KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
43
zaka san ko ni wacece idan har kana buqatar sanin ko
ni wacece xin, ni ce mahaifiyar BADURA."
8
e ce wa?" Na sake tambayarta cikin kaxuwa
da mamaki.
"Ni ce Hajiya Binta Babar Badura." Ta ce dani.
Har yanzu ina tsaye a qofar xakin ban shiga ba.
Abin da Badura ta yi min yasa duk wani wanda
yake sona da 'yan uwantaka da shi na tsane shi, don
haka kallo xaya na yi wa mahaifiyar Badura na ji na
tsane ta, ba kuma na son zama a xakin muddin tana
ciki, akwai wani abu a tattare da Hajiya Binta da ke
bani tsoro, irin kallon da take min da kuma irin yadda
take murmushi tana kuma vata rai a lokaci guda, shi
ya sani na fara tunanin ba kanta xaya ba. Savanin
'yarta Badura ita Hajiya Binta baqa ce mai jajayen
idanu can cikin loko kamar qwanqwalati, duk lokacin
da ta dube ni sai ta zazzaro min su, alama ce ta
mahaukata, don haka sai na toge daga qofa ina shirin
sheqawa da gudu a duk lokacin da buqatar hakan ta
taso. Idan akwai abin da zan yi har ta bar xakin to zan
yi shi, domin zamanta a gidannan haxari ne yana iya
kawo qarshena, shin wai me ya kawo ta ma gurina?
Kuma ta ya ya akayi tasan ina nan? Duk yadda kuma
aka yi akwai wani da yasan ina nan bayan ita.
"Me ya kawo ki nan?" Na tambaye ta.
"Ya kamata ka shigo ka zauna." Ta ce dani.
"Ki tashi ki fice daga gidannan." Na ce da ita,
"domin ban ga hujjar da zata sa ki shigo min gida ba
tare da na sani ba." Hajiya Binta ta qyalqyale da wata
irin dariya. Dariyar da ta sa tsigar jikina ta tashi,
gashin jikina ya mimmiqe gumi ya karyo min. Haqiqa
yanzu na tabbata mahaukaciya ce, cikin lokaci
qanqani kuma sai ta murtuke fuska sannan ta ce dani.
"Kai yanzu ba ka jin kunya ka ce nan gidanka ne,
gidan Amina kuma sai ya zama naka?" Ta sake
qyalqyalewa da dariya, "Ko ka tava ganin saurayi ya
ci gadon Budurwarsa? Fadil ya kamata kasan halin
“K
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
44
da muke ciki, domin ina son sanar da kai wasu
muhimman batutuwa da nake tafe dasu, ko kana so
kuwa ko baka so."
"Me ya sa ki tsammanin za ki iya sani na saurareki
dole?" Na tambaye ta.
"Saboda nasan muddin ina tare da kai dole ne ka
saurare ni, domin idan ka gudu ma baka da wurin
zuwa, ko kana da shi Fadil?" Ta tambaye ni, na yi
shiru, duk da yake nasan ba kanta xaya ba, dole ne na
yarda da abin da ta faxa yanzu, tabbas bani da wurin
zuwa.
"To ki faxa ina daga nan." Na ce da ita.
"Kana tsoro na ne?" Ta tambaye ni. "To idan
tsoro na ka ke ji sai ka zava tsakanina da 'yan sanda
wa zaka saurara? Fadil na gaji da vata lokaci." Ta ce
dani, idanuwanta masu kama da qwanqwalati suka
juya suka yi ja jawur. "Idan baka shigo ba." Ta ce
dani tana murmushi irin na waxanda kansu ya tavu,
"to zan yi ma irin abin da na yiwa Zainab...." Na riqe
numfashina cikin tsoro da kaxuwa.
"Kina nufin kice kika kashe Zainab?" Ta yi dariya
sannan ta ce.
"Ban da ma kashe Zainab da na yi, akwai wasu
abubuwan da duk zan sanar da kai yanzu, kuma dole
ne ka saurara." Na juya da niyyar na fita da gudu
domin na tabbata mahaukaciya ce.
"Gudunka ba zai kai ka ga komai ba sai halaka."
Ta ce dani. Gargaxin da ya fito daga bakinta, shi yasa
na sake juyowa na fuskance ta, sannan ne naga wani
abu kamar qarfe ya turo kansa ta cikin baqin lulluvin
da tayi.
"Idan ka gudu zan harbe ka Fadil, shigo ka zauna
in kuma ba haka ba kai ma ka bi Zainab lahira." Kan
bindigar ya bayyana a fili na kuma tabbata ina
motsawa zata harba, dole qanwar naqi ce ta sani na
nufi cikin xakin kamar kazar da qwai ya fashewa a
ciki, na nufi kan gado kusa da inda Jakar da Yayana
ya bani, take na zauna. Ko da na zauna sai na ce da
ita.
