x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - KIBIYAR AJALI

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 49194 words

Category: Love Stories

Views 522

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ba to sai dai ku mutu tare, kana harbinsa
ina harbin ka." Murya ta ce daga baya. Xan sandan
ya saki bindigarsa qasa yana rawar jiki, kamar
mazari, cikin razana sai ya saki wandonsa qasa ya
faxo, daga shi sai diras. Mutumin ya zagayo ya xauke
bindigar xan sandan, cikin mamaki da razana sai na
gane ko wanene, mutumin da ban tava zato zan gani a
halin yanzu ba, duk da yake akwai duhun dare hakan
bai hana ni ganin kayan jikinsa, koren wando da farar
riga, abin da ya daxa razana ni shi ne, yadda aka yi ya
biyo ni ba tare da na sani ba.
"Salman!". Na kira sunansa muryata na rawa.

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

38


KASHI
NA BIYU












7
uk da yake akwai duhun dare, hakan bai hana
ni ganin kayan jikinsa ba, koren wando da
farar riga. Abin da ya fi bani mamaki shi ne yadda
aka yi ya biyo ni ba tare da na sani ba.
"Salman!" Na kira sunansa muryata na rawa.
Haqiqa al'amura suna ta faruwa a gare ni kamar a
majigi, daga wannan sai wannan xaya-bayan-xaya
kamar jan carbi, ni kam yanzu na fara fitar da rai da
rayuwa, musamman ma da na yi la'akari da irin
bala'in da ke samuna bi-da-bi kamar 'ya'yan carbi.
Sai yanzu ne na yarda da cewa duk wanda ya qi bin
maganar na gaba da shi, to lallai yana tare da
nadama, domin da na bi maganar yayana, na yi
zamana a gida to da yanzu sai dai ni ma na karanta
irin waxannan abubuwa da ke faruwa a gare ni kamar
yadda ku ke karantawa a halin yanzu. Duk wannan
tunanin na yi shi ne lokacin da Salman ya xago kai ya
dube ni yana murmushinsa irin mai sa qananan yara
mafarki. Xan sandan da ke gefenmu ya yi sororo
kamar mutum-mutumi, ga dukkan alamu yana
tsammanin alburushin bindigar Salman zai iya ratsa
jikinsa a kowanne lokaci daga yanzu, domin irin
tsayuwar da xan sandan ya yi, ba dan yana numfashi
D

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

39
ba, da sai ka iya kiransa matacce, amma mutuwar
tsaye.
"Kayi mamakin ganina ko?" Salman ya ce dani.
Na xago kai na dube shi, da niyyar na yi magana
amma tsoro da mamaki suka hana harshena faxin
komai.
"Kada kayi tsammanin zamu barka ka yi ta aiki
ba tare da saninmu ba." Salman ya ci gaba da cewa,
"Dole ne mu sa ido a duk abubuwan da kake don
ganin ka cimma nasara wajen sato sarqar, saboda
haka ko kana niyyar yin wata kurxa-kurxa, ko kuma
wata yaudara don qin bin umarninmu, to ka tabbata
ba za ka kai labari ba, domin duk abin da ke faruwa
tun daga Kaduna, ina nan kusa da kai." Sannan
Salman ya yi dariya ya ce, "Wannan umarni ne daga
uwar gidata Badura, kuma zan ci gaba da binka a
baya-a-baya har sai ran da naga ka ci nasara wajen
sato sarqar, ka kuma kaiwa Badura sarqar, kamar
yadda muka tsara maka cewa Daula Otel ce wurin da
zamu haxu ka bada sarqar, idan ka yi haka to sannan
ne zan rabu da kai, amma yanzu kam da kai Allah ya
haxamu zan yi ta binka kamar yadda ajali ke bin rai,
zan kuma faxa ma wani abu Fadil." Salman ya ce da
ni. Ban ce da shi komai ba, don haka sai ya ci gaba da
cewa, "Masoyiyarka Amina ni na yi mata talfon a
gidan da ta sauka na Kaduna na kuma sanar da ita
inda kake domin ta zo ta qwace ka daga hannun 'yan
sanda, za kuma kayi mamakin ganin mun qyale ka ka
fita garin Kaduna kai kaxai a matsayin mai laifin
kisan kai, kuma ta cikin haxari iri daban-daban, to
mun yi haka ne domin mu gwada ka muga
jarumtarka, to haqiqa yanzu muna sa ran cewa idan
akwai mutumin da zai iya sato mana sarqar to kai
ne." Gumi sai kwarara yake daga goshina zuwa
bayana, tunda na faxa cikin bala'in nan sai yanzu ne
naga Allah ya buxo min hanyar da zata fitar dani.
Idan 'yan sanda sun kama ni, idan ba ka sani ba to
bari na faxa ma. Salman na ta sharara labari ba ya ko
tunanin cewa gaban shaida mai qwari yake bayaninsa,
xan sandan da ke gabana ya ishe ni shaida, fatana
xaya shi ne Allah sa Salman ya barshi da ransa,
wannan tunani shi yasa na fara tunanin cewa Salman
ya tavu, haqiqa mutum mai hankali ba zai tava faxar
laifin da ya aikata a gaban xan sanda ba.
Tunanina ya katse a daidai lokacin da na ga
Salman ya fara murmushin muguntarsa, qirjina ya
fara dakan uku-uku domin murmushin Salman yana
bayyana ne a duk lokacin da ya ke shirin aikata
tavargazarsa kafin na qarasa tunanina, Salman ya
xaga bindigarsa ya daki kan xan sandan, duka ne irin
wanda zai iya jefar da ingarman doki, xan sandan ya
kifa da fuska da wani irin kuka mai kama da na
qaramin yaro bai ko shura ba a tunanina ya mutu,
idan kuwa ya mutu da kuwa damata ta qarshe ta
suvuce kenan, Allah ya sa bai mutu ba." Na ce cikin
zuciyata. "Ya kamata ka kama gabanka." Salman ya
ce dani a fusace. "Amina na can tana jiranka."
"Kada ka sake kiran sunan Amina." Na ce da shi,
"bana son kusa ta cikin wannan rikicin, ni dai da na
riga na shiga to na shiga, amma ita ku barta waje
guda."
"Ta riga ta sa kanta." Salman ya ce dani "Idan ma
kuma da bata yi saurin sa kanta ba, to da dole ne nan
gaba ta shiga."
"Saboda me ka ce haka?" Na tambayi Salman "Ka
tambayi Badura." Salma ya ce dani, sannan ya yi

