tabbatar da cikar burinta na aurensa ko da bai amince ba.
Ta yi tafiya mai nisa a cikin alqaluman sihirin rage
nisan tafiya har ta iso birnin samaras da tsakiyar dare gari ya yi
shiru babu motsin kowa ta nufi gidansu zuhairu kai tsaye ta
shiga ta wuce har xakinsa ta sameshi a kwance yana barci akan
gadonsa ta tsaya a gabansa tana dubansa cikin bege da qauna
har tsawo wani lokaci shauqin sonsa ya qara ratsa mata
zuciyarta anan ta sake xaukar alqawarin cewa ba za ta bari
yayanta ya halaka masoyinta zuhairu ba matuqar tana raye,idan
kuwa ya samu nasara halakashi ba da saninta ba, ko kuma ya yi
masa aikin sihiri na cutarwa to kuwa ta yi alqawarin sai ta
halaka Gimbiya Hasima ‘yar sarki shaiban dan ta rama. Bayan

35

BAKAR GUGUWA
ta gama wannan tunanin na ta ne ta kai hannun za ta shafi jikin
zuhairu saboda shauqin qaunar sa dake qara ratsa zuciyarta.
Kafin hannunta ya kai jikinsa sai zoben da ke xan
yatsan zuhaiu ya yi motsi da qarfi zuhairu ya farka daga baccin
da yake yi saboda motsin zoben ya yi alamar wani matsafine
ko ma’abocin aikin sihiri ya kusanceshi ya duba ko ina a cikin
xakin bai ji motsin komai ba,bare ya ga wani abu ya yi shiru
yana saurare jikinsa ya bashi cewa akwai wanda ya shigo cikin
xakin duk da baya ganin komai, dan ya sa cewa babu yadda za
a yi zobensa ya yi motsi ba tare da wani ma’abocin aikin sihiri
ya kusanceshi ba. Ya tashi zaune ya yi addu’a sannan ya tafi ya
xauko takobinsa dake rataye a jikin bango da Buniyatu ta ga
haka sai ta ja da baya sannan ta juya ta fice daga xakin cikin
aikin sihiri yadda ba zai ji takun sawunta ba bare ya ganta.
Bayan fitar Buniyatu sai zuhairu ya ji kamar motsi a
waje ya buxe qofar xakinsa cikin sauri ya fito ya duba baiga
kowa ba ya sake jin kamar takun sahu an nufi wajen da yake
xaure dokinsa sannan ya ji dokin nasa ya yi haniniya alamar ya
ga wani abu da shi zuhairu baya gani, ya zare takobinsa a
hankali ya nufi wajen cikin nutsuwa yana mai lura da taka
tsantsan dan gudun kada wani abu na cutarwa ya afko masa
cikin duhun dare ya cutar da shi. Kafin ya isa wajen sai ya ji
anyi masa magana da murya qasa-qasa aka ce da shi.
“Kada ka wahalar da kanka zuhairu ka koma ka ci gaba
da baccinka cikin aminci da salama mai qaunarka ce ta kawo
maka ziyara cikin wannan dare, kuma ban zo da nufin cutarwa
gareka ba” Zuhairu ya shaida murya Buniyatu ce duk da baya
ganinta ya amsa mata da cewa.

