x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - BAKAR GUGUWA

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 36828 words

Category: Adventure Stories

Views 114

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
kulleta, sannan za ka ga qofar ta sake

101

BAKAR GUGUWA
buxewa da kanta, ba sai ka sake buxewa ba sai ka bi ta cikinta
ka wuce ka tafi ya zuwa qofa ta gaba”
“Qofa ta qarshe ita ce JAHABU idan ka isa inda ta ke
za ka tadda tana ci da wuta, babu damar ka isa gareta ka sanya
mukullin ka buxe, ka duba daga gefen qofar vangaran dama za
ka ga wani mulmulallan farin dutse ka sanya takobinka ka sari
dutse za ka ga wutar da ta ke ci a jikin qofar ta mutu, daga nan
sai ka isa gareta ka sanya mukullin ka buxeta ka shiga cikin
fadar.
“Idan ka samu nasarar tsallake waxannan siraxi ka
shiga cikin fadar, shi kenan ka gama da duk wani aikin sihiri da
siddabaru da ke bada kariya ga wanda yake zaune a fadar,
kuma babu wani aikin na alqaluman sihiri da zai sake tasiri
akan ka, sai ka yi qoqarin yaqar shi wannan shu’umin matsafi
maci amana a gare ni ka halaka shi, idan ka samu nasara a
kansa sai ka xebo ruwan da ke cikin rijiyar tsakiyar fadar ka
sha, dan karya aikin sihirin da ke tare da kai, sannan ka xauko
wanda za ka kawo a gareni ka taho da shi ka dawo. Sai dai
kafin na baka wannan mukulli zan kafa maka wasu sharuxxa
da nake so ka kiyaye, ka kuma amince da su”
“Da farko idan ka samu nasara hallaka wannan matsafi
da ke fadar kada ka sake ka ce za ka tava komai a cikin fadar,
kada kuma ka sake ka ce za ka fitar da wata daga cikin kuyangi
mata da za ka tarar a cikin fadar. Idan ka yi nufin aikata xaya
daga cikin abinda na haneka babu shakka fadar za ta nutse da
kai ka halaka, kuma kada ka sake ka ce za ka bawa wani
mukullin wannan fada, ka dawo da shi gareni kamar yadda na
baka da kaina”.

102

BAKAR GUGUWA
Zuhairu yace ya amince da wannan sharaxi da ya kafa
masa, sannan Boka Afrahu yace da shi tafi ga waccan
kwatarniya da ke ajiye, za ka tadda ita a cike da ruwa duk
abinda ka ga ruwan yanayi kada ka tsorata ka sa hannu ka
laluba za ka ji mukullan waxannan qofofi a cikin ruwan sai ka
xauko ka tafi ya zuwa wannan fada ka aikata abinda na umarce
ka da sannu za ka kasance ma’abocin samun nasara matuqar ka
kiyaye da abinda na sanar da kai”
Zuhairu ya yi masa godiya bayan da ya gama yi masa
wannan bayani, sannan ya tashi ya nufi inda wannan
kwatarniya take girke a qarshan kogon dutsen ya tadda ruwan
da yake cikinta yana tafarfasa, tirir na tashi sama. Ya kai hannu
zai laluba cikin ruwan ya xauko makullin, akwai wani qaramin
zobe na baqin qarfe a qaramin yatsansa ya suvuce ya faxa
cikin ruwan da ke cikin kwatarniyar nan take zoben ya narke
saboda musiba. Zuhairu bai razana ba duk da ganin abinda ya
faru ya sanya hannunsa a cikin ruwan dan ya xauko mukullin
maimakon ya ji tsananin zafi a cikin ruwan ga mamakinsa sai
ya ji ruwan ya yi matuqar sanyi, tamkar ba shi ne yake tafasa
da tiriri ba, ya laluba a hankali ya ji ya tava mukullin a qasan
ruwan ya sa hannu ya xauko sannan ya juyo ya sake yin godiya
ga Boka Afrahu ya kama hanyar fita daga kogon dutsen don
komawa ga su Buniyatu da ke waje.
Kafin zuhairu ya kai ga fita daga kogon dutsen sai ya ji
wata irin tsawa mai tsananin qarfi da amo mai hauhuawa ta
gauraye cikin kogon dutsen. Ruguginta tamkar zai tsaga dutsen
ya fashe,ya juyo dan ya ga abinda yake faruwa sai ya hangi
wata irin iska mai qarfi da ke cuxanye da baqar guguwa ta keto
cikin kogon dutsen ta lulluve inda boka Afrahu yake zaune