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

40
murmushi kafin na sake tambayarsa wani abu tuni
Salman ya sake vacewa a cikin duhun daren da ya fito
kamar fatalwa.


**
"Rabin raina ina ka tsaya ne haka, nake ta jiranka
har kasa na fara tunanin ko wani abu ne ya faru?"
"Kada ki damu." Na ce da Amina a daidai lokacin
da ta tuqa motar muka ci gaba da tafiya. "Dogon
zagaye nayi, don haka ki kaga na daxe." Ba ni da
tabbacin cewa Amina zata yarda da abin da nake faxa
mata, hakan ya samo asali ne daga irin kallon da naga
Amina na yi min, kallon da take yi min ba kallo ne irin
na so ba, sai dai zan iya kiransa da kallon an xauke ni
maqaryaci.
"Fadil!" Amina ta kira sunana, ba tare da na amsa
ba sai ta ci gaba da cewa, "Akwai wani abu da na
fahimci kana voye min, kuma sanin kan kane bai dace
ace kana matsayin masoyina ba amma kana voye min
matsalarka." Sannan ta dube ni, duba irin naso. "In
dai har da gaske ka ke kana sona, to ka sanar dani
gaskiyar labarin ka tun daga lokacin da ka bar Kano
har zuwanka Kaduna." Amina ta yi shiru na xan
lokaci tana sauraron abin da zai fito daga bakina.
Bai kama ta ba ace Amina ta san gaskiyar labarin,
domin yin hakan yana iya je fata a cikin haxarin da
nake ciki, idan kuma na sake na faxa mata cewa
sharrin da aka yi min yana da alaqa ne da 'yan
uwanta Badura da Amira, to tana iya yin abin da ni
zan kwana a ciki, domin idan ta ji gaskiyar al'amarin
tana iya zuwa ta faxawa Babarta Hajiya Asma'u, ita
kuma Hajiya Asma'u tana iya faxa wa mijinta Kanal
A. Mukhtar ya kai maganar kotu duk yadda aka juya
ni zan kwana ciki, saboda babu wanda zai yarda bani
na kashe Zainab ba. Hakan shi ya sa ni yanke
shawarar cewa zan sake shiryawa Amina qarya, ba
zan sake tasan gaskiyar labarin ba, domin da ta sani
gara na shiga gidan Kanal A. Mukhtar xin na sato
sarqar, idan da kwanana a gaba to dole ne na wuce
koda kuwa ana ruwan wuta ne. Tattausan murmushin
shirin yin qarya ya bayyana a fuskata, a daidai lokacin
da Amina ta xan juyo daga tuqin motar da take ta
fuskance ni, sannan na ce da ita.
"A matsayin ki na masoyiyata ina zaton ya kamata
ki yarda da abin da nake faxa miki koda kuwa qarya
ne, saboda shi so hana ganin laifi ne, ya masoyiyata,
ruwan raina, mai taimako na....."
"Dakata!" Amina ta ce dani "Ba sai ka kurarani
ba, faxi abin da kake son faxa zan yarda da shi koda
kuwa ba gaskiya ba ne." Sannan ta ci gaba da cewa,
"Nasan daman Fadil son da na ke yi ma ya fi wanda
ka ke yi min, amma ni na gode Allah a qalla dai yanzu
kana saurarona akan da, wanda ada ko hira baka so
kayi dani, sai gashi yanzu da bakinka kana cewa dani
masoyiyarka, haqiqa wannan kalma ta masoyiyata da
kake kirana da ita, ita ce kalma mafi daxi da
kunnuwana suka jiye min tunda na zo duniya, in har
kana ganin rufe sirrinka a gare ni shi ne mafi soyuwa
a gareka, to shi kenan nima shi ne mafi soyuwa a gare
ni, farin cikin ka shi ne abin sona rayuwarka ita ce
abar begena, sannan ta ci gaba da cewa "Ka sani
Fadil, duk abin da kake so to nima zuciyata dole ne ta
karkata zuwa qaunarsa koda kuwa a da ba ta yi
amanna da shi ba.