36

BAKAR GUGUWA
“Ba zan gaza ga sanar da ke abinda na sanar dake a
baya ba cewa ki nisanta dani ko kuma na salwantar da ruhinki
da kisa mafi muni ta hanyar kaifin takobina,qiyayyarki gareni
tana daxa hauhawa tsawon rayuwarta kuma ba za ki tava zama
mai daraja a gareni ba har sai ranar da kika rabu da hanyar vata
ta aikin tsafi da sihiri, ki ka dawo hanyar gaskiya ta bin tafarkin
addinin muslunci” Buniyatu ta bayyana gareshi wani farin
haske ya zagey kewayen inda take tsaye yadda zai iya ganin
fuskarta duk da tsananin duhun dare ta dubeshi tana mai
tausasa murya tace da shi “Ni kuma ka ga qauna da begenka ne
ya ke daxa hauhawa cikin zuciyarta a koda yaushe ba zan daina
qaunarka ba har zuwa ranar da zan cimma qudirina cewa ni na
kasance mai sauraron bayyanar wasu bayanai cikin alqaluman
sihirina da za su bani damar mallakarka ka zama miji a gareni
ta kowane irin hali,dan haka ba zan daina qaunarka ba kamar
yadda ba zan rabu da abinda na gada a wajen mahaifina ba na
sirrin tsafi da sihiri.
Zuhairu ya ce da ita “Ke dai kina cikin ruxani da vata
mabayyani, kasancewarki mai yin imani da bayyanar wasu
bayanai na alqaluman sihiri akan cikar qudirinki, kuma cikin
yarda Allah ba za ki tava cimma qudirin naki ba, cewa ni na
kasance mai dogaro dashi akan ya kiyayeni daga duk wani
sharri ma’abota tsafi da sihiri irin ki” Buniyatu tace da shi.
“Kaine rayuwar ka take cikin tasku da razani na
kusantar halaka, sababin alqawarin da xan uwana ya xauka na
halakaka, akan soyayyar Gimbiya Hasima dake wanzuwa a
tsakaninku kalamansa sun munana akan ambato salwantar da
rayuwarka cikin aikin sihirin da yake shiryawa da rayuwarka
cikin aikin sihirin da yake shiryawa a yanzu dan zuwa gare ka,

37

BAKAR GUGUWA
wannan ne dalilin da ya sa zuciyata ta kasa samun nutsuwa
akan maganarsa kuma na shiga halin damwa da begen son
ganinka don haka na taso na taho gareka cikin wannan dare na
yi alqawarin bada kariya gareka akan duk wani aikin tsafi da
sihirinsa, kuma idan har wani abin cutarwa na daga cikin
sihirinsa ya sameka to kuwa na yi alqawarin sai na halaka
Gimbiya Hasima ‘yar sarki shaiban bin Yasar da yake son
cutar da rayuwarka saboda ita” Zuhairu ya fusata da jin
maganarta ya maida mata da raddi da cewa.
“Har ke kina da tasirin bada kariya ga wanda ya dogara
ga Allah cikin lamarinsa, ke kanki ba ki da ikon kare kanki
daga duk abinda Allah ya hukunta zai faru gareki,kuma ina mai
gargaxinki da gargaxi mai tsauri kan cewa duk abinda ya faru
ga Gimbiya Hasima na rantse da wanda raina yake hannunsa
sai na halakaki daga ke har xan uwan naki na share rayuwarku
daga doron qasa” Yana gama faxar maganar Buniyatu bata ko
tanka masa ba, ta vace cikin alqaluman sihirinta ta fice daga
gidan ta yi tafiyarta ta barshi, zuhairu ya tafi ya koma xakin sa
ya yi addu’a ya kwanta yana tunanin maganar da Buniyatu ta
faxa akan Gimbiya Hasima har bacci ya xauke shi.
**
Tun daga wannan rana da Buniyatu ta je wajen zuhairu
ta sameshi a gida da tsakiyar dare, zuhairu bai sake ganinta ta
bayyana gareshi ba, kuma wani abu bai faru gareshi ba, game
da yayanta akan alqawarin daya xauka. Sannan zuhairu bai
sanar da Gimbiya Hasima abinda ya faru tsakaninsu da
Buniyatu ba, akan alqawarin data xauka na idan wani abu na
cutarwa ya same shi daga yayanta itama za ta maida martani
akanta.