103

BAKAR GUGUWA
akan karagarsa wajen ya yi duhu mafi tsanani daga yankin
duhun dare. Nan take zuhairu ya fahimci cewa matsafi Bahalu
ne ya bayyana a cikin kogon dutsen dan ya hana Boka Afrahu
ya sanar da su sirrin shiga fadarsa da suka tunkari zuwa gareta.
Sai dai kuma ya zama makarare dan tuni ya sanar da su abinda
suke son sani daga gare shi.
Baqar guguwar tana gama sauka a cikin kogon dutsen
sai ga matsafi Bahalu ya bayyana ta cikinta ya xaga sandar
tsafi da ke hannunsa cikin tsananin fushi da fusatuwa ya
makawa boka Afrahu a tsakiyar kansa, Boka Afrahu ya yi wata
kaxaitacciyar qara irin ta azabar fitar rai, kansa ya fashe,
qwaqwalwarsa ta fantsama a jikin bango, kogon dutsen nan
take ya zube qasa matacce bai ko shura ba, gawarsa ta kama da
wuta ta qone qurmusu.
Bayan matsafi Bahalu ya halaka wannan boka ya juyo
ga zuhairu a fusace yace da shi.
“Na yi sani da zuwanku wannan waje da abinda ya
kawo ka, kuma kamar yadda na sanar da kai a farko marra
cewa ba za ka tava samun nasara a kaina ba, komai bibiyar
bokaye da masana alqaluman sihiri dan ka samu nasarar zuwa
fadata, kuma kamar yadda na hallaka wannan boka da ku ka zo
gare shi dan neman sani, haka kai ma zaka hallaka a cikin
wannan kogon dutsen ba za ka fita daga cikinsa ba”.
Yana gama faxar wannan magana ya xaga sandar tsafin
da ke hannunsa ya daki bangon kogon dutsen da ita. Nan take
kogon dutsen ya soma girgiza da raurauwa yana tsatstsagewa
tamkar zai fashe ya hallaka duk abinda yake cikinsa. Qasa ta
soma zabtarowa tana zubowa daga saman kogon dutsen ta
ko’ina alamar kogon dutsen ne zai fashe, Matsafi Bahalu ya yi

104

BAKAR GUGUWA
sauri ya vace cikin alqaluman sihirinsa, baqar guguwar nan da
ke cuxanye da qaqqarfar iska suka keta bangon kogon kogon
dutsen suka fice matsafi Bahalu ya tafi ya bar zuhairu a cikinsa.
Kogon dutsen ya ci gaba da girgiza yana tsatstsagewa
da zabtarowa yana zubowa qasa. Zuhairu ya juya cikin hanzari
da azama ya kama hanyar fita daga cikinsa. Yana gudu kogon
dutsen na ci gaba da zabtarowa daidai sanda ya kawo qofar fita
daga cikinsa sai kogon dutsen ya yi wata irin qara mai tsananin
qarfi ya fashe, qarar fashewarsa tamkar faxuwar aradu iska ta
yi sama da zuhairu ta jefar da shi can a gefen wajen da kogon
dutsen ya fashe tare da wata wuta da ba a san mafarinta ba tare
da qura fashewar suka turnuqe suka tashi sama.
Buniyatu da sauran jaruman da suke tsaye abakin kogon
dutsen suna jiran fitowar zuhairu sun ga zuwan baqar guguwar
nan ta keta kogon dutsen ta shiga cikinsa a sanda matsafi
Bahalu ya bayyana. Sannan kuma sun sake ganin fitowar baqar
guguwar daga cikin kogon dutsen ta tashi sama. Daga nan sai
suka ji wannan tsawa mai tsananin qarfi da ruggugi na
fashewar dutsen har sai da suka razana suka ja baya, saboda jin
wannan qarar, sannan sai suka ga dutsen da zuhairu ya shiga
cikinsa ya dagargaje ya fashe.
Hankalin Buniyatu da na sauran jaruman ya yi matuqar
tashi, suka razana matuqa da ganin fashewar dutsen da zuhairu
yake ciki, Buniyatu ta tashi cikin kixima da ruxani ta nufi
wajen da dutsen yake, amma hucin wutar da ya gauraye wajen
ya bugi jikinta tsananin zafi ya sa ta kasa qarasawa inda wutar
take. Dole ta juyo ta dawo da baya, ta fashe da kuka dan razana
da tunanin zuhairu ya hallaka. Suma sauran jaruman da suke