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

41
Idanuwan Amina suka cicciko da qwalla wanda
hakan ya sa da qyar take tuqa motar, "so sartse ne
Fadil." Amina ta ci gaba da cewa "Da kasan irin son
da nake ma da baka voye min abin da ke damunka ba,
idan da ka daure ka sanar dani gaskiyar labarinka, to
a shirye nake na miqa rayuwata wurin ceton ranka.
Domin rayuwata ba ta da amfani idan har ka kasance
cikin qunci, amma tunda kana ganin rufe min sirrin
naka shi ne ya fi alhe ri to shi kenan, bana buqatar ka
sanar dani, saboda sanar dani xin wani abu ne da zia
baqanta ma rai, ni kuma duk abin da zai baqanta ran
abin begena to ina gaba dashi." Daga nan Amina ta
qarawa motar wuta muka nufi birnin Kanon Dabo
bata ko jira qwaqwalwata ta gama nazarin abin da ta
gama faxa min ba, duk da haka sai da qwaqwalwata
ta sake gargaxina.
"Kada ka sake ka faxa mata, idan kuwa ka faxa
mata to kaine ruwa tsundum, kasan kuwa laifin wani ba
ya shafar wani."
Misalin qarfe goma sha xayan dare muka iso
Kano.

**
Qamshin furannin fulawowi ya bugi hancina, a
sakamakon buxe tagar xakin da na yi na leqo kaina
ina nazarin farfajiyar gidan wacce ke haske da wutar
lantarkin dake gidan, bayan hanci na ya gamsu da irin
qamshin furannin dake farfajiyar gidan, sai na juyo
da kaina na sake nazarin falon a tsanake, cike kuma
da mamakin irin son da Amina take yi min duk da
yake ran Amina ya vaci, a sakamakon 'yan
maganganun da suka shiga tsakaninmu a hanya,
amma hakan bai hanata yi min abin da ta yi niyya ba
lokacin da muka zo gidan talabijin na Kano (C.T.V)
sai Amina ta juyo ta kalle ni, murmushin qarfin hali a
fuskata, sannan ta ce dani.
"Zan kai ka gidanmu dake Tarauni ka zauna a
can, kafin 'yan sanda su sassauta neman ka, nasan da
wahala 'yan sanda su yi tunanin nemanka a gidan,
domin gidan sabo ne ba a ko tava zama cikinsa ba,
kaine na farkon zama a cikinsa. Kwanaki huxu da
gama gininsa mahaifina ya rasu na kuma yi gadonsa
daga wajen mahaifina. Sannan Amina ta xan yi shiru,
ta dube ni ta yi murmushi sannan ta ce "Idan kana
buqatar abinci zaka tarar da komai a cikin firji, zan
dawo gobe da rana domin mu sake tattaunawa."
Sannan ta juya ta nufi qofa ta barni ina buxe baki cike
da mamaki. Kafin hankalina ya dawo jikina tuni
Amina ta fice daga xakin. Abu na qarshe da kunnena
ya sanar dani shi ne qarar tayar da motar Amina,
wacce ta fice da gudu ta nufi qofar gidan alama ce
dake nuna cewa har yanzu bata huce ba.