38

BAKAR GUGUWA
Al’amarin Gimbiya Hasima kuwa ta samu nutsuwa da
kwanciyar hankali akan lamarin matsafi Bahalu tun tana
fargaba da tsoron kada ya halaka zuhairu kamar yadda yake
halaka duk wanda yace yana qaunarta,har ta daina fargabar
komai saboda ganin matsafi Bahalu bai sake bayyana gareta ba
tun daga ranar da suka yi artabu da zuhairu ya fasa kurtun
sihirin da yake hannunsa, kuma ta daina yin munanan mafarkemafarken da take yi a kansa, tare da ganin ababen ban tsoro da
firgitarwa dake sata razani a duk sanda zai bayyana a gareta.
Sukan haxu da zuhairu a duk sanda ta ziyarci wannan
lambu da take zuwa tare da kuyanginta su yi hira irinta
ma’abota bege da qaunar juna har zuwa faxuwar rana, sannan
zuhairu ya yi mata rakiya har qofar shiga birninsu daga nan ya
juya ya kama hanyar komawa gida. Duk wannan abin da yake
faruwa Buniyatu ta an kasance tare da zuhairu a duk inda yake
saboda alqawarin da ta xauka na bada kariya gareshi don kada
yayanta matsafi Bahalu ya halakashi kamar yadda ya sha
alwashi, sai dai ta kan yi nesa da zuhairu yadda ya sha alwashi
sai dai ta kan yi nesa da zuhairu yadda ba zai ji motsinta ba,
don ta san idan ta kusanceshi zai gane cewa tana tare da shi
saboda zoben da yake yatsansa.
A duk sanda zuhairu suke cikin lambu suna hira tare da
Gimbiya Hasima, Buniyatu ta kan ji kishi da baqin ciki kamar
ta je ta halaka Gimbiya Hasima, sai dai ba ta da ikon aikata
haka saboda sanin cewa idan ta halakata babu shakka sai
yayanta ya halaka zuhairu, don haka ta kan yi nisa da bakin
lambun dan kada ta ji ko ta ga wani abinda suke yi na soyayya
da begen juna.

39

BAKAR GUGUWA
Wata rana daga cikin irin waxannan ranaku na
rayuwarsu, Gimbiya Hasima tare da zuhairu suna zaune cikin
lambu suna hira, kuyanginta sun basu waje suna zantawa irin ta
ma’abota begen juna, Gimbiya Hasima ta cava ado da kayan
ado mafi daraja da ‘ya ‘yan sarakuna suke sanyawa suna zaune
akan wasu kujeru na alfarma dake tsakanin wasu filawoyi da
furanni masu qayatarwa da kyan tsari, qamshin turare wuta ya
gauraye wajen mafi daxin qamshi daga turaren almiski.
Buniyatu da ta kasance mai bibiyar zuhairu a duk inda
yake, ta yi nisa da bakin lambun ya zuwa cikin wasu duwatsu
dake bayan lambun dan kada ta riski hirar da suke yi ta masoyi
saboda kishi. Gimbiya Hasima ta dubi zoben nan dake xan
yatsan zuhairu sannan tace da shi “Na daxe ina muradin
mallakar zoben nan na azurfa dake hannunka, tun daga lokacin
da na fara ganinsa tare da kai, sai dai ban yi sani ba ko cewa ba
irin zoben da za ka bada kyautarsa gareni bane, kasancewar ko
yana tare da wani sirri na daga rayuwarka a tare da shi”.
Zuhairu ya murza zoben sannan yace da ita “Haqiqa
wannan zobene mai daraja a gareni, kuma yana tare da wani
sirri da ya shafi rayuwata don haka ba zan iya bada kyautarsa
gareki ba, kamar yadda wanda ya mallaka shi gareni ya
umarceni cewa kada na sake na rabu da shi a duk inda nake
cikin kowane irin hali” Gimbiya Hasima tace da shi “Za ka iya
bani shi na gani don na qarewa irin qirarsa kallo, idan na koma
birnin Bahazum na sanya qwararun maqera su qera min irinsa”.
“Zan iya baki ki gani” In ji zuhairu ya cire zoben daga
xan yatsansa ya miqe mata, Gimbiya Hasima ta karva ta
qarewa zoben kallo na irin kyawun qirar da aka yi masa,
sannan sai ta sanya a xan yatsanta dan ta gwada zoben ya yi