105

BAKAR GUGUWA
tare da ita jikinsu ya yi sanyi, saboda ganin abinda ya faru babu
wanda bai yi zaton zuhairu ya hallaka ba daga cikinsu.
Suna tsaye cikin wannan hali na fargaba da jimami sai
suka hangi zuhairu ya keto ta cikin duhun hayaqin da ya
lulluve wajen. Sai dai ga alama ya yi matuqar jigata saboda
ganin yadda yake tafiya a galabaice. Nan take fargabarsu ta
koma farin ciki suka yiwa Allah godiya da ya sa zuhairu bai
hallaka ba, wasu daga cikin jaruman suka tafi gare shi suka
taro shi, suka qaraso da shi inda suke tsaye suna jiransa. Suka
kai shi gindin wata inuwa mai sanyi, suka zaunar da shi dan ya
samu nutsuwa ya huta.
Bayan zuhairu ya huta, ya shaida musu ya samu nasarar
abinda ya shigar da shi kogon dutsen ya basu labarin abinda ya
faru tsakaninsu da boka Afrahu har ya mallaka masa mukullin
da zai buxe waxannan qofofi da kuma bayyanar matsafi
Bahalu ya hallaka Boka Afrahu, da abinda ya faru tsakaninsa
ya yi nufin hallaka shi, su Buniyatu da sauran jaruman da suke
tare da shi suka yi farin cikin samun nasara tare da yin godiya
ga Allah da ya kuvutar da zuhairu daga mugun nufin matsafi
Bahalu bai hallaka ba.
Da yake yamma ta qarato rana ta kusa faxuwa sai suka
samu waje suka yada zango dan su kwana anan kafin gari ya
waye su ci gaba da tafiya.
**
Da gari ya waye su zuhairu suka yi sallar asubahi, suka
yi addu’ar sannan suka tashi suka kama hanya, suka ci gaba da
tafiya kafin rana ta xaga sama sosai suka isa lardin Ashtar da
shigarsu cikin lardin suka ji yanayin wajen ya sauya gaba xaya
dajin ya yi duhu wani farin hayaqi ya gauraye ko ina, iska mai

106

BAKAR GUGUWA
tsananin zafi dake busar da maqoshi tana busawa daga ko ina
suna qara shiga cikin lardin zafin da suke ji na daxa qaruwa.
Haka suka wanzu suna tafiya har rana ta kusa faxuwa
suka yada zango a lokacin zuhairu ya basu shawarar yadda za
su bi wajen yaqar waxannan sadaukan. Jaruman suka amince
da shawarar da zuhairu ya kawo akan yadda za su yaqi baradan
da ke bayan tsauni. Sannan masu harbi da kibiya da masu
majaujawa suka je suke voya a cikin duhun itatuwa kamar
yadda zuhairu ya umarce su. Su kuma su zuhairu,Buniyatu da
sauran jarumai masu faxa da mashi da takubba suka tafi suka
tunkari inda rundunar baradan suke.
Da zagayawarsu bayan wannan tsauni sai suka hangi
dandazon baradan nan sun jeru sahu-sahu, sun yi sujjada gaban
wani gunki da ke kusa da tsaunin. Wasu kuma daga cikinsu
suna tsaye dan lura da duk abinda zai tunkaro wannan waje
daga kowanne vangare da ganin su zuhairu sun tunkaro inda
suke sai xaya daga cikin baradan nan ya daka musu tsawa da
maxaukakiyar murya yace da su.
“Kai waxannan al’umma fanxararru, hallaka ta tabbata
a gareku bisa ga shigowar ku lardin Ashtar da zuwan ku
wannan waje da sanin ku ko kuma bisa ga rashin sani na
kuskure. Haqiqa makoma ta munana gareku cikin qasqanci da
zama ababan shayar da jinin ku ga abin bautarmu dan
girmamawa”
Zuhairu ya maida masa da raddi da cewa “Kaicon mai
ambato da abinda yake ambatawa cikin zantukansa marasa
tasiri, ka sani cewa ba ka da ikon tabbatar da hallaka akan mu
har sai wanda ya halicce mu ya tabbatar da hakan a garemu.
Kuma mun yi imani da shi tare da neman taimakonsa don mu

107

BAKAR GUGUWA
karya rundunar mushirikai ma’abota bautawa gumaka wanin
Allah ba Allah da ya halice su ba. Don haka ina mai yin ishara
a gare ku da cewa; hallaka ce ta gabata gare ku da kawo
qarshen shirka da baxala da kuke aikatawa a bayan qasa”.
Mai maganar nan na farko ya fusata da jin abinda
zuhairu ya ambata ya sake yin magana cikin tsawa yace da shi
“Kai dattijo gajiyaye ma’abocin rauni da gazawa ka bari
matasa masu sauran jini a jikinsu su yi magana ba kai dattijo ba
wanda ba shi da tasiri aikata komai na jarumta. Kuma na rantse
da girman daraja gunki da nake bauta a gare shi sai na hallaka
ka don na tabbatar da girmansa da kuke qasqantarwa” Ya fidda
wata irin baqar takobi daga xamararsa ya tasama zuhairu a
fusace da nufin hallaka shi.
Shi ma zuhairu ya fidda tasa takobin ya tare shi suka yi
haxuwa irin ta karon battar qarfe, tare da kaiwa juna sara, irin
na hallaka abokin karawa. Kaifin takobbinsu ya haxu a sararin
samaniya da qarfi barden nan ya ji tamkar sun haxa qaifin
takobi da matashin jarumi sadauki, savanin dattajo mai raunin
da tarin shekaru da yake kallon zuhairu, suka rabu babu wanda
ya samu wani. Suka sake zaburowa sukai sara ga juna zuairu
ya goce kaifin takobin barden ya wuce, kafin ya juyo ya sanya
tasa takobin cikin gwanintar sara da zafin nama ya sare kan
barden ya yi tsalle sama gangar jikin ta faxi qasa daga nan tasa
ta qare bai ko shura ba.
Da ganin haka sai ragowar baradan da ke tare da shi
suka yi qaraji da kururuwa mai qarfi suna ambatan wasu
kalamai da su zuhairu ba sa jin abinda suke cewa. Nan take
sauran baradan da ke cikin halin yin sujjada gaban gunki suka
xago cikin sauri, sannan suka riqa zare makamansu suna

108

BAKAR GUGUWA
tasowa kan su zuhairu da sauran jarumai da suke tare da shi,
suka ja daga cikin shirin artabu da waxannan baradan duk da
cewa idan suka farmusu wani ma ba zai ga koda gawarwakin
su zuhairu ba, saboda tsananin yawansu.
Kafin su isa gare su sauran jarumai da suke tare da su
zuhairu suka soma sakar musu ruwan kibau da jifa da
majaujawa, daga cikin duhun itatuwan da suke voye. Baradan
nan suka riqa zuba qasa matattu tamkar yayyafi. Duk wanda ya
zaburo kan su zuhairu sai ka ga ya faxi qasa matacce ba tare da
san abinda ya hallaka shi ba. Sai dai masu harbi da kibiyar da
jifa da majaujawa suka ci qarfin rundunar baradan, sannan su
zuhairu da sauran jaruman da suke tare da shi suka farma
rundunar baradan da sara. A ka yi arangama da qazamar
haxuwa. Nan take waje ya yamutse, qura ta turnuqe ta tokare
sararin samaniya. Qarar haxuwar takubba ta cika wajen,
kururuwar mazaje ta yawaita. Zuhairu na kai sara cikin baradan
yana halaka su yana qara dannawa cikinsu. Duk inda ya sa
gaba a tsakanin baradan sai dai ka ga wajen ya zame masa
hanyar wucewa. Haka kuma komai yawan baradan da suka
taso kansa sai ya qarar da su gaba xaya, da kaifin takobinsa.
Haka ya yi ta keta dandazon baradan nan har sai da ya isa inda
wannan gunki da suke bauta a gare shi yake, ya xaga takobinsa
ya yi kabbara ya sari kan gunki da dukkanin qarfinsa, ya raba
shi da gangar jikinsa.
Da sare kan gunki sai suka ji wata irin qara mai
tsananin qarfi ta gauraye wajen, gangar jikin gunki ta kama da
wuta. Tsaunin da ke kusa da su ya soma girgiza yana
tsatstsagewa. Da ganin haka sai baradan da ke bauta ga wannan
gunki suka firgita, hankalinsu ya tashi suka gigita, tsaunin da

109

BAKAR GUGUWA
suke samun abinci da abin sha daga gare shi ya tarwatse ya
fashe. Nan take suka soma watsar da makaman da yake
hannunsu suna fantsama cikin daji a firgice. Su zuhairu da
sauran masu harbi da kibiya da jifa da majaujawa suka ci gaba
da hallaka su suna yi musu kisan qare dangi, har sai da suka
ragargaza rundunar baradan suka tarwatsa su, da yawa daga
cikin baradan sun hallaka. Wasu kuma suka fantsama cikin daji
suka arce a firgice dan su tsira daga hallaka da guguwar ajali
da ta turnuqe a tsakanin sannaninsu.
Bayan su zuhairu sun gama da baradan da suka rage ba
su samu damar arcewa aga wajen ba. Suka qarar da su baki
xaya, sauran jaruman da suka voye a cikin duhun itatuwa suka
taho suka haxu da su zuhairu. Suka dubi baradan da suka
hallaka da irin yawansu suka yi godiya ga Allah da ya ba su
nasara akan wannan rundunar mushirikai, suka ga bayansu don
su yi imani da cewa ba qarfi da dabarunsu ce ta sa suka samu
nasara akan su ba, illa taimako daga Allah.
Bayan sun nutsu qurar yaqi ta lafa, sai suka hangi wani
kogi a kusa da inda suke tsaye, Ruwa yana gudana a cikin
kogin garai-garai fari tas da shi. Da yake su zuhairu da sauran
jaruman da suke tare da shi, suna tare da qishir ruwa ga kuma
gajiya ta artabu da gumurzu da suka yi da waxannan barada.
Don haka suka tunkari wannan kogin da nufin zuwa gare shi su
sha ruwa.suna isa inda kogin yake suka fara xiban ruwan za su
sha. Buniyatu da ke tare da su da ta ga abinda suke shirin
aikatawa ta yi musu magana cikin tsawatarwa ta ce da su.
“Kada wanda ya sake ya sha wannan ruwa daga cikin
ku, saboda musifa dake tare da shi” Jaruman nan suka dakata

