x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - BAKAR GUGUWA

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 36828 words

Category: Adventure Stories

Views 109

01 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
bari a cikin kogon dutsen boka Afrahu bai
hallaka ba. Kuma shi da sauran jaruman da suke tafe tare da shi

112

BAKAR GUGUWA
ne suka shigo lardin Ashtar suka farmaki sansanin ma’abota
tsaro na farko, suka samu nasara akan su suka karya Darul
Uqub. Kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa sansani na
biyu don kai hari akansa. Ya yi matuqar mamaki da ganin
yadda suka samu nasara akan wannan sansani duk da tsananin
yawan baradan da ke cikinsa. Wanda ya dogara a gare su don
bada kariya da kiyayewa daga masu kawo hari akan fadarsa.
Hankalin matsafi Bahalu ya tashi zuciyarsa ta tunzura,
ya tashi cikin sauri dan tafiya ga sauran sansanin ma’abota
tsaro guda biyu da suke rage, don ya sanar da su abinda ya faru
ga sansani na farko, ya kuma qara karsashi a gare su akan su
qara tsaurara tsaro da kiyayewa, su kuma hallaka duk jama’ar
da suka ga sun tunkaro fadarsa ba tare da neman sanin ko su
wanene ba.
Da isarsa sansanin ma’abota tsaro na farko Darul maut
ya yi shela da maxaukakiyar murya mai matuqa qarfi da
hauhawa. Ta bakin gunki da suke bauta a gare shi cikin
alqaluman sihirinsa. Baradan da suke cikin wannan sansani
suka yi saurare ga abinda muryar take ambatawa. Bayan sun
gama jin wannan shela gaba ki xaya suka faxi gaban wannna
gunki suka yi sujjada a gare shi don girmamawa. Sannan suka
tashi cikin sauri suka himmatu ga aikata abinda aka umarce su
da aikatawa, suka qara tsaurara tsaro da kariya ga wannnan
sansani na su. Shugaba daga cikinsu ya qara musu karsashi na
qarfin zuciya, don tunkarar duk abinda ya kusanci wannan
sansani na su suga qarshensa su hallaka shi.
Daga nan matsafi Bahalu ya wuce ya zuwa sansani na
biyu, wato Darul musiba. Ya yi shela makamanciyat wadda ya
yi a sansani na farko. Cikin murya mai hauhuawa ta bakin

113

BAKAR GUGUWA
gunki da suke bautawa su ma waxannan baradan suka shiga
shiri kamar yadda sansani barada na farko suka yi. Matsafi
Bahalu bai baro waxannan sansanin barada guda biyu da suke
bada kariya akan fadarsa da kuma yin shirin tunkarar duk
wanda ya ce zai farmaki sansanonin baradan su ga bayansa,
sannan ya koma fadarsa ya zauna cikin yin imani da cewa
abinda ya aikata zai zama kariya gare shi akan duk wanda ya
ke son zuwa fadarsa dan yin yaqi da shi.
**
Su kuwa su zuhairu da sauran jaruman da suka rage tafe
tare da su, bayan da suka bar wajen da suka yaqi sansanin na
farko suka ci gaba da tafiya a cikin wannan daji suna masu
neman inda za su samu ruwan da za su sha. Suka yi tafiya ta
tsayin yini guda ba su samu inda ruwa yake ba, qishirwa ta
tsananta gare su ga zafi da xumamar yanayi na daxa qaruwa
don haka suka yi matuqar jigata da yawansu suka galabaita. Ba
su samu inda ruwa yake ba sai da rana ta kusa faxuwa, sannan
suka riski bakin wata qorama a tsakanin wasu kwazazzabai,
ruwa yana gudanawa a cikinta, suka yi matuqar farin ciki da
ganin wannan ruwa suka isa ga qoramar su ka sha, suka yi
hani’an sanna suka yi alwala su ka yi sallah magariba. Suka
xebi wanda za su yi guzuri da shi idan sun ci gaba da tafiya.
Da yake dare ya yi ga kuma gajiya sai suka yada zango
a bakin wannan qorama dan su kwana kafin gari ya waye su ci
gaba da tafiya zuwa sansani na gaba.
Da gari ya waye suka tashi suka yi sallah tare da addu’a
ta neman samun nasara, sannan suka kama hanya suka ci gaba
da tafiya ba su isa inda sansani na biyu yake ba sai da kusan
faxuwar rana. Tun daga nesa suka hangi qaton tsaunin nan na

114

BAKAR GUGUWA
biyu inda sansanin baradan yake a bayansa, a jikin tsaunin an
yi rubutu kamar haka.

“Wannan shi ne DARUL MUSUBA, sansanin ma’abota
tsaro da bada kariya ga fadar DARUL SABAR na biyu hallaka
ta tabbata ga wanda ya kusanci wannan sansani bisa ga rashin
sani ko kuma don nuna tijara da jin kai”.
Da suka isa inda wannan tsauni yake sai suka dakata
suka sauka a bayanhsa bayan sun huta sun samu nutsuwa sai
zuhairu ya tashi ya tafi don ya leqa bayan wannan tsauni a
voye, ya ga yadda jama’ar da ke cikin sansanin suke saboda su
san ta inda ya dace su farmake su don samun nasara akan su
cikin salon yaqi.
Da zuhairu ya zagaya inda zai iya hangen sansanin
baradan, sai ya voya cikin duhun itatuwa yadda ba za su iya
ganinsa ba. Ya hangi baradan cikin shirin yaqi ba kamar yadda
suka tadda sansani na farko cikin shagaltuwa da bautar gunki
ba, an zagaye wajen da tsaro yadda babu wanda zai iya keta
wajen ya shiga ba tare da sun gan shi ba. Wasu daga cikin
baradan suna kaiwa da komowa a kewayen sansanin xauke da
miyagun makamai. Suna duba da binciken duk abinda ba su
yarda da shi ba, don bada kariya da tsaurara tsaro da kiyayewa.
Zuhairu ya qare musu kallo tare da wassafa yadda za su
kai hari akan wannan sansani, don samun nasara akan baradan.
Daga nan ya tashi ya koma bayan tsaunin inda sauran abokan
tafiyarsa suke. Yana isa gare su ya kwashe labarin duk abinda
ya gani ya sanar da su, sannan ya qara da cewa.
“Haqiqa suna da labarin karyewar runduna ta farko da
hallaar sansanin baradan da ke cikin ta. Don haka suka kasance
cikin tsaurara tsaro da kiyayyewa kada abinda ya faru da

115

BAKAR GUGUWA
sansani na farko ya faru da su. Saboda haka ba za mu tunkare
su kai tsaye ba, don yin yaqi da su saboda suna xauke da
manya makamai a tare da su, za mu yi amfani da hikimar yaqi
ta voye. Za mu farmake su cikin wannan dare kafin gari ya
waye mu qarar da su cikin yarda Allah.
Yadda zamu samu nasara aikata hakan kuwa shi ne, za
mu tafi cikin duhun itatuwan da ke kusa da sansanin gaba
xayan mu mu vuya, kwararrun masu harbi da kibiya da jifa da
majaujawa za su yi ta kai hari akan baradan suna hallaka su
kamar yadda muka yi a sansani na farko. Ni kuma zan bi duhun
dare na shiga cikin sansanin na je na sare kan wannan gunki da
suke bauta a gare shi, idan na samu nasara aikata haka tsaunin
da suke zaune kusa da shi zai fashe ya tarwatse kamar yadda
tsauni na farko ya yi idan hakan ta faru baradan za su razana
zuciyarsu ta karaya da ganin abin bautarsu ya hallaka. Za su
tarwatse su fantsama cikin daji mu kuma sai mu yi amfani da
wannan damar mu ci gaba da saransy muna hallaka su har mu
ga qarshen su, mu karya sansanin na su kamar yadda muka
karya sansani na farko”.
Da zuhairu ya gama yi musu wannan bayani sai suka
tashi suka yi shiri. Bayan sun yi sallah magariba da isha’i suka
tafi can cikin duhun itatuwa da ke kusa da sansanin suka voye.
Can daga nesa suka hangi baradan nan sun kunna wasu
manyan fitilu na itace masu matuqar haske. Haskensu ya
haskake da’irar wajen baki xaya tamkar rana zuhairu ya umarci
masu jifa da majaujawa su fara jifa kan manya fitilun su kashe
su. Jaruman nan suka aikata abinda ya umarce su nan take
dukkanin fitilun suka mutu duhu mai tsanani ya gauraye wajen.

116

BAKAR GUGUWA
Baradan da ke tsaron wajen suka ta so cikin sauri don
sake kunna fitilun zuhairu ya sake bada umarnin akai farmaki
akan su. Masu harbi da kibiya suka soma sakar musu ruwan
kibau. Wanda kibiyar ta fara samu ya yi qaraji da kururuwa
mai tsananin qarfi saboda shigar kibiyar cikin kwayar idanunsa
na hagu. Ya faxi qasa yana wannan qaraji saboda azaba. Kafin
ransa ya fita, sauran baradan suka tafi gare shi don kai masa
xauki su ga abinda ya faru gareshi, kafin su kai kan shi wasu
zafafan kibiyoyn suka keto duhun dare suka fantsama a
tsakaninsu suka hallaka su.
Wasu baradan suka sake tasowa masu jifa da majaujawa
suka farmake su suka hallaka su. Da ganin haka sai sansanin
baradan gaba xaya suka tunkaro wannan waje don yaqar
abinda yake hallaka ‘yan uwansu, suka taso cikin qaraji da
kururuwa irin ta fusatuwa. Jarumai da suke tare da su zuhairu
suka ci gaba da sakar musu ruwan kibau da jifa da majaujawa
suna hallaka su. Nan take waejen ya hargitse qura ta turnuqe ta
qara wanzar da duhu cikin duhun dare zuhairu ya fito daga
inda yake lave ya shiga cikin sansanin baradan ya hau su da
sara, waje ya sake rincavewa,yanayi ya tsananta ga wannan
barada suka shiga halin kixima da ruxani saboda rashin sanin
taqamaimai abinda yake hallaka su cikin daren. Su da kansu
suka riqa kai sara ga kawunansu suna hallaka junansu cikin
duhun dare saboda firgici da ruxewa kafin wani lokaci baradan
nan sun yi raga-raga da junansu suka karya rundunarsu da
kansu.
Zuhairu ya ci gaba da keta tsakiyarsu yana kai sara a
tsakaninsu dama da hagu, cikin tsananin jarumta da qarfin
zuciya, yana hallaka su da haka har ya isa inda wannan gunki

117

BAKAR GUGUWA
da suke bautawa yake. Yana zuwa wajen ya xaga takobinsa
tare da kabbara cikin maxaukakiyar murya mai qarfi ya sari
wuyan gunkin da dukkanin qarfinsa kaifin takobinsa ya sare
kan gunkin ya faxi qasa.
Da sare kan wannan gunki sai suka ji wata irin qara mai
tsananin qarfi da ban firgici ta gauraye wajen tsaunin da ke
bayan gunkin shi ma ya yi qara ya fashe ya tarwatse, qasa ta ci
gaba da girgiza da raurawa mai qarfi kamar za ta tsage jama’ar
dake wajen su nutse a cikinta su hallaka, gangar jikin gunkin ta
kama da wuta, hasken wutar da haske ko’ina baradan suka ga
abinda yake faruwa a tsakaninsu.
Da ganin gunkin da suke bautawa ya kama da wuta,
sannan sansanin da suke samun abinci daga gare shi ya fashe
ya tarwatse, sai baradan nan suka sake firgita da razana da
abinda yake faruwa, zuciyarsu ta karaya suka ga tamkar ranar
hallakace da azaba mai tsanani za ta wanzu a gare su cikin
wannan dare. Nan take suka zubar da makaman da ke
hannunsu cikin tsaro, suka fantsama cikin dajin a firgice don su
tsira daga hallaka.
Su zuhairu da sauran jarumai da ke tare da shi suka tare
su suka ci gaba da hallaka su kafin su kai ga arcewa. Suka
hallaka da yawa daga cikin su sai ‘yan qalilan daga cikin su ne
suka samu nasarar arcewa suka shiga cikin daji ba su hallaka
ba.
Da su zuhairu suka ga sun karya rundunar baradan sai
suka yi matuqar farin ciki da samun nasara akan sansani na
biyu, tare da yin godiya ga Allah abisa wannan nasara da suka
samu. Daga nan suka koma inda suka fara sauka da farko don
su huce gajiya su kwana anan kafin gari ya waye su ci gaba da

118

BAKAR GUGUWA
tafiya ya zuwa sansani na uku, kuma na qarshe. Wanda daga
shi sai fadar Darul sabar inda matsafi Bahalu yake zaune.
**
Can kuma a Darul sabar fadar matsafi Bahalu a cikin
wannan dare mummunan labari ya isa gare shi na karyewar
sansani na biyu na ma’abota tsaro da bada kariya ga fadarsa.
Ya gari da idanunsa cikin alqaluman sihiri, yadda sansanin
baradan suka tarwatse suka bazama cikin daji a firgice. Dan su
tsira daga hallaka da musiba da ta afka musu cikin sulusin dare
wadda ba su san mafarin ta ba, da yawa daga cikin baradan sun
hallaka. Gunkin da suke bautawa a gare shi ya kama da wuta
ya qone qurmus. Tsaunin da baradan suke samun abinci da
abin sha daga gare shi wanda alqaluman sihirinsa suke tare da
shi don tabbatar da kafuwar sansanin shi ma ya fashe ya
tarwatse.
An samu matuqar damuwa da vacin rai mara musaltuwa
tattare da matsafi Bahalu game da abinda yake faruwa na
karyewar sansanonin baradan sa ma’abota tsaro ga fadarsa da
yadda sua zama marasa tasirin bada kariya a gare shi kamar
yadda ya ta’allaqa dogaronsa gare su, sai dai wannan bai sa
zuciyarsa ta sake karaya ba, ko kuma ya zama izina a gare shi
da cewa hallaka na qara kusantar shi cikin kowacce sa’a idan
har su zuhairu da sauran jaruman da suke tare da shi suka samu
nasarar shigowa fadarsa suka iso gare shi. Don ya yarda da
kansa da kuma alqaluman sihiri da ya mallaka, kuma bayanai
cikin bincikensa ba su tabbatar masa da cewa hallakarsa tana
tare da xaya daga cikin waxannan jama’a ba, sannan ya yi
imani da cewa shi mai samun nasara ne akan su, da ma duk

119

BAKAR GUGUWA
wanda yake yin jayayya da shi ko kuma zai tunkari fadarsa da
nufin yaqi da shi a faxin duniya.
Haka ya kasance cikin wannan yaqini da ke zuciyarsa
saboda tsananin shirka da vata irin na ma’abota aikin sihiri da
tsafi. Allah ka tsare mu da wannan al’amari, Ameen.
Can kuwa a birnin BAHAZUM sarki shaiban ya sanya
malamai suna ta addu’a don neman samun nasara ga su zuhairu
akan wannan shu’umin matsafi su kuvutar da ‘yarsa Gimbiya
Hasima daga hannunsa. A kullum aka yi saukar Alqur’ani mai
girma kamar sau duhu daga sallar Asuba zuwa faxuwar rana.
**
Bayan su zuhairu sun yada zango a kusa da inda suka
yaqi sansanin na biyu, suka kwana da gari ya waye suka yi
sallah Asubahi suka yi shiri suka ci gaba da tafiya. Suka sake
yin tafiya har ta kwanaki uku, sannan suka iso inda sansani na
qarshe yake wato Darul mautu wanda daga shi sai fadar
matsafi Bahalu.
Da suka isa inda wannan tsauni yake suka yada zango a
bayansa don su huce gajiya su kuma shirya sosai yadda za su
kai farmaki akan wannan sansani, da yake sun gama fahimtar
yadda za sy riqa samun nasara akan wannan barada sai suka
bari sai da tsakar dare, sannan suka tafi cikin duhun itatuwan
da ke kusa da tsaunin suka voye. Yadda baradan ba za su gansu
ba, suka soma kai farmaki akan su cikin duhun darebayan sun
kashe hasken manyan fitilun da suka haske wajen.
Su zuhairu sun samu nasara matuqa kamar yadda suka
so, sai dai an xan samu tsaiko da turjiya daga sansanin baradan
inda suka jajirce da nuna juriyarsu ta qoqarin da tabbatar da
tsaro da kiyayewa akan fadar matsafi Bahalu, suka kuma

120

BAKAR GUGUWA
fahimci daga inda ake kai hari akan su duk da tsananin duhun
dare, don haka suka tasarma wajen da su zuhairu suke voye
cikin duhun itatuwa da nufin hallaka su abinda ya haifar da
artabu da arangama mai matuqar muni, har mutum biyar daga
cikin jaruman da suke tare da su zuhairu suka hallaka ita kuma
Buniyatu da wasu jaruman su shida suka samu munanan
raunuka.
An yi xauki-ba-daxi, artabu da baqin gumurzu mai
tsanani a tsakaninsu kafin zuhairu ya samu nasarar kaiwa inda
wannan gunki da suke bauta a gare shi yake ya sare kansa da
takobinsa. Wanda sare kan gunkin ne ya kawo qarshen turnuqu
da baqin gumurzun da ake kwafsawa a tsakaninsu. Gangar
jikin gunki ta kama da wuta, tsaunin da ke wajen ya yi qara da
rugugi mai tsananin qarfi ya fashe. Tartsatsin wuta ya yi tsiri
ya tashi sama ya riqa watsuwa a jikin baradan da ke wajen
suna kamawa da wuta, suna qonewa, suna hallaka. Baradan
suka yi matuqar firgita da razana mara misaltuwa saboda ganin
abinda yake faruwa, suka yi nufin su arce don tsira daga
hallaka sai dai babu wanda ya samu damar kuvuta daga cikinsu
har sai da feshin wutar nan ya riske su,ya qarar da su baki xaya
suka qone qurmus. Ba a kawo qarshen wannan arangama ba
har sai da kusan asubahi bayan ketowar alfirjir.
Su zuhairu suka yi godiya ga Allah bisa ga nasarar da
suka samu na karya wannan rundunar baradan. Suke nemi
ruwa suka gabatar da sallah Asubahi, sannan suka xauki
gawarwakin ‘yan uwansu da suka hallaka suka yi musu sallah
suka binne su. Wanda suka samu raunuka aka yi musu magani,
suka matsa kusa da wani rafi suka yada zango a wajen, daga
inda suke suna hangen Darul sabar inda matsafi Bahalu yake