* *
Qarar qararrawar agogon dake nane a jikin
bangon xakin ita ta tashe ni daga nannauyan baccin
da ya xauke ni qarfe tara daidai na safe agogon ya
nuna, na tashi zaune ina mutsuttsuke idona, hasken
rana ya fara bayyana a sarari, yau garin babu alamar
hadari, sai dai idan iska ta kaxa hanci na yakan shaqi
qamshin damina.
Saura kaxan na faxo daga kan gadon, saboda
tsoro. Wata ajiyar zuciya aka yi a bayana wacce ta
tsorata ni, a iya sanina, ni kaxai ne a xakin, tsoro ya
hani juyawa naga wanda ke ajiyar zuciyar a bayana.
Ina zaune kamar an zare min laka kuma kowanne

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

42
lokaci, ina tsammanin na ji bindiga ta zunguri
quguna. Can kuma sai na ji wata zazzaqar murya ta
qyalqyale da dariya, nan da nan na xago kaina sannan
na ganta, a zaune akan kujerar dake gaban gadon,
fuskarta cike da annuri, da walwala, tana sanye da
doguwar riga fara wacce aka yi mata ado da baqaqen
duwatsu masu kama da zinare, ta lulluve kanta da
baqin qyalle, farin ciki ya kama ni har na manta da
halin da nake ciki.
"Wallahi Amina kin ban tsoro." Na ce da ita.
Amina ta dube ni tana murmushi.
"Daman nasan zaka tsorata." Ta ce dani, "Tun
qarfe takwas da 'yan mintuna nazo, ganin kana barci
ne yasa na qyale ka sai ka tashi."
"Kuma shi ne kika tsorata ni."
"Ko dai ka tsorata kanka." Amina ta ce dani tana
kallona. Har yanzu murmushi bai bar fuskarta ba
sannan ne lura da kurtun zuba shayi akan wani teburi
dake gabana. A gefensa kuma wani kwano ne na
azurfa (Silver plate) wanda ban san ko mene ne a ciki
ba. Amina ta matsa kusa da teburin sannan ta buxe
kwanon, ganin abin dake cikin kwanon shi yasa ciki
na ya fara salati, sai yanzu ne na gane cewa ina jin
yunwa, kwanon yana xauke da toyayyiyar wainar
qwai, da biredi, da kuma hanta.
"Zan tafi makaranta sai na dawo ma sake
tattaunawa." Amina ta ce dani.
"Yaushe za ki dawo.?" Na tambaye ta, duk da
yake kuwa bana son rabuwa da ita, amma tafiyarta ita
zata bani damar tunanin yadda zan fuskanci gidan
Kanal Muktar, wajen sato sarqar zinaren da Badura
ta sani. Amina ta xago kai tana murmushi, sannan ta
ce dani "Ai ba daxewa zan yi ba, yanzu ma wani aiki
ne da aka bamu tun ka fin na tafi nemanka Kaduna
nake so na kai musu, ina kaiwa zan dawo. Kada ka
damu ka ji my darling." A haka muka rabu da Amina,
ba don na so ba. Sai bayan da ta tafi ne na gane cewa,
Amina ta karance takardar da Badura ta bani, domin
ni a aljihun wando na sa ta. Amma dubawar da zan yi
sai ga ta a wandon aljihun rigata, tun da bata nuna
min alamar komai ba na ce cikin zuciyata, to ya
kamata na yi shiru na manta da ita.
Amina bata dawo ba sai misalin qarfe takwas da
rabi na dare, hankalina ya yi mutuqar tashi, ba dan
neman da 'yan sanda ke yi min ba, to da na bita
makarantar. Ina ta faman safa da marwa a farfajiyar
tun qarfe huxun yammacin wannan ranar, har takwas
da rabi, ina shirin yanke shawarata ta qarshe kenan
sai na ji qarar mota ta nufo qofar gidan, Amina ce.
Bayan mun yi 'yan mintuna muna hira, ta kuma faxa
min abin da ya tsayar da ita, sai muka yi sallama,
saboda ta ce ita bata daxewa a waje kasan yadda
gidan su yake, muka yi sallama da ita, akan
yarjejeniyar cewa gobe zata zo ta taya ni zama domin
ba zata makaranta ba, bayan na rakata har gindin
motarta ta tafi, sai na juyo da niyyar na shiga xaki, a
nan ne to na fara ganinta.
Tun kafin na shiga xakin, na ji wani qamshin
qaqqarfan turare ya daki hancina, ina tsammanin zai
iya bugar da mutum, hakan ne ya tabbatar min akwai
mutum a xakin, na dai lallava na shiga, tana zaune
akan kujerar dake fuskantar gadona, qatuwar mata ce
kakkaura zata yi shekaru hamsin a duniya, ta lulluve
kanta da baqin hijabi, haqiqa ban san ko wacece ba.
"Fadil!" Ta ce dani, "kana mamakin ganin
baquwar mace a xakinka ko? To karka damu, yanzu

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
End Ads