110

BAKAR GUGUWA
gabarin shan ruwan suna masu saurarenta da jin abinda ta
ambata gare su, Buniyatu ta ci gaba da cewa.
“Babu shakka duk wanda ya sha wannan ruwa daga
cikin ku to kuwa zai hallaka saboda akwai guba irin ta aikin
sihiri a cikinsa. Su kan su baradan da ke zaune a bakin wannan
tsaunin ma’abota tsaro ga fadar matsafi Bahalu ba sa shan
wannan ruwan kogi sukan sha ruwa ne da yake zubowa daga
saman wannan tsauni da yake kusa da su, sai dai idan wani
daga cikin su ya yi laifi akan yi masa azaba da wannan ruwa a
ba shi ya sha don ya hallaka.
Da suka ji wannan bayani na Buniyatu sai suka haqura
da shan ruwa. Suka tashi suka bar bakin kogin, suka xauki
makamansu da sauran kayayyakin su,suka ci gaba da tafiya
duk da tsananin qishirwa da take tare da su, suna masu neman
inda za su samu ruwan da za su sha. Kafin su isa sansanin
baradan ma’abota tsaron da ke gaba.
**
Al’amarin matsafi Bahalu kuwa bayan da ya bar zuhairu
a cikin kogon dutsen Boka Afrahu a sanda kogon dutsen yake
shirin fashewa ya tarwatse. Ya koma fadarsa cikin yaqinin
cewa zuhairu ya halaka a cikin kogon dutsen. Don ya yi imani
cewa babu yadda za’a yi ya kuvuta ya fita daga cikin kogon
dutsen ba tare da ya hallaka ba. Kuma bai sake komawa takan
jaruman da ke tafe tare da zuhairu ba, don ya san ba su da
tasirin aikata komai akansa, kuma ya san za su hallaka ne a
cikin wannan daji saboda ba su da damar shigowa lardin
Ashtar ko kuma su koma inda suka fito, don haka ya maida
hankalinsa ga sauraren haxewar taurarin nan na aikin sihiri da

111

BAKAR GUGUWA
za su tabbatar da mallakar Gimbiya Hasima a gare shi, ya samu
damar kusantar ta.
Bayan kwanaki uku yana zaune a fadarsa, sai ya ga
fadar ta yi duhu, duhun da ke bayyanar da isowar saqo a gare
shi cikin alqaluman sihirinsa. Ya ji an yi ambato a gare shi da
wata firgitacciyar murya mai nuna gajiyawa. Muryar mai
maganar tana raurawa aka ce da shi.
“DARUL UKUB ta karye, sansanin ma’abota tsaro na
farko ga wannan fada mai daraja, wasu jama’a da ba a san
maqasudin abinda ya kawo su ba, ko kuma aka haqiqance
qarfin tasirin abin bautarsu, sun farmaki sansanin cikin wata
sa’a daga cikin sa’o’in da mazauna sansanin suke gudanar da
ibadarsu. An samu tsaiko da tagaiyara baradan ma’abota tsaro
da ke zaune a wannan sansani. Wanda hakan ya jawo
mummunan yanayi na salwantar rayukan baradan cikin
qasqanci. Da yawa daga cikin su sun hallaka, gunkin da suke
bauta a gare shi ya kama da wuta ya qone qurmus. Tsaunin da
suke samun abinci daga gare shi ya tarwatse ya fashe, hakan
tasa sauran baradan suka razana suka fantsama cikin daji akan
samu nasara akan su aka karya sansanin su Darul Uqub ta faxi”.
Da jin wannan saqon sai ran matsafi Bahalu ya vaci,
zuciyarsa ta harzuqa ya fusata da fushi mara musaltuwa ya
tashi cikin sauri ya tafi ga kaskon bincikensa na alqaluman
sihiri don neman sani ga wanda suka aikata wannan al’amari
akan sansanin baradansa.
Bayan ya zana qasa ya share da yin sauran siddabarunsa
cikin alqaluman sihiri. Bayanai suka bayyana gare shi cewa,
zuhairu da ya
End Ads