40

BAKAR GUGUWA
mata kyau matuqa kamar saboda ita aka qerashi, shi kansa
zuhairu sai da ya yi bege ga kyawun zoben a jikin xan yatsanta,
ya ji ba don wasiyar da aka yi masa ba cewa kada ya sake ya
rabu da zoben da kuwa ya bar mata zoben ta sanya a hannunta.
Suna cikin wannan hali ne kafin Gimbiya Hasima ta
cire zoben daga hannunta ta baiwa zuhairu sai suka ji wata irin
qara mai tsanani qarfi da rugigi mai ban firgici kamar faxowar
aradu ta cika wajen, qasar ta riqa girgiza tana raurawa kamar
za ta tsage su rufta cikinta, wani baqin gajimare ya taho daga
gabas ya lulluve sararin samaniya tamkar hadari, gaba xaya
wajen ya yi duhu mafi tsanani daga yankin duhun dare, rugugin
da suke ji ya ci gaba da hauhawa yana qara kusanto inda suke
har sai da suka daina jin komai sai shi, tamkar qoqon
kawunansu zai fashe saboda tsananinsa.
Kuyangin Gimbiya Hasima suka razana suka ruga inda
su zuhairu suke cikin firgici ita kanta Gimbiya Hasoma sai da
ta tsorata ta shiga halin ruxani da kixima, saboda ta san cewa
matsafi Bahalu ne zai bayyana, cikin wannan hali mafi munin
yanayi daga alamomin bayyanarsa. Shi kuwa zuhairu duk da
ganin abinda yake faruwa bai razana ba, sai ya miqe tsaye yana
duba wannan yanayi cikin tsananin jarumta da qarfin zuciya
kuma ya san wannan ba komai bane face aikin sihiri da tsafi
irin na ma’abota shirka da tavewa, wa iyazy billahi ya ce a
ransa, yana mai hasashen cewa matsafi Bahalu ne zai sake
bayyana garesu.
Bayan wani lokaci sai suka hangi baqar guguwar nan ta
danno daga vangaren yamma, tare da iska mai tsananin qarfin
feshin wuta yana tartsatsi da zubowa daga cikin baqar guguwar
kamar dai yadda matsafi Bahalu yake yi idan zai bayyana.

41

BAKAR GUGUWA
Guguwar ta ci gaba da tahowa har sai da ta iso gaban zuhairu
sannan ta tsaya aka sake yin tsawa da rugugin aradu mai
tsananin qarfi da ya zarce wanda suka ji da farko, wani farin
haske ya keto daga cikin baqar guguwar daga cikin hasken sai
ga matsafi Bahalu ya bayyana sanye da kaya irin na
mashahuran matsafa ma’abota aikin sihiri, hannunsa na hagu
yana riqe da wani kurtun sihirin bayan wanda zuhairu ya fasa a
wancan haxuwar da suka yi sanda suke fafatawa a tsakaninsu.
Matsafi Bahalu ya dubi zuhairu cikin tsananin fushi da
fusatuwa yace da shi “Kaicon ranar dana-sani marar amfani
gareka, da za ka hallaka sababin bijirewa umarni da gargaxin
da na yi gareka, akan ka rabu da Gimbiya Hasima amma ka qi
ji. Yau ne ranar da zan tabbatar da isa da qarfin ikona a kanka.
Yau ne ranar da za ka tabbatar da tasirin tsafu da sihiri da kake
inkarinsa ya zarce tasirin duk wani abin dogaronka. Yau ne
ranar da za ka halaka da salwantar ruhinka daga doron qasa ta
hanyar kisa mafi muni da uquba mai tsanani kafin fitar ranka.
Kuma yau ne ranar da na jima ina sauraron zuwanta da
alamomi za su bayyana gareni na mallaki Gimbiya Hasima ta
zama matata, idan na hallakaka zan xauketa na tai da ita
DAHRUL SABAR dake lardin ASHTAR mu zauna tare da ita
har abada, fada ce da mahaifina yasa aka gina masa a wannan
lardi da babu wani mahaluki da ya isa zuwa inda take ya shiga
cikinta idan ba mamallakinta ba, kuma shima kafin ya kai ga
tarewa a cikinta ya rasu, don haka ni ne zan tare a cikinta tare
da Gimbiya Hasima”.
Zuhairu ya amsa da cewar “Kada ka zama mai alfahari
da bayyana abinda ba za ka iya aikatawa ba, cewa kai ka
kasance mai yawan alwashi da yawan rantse-rantse ga abinda

42

BAKAR GUGUWA
ka ke hasashen samu nasara a kansa, kuma tun wancan lokacin
har ya zuwa yanzu ababen bautarka tun wancan lokacin har ya
zuwa yanzu ababen bautarka da ka ke yin rantsuwa da su sun
kasa baka nasara bisa ga tasirin tsafi da sihirinka”.
Bahalu ya fusata da jin maganarsa ya yi qaraji da gunji
dake tattare da aikin sihiri gabaki xaya wajen ya yi amsa kuwa
da amo mai hauhawa, ya zaro wasu kibiyoyi irin na aikin sihiri
ya jefa zuhairu da su, kafin kibiyoyin sukai kansa sai wani
farin haske ya ratso ya shiga tsakaninsu daga cikin farin hasken
sai ga Buniyatu ta bayyana a gaban zuhairu ta sanya wata
garkuwa ta kaxe kibiyoyin suka zube qasa, wajen da kibiyoyin
suka faxi ya kama da wuta qasar wajen ta qone ta yi baqi.
Bahalu ya fusata da ganin abinda ya faru ya dakawa
Buniyatu tsawa yace da ita “Me ya sa ki ka kare abinda na
aikata cikin alqaluman sihirina da nufin halaka wannan jarumi,
ki sani cewa ba zan fasa abinda na yi niyyar aikatawa ba, na
halaka wannan mutum ko ta wanne irin hali” Buniyatu ta ce da
shi “Na yi rantsuwa da duk abinda nake yin rantsuwa da shi ba
zan bari ka halaka masoyina ba, idan kuwa wani abu na
cutarwa ya sameshi daga gareka to kuwa sai na halaka
Gimbiya Hasima wadda ka ke son hallakashi saboda ita”.
Matsafi Bahalu yace da ita “Idan kin zama mai bada
kariya a gareshi to kuwa ba za ki iya kuvutar da shi daga
abinda na yi niyyar aikatawa a kansa ba, na yi rantsuwa da
tasirin tsafi da sihiri na tare da yanka ga ababen bauta ta na
kuma nemi sa’a daga garesu ina mai fatan samun nasara a
kansa”. Ya sake turawa zuhairu wani aikin sihirin wuta ta yi
kansa za ta kama jikinsa ya qone, Buniyatu ta yi nata surkulen
ta tare wutar, nan take wutar ta mutu kafin ta kai kan zuhairu.

43

BAKAR GUGUWA
Ya sake jifansa da wani irin mashi na aikin sihiri ja
jawur dashi kamar qarfen da aka curoshi daga wutar maqera,
Buniyatu ta tura wasa iska mai tsananin qarfi ta ture mashin ya
tafi ya faxa cikin wata qorama dake gudanawa a tsakiyar
lambun, ruwan cikin qoramar ya kama tafasa saboda masifa
nan take launin ruwan ya sauya ya koma ja jawur kamar jini.
Matsafi Bahalu ya sake fusata da fushi mai tsanani ya yi
qaraji da kururuwa mai matuqar qarfi ya daki qasa da sandar
tsafin dake hannunsa, iska da baqat guguwa suka turnuqe suka
rufe wajen har sai da su zuhairu suka daina ganin junansu ya
biyo ta cikin duhun baqar guguwar da nufin halaka zuhairu,
Buniyatu ta tura wani farin haske cikin qabar guguwar sai ga
matsafi Bahalu ya bayyana tana ganinshi, ya xaga sandarsa ta
tsafi dake hannunsa zai makawa zuhairu Buniyatu ta sanya
hannunta ta kaxe sandar bai same shi ba.
Bahalu ya sake fusata ya kai mata sura cikin sa’a ya
fizge kurtun sihirin da yake hannunta, wanda a tare da shi ne
duk wani abu da ta gada na daga alqaluman sihiri yake ciki,
Buniyatu ta yi qaraji da kururuwa mai tsananin qarfi, saboda
suvucewar kurtun sihirin daga hannunta zuwa hannun matsafi
Bahalu.

44

BAKAR GUGUWA

BAKAR GUGUWA 2
afin matsafi Bahalu
ya bar wajen Buniyatu ta
tasar masa da nufin karve
kurtun
sihirinta
daga
hannunsa, ta kai masa sura
za ta fizge kurtun sihirin
shi kuma ya sanya sandar
tsafi dake hannunsa ya maketa. Buniyatu ta yi qaraji ta tafi ta
bugu da jikin wata itaciya dake tsakiyar lambun nan take ta
zube qasa sumammiya, jini na zuba ta hanci da bakinta.

K

Zuhairu ya fusata da ganin wannan al’amari ya zare
takobinsa cikin kabbara ya tasarma matsafi Bahalu da nufin kai
xauki gareshi ya ketashi gida biyu ya halaka,shima Bahalu ya
juyo gareshi a fusace, ya tasar wa zuhairu cikin qaraji da gunji
mai tsananin qarfi dake tattare da aikin sihiri gaba xaya
dukkanin wajen ya yi amsa kuwwa da amo mai hauhawa da ya
gauraye ko ina, suka haxu a tsakanin fusatuwar su suka kaiwa
juna sara da bugu da makaman da yake hannunsu,kaifin
takobin zuhairu ya haxu da sandar sihiri dake hannun matsafi
Bahalu wani farin hayaqi ya tashi sama tare da tartsatsin wuta
tamkar haxuwar qarfe da qarfe.zuhairu ya sake kai masa sara a
fusace kafin matsafI Bahalu ya kare kaifin takobin ya sauka a
jikinsa amma abin ka da shu’umin matsafi sai Bahalu ya zama
hayaqi saran ya wuce ta jikinsa ba tare da ya ji masa rauni ko
wata illa ba, ya sake bayyana a gabansa da saran ya wuce.

45

BAKAR GUGUWA
Zuhairu ya sake maida kaifin takobin a tsakiyar kansa
Bahalu ya kare saran da sandar sihirin dake hannunsa suka
kaiwa juna sara irin ta neman makasar abokin karawa kaifin
takobin zuhairu ya wuce ta gefen wuyan masafi Bahalu da
karfi kaxan ya rage ya sare kansa daga gangar jikinsa, suka yi
tirjiya irin ta arangama sannan suka sake zaburowa suka yi
wata bahaguwar haxuwa irin ta zaratan sadaukai dake sanya
halaka da matuqar tsoratarwa ga qananan jarumai masu raunin
zuciya.makaman dake hannunsu suka haxu da qarfi har sai da
dukkaninsu suka yi baya taga-taga kamar za su faxi sannan
suka tirje suka tsaya.
Suka sake zaburowa suka kai xauki ga juna, zuhairu ya
suri matsafi Bahalu ya cirashi sama da dukkanin qarfinsa ya
makashi da qasa, ya bi shi da sara cikin azama da zafin
nama,kafin kaifin takobin ya sauka a kansa Bahalu ya vace,
takobin ta sari qasa, ya sake bayyana a gefen zuhairu ya sake
yin kansa da sara cikin fusatuwa ya riqa kai masa sara cikin
jarumta da qwarewa irin ta sadaukantaka, shi kuma matsafi
Bahalu ya riqa karewa da sandar sihiri dake hannunsa ko kuma
ya goce, wani lokacin ya kan tsage kashi
End Ads