"Mene ne wannan ne ki ke ta faman nuna ni da
ita? Ai ya kamata ki daina nuna ni da ita tunda na
zauna."
Hajiya Binta ta yi dariya, sannan ta ce.
"KIBIYAR AJALI ce maganin yara masu taurin
kai irin ku, idan baka yi min shiru ba da tambayoyin
rainin wayon da ka saba, to ka ayyana a zuciyarka
tsakanin ka da mutuwa bai fi ni da kai xin nan ba."
"Ai daman duk mai rai matacce ne." Na ce da ita,
"don Allah kuma bari nayi miki tambaya, shin da
wannan bindigar ki ka kashe Zainab.....?" Kafin ta
bani amsa sai qofar xakin ta buxe, sannan ya shigo
xakin, hannunsa sanye cikin koren wandonsa, akwai
alamar datti a jikin farar rigarsa, Salman ne.
"Taurin kai zai nuna miki ne Hajiya? Yanzu na
xan tausasa shi." Ya ce da ita yana murmushi.
"Fice daga nan shashasha, wa ya ce ka shigo."
Kafin ta rufe bakinta tuni Salman ya vace daga xakin
kamar Aljani.
**
"Ina son sarqar ta zo hannuna gobe da misalin
qarfe biyu na dare." Ta ce dani.
"Wacce sarqa kenan ki ke nufi?" Na tambaya, duk
da cewa kuwa nasan sarqar da take nufi.
"Sarqar da na daxe ina burin mallaka." Ta ce da
ni, "na kuma jefa rayuwata cikin haxarin gaske domin
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
45
ganin na cimma burina, kada kaja min rai Fadil,
nasan kasan abin da nake nufi, ya kamata kasan
matsayinka a gurina yanzu, idan baka sani ba to bari
na faxa ma." Sannan ta ci gaba da cewa "Kai yanzu
kana matsayin karan farauta ta ne, ya kuma zama
dole kayi duk abin da na saka domin idan ka qi bin
umarnina, to ba zan saurara ba wajen ganin na
baqanta rayuwarka kamar yadda idan ba ka xauko
min sarqar nan ba zaka baqanta tawa rayuwar, ina
kuma yi maka tuni da cewa duk abin da ya faru a
kanka ba laifin kowa ba ne sai laifina, don haka ina
fatan ba za ka zargi 'yata Badura ba, akan duk abin
da ya faru, ita ma ta taimaka minne wajen haxama
tarkon ne don takura mata da nayi da kuma tsorona
da take ji, ina son ka sani Fadil!" Ta ci gaba da cewa
cikin xaga murya "In da ta Badura ne to da yanzu
baka cikin halin da kake ciki yanzu, haqiqa Badura ta
daxe da kamuwa da sonka. Idan baka manta ba,
lokacin da kake otel xinnan ta Kaduna, kun yi da
Badura cewa zata zo da yamma ta same ka, wannan
alqawari da tayi ma ta yi ma shi ne ran da ku ka fara
haxuwa da kai a lambun otel xin, wanda daga qarshe
baka samu damar ganin ta ba sai a daren wannan
yammacin, inda ta yi ma qaryar cewa wai wani na
barazana ga rayuwarta. Ina son kasan cewa rashin
ganin Badura da baka yi ba a wannan rana, ya samo
asali ne da rashin son da take yi ka faxa cikin bala'i.
Ina kuma faxa maka duk waxannan abubuwa ne
domin kasan cewa Badura bata da laifi, kuma
masoyiyarka ce, ba dole ba ne ka yarda, amma zaka
gane nan gaba.
Ina fatan duk ka gane abin da nake faxa?" Hajiya
Binta ta ce dani, "Daga qarshe kuma ina son na sanar
da kai cewa, ni ce umul aba'isin duk abin da ya faru a
gare ka, ni ce kuma na kashe Zainab, na sake
maimaitawa, ni na kashe Zainab don ganin na cimma
burina kuma kaima na jefa ka cikin bala'i, ba don
komai ba sai don na baqantawa Amina rayuwa, sanin
kanka ne Amina na mutuwar sonka, nasan kuwa jefa
ka cikin bala'i kamar jefa Amina ne domin nasan zata
iya yin duk wani abu don ganin ta kuvutar da kai.