121

BAKAR GUGUWA
an zagaye ta da manya katangu masu matuqar tsawo da kauri.
Akwai qofa ta baqin qarfe da ke farko a kulle daga vangaren
da suke.
Da gari ya gama wayewa sosai rana ta fito sai zuhairu
ya dubi Buniyatu da sauran jaruman da suke tare da su yace da
su.
“Tunda Allah ya nufe mu da samun nasarar isowa inda
wannan fada take, sai ku tsaya anan gaba xayanku ku jirani a
wannan waje,ni kuma zan je na shiga fadar don yaqar matsafi
Bahalu na kuvutar da Gimbiya Hasima daga hannunsa, ku ci
gaba da yi mini addu’a don fatan samun nasara, tare da jinyar
wanda suka samu rauni har zuwa sanda zan dawo, idan na
samu nasara akan wannan shu’umin matsafi cikin yarda Allah”.
Buniyatu da sauran jaruman da suke tare da zuhairu
suka amince da wannan shawarar tasa. Da su zauna a bakin
wannan rafi su jira shi har ya dawo, suka yi masa addu’a ta
fatan samun nasara, sannan zuhairu ya tashi ya kama hanyar
tafiya ya tunkari inda wannan fada take.
Da isarsa inda qofar fadar take ta farko ya dubeta da
kyau. Ya ga an yi ta ne da xanyan baqin qarfe, yadda babu
wani abin hallita daga jinsi mutum ko aljani da zai iya karya
qofar ya shiga cikin fadar komai qarfinsa na jarumta da
sadaukantaka. Ya sa hannu ya fiddo da mukullin da Boka
Afrahu ya basa daga xamararsa ya saka a jikin qofar ya murxa
a hankali. Qofar ta xan yi qara a hankali, sannan ta soma ja da
baya tana buxewa da kanta. Zuhairu ya zare makulllin daga
jikin qofar ya maida xamararsa sanda qofar ta gama buxewa da
kanta, sannan ya zare takobinsa ya ja daga bai yi gaggawar
shiga qofar ba, kamar yadda aka aka umarce shi. Ya yi saurare

122

BAKAR GUGUWA
don ganin abinda zai fito daga cikinta ya gama da shi kafin ya
kai ga shiga ciki.
Huci ya fara ji irin na tahowar iska da ke cuxanye da
mutsanancin zafi kamar tiriri ya bugo daga cikin qofar sannan
sai ga wani qaton baqin maciji mai matuqar girma da kauri ya
fito daga cikin qofar a fusace, ya fasa kai girmansa ya zarce na
macijiyar da suka hallaka a cikin ruwan kogin da suka wuce
kafin su shiga lardin Ashtar. Zuhairu ya yi sauri ya sanya
takobinsa cikin azama da zafin nama ya sare kan baqin macijin
tun kafin ya kai masa sara. Macijin ya yi wata tsiwa ta azabar
fitar rai ya zube qasa matacce. Wani irin baqin jini mai kauri
da yauqi ya zubo daga inda zuhairu ya sare kan macijin.
Sannan sai macijin ya riqa narkewa yana zagwanyewa har ya
zama jini gaba xaya.
Zuhairu ya sake tsayawa a wajen yana saurare.ko zai
sake ganin wani abin cutarwa ya fito daga cikinta, amma har
aka xau lokaci mai tsawo babu abinda ya sake fitowa daga
cikinta. Daga nan sai ya tafi gareta ya shiga ciki, babu abinda
ya gani a tsakanin wajen illa wata doguwar hanya ta miqe ya
zuwa qofa ta gaba. Ya bi wannan doguwar hanya da ta miqe ya
ci gaba da tafiya har ya isa inda qofa ta biyu take.
Yana isa wajen ya iske qofar a buxe kamar yadda aka
sanar da shi, tun kafin zuwansa. Yana iya hangen abinda yake
cikin qofar daga inda yake akwai wasu bishiyu na ‘ya ‘yan
itatuwa masu zaqi na marmari tare da furani masu matuqar
qayatarwa ga wasu fararan tsuntsaye suna shawagi a sararin
subahana tare da sauka daga wannan bishiya ya zuwa waccan
bishiya. Ya hangi wani xawisu yana tafe a qasa daga cikin
qofar ya taho zai fito waje ya zuwa
End Ads