Sannan Hajiya Binta ta kalle ni ta qyalqyale da
dariya. Hakan shi ya qara tabbatar min da cewa ta
gama zarewa. "Sai kayi hankali kuma." Ta ce dani, na
sami labarin akwai 'yan sandan ciki a qalla guda uku,
suna nemanka, an kuma turo su ne daga Durba Hotel
Kaduna, a iya sani na kuma ba a tava samun
gwanayen 'yan sandan ciki kamar su ba, na tabbata
kuma muddin suna nan ba jimawa za su kamaka,
muddin kuma kana qasar nan, don haka ma nake
baka shawarar ka sato min sarqar gobe, mu kuma
haxu a Daula Otel qarfe biyu na dare." Sannan ta ci
gaba da cewa, "Ban yi ma alqawari ba, amma idan ka
yi sa a zan iya baka isassun kuxin da za su fitar da kai
daga Najeriya ko kuwa me ka gani? Idan kuma kana
ganin zaka koma gidan yayanka to bismillah, kana
komawa zan bugawa 'yan sanda waya in sanar da su
cewa yayanka ne ya voye ka, kasan kuwa sai sun
wahalar dashi, ko kuwa kana son yayanka ya wahala
akan ka?" Ta tambaye ni tana zazzare idanu, har
yanzu ban saki jikina da ita ba, domin a shirye nake
na ruga da gudu, a duk lokacin da ta taso min sai dai
kuma abin da ya fi damuna shi ne bindigar dake
hannunta. Haqiqa ko ban faxa maba, kai ka san ba
abin da ya fi kome haxari irin ace mahaukaci ya tsara
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
46
ka da bindiga, da dutse ma yaya, ballantana kuma da
bindiga.
"Zan tafi Fadil!" Kakkausar muryar ta ce ta dawo
dani daga tunanin da na fara.
Tana tsaye a kaina tana muzurai, har yanzu
bindigar na hannunta, tana kuma saitin qirjina, cikin
murya mai xauke da tsananin gargaxi ta ce dani.
"Ina fatan gobe war haka kana can kana xauki-ba-
da-xi da Sojojin Kanal A. Mukhtar, kuma gobe war
haka ina Daula otel ina jiranka, ka kawo min sarqar."
Sannan ta zazzare min idanu ta ce dani, "Idan har
qarfe biyu da rabi ta yi ban ganka ba, to zan yiwa 'yan
sanda waya na faxa musu cewa nasan inda wanda ya
kashe Zainab yake, zan kuma sanar da su cewa nasan
yarinyar da ta tserar da kai daga Kaduna. Daidai
nake kuwa don ayi musu bayanin kamannin Amina,
nasan ba za ka so ba ace budurwarka ta wahala
saboda kai, ko zaka so Fadil?" Ta tambaye ni. Akwai
alamar gajiya da surutu a muryar ta.
"Abu na qarshe kuma Fadil!" Ta ce dani a daidia
lokacin da hannunta ke qoqarin kaiwa ga kunamar
bindigar, gumi ya fara tsattsafowa daga goshina,
domin nasan tana iya harbawa tunda ba cikakken
hankali ne da ita ba, kafin ta sake cewa wani abu tuni
har na yi kalmar shahada cikin carbi a zuciyata,
domin cikin 'yan daqiqunnan ni ina tsammanin tawa
ta qare. Na rufe idona ina jiran na ji harasashi ya sami
matsugunni a qirjina.
"Kada ka tsorata Fadil." Ta ce dani. "Duk da yake
nasan ka fara tunanin ko ba kaina xaya ba, amma
hakan ba zai sa na harbe ka ba, domin harbinka
yanzu na nufin ni da na mallaki sarqar (kishiyata
Hajiya Asma'u) har abada kenan, na tabbata babu
mai iya sato sarqar idan ba kai ba, ko banza dai kai
jarumi ne.
Haka kuma da kake tunanin ko ni mahaukaciya
ce, banga laifinka ba, domin kuwa lokuta da dama tun
bayan rasuwar mijinmu, na fara tunanin cewa kaina
ya tavu, ina son ka sani cewa, babu abin da ya
haukatar da qwaqwalwata, sai tsabar tunani da baqin
cikin son kan da mijinmu ya nuna wajen rabon gado,
kuma kishi da son ganin na mallaki sarqar nan shi ya
qara lalatar da al'amuran har kai ma na jefa ka cikin
bala'i.
Amma duk da haka." Ta ci gaba da cewa "Da ace
na bar wa Hajiya Asma'u sarqar nan, gara nayi
sanadiyyar hallakar mutane dubu. A cikinsu har da
kai."
"Allah ka yi mana tsari da tavin hankali" na ce
cikin zuciyata. Yanzu na qara tabbatarwa da cewa
wannan matar dake barazana ga rayuwata ta
haukace, saboda tsabar son zuciya, kishi da kuma
rashin tawakkali ga Ubangiji.
"Idan qarfe biyu da rabi ta yi ban ganka ba, zan
baiwa Salman izini da ya harbe ka domin ban ga
amfanin zamanmu a duniya ba, saboda in har ba ka yi
nasara ba to banga amfanin rayuwata ba, ban iya
rayuwa da baqin cikin kishiya kuma......" Ga
mamakina sai naga hannunta ya yi sanyi bindigar ta
fara rawa a hannunta kamar zata faxi, sannan sai
hawaye ya fara kwaranyowa ta kan manya-manyan
kumatunta masu kama da qwallon qafa. Xakin ya yi
shiru na xan lokaci ita a tsaye ni kuma a zaune ina
ajiyar zuciya, baka jin komai sai shasshekar kuka
daga Hajiya Binta. A can wani vangare na gidan ana
ta danna hon xin mota, ya yi wata qara fom! fom!! har
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
47
sau uku kafin a qara na huxu, Hajiya ta fice daga
xakin kanta a sunkuye, bayan na bari ta kai tsakiyar
furannin dake farfajiyar gidan sai na miqe, na biyo
bayanta da gudu-gudu, ina zuwa qofar gidan direban
Hajiya Binta ya yi ribas. Wane to direban, na tambayi
kaina, Salman ne ko kuwa....? Nan da nan zuciyata ta
qi na'am da tunanin da ta fara yi. Ba Salman ba ne,
saboda Salman qato ne, mai faxin kafaxa kamar qofar
garejin mota, wannan kuwa dake tuqin motar xan
tsatsama ne, duk kuma da yake duhun cikin motar bai
bani damar ganin fuskarsa ba nasan fuskar matsorata
ce da shi, to wanene kuwa? Kamar an so a bani amsar
tambayata, sai direban ya kunna fitilar dake cikin
motar, cikin zafin naman da ya bani mamaki sai
Hajiya Binta ta yi sauri ta sake kashe fitilar, duk
motsin da suka yi ya xauki abin da bai gaza daqiqa
huxu ba ne. Jikina ya xauki rawa, zuciyata ta fara
bugawa da sauri, direban motar ne ya sani rawar jiki,
ba kuma wani ba ne, sai xan tsohon nan mai fuska
kamar matsatsen lemon tsami, mai aiki a durba otel,
idan ba ka manta ba lokaci na qarshe da muka haxu
da shi, shi ne a Durba otel lokacin da na shaqe shi a
jikin bango ina gargaxinsa da cewa kar ya sake ya ce
wa 'yan sanda ya ganni. Yau kuma sai gashi tare da
Hajiya Binta, motar ta ci taya quu!! Sannan ta hau titi
da gudu.
**
Zuciyata cike da tunani da kuma matsanancin
mamakin ganin xan tsohon nan, a haka na nufo xaki,
jikina kamar an yi min duka, kwanaki biyu da suka
wuce nasha yiwa kaina tambayar cewa ya ya aka yi
har wani mahaluqi zai saci jiki ya shigo qasaitacciyar
otal kamar Durba, ya kuma kashe mutum ba tare da
jami'an tsaron otal xin sun gan shi ba, wannan yana
bani mamaki, to amma yanzu na daina mamaki domin
na samu amsar tambayata. Yanzu kam na tabbata
wannan xan matsattsen tsoho da shi Hajiya Binta ta
haxa baki, har ta sami damar halaka Zainab. Saboda
nasan kuxi yana iya sa mutum ya yi komai, koda a da
ne ballantana yanzu, to amma abin da ya ke bani
mamaki har yanzu shi ne, mene ne haxin Hajiya Binta
da xan tsohonnan da har zai zama direbanta? kuma
shin ya bar aikin otal xinne ko kuwa gaskiya fa naga
xan tsohonnan ya dage tsakaninsa da Allah yana bai
wa 'yan sanda bayanin kamannina a Jarida, ashe saye
shi aka yi, aka kuma shirya tuggun jefa ni bala'i tare
da shi to Allah ya toni asirinsa.
Na nufi gado na yi zaman 'yan bori akai a
lokacinne na ji wani abu ya xan yi qabarbar a cikin
aljihuna, gaban rigata nasa hannu na zaro takardar a
hankali na manta sam-sam da ita. Na buxe takardar
na fara karantawa kamar haka takardar da Badura ta
bani ce tun ina Kaduna.
TSARIN GIDAN KANAL MUKTAR
Fadil ina son kasan cewa wannan takarda na rubuta
ta ne don na sanar da kai wani abu da ke cikin duhu,
wanda kai baka sani ba, na farko dai ina son ka sani
cewa duk abin da ya faru a kanka ba laifina ba ne, ba
kuma laifin 'yar uwata Amira ba ne, ko kusa babu laifin
kowa a cikinmu. Babarmu Hajiya Binta ita ta takura
min don na yaudare ka ka faxa tarkon ta, ni
masoyiyarka ce Fadil, kuma ina taya ka baqin cikin
abin da yake faruwa a kanka, ina kuma fatan Allah ya
taimake ka ya kuma tsallakar da kai sharrin
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS)